Showing 201001 words to 204000 words out of 227321 words

Chapter 68 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1533

a fuskar wasu, sai na rabata da duk mai kaunarta

 So tell ke kika saka ma gidan iyayenta wuta saboda ki rabata da rayuwarta da duk masoyanta ko kuma saboda ta yi recording dinki?

Ta yi murmushin takaici ta girgiza kai.

 Indai ina raye Kareem sai kun rasa farinciki kai da ita, ka gama da jikina yanzu ka daina sha'awata ko? Ita wane tabbaci kakw da shi cewar tana da tarbiyar? Ita ka san da waye da yi tarayy...

Bata karasa ba ya zabura ya mike tsaye sai ita ma ta yi tsaye tana kallonsa har ya karaso kusa da ita ya nunata da yatsa.

 One bad word for Noor... Zan dauke rayuwarki gaba daya...!!

Babu annuri yake kallonta har wani kashe ido yake yana kankance su tsabar tsana da jin haushinta da yake, ita ma kallonsa take tana hawaye masu kumshe da nadama... Kamin ta kauce ta fice daga falon da gudunta. Dinning ya nufa ya ya dora hannayensa ya hura iska, sai da ya burzar da iskar bakinsa sau bakwai sannan ya samu sukunin maida numfashi, kansa ya daga sama ya sauke. Ya fada Safeena tsantsan gaskiyar abun da ke ransa ne a yau saboda ta san bata da matsayi a gurinsa kuma ta san baya kallonta ta kauna ko na kwayar zarra ya sani yanzu ko babu masu gadi ba zata sake sha'awar kusantar gurin da yake ba.

Ya raya daren yana tunanin abokinsa da shawarar da yake yawan ba shi a lokacin da yake raye, ya taba fada masa Safeena bata da zuciya mai kyau kuma a yanzu ya yarda domin ga zahirin ya gani, ta dayan bangaren kuma yana murnar hana shi auren Safeena da Momy ta yi a yanzu ya gane ba karamin gata ta yi masa ba. A lokacin da dare ya raba sai ya tashi yayi alwala yayi sallah ya rokawa mahaifiyarsa da abokinsa gafara kuma ya rokawa kansa da yayansa shirya, sannan ya rokawa Noor mafita.

Da ya koma kan gado kuma sai tunanin yadda zai karbi yaron dake hannun Safeena ya saka shi gaba, hakkin yaron a kansa da kuma yadda zai bullowa yaransa da yan'uwansa su fahimce shi. Misalin tara da mimtuna Yellow ya shigo gidan bayan Kareem ya bawa mai gadi umarnin barinsa ya shigo. Kareem be shiga da shi falonsa ko wani bangare na gidan ba suka tsaya a waje Yellow na labarta masa yadda suka yi ma Zafeer kacha kacha a daren jiya

 Hope dai baku taba matarsa ba?

 Ko hararar ta idan na yi Allah ya tsinen, kallonta ma dan ya zama dole ne, da ba zan kalleta ba

 Kuma baku dauki komai a gidan ba, baku bar wata shaida da za a gane ku ne ba?

 Ni fa sai dai ace dan iska ne amman bana tsaba alkawari kuma na san aikina balle kuma aikin ka babban yaya

Kareem yayi murmushi, ya tashi ya shiga ciki ya fito ya mikawa yellow 300k

 Ga sauran biyanku, ko da an kama ku karka kuskura sunana ya fito

Yellow ya kai kasa yana godiya sannan ya karba, yana rantsuwar ko da an kama su ba zai fadi sunan Kareem ba kuma ba zai labarta ma kowa ba. Kareem yayi tsaye yana kallonsa har ya fice sannan yayi murmushi gefen baki wannan ne karo na farko da ya saka aka zalinci wani kuma yake jin kamar yayi daidai har ma yake jin dadi a ransa.





*** *** ***


Da wani irin karfi ta fisgi motarta ta fice daga gidan, yadda take gudu da mota kai ka dauka bata son ranta, ko kuma she's ready to kill someone domin bata damu da rayuwarta a halin yanzu balle ta wasu.

 Ni Kareem zai fadawa haka yau ni k. Kareem zai juyawa Baya? Ni zai wulakanta saboda wata yar iska da bata shirya zaman aure ba kuma ba zata shirya shi har bada

Tana ta magana da kanta tana kuka har ta isa gidanta a harabar gidan ta faka tana ta kuka na rashin arziki kuka sosai kamar wadda ta rasa uwa ko uba. Gaba daya bata lura da motar Abdull dake gidan ba sai da kwantar da kujerar motarta da nufin zata kwanta sannan idonta ya sauka a motarsa dake kusa da entrance. Veil dinta ta saka ta share hawayen ta goge fuskarta tashin hankalin da take ciki fa kuma wanda take tsoron fuskanta a gurin Abdull a yanxu ya mantar da ita tissue dake cikin motar.

Bude motar ta yi ta fito kamar wadda ta yi shaye shaye tsabar mayen damuwa da ta yi mata yawa, ta kusan minti uku tana kallon motarsa sannan ta nufi kofar falon ta kai hannu tana hade yawu ta murda ta shiga. A falo ta zame shi zaune da alama yana jiranta ne. Cikin yanayi na rashin gaskiya ta karasa falon ta zauna tana kallonsa sai tauna cingan yake fuska kamar bakin maciji.

 Ina kika fito?

 Wata kawata ce Maryam Mamanta ta rasu shi ne na je gaisuwa

 Kuma da gyale? Taya ta kukan kika yi a can?

Ta yi shiru tana hade abu da karfi.

 Na baki dama da yawa Safeena, sai kuma kika yi wasa da ita har ta bude miki kofar tafiya ki yi lalata da wani

 Sheri Noor take min

Ya zaburar mata irin na mai shirin kai duka.

 Rufe min baki, idan sheri take miki jinin da aka auna ma karya yake ko? Ko kuma kin maida ni mahaukaci?

 Ni da kai duk jirgi daya ya kwaso mu, na san na yi kuskure yanzu ina neman yafiyarka, hakan ba zai sake faruwa ba, kai ma ka aikata laifi ai, na san na fika laifi but I'm sorry

 Sorry banza, ni ban wadace ki? Miye bana miki?

 Kana ba ni kudi da abinci amman baka ba ni kulawa da nake so, baka dubana yadda kake duban matan waje, baka bani cikankiyar kulawa irin ta asalin masu aure, amman duk da hakan na san ni mai laifi ce I'm sorry

 Kin san zafin dake cikin abun da kika aikata? Tun da kika samu cikin yaron nan da awa daya abinci na kike ci, da ruwan gidana kike wanka, karkashin kulawata kike har kika haife shi, na yi masa suna na yi masa hidima kamar ubansa, ba zan iya zsma dake ba Safeena

Ta yi saurin sauka daga kan kujerar tana girgiza masa kai ta rike kafufuwansa.

 Aa dan Allah Aa ka hukunta ni da ko wane kalar hukunci amman ban da Saki Abdull, mu rufawa junanmu asiri mu zauna dukanmu masu laifi ne na sani dan Allah ka yi hakuri

Kamar jira yake sai kuwa ya furta mata sakin da kakkauran halshe.

 Na sake ki ki bar min gidana in less then 48 hours, na tsane ki na tsani ne ki

Ya fisge kafarsa ya fice ya barta da kallonsa baki sake. Marin kanta ta yi har sau biyu kamin ta rushe da kuka, ta fara yamutsa duk wani abu dake falo, abun da ke fashewa na ta jefar da shi, ta fisgo curtains din dake falon ta zubar kasa kamar mahaukaciya. Kwance ta yi a gurin tana kuka sosai har yarinyar makota dake rika mata yaronta ta shigo kawo mata yaron da ya fara kuka. Cikin kuka ta tashi ta karbe shi ta rufe kofar sai ta rumgume shi tana kuka.

Wayarta ta nufa ta dauka ta kira mahaifiyarta, ta labarta mata sakin da Abdull yayi mata.

 Me kika masa? Ina Mahaifinsa be sani ba?

 Mun dade a cikin rashin jituwa Ammy, kuma sun sani ba su shiga tsakani ba, yanzu ya sake ni, rayuwata ta kare Ammy

 Rayuwarki bata kare ba Safeena saboda namiji? Karki sake fadin haka

Ta kashe wayar tana kuka gaba daya ta rasa wa zata sake kira again. Rayuwa ta juya mata a yadda bata zata and she's still blaming Noor domin ita ce silar komai. Ji ta yi bata bukatar zama a garin Kano gaba daya, hakan ya saka ta shiga daki ta hada kayanta a akwaiti ta fito falo ta dauki wasu abubuwan da ta san yaronta zai bukata, ta zauna a kujera tana dubawa ko zata samu flight from Kano to Dutse da yammancin nan ba.

Sai kuma ta yi rashin sa'a bata samu haka ba, saboda haka ta yanke shawarar driving kanta, domin ta san ko take tasha ba lallai ta samu motar garinsu a yanzu ba, ita kuma ta shirya ko ta halin yaya ba zata kwana a kano ba yau ta riga ta sakawa ranta wannan, and one of her mugun halinta akwai nace akan kudinta. Tana saka akwatinta a mota mahaifiyarta ta kira wayarta ta kwantar mata da hankali kuma ta fada mata mahaifinta yayi waya da dan'uwansa, kuma gobe zai taso daga Dutse zuwa Kano ya ji abun da ke faruwa, after Ammy ta kashe mahaifinta Pro Dahiru ya kira waya ya tambayeta me ya faru.

 Ban sani ba, ban masa komai ba

 Ko ma dai minene gobe zan zo, kuma Alhaji yace idan ya dawo gida zai saka a dauko ki ya ji dalilin haka, domin ba shi da labarin komai

 Tohm

Ta kashe wayar, saurin saka kayan ta yi ta shiga motar ta saka danta a front seat ta ja motarta ta fice daga gidan, kunyar hada ido take da Alhaji wanda ya kasance uba a gareta kuma a gurin mijinta, gani take kamar Abdull ya labarta musu komai, but iyayenta fa? Zata iya daukar musu abun kunya ta kai musu? Neman amsar wannan tambayar ne ya saka ta fakawa gefen hanya ta kalli danta sai ta fashe da kuka.

Sanin bata da wani gata da mafita da ta wuce ta mahaifinyarta ya saka ta sake hawan titin ta cigaba da tukin, daman ta kware tun kamin aure take tuka kanta sai dai bata gangancin tafiya wani gari ba, ko da rana balle yanzu da ake ta kiran sallah magariba a ko'ina. Ta sani mahaifiyarta zata fahimce kuma zata karbe ta no matter what ta aikata, and tana bukatar komawa gida ko dan ta dauki matakin abun da Noor ta janyo mata, da kuma wulakancin da Kareem yayi mata...!




NOOR POV.

Kin san halin Noor ba zaman aure take so ba, kin san halin Noor da rashin jin magana ba mamaki wani abun ta aikata kuma ba zata fada ba. Haka kowa yake ta dora min laifi a lokacin da muka isa gida tare da Mama duk yadda ta so ba ni goyon baya sai suka nuna mata ba haka ba, wannan ya saka ta sauko daga fushin da ta yi na daukar zafin boye auren da kuma dukan da yayi min. Aka aje maganar akan cewar idan ya ji sauki za a zauna aji ba asin komai.

Mama ta saka na shirya na tafi asibitin duba shi ni ma a lokacin bana jindadin nawa jikin saboda dukan da yayi min, amman a haka na daure, a gurin mahaifiyarsa da yan'uwanta kam ban ishe su kallo ba. Kwana biyu yayi be san inda yake ba sai a rana ta uku ya dawo hayyacinsa a duka ranaku babu ranar da bana tafiya yan'uwana Mama da Baba ma duk sun tafi duba shi har Mama amman ban da Yaya Nabil Mama ta yi juyin duniyar nan yace ba zai je ganinshi ba. A duk zuwan da bake ina samun yan'uwan matarsa ko surukansa sun zo duba shi amman ban ga Fanna ba.

Ban shiga duba shi ba sai da kowa ya gama shiga ya rage daga mahaifiyarsa sai shi, ita kanta tsoron kallon da take min nake bana da sakewa a gurin yan'uwansa ko kadan. Daga bakin kofa na fara tsayawa a lokacin da na shiga dakin, ina jin wani abu yana taso min, wulakancin da yayi min a gidan Fanna yana dawo min sabo. Mahaifiyarsa na ganina ta fice daga dakin, Zafeer ya dauke kai yana juya idonsa kamar baya son kallona

 Iyaye ne suka ci karfina shiyasa na zo dubaka, ba dan haka ba ba zan zo ba saboda ka ce baka san ni ba

 Ji kamar mai jin maganar iyayenta, na san ai kin yi fatan na mutu ko?

Ban sake ce masa komai ba na fice daga dakin. Ban sake dawowa asibitin ba sai da ya kwana biyar har ana maganar za a sallame shi kamar yadda na ji Kawu ya fada, wannan karon Kawu ne ya rakani da kansa asibitin saboda yana son naje na duba Zafeer, so suke ko ma minene na hakura na zauna saboda an riga an daura kuma mai faruwa ta faru. Na ci kuka sosai kamin na fito muje duba shi saboda bakincikin wulakancin da Zafeer yayi min, kuma na san ba ni da wata mafita a yanzu sai ta zama da shi ko da kuwa zai kashe ni.

Har bakin kofar dakin da Zafeer yake Kawu ya rakoni sai da na shiga sannan ya juya. Zafeer yana zaune akan gadonsa jiki yayi sauki amman har yanzu akwai tabo a tare da shi, kuma ba a cire bandejin da aka saka masa ba waya a kunnensa yana amsawa.

 Wallahi har yanzu ba a gano ba, amman dai za a gano ko suwa ye da yardar Allah, kuma sai sun fuskanci hukunci

Na dan tabe baki na juya zan zan bude kofar dakin. Sai yayi saurin sauke wayar kunnensa ya ce

 Tsaya ina da magana da ke

Na juyo na tsaya har sai da ya gama wayar, sannan ya kalleni.

 Cilasta miki ake yi kina zuwa duba ni ko?

Na yi shiru.

 To daga yau ba za a sake forcing dinki ba, ba zan bari ki sake zama silar lalacewar rayuwata ba, you broke me first, kin bi kudi kin yi aure, kin bar ni kin manta duk soyayya da wahalar da na yi akanki, you don't care how bad it hurt, gashi amanata ta hana ki zaman aure, daman na gwada aurenki ne dan na gwadaki, na yi nufin sakinki tun a ranar da na aureki but this stupid innocent face dinki ta saka ni daga miki kafa, kin yarda kin aure ni saboda kina ganin na yi kudi ko? Yes na yi kudi ne Noor, amman Zafeer din da kika sani a da ba shi ba ne a yanzu, ba zan iya zama da mace mai irin zuciyarki ba, ba ki kuma kai matsayin da zan zabe ki na bar Fanna ba, saboda haka ki tafi na sauwake miki, daman mutane sun fada ba zaman aure kike so ba, saboda kwadayi da dogon buri karamar yarinya da ke kin lalata rayuwarki, na yi nadamar aurenki Noor! Kuma Allah ya isa amanata da kika ci, har abada ba zaki ga da kyau ba, ba zaki taba zaman aure ba... Kuma Wallahi idan bincika ya tabbatar da da sa hannunki ko wani dan'uwanki aka min wannan dukan na mutuwa sai kin sha mamaki...

Kafe shi na yi da ido ina kallonsa hawaye na sauko min, ashe haka butulci yake da zafi...?Shi ma da nake tsammanin zai rike ni ya sake ni yanzu kuma me ya rage? Me zan fuskanta? Ni haka kaddarata take kenan, mutane sun chanfa ni kuma na chanfu. Kowa na raba sai wani kaddara ta raba mu, wata kila aure baya nufin na rayu da shi....
Na juya na bude kofar dakin na fice ina tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, kullum haka nake da tsoron da fargabar abun da zai faru da ni. Nufin nake na samu kulawa da kwanciyar hankali kawai a gidan miji, ko da ban samu soyayya ba zan zauna. Amman na kasa samu ko daya, to ni din me na yi?

Aure ya kake min haka? Farinciki me yasa kake guje min? Wane laifi na aikata na cancanci tukuicin bakinciki da kunci da damuwa? Peeee3eeeeeee karar motar dake kokarin kade ni ta dawo da ni hayyacina

 Ke baki da hankali ne zaki tsallaka titi babu dubawa

Na kauce na ba shi hanya, na raba gefen hanya ina tafiya, har na isa gindin wata bishiya na zauna a karkashinta na nade kafafuwana na noce kaina kasa ina kokarin hana kaina kuka.
Kuka na yi sosai sai da na koshi sannan na cire kaina na saka gefen hijab dina na share hawayena. Number wayar Yaya na kira yana jin yadda na amsa sallamarsa ya san ba lafiya ba, domin muryata ta shake sosai gashi sai shakkuwa nake saboda kukan da na yi.

 Noor lafiya?

 Yana nan gafen hanya Yaya Zafeer ya sake ni, bana son na yafi gida, Mama zata min fa??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????da ta ji haushina

 Kina ina?

 Ban sani ba a hanya ne na fito daga asibitin ne

 Ki zo gida yanzu nan gani nan zan dawo daga restaurant

 Tohm

Na amsa sannan na kashe wayar na mike tsaye, napep na tsayar na shiga muna tafiya ina hawaye har muka isa. Makota na shiga na karbo kudin na bashi sannan na shiga gidan na zauna jiran Yaya ya kira. Fargabana yadda Mama da yan'uwanta za su kalli abun ne, na san duk yadda zan juya zance na je na dawo laifina kaina zai fada.

 Kina ina?

 Ina makota gidansa Maman sani

Na bashi amsa bayan na amsa wayar.

 Fito ina waje

Na tashi na fita maman sani na nanata min na karbo mata kudinta da na ara na bawa mai napep. Da ace damuwa mutum ce na tabbatar da zarar mutane sun yi arba da ni za su san sun hadu da damuwa.
Na kalli Yaya hawaye na saukowa min, sai ya umarce ni da ni da na shiga cikin gidan, amman na kasa har sai da ya wuce gaba na bi bayansa.

Kusan ko wace ya idan tana cikin damuwa mahaifiya ce farkon mutumen dake kawo mata dauki kuma take ganin zata fahimce ta, amman ni tsoro fuskantar tawa nake saboda kaddarar dake faruwa da ni. Na shiga dakin Mama ina labe a bayan yaya kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login