Showing 168001 words to 171000 words out of 227321 words

Chapter 57 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1545

Dakinmu na shiga na samu yar'uwata ita ma tana nata kukan.

 Hana me ya faru ina Baba?

 Ya tafi yanko sammaci ya ce ba zai kyale maganar nan ba, shikenan rayuwata ta lalace

Na tashi da sauri na fice daga dakin waje na fito na samu Kareem tsaye yana kallon kofar gidanmu.

 Baba ya tafi kotu zai saka karar

Motar ya bude ya dauko wayarsa ya zagayo ya mika min wayar.

 Saka min number Baba

Na karba na saka masa jiki na rawa na mika masa kasa ya sunkuya ya aje min sim dina ya juya ya wuce, ina tsaye a gurin ina kallon motarsa har ya bace min.





KAREEM POV.

Be yi nisa da unguwar ba ya faka motarsa ya jingina kansa yana ya runtse ido, wani azabben ciwo yake ji a kirjinsa da ya wuce misali, ya kusa minti talatin tsaye a gurin sannan ya dago ya kira number mahaifin Noor. Da farko be daga ba har sai da ya sake kira. Cikin mutumci Kareem ya gaisa da shi sannan ya gabatar masa da kanshi, sannan ya kora da dalilin kiransa.

 Baba na wani labari na ji marar dadi, cewar an yi ma Hana fyade abun ba dadin fada ma, ban jidadi ba gaskiya sai dai abun da ya fi daga min hankali shi ne cewar da aka yi zaka yi karar wanda ya aikata abun ko haka ne?

 Haka ne mana, ta ya zan bar wanda ya keta haddin yata ya tafi a banza, dole na kai shi kotu hukuma ta hukunta shi, suna aikata hakan ne saboda suna ganin ba a musu hukuncin komai

 Haka ne, kaiwa kotu yana da amfani musamman idan har za a musu hukunci, sai dai Baba ina son ka sani kotun yanzu ba irin ta baya ba ce, kuma mutumen nan yana da rufin asirin da zai iya komai dan ganin asirinsa ya rufu, mahaifinsa ma babban mutum mahaifiyarsa ma haka kuma ita ma babban mutum take aure, baka tunanin aikata hakan zai janyo ka jefa rayuwarka cikin hatsari?

 Bana tsoron komai ni, Allah yana tare da mai gaskiya, tarin kudinsu ko ikon da suke da shi ba zai hana na kaisu kotu ba, shiyasa ma zan yi karar uban ai, domin shi yake gari ba dan ba, kuma ya san dansa ba ban kirki ba ne ya zo nema masa aure? Ko da lamarin nan ya faru ai ya kamata ya zo ya same ni ya ba ni hakuri kuma ya samu dan wani abu ya ba ni ko? Duk be yi ba sai ya zuba min ido yarinya ace har ciki aka zubar mata kamar wata karuwa, ai an fada min kai ka zubar da cikin, ashe kai ma zaka iya cutata Alhaji na yi zaton ai an zama daya yanzu

Kareem ya shafa goshinsa ya sauke ajiyar zuciya.

 Duka mun yi wannan abun saboda kar kowa ya ji, idan maganar nan ta fita Hana zata rasa abubuwa da yawa, zata takura cikin mutane kuma abun zai zama abun magana ba lallai ta samu mai aurenta a haka ba, dan Allah Baba ka bar maganar nan ko dan mutuncin yaranka, kuma karar mahaifinsa be dace domin ba mahaifin ne ya aikata ba, hakan zai iya janyo alakar dake tsakanin Mama da mahaifinta ta samu rauni

 Idan ta samu rauni ni miye nawa a ciki Alhaji? Daman ai an fada min Hajara ta boye wannan ne saboda uban wai kar aurenta ya mutu saboda yana da kudi ko, wato ta fi son rayuwarta akan rayuwar yaranta saboda kwadayi da son abun duniya

 Ina da tabbacin ba dan haka ba ne Baba, saboda kar rayuwar Hana ta lalace ne kawai ba dan wani abu ba, dan Allah Baba karka shigar da karar nan ka tsaya ka yi nazari

 Na yi iya nazarin da zan yi daga jiya zuwa yau, kuma na duba na ga abun da ya dace na aikata kenan, yanzu haka na biya kudi an yanka sammaci an aika wa ubansa zamu hadu kotu litanin mai zuwa rana irin ta yau

 Baba zan biya duk wani kudi da ka kashe na kai sammaci kuma zan samu wani abu na baka, zan yi duk abun da ya dace zan dauki abubuwa dan Allah Baba ka bar maganar nan

 Ka gani Alhaji Kareemu ina ganin mutuncinka sosai ina mutumta ka, dan Allah mu tsaya a matsayinmu kar abun ya wuce nan, ni ba makwadaici ba ne, ba irin uban nan ba ne da zaka ce ka dauki kudi ka ba ni ka rufe baki, wato saboda ka raina kuma ka maida wannan matsalar ba komai ba ko? Shiyasa kake son ka rufe bakina, ba dan na san ka da dadewa ba ai sai na ce Abdullahin ne ya aiko ka, ni ba zan bar maganar ba sai na kwaci hakkin yata

 Ayi hakuri Baba

Kareem ya sauke wayar tare da sauke ajiyar zuciya, wannan karon ya kasa shawo kan Baba yana mamakin me aka nuna masa haka da har ya dage dole sai yayi wannan karar, shi dai kam zai iya fada be taba ganin mutum mai zuciyar Baba ba, baya tsayawa tunani idan zai aikata abu.
Nurse da ya saka ta yi ma Hana wankin ciki ce second person da Kareem ya kira after Baban Noor.

 Hello

 Juwairiyya ya kike ya gida?

 Lafiya kalau Alhamdullahi ranka ya dade ya aiki?

 Kwanan baya akwai wata yarinya da na kira kika mata wankin ciki zaki iya tunawa?

 Eh ba a dade sosai ba ai ko?

 Haka ne, kuma ina tunanin lokacin da na kiraki na fada miki cewar yarinyar kaddarace ta hau kanta, kuma tana da matukar muhimmanci a gurina shiyasa na kasa yi mata da kaina na saka ki yi, domin zan iya cire ciki ko ya kai wata takwas kuma mace ta rayu, abu da kika san na kwarai a kansa, amman na kira ki na bukaci ki mata ne saboda bana son na ga yarinyar a wani yanayi da be dace ba, abu na biyu duk mai aikin lafiya ya san aikin lafiya sirri ne cin amana ne ka dauko sirrin wani ka yada kin san da wannan?

 Na sani, me ya faru?

 Da wa kika yi hirar yarinyar nan? Saboda abun ya zagayo yana bibiyar yarinyar nan

 Ban yi maganar da kowa ba gaskiya

 Don't lie to me please, mahaifinta da bakinsa ya fada cewar har wadda ta cire mata cikin ya gani da idonsa

 Ni Wallahi ban san na samu wani na yi wannan maganar da shi ba, me zai saka na yi haka? Gaskiya akwai dai yadda aka yi amman Wallahi ni ban yi magana da mahaifinta ba ban san ma mahaifinta ba ban san kowa nata ba, wata kila dai ita can ta fada har maganar ta juyo amman ni ban fadawa mahaifinta ba

 Ba ki yi maganar da kowa ba?

 Gaskiya ban yi maganar da kowa ba

 Lokacin da na kiraki na fada miki ciki ne nake son ki wanke waye a kusa da ke?

 Akwai kawayena guda biyu lokacin mun je barka kawata yar makarantarmu da ta haihu, amman ko su ban yi maganar da su ba?

 Zan iya sanin sunansu?

 Yeah Safeena Jafar Ishaq da Amina Alhassan

Sunan farko da ta ambata ya sanyaya guiwar Kareem a nan ya gane gurin da maganar ta fita, wata kila bata son fada masa cewar ta sanar da Safeena ne, wata kila kuma gaskiyar take fada masa idan har zata boye wani abu ba zata ambaci sunan Safeena ba.

 Mi ya faru?

Ta tambaya jin yayi shiru.

 Kawai ina tunani ne, wata kila ita ta fada ko yayarta zan bincika ta can na ji a ina maganar ta fita

 Sai dai idan can domin ni ban yi maganar da kowa ba

 Okay

Ya sauke wayar ya bugi sitiyarin motar da karfi.

 Safeena...!!!

Ya lalobo number Safeena yayi mata kira ya fi a kirga bata daga ba har sai da ya aika mata da sako.

 I need to talk to you abu ne mai muhimmanci

Few seconds da delivery sms din kiranta ya shigo wayarsa.

 Magana nake son mu yi mai matukar muhimmanci, ki same ni a guest house, yanzu

Yana fadar hakan ya kashe wayar ya hau titi ya dauki hanyar gidansa da suka saba haduwa.
Ya rigata isa domin shi yake son magana da ita a yanzu, a yanzu ikon a gurinta yake hakan ya saka ta bata masa lokaci na tsawon mintuna arba'in sannan ta shigo gidan. Yana tsaye ta window falon yana kallonta har ta fito motarsa ta turo kofar falon ta shigo.

 Lafiya kake son ganina?

 Me kike so Safeena

Kamar jira take sai ta sauke gyalenta ta aje jakar a kujera ta nufo shi tana nuna shi.

 Kai Kareem kai nake so!

 To miye matsalarki da Noor? Miyasa kike cusata a cikin matsalarmu?

Ya tambaya ba tare da ua juyo ba hannayensa duka biyu suna zube a aljihunsa.

 Saboda Noor ce ta raba ni da kai, Noor ce macen da ta cike gurbina da ita, kuma ita ce ta kashe min auren da takardar kawai ya rage Abdull ya ba ni

 Ban cike gurbinki da na noor ba, wani gurbi na gina mata mai kyau mai tsabta, mai cike da kauna da soyayya, dan Allah ki cireta a cikin matsalarki

Har lokacin da yake maganar be juyo ya kalleta ba.

 Ita ce babbar matsalata a rayuwar nan Kareem, ta lalata min aure tun da mijina ya dauki yaran nan ya tafi da su ya auna jininsu be sake dawowa gidan nan ba, last week ya aiko kanensa ya dauki yaransa biyu aka bar karamin da na haifa da kai, yanzu haka mijina yana garin nan amman be tako kafarsa gidana ba, ya daina min aike ya daina kulani baya amsa wayata baya ba ni amsar sakona, na sani saki na zai yi bayaj ya gama kwance min zane a kasuwa, zai saka kowa ya tsane ni a danginmu saboda abun da na aikata Mijina cousin dina ne, kuma duk sanadin Noor ce ne domin ita kadai ta san sirrina ita kadai zata iya fallasa wannan

Ya juyo ya kalleta.

 Ta aikata kuskure na fahimta, mu ma mun aikata dukanmu mutane ne, amman saboda me zaki lalata rayuwar kanwata me ya shigo da kanwarta ciki? Kina da tabbacin Abdull din ne ya aikata?

Ta matsa kusa da shi tana masa wani kallo na tsana for the first time.

 To waya aikata kai? Ko kuma dai ita ta aikatawa kanta?

 Baki da tabbacin Safeena karki jefa rayuwarki a matsala

Ta yi wani shu'imin murmushi.

 Na san komai Kareem kai ka san wacece ni, ina da tabbaci mana, a gabana ka kira kawata ina jin muryarka lokacin da kake fada mata cewar wata yarinya kake son ta yi ma wankin ciki ka mata allura amman dai ka fi son a wanke saboda ka samu tabbacin komai ya zube, ka fada mata kaddara ce ta hau kan yarinyar fyade aka yi mata ko ba haka ba?

 Ita Juwairiyya ce ta fada miki haka?

 No Wallahi bata fada min komai ba, amman na ari wayarta na duba bangaren kira sai na ga number ka, daman kuma na ji muryarka domin wayarta ana ji duk abun da mutum ke fada sound din kiranta a karshe yake, lokacin da na duba zuciyata ta fada min Hana ce, there is no way da zai saki Noor da ciki ba tare da wani abu ba, kuma ya fadawa yan'uwansa wai ta tayar masa da fitina ne sai ya sake ta shi kuma ya sake ta saboda TA KI ZAMAN AURE, kana ganin hankalina zai dauka? Idan babu wani abu me zai saka Noor ta fada masa cewar dan da na haifa ba na shi ba ne? Mw zai saka yar'uwarta ya yanke karatunta da duk wani gata da yake musu ta dawo ita da kanwarta su zauna a gida? Daman ni ban yarda ba na san akwai wani abu a kasa, domin na san waye mijina ba kasafai yake iya rike kansa ba, a tsawon watanin da yake a Lagos da sunan aiki na san me yake aikatawa, kawai na zuba masa ido ne saboda babu yadda zan yi, kana tunanin namiji zai saka al'adar neman mata a gaba kamar yadda Abdull yake kuma ace matarsa bata sani ba?

Ta share hawayen da suka zubo mata cikin daga murya ta cigaba da fadar.

 Neman matansa ya taimaka min gurin bibiyarka da kokarin kulla alaka da kai Kareem, na san yana neman mata tun kamin na aure shi, na aure shi ne saboda an matsa min a gidanmu na yi aure, kai kumaka guje ni, duniya ta min zafi, shi kadai ne mutumen da ya zo zai share min hawaye a lokacin, bayan mun yi aure ya zama bana burge shi saboda ya saba da matan waje, mijina ba shi da lokacina, baya ganin kyauna, ba ya ganin ado na, kullum idonsa akan matan waje ne, mijina baya iya gamsar da ni yadda kake min Kareem, gaba daya ban yi dacen rayuwa ba, amman a haka nake zaune kullum burina idan har na bar Abdull kai ne

Wannan karon da cinyar hannu ta goge hawaye idonta na dama.

 Na san na yi kuskure na haihuwar ba ta sunna ba, dukanmu yin yi kuskure amman sai mu rumgumi wannan kaddarar, nan gaba kadan Abdull sakina zai yi, to sai ka aure ni mana Kareem

Ya juyo da kyau ya fuskance ta.

 Ba zan taba aurenki ba, amman zan tabbatar maki da abu daya, Noor ba zata aure ni ba, saboda bana cikin mazan da take so, please ki cireta a cikin matsalarki

 I don't care ka auri Noor ko karka aureta ba matsalata ba ce, abun da kawai na damu da shi, shi ne idan Abdull ya sake ni zaka aure ni

 Har abada ba zan taba aurenki ba, aure ya haramta a tsakaninmu

Ta rausayar da kai tana murmushi.

 Na fahimci hakan ai, shiyasa na bullowa ubanta ta wannan sigar na fada masa gaskiya kuma na kwadaita masa dukiyar da zai samu idan ya Abdull ko mahaifinsa suka bukaci a sirrinta abun, na samu wata kawata muka je a zuwan ita ce nurse din da ta cire ciki, kuma na samu kudi mai kauri na ba shi. Ka ga yanzu hankalin Abdull zai koma gurin abun da ya aikata ne ba wanda zai aikata a gareni ba, kuma idan ya fallasa sirrina duniya zata zage mu a gaba dayanmu mu uku, kai ni da kuma shi

Kareem ya sasauta fuskarsa ba dan tsoron furucinta ba sai dan yana son ta fahimcin illar fa hakan zai mata ba mijinta kadai ba. Ya busar da iskar bakinsa ya jin kirjinsa na ciwo sosai.

 Ki rika yin tunani kamin ki aikata abu, kina da yaya Safeena, tun farko baki rike aurenki kika biyewa shaidan muka aikata alfasha, hakan be wadatar da ke ba sai da kika ga mun haihuwa, yanzu gashi abun ya dawo yana bibiyarmu, kuma duk yadda wannan abun zai taba ni be kai yadda ke zai miki illa ba Safeena, saboda ke mace ce ni kuma namiji ne, shiyasa da Allah zai ambacin mazinata a kur'ane sai ya fara da mace, domin ita ce mai rauni kuma ita ce mai shiga kaso 90 na matsala sama da namiji

 Zaka aure ni Kareem? Ka min alkawari kawai zaka aure ni Wallahi zan yi duk yadda zan iya mahaifinta ya janye shari'ar nan

Ya cire hannunsa daya a aljihu yana nuna mata.

 Let me make this clear to you, idan har zan sake wani aure a rayuwata, to mace daya ce zan aura Noor, idan har ba zan auri ba ba zan sake aure ba, so ki saka a ranki ni da ke ba mu taba sanin juna ba, ba zan taba aurenki ba Safeena!!

Wani mugun kallo take masa zuciyarta na bugawa da karfi. Cikin ihu da takiya ta ce

 Ba zan saka ya janye shari'a ba Kareem kuma zan daukar masa lauya, domin ina bukatar abun da zai daga hankalin Noor ya zubar da mutuncinta da na iyayenta ya kashe auren uwarta ya jafata a matsala, ba ni da makiyaya a duniya irin Noor yarinyar da saboda ita igiyar aurena take rawa? Saboda ita juya min baya, yar sikar yarinya shashasha mahaukaciya, yarinya da bata kai ta goge talkamin kafata ba, yarinyar da bata kai ka rika hannunta ba, amman ita kake so? Yarinyar da ubanta baya jin wani yare sai na kudi? Yarinyar da ubanta be san wani mutuncin ba sai na k????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
udi? Yarinyar da babu komai akanta sai hauka da gidadanci, fasika da bata iya komai ba sai bibiyar mazan mutane yarinyar da...

Tassssss ta ji saukar lafiyayyen mari a fuskarta daga hannun masoyinta Kareem, Wani irin numfashi taja da karfi ta kai hannu ta dafe kuncin hawaye masu zafi na sauko mata. Cikin wani irin bacin rai da Kareem be san yana da shi ba ya nuna ta da yatsa ya ce.

 Kul bakinki ya sake kiran Noor dita da wata kalma marar kyau, iyakar kiyayar da kike mata saboda tana da alaka da ni ne, ni kuma ba aurena zata yi ba, ki fadawa mahaifinta karya kike ya janye shari'ar nan idan ba haka ba...

Wayarsa ta yi ringing ya ciro wayar ya duba farincikinsa ce take kira wato Noor, ya amsa wayar ya kara a kunne shi ma dai sound din kiransa a karshe yake kamar yadda na mutane da yawa yake a manyan wayoyin yanzu.

 Kareem ka yi magana da Baba? Me ya fada maka?

Sai da yayi iya yadda zai ya danne yakin dake zuciyarsa ya amsawa Noor da murya mai sanyi.

 Na yi magana da shi be yarda ba, amman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login