Showing 213001 words to 216000 words out of 227321 words

Chapter 72 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1542

hada da wanda ta bashi a yanzu ya kai hancinsa ya shamki kamshinta ya lumshe ido ya bude.

 I love you so much girl, you're my dream my life, i will be your prince charming

Ya bude idon ya kalleta with so much love, respect and lonely.

 Can you say i love you back?

 I love you Kareem...

Ta furta slowly cikin kunya da murya mai dadi har wani lumshe ido take ga murmushi mai rikita hankali Jarumin namiji.

 Ooooooooooooooooo...

Ya ji wani abu ya fada a zuciyarsa mai sanyi, ears dinsa suka sosu da dadi mai mantar da bakinciki, is like be taba jin wata kalma mai dadin wanda ta fito yanzu a bakin Saraniyarsa ba. Feeling like ya daga ta sama ya jujuyata ya rumgumeta ya nuna mata yadda yake kaunarta sai dai babu dama domin ba halalinsa ba ce a yanzu.

 Ba zan iya jira ba, yau za'ayi mana Baiko

Ya juya da sauri ya nufi motarsa mamaki ya saka Noor binsa da ido baki bude.

 Kareem...

Ya girgiza mata kai ba tare da ya kalleta ba.

 Please don't, a bari ya huce shi ke kawo rabon wani, irinki ce zan tsaya bata lokaci Noor? Nooooooo ba da ni ba gada a makabarta, just make sure idan suka tambaye ki ki amsa musu da yes





NOOR POV.

kallonsa kawai nake har ya tashi motar ya juya da ita ya fice, na taba fuskata na shafa jikinta ina mamakin ko dai na kara kyau ne? Ko kuma wani abu ya ga ni a fuskata da ya saka shi kaunata da jindadin amincewarta har haka? Wani be taba min haka ba, wani be taba sakawa na ji cewar ni din ta musamman ce ba irin yau. Da sauri na dawo cikin gida na dauki madubin Mama dake aje tun bayan da aka kwaso kayan dakinta a gidan Mahaifin Abdull bata taba shi ba.

Na duba fuskata ba ga wani abu ya sauya daga kyakkyawar hallitar da Allah yayi min ba, but why Kareem ya bude har haka? Haka yake so na daman? Allah yasa zai rike ni amana dai kar yayi min irin na sauran. Na yi murmushi na aje madubin na kwanta a katifar Mama ina jin kaunarsa na tsara birnin zuciyar zuwa ruhina.

Na rufe ido ina jin wani yanayi mai dadi, daman ni a rayuwata ba mai kudi ko mai mukami nake nema ba, ni dai ina neman wanda zai mutunta ni ne zai kwantar min da hankali ya ba ni kulawa da so ni ko da kadan ne. Ban dauka da gaske Kareem yake ba har sai da iyayensa maza suka zo tambayar aurena bayan Sallah La'asar.

Kawu ya shigo ya tambaya ko na san da zuwansu, sai na fada masa na san shi kuma mun yi magana da shi amman ban san da zuwansu ba. Na yi wannan karyar ne gudun yayi min fada yace na san da zuwan kuma ban fada musu ba, kuma yace yaushe auren nawa ya mutu amman har nake karkarin yin wani.

Bayan fitar Kawu Mama ta shigo ta zauna kusa da ni ta kira sunana cikin natsuwa na amsa.

 Na'am Mama

 Ke kika ba shi izinin tambayar aurenki?

 Mun yi magana da shi dazun na fada masa na amince zan aure shi, amman ban dauka zai aiko yanzu ba, ban san da labarin aikowar ba

 Yanzu abun da ya fi muhimmanci nake son na sani shim kina son shi?

Na dago na kalleta Mama bata taba yi min irin wannan tambayar ba, balle kuma Baba. Na daga mata kai.

 Kin tabbatar kina son shi? Babu cilastawa ko takurawa ko kawauci? Bude baki yi min magana

 Ina son shi Mama

 Toh Alhamdullahi Allah ya tabbatar da alheri, yasa mijinki ne har aljanna kuma ya sanya alheri ya sa mu ci dadin wannan auren, yasa kuma an tafi kenan Babu dawowa

 Ameen

Ta tashi ta fita. Kawu ne yayi musu jagoranci har Family house din Baba, a can din ba waya suka kira suka aka ba ni Yayan Mahaifina ya tambaya ko ina son Kareem na amsa musu kamar yadda na amsawa Mama. A daren aka yi Baiko duk wani abun da ake kawowa budurwa na baiko sai da Kareem ya kawo min, a daren Farinciki be bar shi yayi bachi ba.

Waya muka fara yi yana fada min yadda take ganin ranar yau da daren kamar mafarki daga baya kuma ya kira ni video call na fita daga dakin na dayan bangaren muka yi video call din, bayan da dare ya raba muka yi bankwana na dawo dakinmu na kwanta a lokacin Mama ta yi nisa da nata bachin ma. Na rufe kofar na kwanta sai ya sake kirana video call na yi sa'a wayata tana a silent ne if not Mama zata ji kuma zata min fada.

Akan doguwar kujera na koma na kwanta na rike wayar muka cigaba da call din ina magana murya kasa dan kar Mama ta ji, ban san ta ya wayar ta subuce a hannuna ta fadi ba, bachin ma ban san lokacin da ya dauke ni ba. Sai farkowa na yi na ji ana jiran Sallah na tashi na kunna wutar dakin na nufi wayata na dauka.

 Good morning

Ya fada yana kallona babu alamar bachi a idonsa tana daga zaune kamar yadda yake a jiya da muka fara wayar.

 Je ki yi sallah ni ma zan yi sallah yanzu

 Okay

Na amsa ina murza ido sannan ya kashe wayar, ni kuma na nufi Mama na tashe ta. Be sake kirana ba sai da gari ya waye yayi haske na amsa video call dinsa na samu yana saka button din hannun rigarsa.

 My Beb My One and Only, the only girl da ta hana ni zaman lafiya, ta fitini zuciyata ta hana ni zaman lafiya, ta kore kowa ta zauna ita kadai

A laugh laugh out loud saboda ni kadai ce a dakin lokacin, kirarin ya ratsa ni shi kuma sai ya tsaya yana kallona yana murmushi.

 Wannan ce Noor dita, wannan yarinyar zan aura mai yawan dariya mai yawan shagwaba mai yawan kiriniya mai yawan rauta mai bakin cin dadi ba wacan mai kuka da kunci da bakinciki ba. Haka na san ki kuma haka nake son ki tabbata har abada

Kusan wunin ranar a tare muka yi aikin asibitin domin ya aje ta inda zan rika ganinsa, ni kuma data da ya saka min tana bude ni ma yana kallon duk wani motsina. Sai idan zan yi sallah ko Mama ta shigo kawai yake kashewa, kamin na sake amsa kira kuma sai ya kira wayata sau goma wai ji yake kamar guduwa zan yi ko wani ya kawace min shi.

Da daren ranar da ya zo yayi min tsarabar kayan dadin restaurant dinsa, a nan ma mun sha hira kusan duk dagowar da zan yi idonsa yana kaina. Tun ina jin rashin sakewa har na sake jiki.

 Ji nake kamar na cinye ki, kai Noor ina sonki kamar na yi haka ban taba jin haka ba, ban taba jin ina son wata mace yadda bake sonki ba, i want you i can't hide this

Na yi murmushi ina sauke kaina kasa.

 Love...

Na kalleshi sai ta taba kirjinsa.

 You're, sha zamanki ki huta, daga ke babu kari, Kareem na ki ne har abada, ke din tawa ce har Aljanna, Noor ta Kareem, Kareem na Noor for every, duniyar nan ta mu ce mu kadai

Kauna da shauki sun rufe ni, muka yi hara cikin kauna da son juna, lokacin da zan fita motar sai ya zagaya ya Bude min na fito ya raka ni har kofar gida.

 I just want to make sure kin shiga gida Safe, kar sai bayan na wuce wani ya sace min ke

Na yi siririyar dariya a shagwabe na rausayar da kai na ce

 Kareem...

 Uhmm Babena

 Good Night

Na juya sai kuma ya kira ni.

 My diamond Girl

Na juyo sai yayi blowing kiss gareni.

 You hold my love, you're my beath, karki manta da wannan

Na yi murmushi na shiga cikin gidan kamin na kai bakin kofar dakin da Mama take na tsaya na jingina jikin ginin na lumshe ido, kalaman Kareem sun fi tsarabarsa dadi, kamar ya san tunaninsa nake sai ya aiko min da sakon karta kwana.

 My Golden Girl, I love you

I reply to him.

 I love you too

He then reply back again

 I love you more

Na yi dariya sannan na shiga dakin, ni da Mama muka ci muka koshi. The following day Baba Ibrahim wanda yake Yaya a gurin Mahaifina yana fadawa Mama wai Zafeer ya zo yana ta ba su hakuri yana rokon afuwar abubuwan da suka faru.

Bayan Mama ta gama wayar takr fada, ni kam na cika da mamakin rashin kunya da karfin hali irin na Zafeer yanzu duk bayan abun da ya faru yana jin idan na yafe masa zan iya komawa na zauna da shi? Ya shirya wata sabuwar azabar ne da zai min ko kuma dai yayi nadamar da bata da amfani ne.

 Wata kila dai ya samu labarin baikonki ne yake kokarin ganin ya lalata, domin Yaya Ibrahim ya fada sai da ya fara cewa wai yana son ya maida aurensa ne, suka ce ai kin cika idda har an miki baiko shi ne fa ya fara bada hakuri, sun ce zai zo ya baki hakuri ai

 Kamar ya zai ba ni hakuri? Ni fa hurumin Kareem ce a yanxu, be kamata ya zo ba

 To sun ce zai zo na isa na hana ne Noor? Yan'uwan ubanki ne yadda suka juyaki dole haka zaki tafi, kawai dai yadda za'ayi idan ya zo za'ace baki nan, idan kuma ya bukaci ganina ba zata masa dadi ba, domin sai na dauke shi da mari

Abu kamar wasa, sai ga Zafeer a gidan ya zo ba ni hakuri yana aikowa aka ce bana gidan sai ya tafi haka ya kwashe kwana uku yana zuwa da sunan ba ni hakuri be samu gani ba. Ban yarda na fadawa Kareem ba na san yadda yake ji na a yanxu zai iya sakawa a rufe Zafeer ma, kuma hankalinsa zai iya tashi yayi tunanin ko zan iya barinsa ne na zabi wanda a yanzu bake jin be kai kafarsa ba ma.

It take us 2 good months kamin Kareem ya gama shirye shiryensa, sabun lefe aka yi min lefen da ko budurwa sai yar wane da wane ake yi ma, lefe ne mai dauke da komai a ciki idan na ce komai ina nufi tufafi masu tsada da aka siya gurin Khadeeja Candy Store, tun daga kan akwatuna har lace da atamfa da materials, kudin ya bata ta hada min lefe complete kamar yadda ya fada min. Akwane set din akwati an saka min dan kunne zinari da sarka kai kace auren fari ne.

Ba a unguwarmu kadai ba har makotan unguwarmu sai da aka yi ta zuwa kallon lefen da ni kaina ban taba mafarkin irinsa ba, ba budurwa ba ce ni, amman haka ya kawo kayan al'adar na auren budurwa kuma ya biya sadaki ya siye ni da kudi har naira miliyan shiri. Da kudin sadakina Mama ta yi hidimar komai tun daga kan siyen furniture da sabin kayan kitchen gurin Khadeeja Candy.

Na gayyato mutane da yawa a bikin irin gayyatar da ban samu yi a duka auren da nake musamman na fari kasancewar bana son auren, Mai dilke kullum sai na tafi ta gyara min jiki ta turare ni da turaren kamshi mai kyau mai dadi, wanda zata ba ni na yi tsuguno dabam na jiki ma dabam bayan humurar da take ba ni ina shafawa kullum a jiki da kuma turaren da nake sakawa a ruwan wanka kullum idan zan shiga wanka.

Har ta kai ko zama na yi na tashi kamshi ke fita a gurin da na zauna. Na yi Walima a wani babban gida da yake unguwarmu, Kareem kuma ya shirya mana dinner a Charming Hotel dake Garin Kano kusan babu wanda Hotel da ta kai ta kyau da tsari da kashe kudi.

Ni da shi muka yi ankon Marron color ni na saka dubai bridel material shi kuma ya saka Gizna mai kyau maroon color. Babu wanda zai kushe hallitar da Allah yayi mana a ranar sai makiyi, domin na yi kyau mijina ma yayi kyau ko da yake ban samu damar kallonsa yadda nake so ba, domin ya tsare ni da ido. Kusan sai da kowa ya shaida yana kaunata a ranar.

The following Day aka daure aurenmu a babban masallacin Juma'ah, a ranar Mama ta yi taron biki, and all abun da aka ci ko aka sha a gurin daga Kareem restaurant aka kawo shi, ma'aikatansa ta turo gava dayansu suka tare a gidanmu idan bako ya shigo sai sun tambaye shi me yake so kamin su kawo masa. Bayan Sallah Isha'i manyan motoci na alfarma suka yi layi a kofar gidanmu har sai da suka yi yawa.

Ni dai a sabuwar mota aka dauke ni motar da ba a ko cire mata leda ba, na yi zaton tsohon gidansa za a kai ni, gidan da yayi rayuwa a baya gidan da ya zauna da Yusura, amman sai aka kaini wani gida dabam wanda ya fi wacan kyau da fasali, shi ma dai gidan sama ne mai hawa daya sai dai ya fi wancan tsari nesa ba kusa ba. Sai kamshi turaren wutar da Mama ta saka ka yi ke tashi. Na shiga falona da kafar dama tare da bismillah kamar yadda Mama ta fada min na yi idan zan shiga, a lokacin da aka shiga da ni falona sai da na yi kamar na saka karamar ihu saboda murna, i can't believe falona ne, balle kuma dakin da kalamai suka kare akansa, ta cikin farin mayafina nake ganin komai kasancewar mai shara shara ne zaka iya ganin komai.

A kan gadona suka zaunar dai suka min nasiha irin ta gwaggwanin, kanen mahaifita ma suka min sannan suka kora kowa suka tafi, ganin cewa ni ba budurwa ba ce a yanzu balle ace sai an tsaya siyen baki.
Shi ma dai yan'uwa da abokan arziki sun rako shi suka mana nasiha sannan suka tafi. Mayafina ya fara cirewa ya dago kaina na kalleshi sai ya saka hanayensa duka biyun ya rike fuskata yana yawo da idanuwanshi a fuskata kamin ta samu saka idanuwanshi cikin nawa.

Sai kuma ya lumshe ido ya hade goshinsa da nawa, hancinsa ma yana taba nawa ni ma lumshe idon na yi ina jin lips dinsa saman nawa yana motsa su yayin da yake magana.

 Na mutu a kaunarki mabanbanta lokuta mabanbanta ranaku, kin zo min a lokacin da ban yi zato ba kika dauke min zuciya kika guda and heart Speak to me, son ki ya fara kamar tsiro, da ya girma sai ya hana ni zaman lafiya, tun ina iya boyewa har hakan ya gagara, Noor har a mafarki zuwa min kike, ada ina jin bancancanta ba amman yanzu Allah ya saka min natsuwar hakan... Ina sonki irin son da kalmomin duniya za su kare gurin bayyana sona a gareki

Na sauke numfashi a hankali mai gauraye da nasa, jin ya daga daga fuskata hawayen da na ke kyautata zaton na farinciki ne a fuskata Kareem ya saka halshensa ya lashe har saman idona da suke rufe.

 No more tear my golden Girl

Na ji bakinsa a hancina, a hankali kuma sai na ji lips dina sun jika da yawun bakinsa, he then kiss my front head. Ya mike tsaye ya cire babbar rigarsa ya fita be dade ba ya dawo muka shiga muka yi alwala muka yi sallah, bayan mun gama yayi addu'a ni ma na yi. Ya dauko mana abun tabawa madarar kawai na sha ban iya cin komai ba, shi ma be ci ma, da adama farincikin aurena sa kallona ya kosar da shi.

Bandaki na shiga na canja kayan jikina zuwa na bachi, na fito sanye da riga da wando matching color da na shi. Madubi na nufa ina cire agogo da dan hannun dake hannuna. A hankali na ji yana cire min sarkar wuyana ya aje a gaban madubi yana kallon idona ina kallon na sa ta cikin madubi. Hannunsa ya kai ya bude saman rigata kadan ya sumbanci kafadata, ya dora hancinsa a wuyana yana shakar fitinannen kamshin dake tashi a jikina, har wani lumshe ido yake.

Juyowa yayi da ni ashe ya bude maballan rigarsa ban sani ba, kunya ta saka ni rufe ido kwarjininsa ya kama ni fiye da kullum. Nawa maballan ya fara budewa ina jin kamar na hana shi domin daren yayi min kamar darena farko a gidan miji.

Ban yanke shawarar hanawa ko bari ba, har yayi nasarar bude min rigar bachi, na rufe idona da sauri jin skin dina yana taba na shi, and i feel something so soft, so scent, so fresh, so cool, so hairy har yana shigar min baki. Na ji wani abu so special wani abu mai dadi mai kwantar da hankali mai saukar da natsuwa mai faranta zuciya. Kirjinsa faffada ne sosai ya yawalwace ni na yi lamo a kirjin mai cike da sanyi da yalwar gashi.

 I just want to feel the connecting... I love you unconditionally, you're forever mine, at long last we are together...

Ya furta min saitin kunnena har bakinsa yana taba kunena, yana kara rumgume ni, ni na na daga hannayena na rumgume bayansa ina jin gamsuwa da natsuwa, feeling so comfortable, wani spark nake ji daya hada skin to skin heart to heart wani be taba rumgume ni na ji abun da nake ji a yanzu ba. ?in din din bugun zuciyata ke tafiya tare da na shi.

Mun dade a haka kamin ya dauke ni cak kamar jaririya ya dora akan gado, sannan ya nufi wutar dakin ya kashe, then ya sake dawowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login