Showing 186001 words to 189000 words out of 227321 words

Chapter 63 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1570

kira sunana a natse sai na kara narke masa da kuka.

 Ki yi hakuri, kuma ina son na fada miki ni Alhaji Sule gidana be fi karfina ba, kuma ban zo gurinki domin shashanci ba, aure nake sonki kuma shi ya kawo ni, abu daya zaki min a yanzu ki burge ni, ki amsa cewar zaki aure ni!

 Na aureka taya? Mata hudu fa haka uwargidanka ta aiko a fada min, kuma idan ma na aureka na je matanka su rika min duka

 Wallahi Wallahi babu wanda ta isa ta saka miki hannu Khadija, kuma zan tabbatar miki da haka, ki bawa Mama hakuri zan zo yanzu da kaina na ba su hakuri, kuma ki jira matakin da zan dauka

 Amman da gaske zaka aure ni? Ni tsoro nake karka cutar da ni ba ni da kowa sai Allah sai Mamana da suka yi ma duka dazu, har kusan karya min hannu suka yi

 Wallahi Wallahi zan aureki Khadija, idan ma kin amince cikin satin nan sai a daura mana, ni bana bukatar komai daga gareku, zan zo yanzu nan na bawa Mama hakuri

 Toh sai ka zo

Na kashe wayar ina murguda baki, daman bahaushe yace idan ka san me zaka fada baka san me zai dawo maka ba. Ba a jima ba Alhaji Sule ya zo gidanmu tare da abokinsa ya bawa Mama da yan gidanmu hakuri ya aje mana kudi mai kauri sannan ya tafi, ko be bani labari ba na san ba za'ayi mai kyau ba. A daren ne Zafeer ya sake sallamawa a gidanmu sai dai wannan karon ba da ni yai magana ba sai da ya shiga ciki yayi magana da Mama ban san me suka tattauna domin fita na yi na bar musu dakin.
A dakin Anty Amarya ina amsa facetime with Kareem. Fada yake few hours suka rage ya shiga da shi tiyata.

 Da dare za'ayi maka?

 Mu nan safiya ce, akwai banbanci lokaci

 Na maka addu'a sosai da dare, a kowace sallah ma ina maka, Allah ya baka lafiya Kareem

 Amman baki min addu'a ki ce Allah ya ba ni ke, idan ni din alheri ne a gareki?

Na dan yi shiru ina jin wani iri domin kudirinsa akaina ba zai ga ci ba, kuma ban san taya zan buda masa littafin ya karanta har ya fahimta ba.

 Babyna

Kallonsa nake ba tare da na amsa ba.

 Zafeer ya sake dawowa ko? Kuma Baban Aisha ya zo?

 Taya kake sanin duk wannan Kareem

Yayi murmushi daya kara bayyana ramarsa.

 Karki da wannan, i just hope idan an yi min tiyata na tashi zaki min albishir mai dadi

A kokarina na karfafa masa guiwa domin samun yin aiki a cikin nasara na daga masa kai na jadda masa zan tarbe shi da labari mai dadi.

 Ina fatar hakan, zan huta na tsawon kwana hudu, ba lalle na sake facetime dake ba sai na ji an samu results din da ake bukata, but what so ever dai i love you i want you to know that i know you

Na yi murmushi ina jindadin furucinsa har cikin raina, for the first time na ji ina sha'awar kwantawa a jikinsa na rumgume shi mu yi bankwana amman babu dama, na shafa screen din wayar.

 Hey... No more tears, bana son na ga idonki da kuka, i love you so much

Na share hawayen wasu na zubo min.

 Allah yasa ayi aikin cikin nasara Kareem get well soon please

 I will

Ya laka yatsunsa biyu a screen din wayar, ni ma na lika nawa a saitin nasa, ni da shi aka rasa wanda zai dauke ido daga barin kallon dan'uwansa, tausayin halin da yake ciki a yanzu da kuma wanda zai shiga idan ya tasa ni, ya saka ni zubar da hawaye kamar babu gobe. Ya maida hannunsa gurin bakinsa ya sunbanci yatsun ya sake lakawa saitin da nawa suke.

 Idan har na rayu na aure ki Noor, sai na mantar da ke duk wani daci da bakinciki da yake cikin duniyar nan, sai na saka kin gamsu cewar wata mace bata fiki gata da samun soyayya ba a gurin miji, zan so ki har abada Noor

Na lumshe ido na maida lips dina na kaaa tsakanin hakorana ina tauna zafin rabuwar da ba mu riga mun yi ba.

 Noor ta so ana kiranki

Na kalli Anty Amarya sannan na kalli wayar dake aje gabana.

 Zan tafi Kareem ana kirana

 Okay Love... Fada min wani abu mai dadi kamin ki tafi

 I love you

Na fada with no hesitation, murmushi yayi ya shafa fuska ta jikin wayar sannan ya daga min hannu.

 Bye

 Bye

Mun dade muna kallon juna ni da shi, kewaraa ta hana ni kashewa shi ma kuma baya son ya daina ganin fuskata. Sai da na yi da gaske sannan na iya aje wayar na share hawayena na fita daga dakin Anty Amarya. Bangaren da Mama take na koma na shiga a wani yanayi kamar ba ni ba, gaba daya Mood dina ya canja.

 Ki tafi Zafeer yana waje yana jiranki

Na cire hijab dina da ya jike da hawaye na dauki wani na saka, sannan na fita na tsaye a kusa da motarsa har muka gama gaisawa ban kalli fuskarsa ba.

 Noor na yi magana da Mama na tambaye ta ko akwai wanda kike so da har ya hana ki amsa aure na a karo na biyu bayan duk wulakancin da kika min? Ta fada min babu ta tabbatar min har yanzu kina kaunata kawai dai kina wasu hange hange ne da ba su da amfani

Ya gyara tsayuwarsa.

 Ni kuma na san akwai mai wasa da hankalinki har yanzu, wannan Kareem din ko? Ba aurenki zai yi ba Noor kawai yana wasa da hankalinki, ya raba ni da kw farko Noor ban yi tunanin zaki sake kula shi ba, balle har ya zama dalilin da zai saka ki amsa cewar zaki aure ni

 Ba shi ne dalilin ba, kai da Mama kun yi kuskure fahimta ne kawai

Na fada domin a zatona Mama ta yi masa maganar Kareem ne. Sai ya tari numfashina

 Mama bata min maganar Kareem ba, kuma bata fada min komai akansa ba Wallahi, amman kin san ba zan rasa sanin halin da makiyina yake ciki ba ko?

Na yi shiru ina jin babu dadi, na kasa sakewa zuciyata na raya min zan ci amanar Kareem ne, amman kuma. Zafeer ya cancanci komai a gurina, ba ni da masoyi irinsa, ya nuna min so iyakar so.

 Ina hango yadda kake kallona a idonka nw Zafeer

Ya sassauta muryasa.

 Ki bar wannan maganar, ni dai babu abun da na iya kuma na sani sai kaunarki, zan iya yin komai saboda na aureki, na so ki Noor kin sani, na kusan mutuwa a lokacin da na rasa ki, ba ni fa wani buri a yanzu da ya wuce na aureki, rayuwar da muka sha alwashin ginawa a baya ba mu samu dama ba nake son mu gina a yanzu, shin kina so na har yanzu?

A nan kam na daga kai na kalleshi da idanuwa dake hasko min irin rayuwar d muka yi a baya.

 Ina sonka har gobe har jibi har gata Zafeer

Yayi min murmushin da na manta rabon da na ganina fuskarsa, ya matso kusa da ni cikin wata siga da ta fi kama da rada ya furta min.

 Zaki aure ni Noor?

Na daga mishi kai.

 Zan aureka Zafeer

Wani kuka mai karfi ya zo min. Tun daga ranar sai soyayya tsakanina da Zafeer ta dawo sabuwa ya karbe liyi na ya siya min wata wayar da sabon layi, kowa a gidanmu sai da ya san Zafeer ya dawo gareni, domin ya hanani kula kuwa ciki har da mahaifin Aisha da ya saki uwargidansa saboda ya aureni, kamar yadda ta sake zuwa har gida ta yi min cin mutunci ta fada min na kashe auren uwarta ni kuma na jira nawa sakamakon. Duk wani shirye shiryen aurar da ni Mama ta fara domin Zafeer ya fada min ba zai bata lokaci kamar yadda yayi a wacan karon har ya rasa ni ba.

Dawowar Zafeer ta min dadi, musamman da ya sanar min an kori Abdull a kamfanin da yake aiki, sai dai bana jinsa a yadda nake jinsa da farko, idan kuma na tuna Kareem ba da masaniyar komai akaina babu ta inda zai same ni sai hankalina ya tashi, lokuta da dama na kan so gwada kiransa a sabuwar wayar da Zafeer ya siya da sabon layi domin na haddace number sa, sai kuma na tambayi kaina me zan fada masa idan ya amsa kiran nawa. Na san an yi nasarar aikin a satin da aka amsa aikin na ji a gurin Yaya Nabil an masa aiki kuma anyi a nasara, amman na kasa kira na tambayi jikinsa ko na yi magana da shi.



Ya miko min zobe daya ya saka daya.

 Wannan na ki ne

Na karba ina murmushi na yi saka a yatsana, soyayya sabuwa ni da Zafeer kamar ba mu taba shiga damuwa a baya ba.

 Dukanmu mun taba yin aure, ni na yi aure na farko ke ma kin yi har biyu, so ni a yanzu bana son ayi wani biki ko taro, ba zan yanke hanzarinki ba, na san mata kuna da son biki wata kila zaki yi walima ko?

Na dan yi shiru ina nazarin abun da zan yi, domin Mama ce take ta shirye shiryen auren, har yanzu ban yi wani yunkuri ba.

 Bani ba ko Mama zata yi, amman dan ta ni bana sha'awar wani shirye shirye

 Good, zan fi jindadin haka, ba sai an wahalar da ke ko Mama ba

 Babu wahalarwar a ciki, ba za mu bukaci komai ba

 No ba ina nufin kudin da zan bada ba no zan baki kudi enough ki yi hidimarki, kawai dai dauaniniyar ce wahala ai, kuma ina son na fada miki na kama gida a bypass ba laifi gida ne mai kyau sosai kuma yana da tsari mai kyau sai dai ba ma kusa da mutane

Na dan kalleshi da mamakin jin furucinsa domin a tunanina yana gidan kasansa ko da yake gidan ba zai amfana min komai ba. Yayi murmushi yana kallona.

 Ya na san zaki yi mamakin na fadi haka ko? Gidana da nake zaune wanda nake tare da Fanna ne, kin ga yadda muka sha soyayya ni da ke kamata yayi ace mun tare a gidanmu mu kadai babu sa ido babu ganin laifi ko?

Abun da ya fada haka ne, za mu fi sakewa idan muka tare mu kadai.

 Wai ni kam taya ka lallabata ta amince ka kara aure?

 Ban gane ta amince ba, ni ne fa mijin ba ita ba! Tun kamin na aureta ai ta san ina sonki kuma at any chance zan iya aurenki, abu na biyu Fanna ba mace ce mai matsala ba, kuma bata cika zama ba, saboda ita ce tabbar yar mahaifinta yawancin abubuwan da suka shafi kasuwancin mahaifinta ko kamfaninsa ita take tafiyarwa, yanzu haka bata kasar ma

 Amman me yasa baka bita ba?

Ya daga fadunsa.

 Ra'ayi, tana son muna tafiya a tare sosai saboda tana son na zama a namiji da mahaifinta ya rasa, na maye gurbin a namiji da ba shi da, so nan din ma akwai abubuwa da nake kula masa da su

 Amman ance ta tsofe ka wai haka ne?

 Ko ma dai minene ai ta taimaka ta aure ni a lokacin da kika zubar da ni a kasa ko? Ita ta rarrashi zuciyata na samu sukuni har na rayu

Na ji wani abu ya soki zuciyata.

 Daman tun a farkon zuwan da take na lura da sonka take yi, shiyasa take baka kudi mai yawa har ta taba tambayata wai kai saurayina ka tuna?

Yayi murmushi ya shafa kansa.

 Manta da duk wannan, yanzu dai ya maganar tufafinki? Ina tunanin kudi zan baki ki siya duk abun da kike so

 Me yasa ba zaka hada min da kanka ba?

 Kawowar ne nake tunani kamar zai fi dai ki hada da kanki

Bana masa jayyaya akan abubuwa daman can ni ba mace ce mai son ja'in ja ba, balle kuma shi da bana son ya ga laifina a yanzu ko da kuwa kan akaifa ne. A yadda ya tsara a hakan na bi sai ya kawo min kudi mai yawa da sunan siyen kayan lefe, Mama ta siya min kadan sauran kudi kuma ta kara gurin siyen kayan daki da na kitchen domin komai sabo ta yi min kamar auren fari. Yan'uwan Mahaifina sun yi kokari matuka, sun hada kudi mai yawa suka kawo gun Mama a matsayin gudunmawarsu.

Mama ta hada da wanda ta samu a danginta da kuma kudin da Zafeer ya ba ni na lafe ta siya min kayan daki fa kayan Kitchen masu kyau irin na mai rufin asiri. Ba ayi walimar ba kamar yadda Zafeer ya bukata, saboda Mama tace ta fara gajiya da shidawa mutane aurena a yanzu, gwara kawai mutane su ji an daura. A iya cikin gida muka yi bikinmu ba tare da tara makota ko kawaye ba. Iyana yan'uwan mahaifina sai na Mama da suke gidan kawai suka san da daurin auren da aka daura a ranar Jumma'a. Jikina ya sha gyara ta ko'ina ba a taba yi min gyaran jiki ciki da waje mai kyau irin wannan ba, Mama ta kashe kudi sosai gurin gyara yarta mace da ta rage mata daya tilo wato ni kenan.

Ni kaina na san na gyaru domin fatar jikina har wani tsantsi take kamar auduga. Ranar assabar aka yi wunin biki bayan an yi jere ranar alhamis, na yi zaton ganin yan'uwa da dangin Zafeer amman ban ga ko daya ba, daman tun da aka fara neman auren bayan iyayensa maza da suka kawo sadaki, wani daga familynsa be sake leko mu ba. Wata kila har yanzu mahaifiyarsa da kannesa ba su gama da hukuncin Allah ba, domin komai kaddarrawar Allah ne, ya rubuta ba zan auri Zafeer a wacan karon ba sai a yanzu.

Na sha huduba na sha nasiha na sha gargadi tun daga kan Mama har zuwa kanenta da yayye fa kuma yan'uwan mahaifina, ba laifi kawata Zainab na ta yi ta min nasiha akan aure da zaman aure ta nan na fahimci har yanzu wasu ganin suke kamar ni nake kashe aurena dan ra'ayin kaina, ko da yake dole ne na musu uzuri domin ba kowa ya san dalilin mutuwar auren ba, ba kowa ya san abubuwan dake faruwa ba.

Tsofi biyu ne suka zo daukar amary sai kanwarsa daya da wasu yan mata da ban waye su waye ba. Mun yi tafiya sosai kamar zamu bar gari kamin mu isa gidan da ya kama haya, kaina a lullube aka shiga da ni gidan amman hakan be hana ni ganin kyau da gidan yake da shi ba. Sai karnuka biyu dake ta haushi ganin Shigowarmu. Anty Larai na rike da ni har cikin dakin Farincikina. A gafe gadon ta zauna da ni ta sake yi min nasiha yan'uwanta ma suka min sannan suka tafi aka bar ni da cousins dina sai Zainab da wasu kawaye biyu, domin ban gayyaci kowa ba sai wanda ya ga dama ya zo dan kansa.

Bayan iyaye sun tafi na daga mayafina na kalli dakina idanuwa dauke da abun da ya zame musu ibada wato hawaye. Akwai farinciki akwai jindadi akwai kwanciyar hankali da sakewa a auren wanda kake kauna, masoya ne kadai za su iya labarta haka. Ban taba samun kaina a yanayi da na samu kaina a yanzu ba, farincikina na ninku, samun cikar buri ba abu ne mai sauki ba. Take a gurin na sauka kan gadon na yi sujadar godiya ga Allah.

 Awwww finally yau dai buri ya cika Noor ta zama matar Noor halak malak

Cewar Zainab tana tsokanata. Sai na yi murmushi na shafa fuskata, for the first yau na yi aure na shigo gidan mijina ina mai farinciki da jindadi, kuma ina mai fata aure ne sai idan na mutu na bar shi domin bana fatanya mutu ya bar ni, bana sha'awar rayuwar zawarci bana burin aurena ya sakw mutuwa a yanzu. Mun kusa awa biyu a gidan sannan ango ya shigo tare da rakiyar abokansa biyu Mansur da Yusuf daman na san su tun muna tare da Zafeer.

Kusa da ni ya zauna ya kama hannuna ya rike yana dariya, Mansur na tsokanarsa wau tsohuwar soyayya yau ta tabbata daman hausawa sun ce da tsohuwar zuma ake magani.

 Noor muna muku addu'a Allah ya ba ku zaman lafiya da zuri'a dayyiba, kuma Allah ya hada kanku da abokiyar zamanki, dan Allah ku yi zaman lafiya ta yadda hankalinsa zai kwanta, kin san dai irin gwagwarmayar da aka sha kamin buri ya samu cika, to ki yi ma mijinki biyayya dan Allah

Na ji dadin Shawarar Yusuf, Mansur ma ya kara da nasa yana tsokanar Zainab wai ba A su siya baki ba domin ba ba su ni lokacin da suka bukata ba, kuma ni din a yanzu ba budurwa ba ce ba sai an yi sayin baki ba. Wannan kuma haka yake a iya sanina budurwa ake yi ma siyen baki ba bazawara ba.

 Aa za a siya bakin Matata mai tsada ne ko aure dari ta yi sai an siya

Zafeer ya amsa da kansa yana murza hannuna a hankali. Sai duk suka saka dariya, abokansa suka ciro kudin da zai kai 100k suka mikawa Zainab, ba sai sun fada ba na san Zafeer ne ya bada kudin domin cikinsu babu mai arzikin da zai iya kyautar 50k ma balle 100k. Zainab ta karba tana ta ihu da murna kamar ba matar aure ba, gaba daya ta cire auren ta aje a gefe sai sha'aninta take saboda bikina ne, abu ne da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login