Showing 150001 words to 153000 words out of 227321 words

Chapter 51 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1517

ni dai dan Allah a zubar

 Kin yi alkawari?

 Eh, dan Allah a zubar

 Ki kwantar da hankalinki mana, na san abun da zan yi, kin san ina sonki sosai ai, ina son ki Hana, amman ki yi ta wahalar da ni, Wallahi da ace ke na fara gani ba zan auri yayarki ba...

Ban sake jin komai ba sai shesshekar kukanta kadan kadan. Tashin hankali ne be bari na sake jin komai ba ko kuma dai ba su sake cewa ba din. Na dauke kunne na shafa wuyana ina lalaben sarkar da babu ita a wuyana. Jikina ya fara rawa hawaye suka yi ambaliya a idona. Na shiga na same su a ciki na nuna musu na sa komai, ko dai wai ban ji daidai ba, ko dai gizo kunnuwa suke min. Na bar kofar na fara takawa na nufi dakina na shiga na hau gadona na kwanta na rufe ido na tsawon min biyu sannan na bude.

Wai ko zan ji cewar mafarki, amman ban ga alamar haka ba. Na mari kaina sai na ji zafin na tsara kunci na, tabbas gaske ne ba mafarki nake ba. Amman taya? Kanwata ce fa uwa daya uba daya, kanwata da mijina? Kanwata ta jini mai bina, kanwata da muka kwanta a mahaifa daya ciki daya uwa daya ta kawo mu duniya? Kuma mijina mijin da nake aure auren sunna! Mijin da nake dauke da cikin dansa ko diyarsa. Tun yaushe haka take faruwa?

Na mike tsaye na nufi madubi na sai kuma na zauna a kasa. Me na yi da na cancanci haka? Why me? Why? Kanwata? Jinina?

 Wayyo Allah na

Na dafa zuciyata sai wani irin kuka mai ban tausayi da taba zuciya ya zo min. Wannan abun yayi min muni ina ji a wasu gurare amman ban dauka abun zai zo kusa ni ba. Na tashi daker na koma saman gadon na kwanta jikina na rawa na takure guri daya na rumgume fillo, a wannan daren bachi be samu damar ziyarta idona ba, kunci be bar ni, kamin safe zazzabi ya rufe ni, filon da na rumgume kuma ya jike da hawaye na. Abdull be dawo dakin ba sai asuba, ina jin shigowarsa da lokacin da ya kwanta saman gadon ya lulluba...







Littafin nan ba kyauta ba ne. Biya ki karanta cikin aminci. Pay 500 to

Zenith Bank
Hadiza Abubakar
2451879008

And send the evidence of payment to my WhatsApp number 08036126660.

Be dade da kwanciya ba na ji nishanrinsa alamar bachi mai nauyi ya dauke shi. Juyowa na yi na kalli kwanciyarsa, ina mamakin karfin hali irin na a namiji a haka kuma yake kallo muna ta rayuwa a gidan kamar babu komai a tsakaninsa da Hana. Sallah bata wani dame shi ba daman ni ce mai tashi da wuri na yi, dan haka na sauko da kafafuwana kasa na nufi bandaki, wanka na fara yi sannan na yi alwala na fito sanyin ruwan da kuma ac dakin yana ratsani sai ya saka na dan ji sassauci a jikina.

Na zuciya kan na san har abada ba zan samu ba. Ni da farinciki mun yi bankwana. Doguwar riga na zuba na shimfida sallaya na sauke farali sannan na fara tasbihi. Ban daga sallayar ba har sai da na ji farkawarsa misalin bakwai na safe.

 Miyasa ba ki tashe ni ba gashi rana ta yi

 Ni ma ban farka da wuri ba

Shi kawai na iya amsawa na koma saman gadon na kwanta na lafe kamar mai bachi, domin har lokacin ban san me zan yi ba. Na nuna musu an san komai na rufe su da fada ko kuma na danna na barwa zuciyata komai na bar su da Allah? Amman zan yi? Ina jin abun kamar ba shi da sauki, ina jin zaba da radadin cin amanar da yar'uwata ta yi min fiye da kunar garwashin wuta. Ina jin da ya taba ni yana fadin.

 My soul ta so muje mu yo breakfast

 Sai anjima bana son komai yanzu

Na amsa hawaye na min zuba yayin da fuskata take lullube a cikin bargo.

 Okay, ba ki da lafiya ne?

 Lafiya kalau bana son damuwa dan Allah ka tafi

 Okay.. I'm sorry dear...

Ya fice daga dakin sai after like 40m ya dawo yayi shirin office.

 Bachin be ishe ki ba kenan? Ni zan wuce aiki sai na dawo

Bance masa komai har ya fita. Sannan na tashi zaune gaba daya na rasa me zan yi kaina ya daure abun yayi min muni. Sauka na yi saman gadon na fito falo na nufi windows ya na daga curtain ina kallon motar da Abdull ya shiga Hana kuma ta bude front seat ta shiga ta zauna. Hawaye ya sauko min a haka suke kallona? Yar'uwata ta zama kishiyata ta san sirrina ta san komai akan mijina.

Kusan a falon na wuni ina ta yawo ya kasa sukuni na rasa kalar tunanin da zan yi, kamin na samu natsuw????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ?  ar yankewa kaina shawarar da nake ganin ta dace da ni. Bayan ruwa ban iya sha ko cin komai ba har karfe biyu ta yi na rana na je na yi sallah na fito falo na zauna ina jiran dawowar Hana, domin ita ce mai dawowa da wuri Abdull sai biyar ko shida yake dawowa gidan. Na bata awa daya a zaune sannan ta turo kofar falon ta shigo da sallama na amsa mata ba tare da na bari ta kalli ido na.

Domin na yi kuka har idon ya kumbura, kai tsaye ta wuce dakinta, kaya kawai ta canja ta fito ta nufi kitchen kamar yadda ta saba sai na bi da kallo wai yanzu ita ma tana dauke da ciki kamar yadda nake dauke da shi kuma cikin mutum daya. Sai da ta shiga ta kunna gas ta dora ruwan zafi sannan ta tambaye daga can kitchen din.

 Noor me za a dora

Na mike tsaye na nufi kitchen din na shiga, sai na zame ta tana yanka lemu zata sha sai dai gani na ya saka ta tsayar da yankan da take.

 Lafiya? Me ya samu idonki?

 Kuka na yi

Ta aje lemun da wukar ta matso kusa da ni.

 Kuka dai? Fada kuka yi da Ya Abdull ne ko baki da Lafiya?

Na kalleta ina mamakin yadda take nuna min kulawa kamar ba zata ci amanata a bayan idona ba.

 Na san muna samun tsabani Hana, amman ina sonki ina sonki sosai, zuciyata bata taba raya min na cutar da ke ba, ni ba zan iya?

 Me ya kawo wannan maganar Noor?

 Ina tunanar da ke ne idan kin manta, Wallahi Hana ko rayuwata kika ce kina so zan iya baki, balle mijina zan iya mallaka miki Abdull mallakawa ta har abada Hana, Wallahi zan iya yin duk yadda zan yi na ga ya sake ni in ya so sai ki aureshi

Ta matsa baya tana kallona cikin tashin hankalin da ya bayyana a fuskarta.

 Me Abdull ya fada miki? Wallahi sheri yayi min

 Babu wanda ya fada min komai, ni na ji da kunena, na kuma gani da idona, kika hada kai da mijina yana ba ni maganin bachi saboda yayi tarayya dake

Ta daga hannu biyu tana yi min rantsuwa.

 Wallahi Wallahi Wallahi Noor ban hada kai da shi ba?

Na daka mata tsawa.

 To me yake zuwa yi dakinki? Kullum sai ya ba ni maganin bachi na sha sannan ya tafi dakinki kishiyata ce ke?

Ta girgiza kai tana kuka.

 Aa amman ba yadda kika tunani ba ne, Wallahi ni ban ci amanarki ba, Wallahi Noor ba son raina ba ne

 Haka ne, shiyasa ai yake tafiya dakinki har kuna hira kina tambayarsa yaushe za a zubar da ciki, ina dauke da cikinsa kina dauke da cikinsa wane irin wulakanci da kaskaanci ne wannan?

Ta zube kasan guiwoyinta tana kuka.

 Na shiga uku dan Allah Noor ki yi hakuri ki fahimce ni

 Wace fahimta zan miki wanda ta wuce wannan? Ko karya nake baki dauke da cikin Abdull ba ki tarayya da shi?

 Gaskiya ne ina dauke da cikin ina tarayya da shi, amman ba ta yadda kike tunani ba ne, ina son dan Allah ki fahimce ni

 Toh ina jinki fahimtar da ni

Ta kasa magana sai kuka take daman ai ba zata iya magana ba, tun da bata da kalaman da zata wanke kanta da su a gurina.

 Tun yaushe kuke cin amanata?

Nan ma ta kasa magana, sai na matsa kusa da ita na tabbatar mata da abun da shi ne tabbbatacce a zuciyata.

 Na bar miki Abdull har abada, na bar miki Hana, yau ba zan kwana da aurensa ba

Na wuce na shige dakina na fada kan gadona ina kuka mai karfi. Abincin da bata girka ba kenan ni kuma ban sake fita dakin ba sai da na ji motar Abdull. Tsanar hada ido da shi ne ta saka na fice daga dakin na nufi kitchen na tsaya a cikin har ya shigo.

 Bacchi kuke ne?

Na ji ya fada domin yayi sallama be ji kowa ya amsa masa ba. Sai da na tabbatar ya shiga dakin, sannan na fito kitchen din.
Dakin da Hana take na shiga na nufi gurin da takardunta suke na bude jakarta na dauko littafi na cire paper na dauki pen, sannan na kalli kofar bandakinta da nake jiyo kukanta na munafurci daman na san haka zata yi ai, karshen munafuki jin kunya.

Na shiga da kuzarina, domin na gama yanke shawara Wallahi ko auren Abdull ne rayuwata yau kam na shiryawa mutuwa domin ba zan iya kara awa daya da aurensa ba. Zaune na same shi sanye da suit dinsa na aiki da be cire ba yana duba wayarsa da alama wani abun yake kallo. A lokacin da na kalli fuskarsa sai na ji ban taba tsanar kowa a duniya kamar yadda nake jin tsanarsa ba. Kusa da shi na karasa na aje masa takardar da biron.
Ya kalli takardar da biron da na aje masa.

 Miye wannan?

 Me ka gani?

Na tambaya ina kallonsa cike da tsana da kyama.

 Takardar da biro

 So na nake ka rubuta min saki

Ya kalleni.

 Are you okay?

 Ka ji ni ai i mean it ka rubuta min saki na ce!!!

Na karashe zance a tsawace. Ya aje wayar hannunsa ya mike tsaye.

 Saki? My soul kin san me kike fada kuwa? Ba a wasa da wannan kalmar fa

Ya dafa ni sai na buge hannunsa ina tauna hakora ta cikin bakina.

 Wani abu kika sha yau?

 Eh... Na sha bala'i da masifa da wutar da zan amayar maka a yanzu nan idan baka sake ni ba

 Na sake ki kamar yaya me yake damunki?

 Kai ne kai kake damuna Abdullahi, na tsane ka, damba marar tunani dan duniya wulakantacce, barikin ta wuce waje har sai ta shigo cikin gidana? Sai ka hurumina da yar'uwata?

 Kina da hankali kuwa? Ni kike kira damba...

Ya daga hannu zai mare ni, a nan Allah ya ba ni iko da karfin iya rike hannun da dukanin karfina.

 Maci amana, karka sake tsinanen hannunka ya kai ga halattaciyar fuskata ma ci amana ka bi yaya ka bi kanwarta, haihuwar hasara

 Okay ta kwashe karya da gaskiya ta fada miki kin zo kina zargina da abun da ban aikata ba ko? Saboda tsaurin ido har ki kalleni kina kirana da suna kala kala ko? Ni fa mijinki Noor

Na tofa masa yawu a fuska.

 Allah ya kiyaye Allah ya kiyaye yanzu kam, da can amman ban da yanzu

 Okay rashin kunya zaki nuna min ko? To sai na ga idan akwai uban da ya isa ya saka na sake ki, kuma kika sake fada min wata maganar banza sai na ci ubanki yanzu nan

 Ubana yayi maka yawa, kuma babu wanda zai saka kaka kai zaka sake ni dan kanka, wato kai da yake namiji mai karfin hali dan duniya har kana da bakin yakata ko? Taya zaka ba ni maganin bachi ka tafi ko wane dare ka kwanta da yar'uwata sai asuba ka dawo ku ci amanata a tare kuma ka ce ba zaka sake ni ba? Wallahi karya kake Abdullahi

Ya nuna kansa yana murje ido kamar da gaske be aikata ba.

 Ni nake saka miki maganin bachi?

 Aa ni nake sakawa kaina, wanda ka ba ni jiya ya zube ban sha ba, ina kallon lokacin da ka tashi daga dakin nan ka tafi dakin Hana, na labe na ji abun da kuke magana a kai, har ciki za ku zubar

Na fashe da kuka domin ba ni da wani abun yi a yanzu kamar shi.

 Ba laifinka ba ne, laifin yar'uwata ne ita da ta ci amanata, dama kum jira wata kila gurin haihu zan mutu ai sai ka aureta ku zauna

 Innalillahi Wa'Inna Ilaihirraji'un

Ya sassauta muryarsa.

 Noor Wallahi aikin sheidan ne, kuskure ne aka samu, me Hana ta fada miki?

 Ban saurareta ba, kamar yadda ba zan saurareka ba, saki kawai nake so ka sake ni

 Ni ba zan sake ki ba Ina son ki Noor shedan ne Wallahi

Kalmar ina son ki ta saka na ji kamar da wuka a kusa na daka masa a sautin zuciya. Ya matso kusa da ni

 Abu ne da zamu tsaya mu rufawa juna asiri, ita yar'uwarki ce ni kuma mijinki ne, kuma ga cikina a jikinki Noor, Wallahi na miki alkawari ba zan sake ba

 Gobe zan tafi na bar muku gidan, ku cigaba da aikata abun da kuke har mahadi ya bayyana, ni dai ka sake ni

 Ba zan sake ki ba Noor ni ba zan sake ki ba, ni ban taba aikata komai ba sai a wannan karon da Allah ya kawo tsautsayi

 Karya kake, ba wannan ne karon farko ba Wallahi kawai dai ban gane ba sai yanzu, shiyasa tun kamin ka aure ni kake ta taba ni, da na yi magana ka ce gwada ni kake yi, ashe gwadawa kake ka gani idan ni yar iska ce na amince maka a waje, ka gama da ni ka tafi, da hakan be samu sai ka bijiro da maganar aure, da na samu ciki kuma sai na daina burge ka saboda ba auren Allah ba ne, auren sha'awa ka yi min. Sai kuma sha'awarka ta koma gurin kanwata jinina, ita kuma bata duba alaka ba ta yarda kuka taru kuka ci amanata

Na dafe zuciyata ina bakincin da ban fahimci wannan red flag din ba tun farko, ga kuma Safeena ma ai izina ce.
Ya dafe kansa ya juya ya juyo ya fara safa da marwa kamin ya samu tsayawa gabana a rikece har da fashe min da kuka.

 Dan Allah ki kwantar da hankalinki mu yi magana ta fahimta, sakinki zai bata abubuwa ne kawai, ina zaki je da ciki? Abun nan aikin shaidan ne Noor zai iya fadawa kan kowa, zan tafi na bar miki gidan har hankalinki ya kwanta amman ni ba zan sake ki ba

A take kukan ya yanke min.

 Ba zaka sake ni ba saboda kana tsoron kar a tambayi dalilin mutuwar na fadi cewar kai da yar'uwata kuka ci amanata?

Yayi kamar be ji ba dauki wayarsa yana kuka zai fice dakin.

 Ba zaka sake ni ba, sai na hada maka cewar dan da Safeena ta haifa maka yanzu ba jininka ba ne, an falkanta ne, ex-boyfriend dinta? Sai na fada maka dalilin da ya saka Safeena ta daina daga maka hankali akan aurena? Sai na fada maka na san Safeena irin wanin da baka yi mata ba? Sai na fada maka a duk lokacin da ka bar Kano tana tarayya da Ex dinta ne har sai ka dawo? Sai na fada maka Safeena ta taba ji min ciwo a hannu saboda ta yi tunanin Ex dinta kuma falkamta so na yake, saboda kishinsa?

Ya juyo ya kalleni kukan da yake ya tsaya.

 Kina cikin bachin rai ne, zaki iya fadar komai Noor na sani

 Ina cikin bacin rai, amman ba cikin gushewar hankali ba, idan baka yarda ba ka dauki yaron ka gwada jininsa da naka mana, ka cancanci haka ai, daman shege sai dan iska, a da har mamakin dalilin Safeena nake na aikata haka, ashe ta yi daidaita kai din tsohon shege ne

Ya daka min tsawa.

 Ya ishe ki haka yanzu kam ya ishe ki haka? Mace nawa take kama mijinta yana abun da be dace ba amman ta rufa masa asiri a zaune, balle ni da kaddara ce kuma ba ni kadai ba har da yar'uwarki, kusan ma ita ta ja ra'ayi a komai

 Wallahi ko kai ne dan autan maza na gama zaman aure da kai Abdull, ko ka sake ni ko na daga na kira uwarka a yanzu na fada mata abun da ka aikata da kanwata kuma na tabbatar mata cewar an da Safeena take shayarwa a yanzu ba jikanta ba ne? Domin ba jininka ba ne, na yarda idan aka bincika aka tararda tsabanin haka a kai ni kotu, ko dai so kake na kira kanenka da mahaifiyata ma fada musu? Kwanciyar hankalinka ka sake ni, Ba zan fadawa kowa abun da kuka aikata ba ni na bar ku da Allah

A fusace ya nufi takardar ya dauka yayi rubutu a kai ya jefa min a fuska.

 Ke ce da bakinciki ba ni ba...

Ya nufi kofa.

 Allah ya raba ni da bakinciki tun da ya raba ni da kai

Na fashe da kuka mai karfi. Na yi kuka kuka sosai kuka irin na macen da rauni ya mamayeta ta rasa makoma, saki nake so kuma na samu yanzu idan na koma gida me zan fadawa iyayenmu? Na fada cikina ina bakinciki da ban zaba masa uba na gari ba. A dakin na kwana, sai dai bachi be

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login