Showing 204001 words to 207000 words out of 227321 words

Chapter 69 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1565

waya yar yarinya.

 Lafiya?

Ta aje plate din abincin dake hannunta. Yaya ya juyo ya kalleni.

 Wuce mana

Ganin bana da wata mafita data wuce shiga dakin na zauna, ya karfafa min guiwa fitowa daga bayansa na nufi gurin da Mama take zaune na zube a kasa na rike kafarta.

 Babu abun da nake yi saboda na bata ranku, hankalina da kaddararta ba kamar ta sauran ba ce shiyasa kuke ganina dabam, Mama Wallahi ban fadawa Zafeer wata maganar marar dadi ba, ban ce ya sake ni ba, shi ma dai kawai ban dace ba, dan Allah ki fahimce ni Mama karki dora min laifi, babu mai share min hawaye sai ke, Mama ki yi hakuri da yadda Allah ya tsara min

Tun kamin na farasa zangon da zaren lamarin sakin yake, na ji Mama ta rumgume ni ta fashe da kuka.

 Shi ma ya sake ki ko?

Yaya ya amsa mata.

 Haka ta fada min, kuma tana tsoron abun da zaki ce

 Me zan ce? Idan na dora miki laifi a auren baya, ba zan dora miki laifi a yanzu ba domin na san yadda kike son Zafeer, kuma idan har zai iya boye aurenki, be cancanci zama da ke ba

Ta dago ni daga jikinta ta share min hawayen idona.

 Indai addu'ar uwa tana aiki, Noor sai kin dace na gane kaddarar kenan, amman bakinciki baya dawwama, a kurciyarki kin yi ta shirme, ki yi ta bata min rai mahaifinki ma haka, wata kila a cikin bacin rai na yi wani furuci a gareki ban sani ba, idan har shi ne yake bibiyar rayuwarki ina rokon Allah ya yafe miki ya yafe min, kuma na yafe miki duk wani abu da kika taba min, na janye duk wani kalami da na taba miki marar dadi Noor, albarkar Allah, amincinsa da rahamarsa su zama a tare da ke, Allah ya kwantar miki da hankali ya yaye miki damuwa Noor, Allah ya baki wani gurin da zaki ji sanyi ki manta da dukan damuwa ni ma hankalina ya kwanta.. Allah ya miki albarka Allah ya miki albarka Allah ya miki albarka... 

Ta furta min har sau uku, lallai uwa rahama ce, uwa farinciki ce, uwa maganin dukan damuwa ce, uwa waraka ce uwa mai dadi, take yanke kun fa ya kun in ji Allah sai damuwar sakin da Zafeer yayi min tsoron abun da Mama zata fada ya yaye min lokaci daya. Na kwantar da kaina a cinyarta na rufe ido zuciya fess har ina jin kamar babu wanda ya fi dace da farinciki a yanzu.

 Alhamdullahi Allah ya kara miki tsawon rayuwa Mama

Yaya ya fada cikin shauki da jindadi, ina jin lokacin da Mama ta kai hannu ta shafa fuskata da hannunta mai sanyi.

 Allah ya hada kanku, ya yaye damuwa ko wace kala ce, duk abun da nake yi ina yi saboda ku gyaru ba dan bana kaunarku ba

Ina daga kwance a cinyarta na cika mata cinya da ruwan hawaye na farinciki. Ashe dai ni ma wata rana zan rabi mahaifiyata ta karfafa min guiwa na ji sanyi.

 Duk wanda ya cutar da ke, sai yayi nadama sai rayuwarsa ta fi taki shiga damuwa, bakin uwa lalle ko? To na daura miki shi daga yau Noor, Wallahi ba zaki sake bakinciki ba, indai addu'ar uwa tana aiki to Allah ba zai kunyata ni ba, Wallahi sai farincikinki ya mantar da ke damuwa Noor, Allah ya kwantar miki da hankali, na fara miki addu'a kenan daga yau har karshen rayuwata

A hankali na motsa kaina ina murmushi, ji nake kamar na tsaga cikinta na shiga tsabar farinciki da jindadi. Bayan komai ya laba ne Mama take tambayar saki nawa yayi min na amsa mata da cewar ban sani ba, domin be fada ba yace dai na tafi ya sauwake min dai kawai. Fita ta yi ta fadawa yan'uwan saboda su san halin da ake ciki, a take Yayanta ya fara dora min laifi wai Allah kadai ya san me na fada saboda ban so tafiya ganinsa ba.

Abun Mamaki sai gashi Mama ta yi ruwa ta yi tsaki gurin tare min laifina, da alama boye aurena da zafeer yayi ya fi komai yi mata zafi, domin fadar take tun da ta ji cewar ya boye auren yayi a boye ta san da manufa yayi. Har tana fadar ko da na zauna zan yi zaman kunci ne domin alamu sun nuna tsoron matarsa yake kuma ba dan Allah ya aure ni ba.

Duk yadda Kawu ya so ya tafi a shirya auren Mama sai ta hana har tana ikirarin ko da ya maida auren ba zata bari na zauna ba. Ta bangaren Baba ne dai ba su saurara ba sai da suka tafi suka samu Zafeer da zancen bayan an sallame shi daga asibitin. Sai yayi ta hada karya da gaskiyar abun da ban yi ba ya fada musu kuma yace shi dai ba zai iya zama da ni ba.

Da suka dawo sai suka rufe ni da fada, duk yadda na karyata basa yarda da ni sun fi yarda da zancensa saboda ni noor ce mai tambo kowa a zuci da ido. Na sha mamaki a ranar na fada musu ni da laifi wai har na tafi na ci mutuncin matarsa, kusan duk mazan da na aura babu wanda ya taba juyar da gaskiyar zance ya dora min laifi sai Zafeer. Kuma a cikinsu babu mai kyamata sai shi babu wanda ya aure ni domin daukar fansa sai shi.

Daga ranar na maida kur'ane abokina sallar dare ta zama majinginata, sai kuma hakan ya saukar min da natsuwa da kwanciyar hankali fiye da gidan auren ma. Wani abun da na sakawa zuciyata kuma ya zauna min shi ne ba zan sake yin aure ba, domin na gane idan wani yayi rawa aka ba shi kudi ni idan na yi duka zan sha.


KAREEM POV.

Ya dade yana kallon hoton yaron kama yake da shi sosai fari ne kyakkyawa kamar dai mahaifinsa.

 Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un

Ya furta yana jin sauyin yaron da bar duniya tun a satin da ya wuce amman ba shi da labari sai yau. Idonsa ya cika da hawaye hakkin yaron yake tunani idan sun hadu a gaban Allah ya zai yi da hakkin yaron nan me wace kalar amsa zai bada. Yara ma suna da hakki akan iyayensu kamar yadda iyaye suke da hakki akan yara sai dai na iyaye ya fi yawa.

 Ka samu abun da kake so Kareem, sai ka je ka kashe auren Noor ka aureta

Shi ne sakon da ta rubuto masa, domin a lokacin bata da labarin auren ya mutu ko yana nan.

 Miye hadin mutuwar yaron nan da auren Noor? Ashe har yanzu baki yi hankali ba?

 Ban yi ba, kai ka haukata ni, saboda kai komai na rayuwata ya lalace saboda kai nake kwance a asibiti yau, saboda da bakincikin na butulcin da ka yi min na kama hanya a dare, gashi na halaka kaina na kashe ana, saboda bakincikinka na dauki tsawon lokaci ban farfado ba, har mutane suna zaton na mutu, ka cutar da ni Kareem kuma hakki na ba zai barka ba? Rayuwata shiga matsala, zaka taba ganin farincikin ba zan tana yafe muku ba, kai da Noor kun ruguza rayuwata

Ta fashe da kuka Kareem na gama sauraren voice note din da ya biyo bayan sakon da ta aiko masa da bakuwar number ya rubuta mata amsa jikinsa a sanyeye mutuwar yaron ta taba shi sosai duk kuwa da kasancewar be yi rayuwa da shi kamar sauran yayansa ba.

 Allah yasa hakan ya zame mana darasi, ba ni da sauran wata alaka dake Safeena daga yau

Yana bata amsar yayi blocking din sabon layin nata. Ya aje wayar cikin rashin jindadi.

 Na yi kuskure, Allah ka hana na aikata yanzu na gane illar hakan na tuba Allah ka yafe ni, Allah ka so ni, karka duba tarin zunubaina na sani ni mai yawan tsabo ne mai yawan aikata ba daidai ba, na gane kuskurena na tuba ka yafe min Allah

Ya busar da iskar bakinsa be sani ba, da ba zai bari Safeena ta aje cikin nan ba, ba zai bari su kawo a ta mummunar hanya ba. Harabar gidan ya fito ya tsaya yana ta kallon gurin tsantsar nadama da damuwa suka yi masa kawaya.



*** *** ***

Wani kalar numfashi ta aje da karfi ta aje wayar dake hannunta a gefe tana kuka. Ji take ta rasa komai a yanzu saboda ta rasa Kareem, ta rasa aurenta kuma ta rasa anta ta kuma rasa lafiyarta tun da likotocin sun tabbatar mata da spinal cord dinta ya samu matsala, tun a wacan daren da zuciya ta debeta ta kasa hakurin zaman garin Kano ta kama hanyar Dutse da kanta bayan kuma bata taba tuka mota da nufin barin gari ba.
Idan ta tuna yadda mota ta kwace mata motar sakamakon overtake din da motar bayanta take kokarin yi har ya zama silar da ta bugu babbar motar dake dakon kayan masarufi sai ta ji abun ya dawo mata sabo.

Wani karin bakincikin shi ne, sati daya tayi a asibitin Kano amman mutumen da a sanadinsa ta rasa lafiyarta, ba shi da labarinta, a yanzu kuma da ta yanke shawarar aika masa da sakon mutuwar danta da abun da ya faru da ita, madadin ya tausaya mata sai yayi blocking dinta. Hannu ta kai ta shafa gefen kanta kanta da babu gashi ko daya saboda askin da aka yi mata bayan an mahaifinta ya saka an yi mata transfer daga Kano zuwa Dutse domin kula da lafiyarta. Gurin da ba a kwance dinkin da aka mata a kai ba ne take lalabe daga kwancen da take tana kuka.

Nadamar soyayyar Kareem take domin ita ce silar faruwar komai, butulcin da yayi mata yafi komai kona mata rai fiye da rasa lafiyarta da ta yi a yanzu. Har ga Allah bata yi tsammani Kareem zai gujeta ba, to a yanzu waye zai rabe ta? Mutumen da ya kamata ya hakura ya zauna da ita a kowane kalar hali domin ya fi kowa amfana da rayuwarta ya juya mata baya. Wata kila da zai dawo a yanzu zata aurareshi ta ba shi lokacinta, domin tana masa wani irin so nw da zata iya mutuwa domin shi ya rayu.

 Allah ka isar min a gurin Noor, da tuntuni kashe ki da na huta, Allah ka hana yarinyar nan farinciki

Addu'a take tana jin za a amsa mata, ta manta duk abun da ta yi, zina da aure, hakkin mijinta da na yayanta da na ubangiji, har tana sha'awar haihuwar shege, ta manta daukar hakkin rayuwa uku da ba su mata komai ba saboda selfishness irin nata a kokarinta na boye laifinta. Yan jagaliyar da ta dauka a daren ranar da Noor ta bar gidanta da recording din voice dinta ta biya su suka kona gidan mahaifin Noor a tunaninta Noor tana ciki har ita ta mutu. Har gobe mutanen ba su daina zuwa mata a mafarki ba.

Tun a ranar da ta aikata take cikin kunci da azaba na hakkin rai har yau da take kwance akan gado da bata da ikon juyawa, sai an juyar da ita.



NOOR POV.

Ranar jumma da nake cika wata daya da saki Kawu ya samu Mama da zancen komawarta gidan Alhaji wato mahaifin Abdull, a yadda na lura gaba daya rayuwar Mama bata yi dadi da zancen ba. Ba ita kadai ba ni kaina bana mata sha'awar komawa gidan saboda abun da Abdull ya aikata. Haka ta fada cewar tana ganin mahaifinsa yana tuna mata da Abdul ne tunawa da shi kuma tunawa da yarta ne.

 Amman ba shi ya aikata ba Hajara, kuma shariyar nan da kike ganin zaki iya da shi, wahala kawai zaki sha, domin yana da arziki zai iya wasa da shariyar yadda ya ga dama tun da ya san manya, ba ma abun alfaharinsa ba ne ace shi yana shari'a dake yadda yake babban mutum, kuma tun da kika ga ya nace ya ki ya sake ki to yana son ya wahalar da ke ne kawai

 Yaya ba zan iya zama da mutumen nan ba

 Ni kuma a ganina be kyauta ace ke kina gida yarki ma tana gida ba, kamata yayi ace daya daga cikinku tana dakinta, da zaki bi shawarata da kin hakura kin koma dakin mijinki, ita Noor ki barta nan ta zauna har Allah ya kawo mata wani mijin aure

 Zan duba yaya, ba akin ta mutane wai ance da barawo ya gudu, amman dai abu ne mai wahala

 Ki dai yi tunani ko dan mutuncin yarki da ke kanki

Da wannan ya fita a barta. Ni dai bana cewa kuma daman kuma idan iyaye suna magana ban isa na furta wani abun ba a yanzu. Na san matsayi na san limit dina.
Na yi idda na wata uku like every Muslim girl. daga lokacin sai na fara tunanin abun da zai dauke min hankali kamar karatu, abu makarantar islamiya wannan dole ce na sani dan haka dole na saka ta a lissafi. Boko ne kawai nake da tantama kamar ba zan iya ba kai nake jin abubuwa sun masa yawa, kuma ban maida hankali na yi karatun da farko da kyau ba kamar Hana gani nake a yanzu kamar zai yi min wahala.

Sai dai karfafa min guiwa da Yaya Nabil yayi ya saka na ji sha'awar karatun sosai kuma na ji kamar zan iya, idan ma na zauna ba wani abu zan yi ba sai zaman gida amman idan na hada da karatun both boko and islamiya zan kara ilmi kuma zan samu experience na rayuwa, kuma hakan zai rage min damuwa.

 Kuma karatun zai rage miki damuwa sosai, indai zaki iya to sai a nema miki, gashi Yayanki ma ya kusa gamawa, ke ma sai ki samu ko diploma ce ko nce ake cewa ko?

Mama ta fada sai muka yi dariya ni da Yaya

 Bari na bincika idan sun fara siyar da form idan kuma ba su fara ba

 Kai da zaka wuce jibi Yaya?

 Ko da na tafi ne zan saka abokina ya siya miki

 Okay wace makaranta?

 Wace kike so? Kuma wane course ma kike so tukuna

Na yi shiru alamar nazari.

 Ina son irin aikin da zan rika zaunawa kujera ina juyawa, kuma ina son aikin jarida

 Ai sai aikin jarida kam wannan baki naki

Mama ta fada sai muka saka dariya ni da Yaya. Haka muka yi hira har aka kira sallah magriba. After two days Yaya ya koma makaranta aka bar ni da Mama daman ya dade be samu hutu mai yawa irin wannan ba. Tafiyarsa da sati daya na cika wata uku da sakin da Zafeer yayi min, domin na cika idda ne da period ba da kirgar kwanakin saki ba.

Ina kwance misali karfe biyar na yamma wani yaro ya shigo kirana wai wani abokin Yaya Nabill ya aikoshi na zo na karbi sako, ba tare da tunanin komai ba na tashi na saka hijab dina na fito ina rike da wayata, sai da na shiga bangaren Kawu na sanar da Mama dake can tana hira sannan na fita, a tunani abokin Yaya Nabill ne ya zo da zancen karatu na domin ya fada min idan an fara siyar da form abokin sa zai siyo ya kawo min na cika. Abun da zuciyata take raya min dabam abun da idanuwana suka gani dabam.

Ban cancanci na juya na koma a ciki na ce ba zan yi magana da shi ba, domin be yi min laifin komai ba a yanzu, sai dai a yanzu ina kallonsa ne da irin idanuwan da nake kallon sauran mazajen duniya, domin na gane ba a gane rashin mutunci ko butulci a idon maza ko goshinsu, sai an zauna. Kallona yake da dan murmushinsa na kwarin guiwa har na karasa na tsaya gefensa.

 Barka da yamma

Ya leko fuskata domin na furta hakan ne a lokacin da na dauke ido daga barin kallonsa, na kasa sake masa fuska duk wani shauki da farinciki da nake ji idan na ganshi yau babu shi a tare da ni, saboda maza sun fita raina a yanzu babu wanda ke burge ni kuma babu wanda zai burge ni.

 Na bata miki rai ne? Ko kuma baki jidadin zuwana ba ne?

 Ba ko daya?

 Toh meyasa baki far'a? Ba haka na saba ganinki ba Noor, ko wani abun ya faru?

 Babu komai fa Kareem

A take yanayinsa ya sauya ya sauke ajiyar zuciya.

 Wata kila ni na bata miki rai ko kuma kin tuna da wani abu ne, ko a gida aka bata miki rai, ko ma minene I'm sorry amman bana son ganin bacin ranki

Na dan daga ido kadan na kalleshi, maza kenan idan ana waje a nuna maka soyayya kamar da gaske, shi ma yanzu da zan aure Allah kadai ya san kalar ayar da zai gasa min a hannu.

 If I'm not mistaking yau kike cika wata uku da sakin da Zafeer yayi miki? I count every second, every minute, every hour, every day, every month, a lissafina yau ne kwana casa'in da awa bakwai da minti arba'in da da hudu, da second bakwai takwas tara goma...

Haka yayi ta kirga dakikun yana kallon agogon hannunsa. I was surprised sanin aurena ya mutu ba abu ne da za a boye ba, but counting minutes, hours and day ya ba ni mamaki.

 Ta ina ka ji aurena ya mutu har kake kirgawa?

 Lokacin da kika kira Nabil yana tare da ni, tun daga lokacin na fara kirga har yanzu

 Meyasa kake kirgawa?

 Saboda na san lokacin da ya dace na yi magana da ke, gudun kar na taka dokar Allah a karo na biyu, bana son ki haramta a gareni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login