Showing 195001 words to 198000 words out of 227321 words

Chapter 66 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1527

saboda baki da kunya?

 Idan na guji Zafeer saboda talauci, ke miyasa kike aure shi? Saboda kin yi alo babu Mijin aure ko? Domin na san mai arziki baya son talaka, shiyasa aka fada mana ai kin ba shi shekara biyu, that's mean kin matso ki yi auren kenan sai kika same shi a arha

 How dare you talk me like that in my own house?

 Saboda kin bukaci haka, na fada miki ba gurinki na zo ba gurin Zafeer na zo

 Ya miki me? Zafeer ai ya gama dake yarinya talkaminsa ma baki isa ki wanke ba a yanzu get out of my house

 Aurensa nake ko be fada miki ba?

Ta mike tsaye tana kallona.

 Kam bantan uban nan...!!!

Da alama dai kamar bata da labarin aurena da Zafeer wata kila a boye yayi aure shiyasa ya dauke min kafa gaba daya, kuma ya kasa fada mata a inda yake ranar da ta kira shi ina gidan. A yanzu na gane dalilinsa na cewar na yi shiru idan yana waya da ita ko ma ya fita daga gidan gaba daya dan kar ta ji hayaniyata.

Upstairs ta nufa ta haura sama da gudunta, ni kuma tsoron lalata rayuwar Zafeer da aurensa ya kama ni, na tsaya a gidan jiransa ko dai na kama gabana na yi tafiyata? Na kasa tashi tsoro da fargabar abun da zai faru ya hana ni sukunin zama cikin natsuwa a katon falon, mai kama da daular larabawa. Ban tabbatar da gaske boye mata aurena yayi ba har sai da ya turo kofar falon ya shigo hankali a tashe.
Kamar be gan ni ba haka ya zo zai wuce ni ya haura sama har sai da na kira shi.

 Zafeer...

Ya juyo ya kalleni.

 Na'am ya kike wacece ke?

Kokarin yake ya nuna kamar be waye ni ba na lura da yanayinsa da kuma yadda yayi min tambayar.

 Kamar ya? Ni ce fa Noor

 Na sanki ne?

Mamaki ya hana ni furta komai. Dawowa yayi saitin da nake zaune ya tsaya

 Yanzu na gane ki! Me kike yi a nan?

Na mike tsaye da sauri jikina na kyarma domin tsawa ya daka min har na rasa ta ina zan fara.

 I thought tun rabuwar da muka yi a can baya na yanke alaka da ke? Waya nuna miki gidan nan me yasa kike bibiyar rayuwarta a yanzu, and ya aka yi kika shigo cikin falon nan?

Gaba daya ma sai na rikice, shim shirin film ne ake shiryawa da ni ko kuma dai littafi nake karantawa, wata kila kuma mafarki nake domin wannan be yi kama da zahiri ba.

 Tambaye ta domin tun da ta shigo gidan nan take fadar ita matarka ce, gaskiyar nake son na sani a yanzu, shiyasa na kira ka

Na juya na kalli Fanna dake saukowa daga stairs.

 Me kike yi a nan? Me kike so? Kin guje ni yanzu kuma kin ga na samu kwanciyar hankali kike kokarin ganin kin ruguza rayuwata? A mafarki muka yi aure ko kuma wani sabon makarcin ne kika shiryo

Na nuna kaina wasu hawaye masu zafi na sauko min.

 Ni ce baka sani ba? Ni ce baka aura ba?

Murya na rawa nake masa tambayarsa sai ya murje ido ya kara tabbatar da zancensa.

 Yaushe na aureki? Ko kin fara shaye shaye ne?

 Aa ban yi shaye shaye ba, ban taba shaye shaye ba, kuma bana fatan yi, amman zaka maimaita hakan a ranar lahira, na yi nadamar saninka a rayuwata, na yi nadamar soyayya da kai, na yi nadamar aurenka Zafeer...

Na juya gurin Fanna na kalleta idon cikin hawaye.

 Zafeer shi ya nuna min gidan nan, ni da Zafeer ma'aurata ne a yanzu weather you believe it or not, ya dauke min kafa saboda kin dawo, yace ba zai koma bangarena ba sai kin tafi, ya kama min hayar gida a bypass, ranar da....

Ban iya karasa furucin da na dauko ba saboda marin Zafeer da na ji a fuskata, kamin na maida numfashi ya rufe ni da duka, kamar be san inda na fito ba. Dukan namiji ba daya da mace ba, a take kamanina ya sauya, idona na hagu ya kumbura, bakina yayi kamar an kunsa min dutse a ciki.

 Ni ban ce ka kashe yar mutane ba, kawai ka amsa min abun da take fada gaskiya ne ko karya...?

Ban san irin amsar da ya bata ba, domin ban tsaya ya kashe ni ba, da rarafe na fito daga falon mayafin abayata a hannuna, ban tsaya daukar jakata ba, talkami ma ban saka ba na nufi gate, suka bude min na fice ban san ina zan je ba, ba kuka nake ba mayafin a hannu haka na kama hanya ina tafiya ina jin jiri na kama hanya ba talkami ba jakar kudi ba wayar da zan kira na bar komai a gida, mayafin abayar kuma na gagara yafawa na rike a hannu kaina a bude tafiya kawai nake.

Gaba daya na rikice mutane sai kallona suke na san suna min daukar mahaukaciya ne, ni ma dai ba zan iya shaida ba a yanzu ko ina da hankalin ko babu, kafa nake ta tafiya bana ma jin gajiya ko zafin hanya, har na iso a gurin mayan itattuwan nan da Kareem ya taba zuwa da ni, a gurin da ya labarta min labarin rayuwarsa kuskurensa da nadamarsa. Kusawa na yi ciki na shiga na isa har gurin da muka saba zama na zauna akan wasu abun zama na sumitin da aka yi a gurin. Sai a lokacin wani irin kuka mai tafiya da numfashi ya zo min.

Na kwanta a gurin an takure guri daya daman gurin zama ne ba kwanciya ba, ina kwance hawaye na zuba.

 Har abada ba zan taba jindadi ba, yanzu ina zan je? Gida zan koma? Ko na tafi na fadawa Mama? Me yasa Zafeer zai min haka? Ni haka zan yi ta aure ba dacewa...

Magana nake da kaina, ina karkartawa kadan sai idanuwana suka fara min gizo, Kareem nake gani tsaye a kaina yana kallona sanye da facing cap. Tashi na yi sannan na mike tsaye ina kallonsa a yanzu kam na tabbatar rayuwar yau gaba daya mafarkice. Na lumshe ido kamshin turaren mai dadi da ya gauraya da iska bin numfashina. Fuskarsa nake tabawa har lokacin hawaye nake even though idona yana rufe.

Ji na yi an rika hannun nawa an sauke daga imaginary fece din da nake tabawa, na bude ido na bi hannun da kallo har aka sauke shi kasa sannan na kalli fuskar Kareem, facing cap dinsa ya cire yana kallona.

 Waya taba miki jiki haka Noor?

Lallai mafarkin yau mai nauyi ne, slowly na zube kan simitin na zauna ina lumshe ido kamar mai jin bachi.

 Noor...

Na zabura na zabura na bude idon da sauri ina kallonsa.

 Subhanallahi, I'm sorry

Na ji ya fada.

 Mafarki ne wannan?

 Zahiri ne? Waya taba ki haka? Ina mayafinki ina talkaminki idonki jini ya kwanta, me ya faru da ke?

 Ban dace ba Kareem, Zafeer is the worse, ba zan taba dacewa a rayuwata ba? Ji yadda ya dake ni ya fadawa matarsa shi be sanni ba

Na fada ina kuka sai kuma na yi kauce shi na yi gaba zan kama hanya.

 Noor...

Ya sha gabana, iska mai karfi ya hura min a ido har sai da na rufe idon, ruwa mai sanyi na ji ya sauko daga saman kaina zuwa jikina, kamin ya karbi mayafin dake hannuna na karba ya rufe min kaina, a lokacin ne a gane ba mafarki nake ba zahiri ne. Sanyin ruwan ya dawo min da hankalina, bude idon na yi na kalleshi sai na yi sauri dauke kaina na bar shi a gurin tsaye na yi tafiyata. Ina fita gurin na tari Napep na hau, tun da na shiga nake kuka har muka isa gidan, gurin mai gadi na karbi kudi na ba mai Napep din sannan na wuce cikin gidan.

Ko da na shiga na samu Jakata da talkamina da wayana akan kujerar falona, da alama Zafeer ya riga ni isowa gidan sai dai ban same shi ciki ba. Na zauna a gurin ina ta rusar kuka har aka sauko daga sallah magariba. Bayan na yi sallah na kwanta a gurin ban daga ba sai da aka yi isha'i. Misalin goma na dare Zafeer ya shigo dakina saman gado ya hau ya kwanta ba tare da yace min komai ba. Da na dago na kalleshi sai na ga hararata yake da alama idan na sake kallonsa zai iya kara min wani dukan.

 Gani na dawo sai ki dafa ni ki ci

Tashi na yi na koma falo na zauna har dare ya raba ban iya runtse ido ba. Haushin karnuka na ji yayi yawa sai kuma karar bude gate hakan ya tsorata ni, na kalli agogon falon sai na ga karfe biyu ne da rabi. Da sauri na kashe wutar falon sai na ji ihun mai gadinmu, baya baya yi a lokacin da na ji ana kokarin balle kofar falon. Da gudu na shiga dakina sai na samu Zafeer a tsaye ya shiga bandaki ya rufe.

Saman gado na hau ina kallon kofar dakin cikin tsoro da tashin hankali marar misaltuwa. Kamar daga sama maza hudu suka fado dakin dukansu fuskarsu rufe da kyale wasu kuma sun kara da facing. Wutar dakin suka kunna dukansu suna rike da kami irin na jagaliya.

 Ke ina mijinki? Idan kuma baya nan ki fada inda za mu same shi

Na nuna kofar bandaki jikina na kyarma.

 Kwantar da hankalinki ba gurinki muka zo ba

Ina ji ina gani suka balle kofar bandaki suka shiga ciki, babu abun da kake ji sai ihun Zafeer, duka suka masa abun da yake duka duka na rashin imani, duka na rashin na rashin tausayi, duka na fitar hankali, sai da suka masa jina jina sannan suka fice ba tare da sun harare ni ba balle su taba ni.

Sai da suka fice sannan na sauka daga kan gadon jikina na rawa zuciya kamar zata fado domin tsoro, na nufi bandaki na leka sai na same shi kwance jina jina sai numfashi yake, gafen kansa sai jini yake sun yanki hannunsa bakinsa sai jini yake. Hannu na dora a kai na kwala wani irin ihu

https://chat.whatsapp.com/Hg8DYsNGb6R8F294cRUu3j

*Ina matan da suke son fara siyar da kaya masu sauki kudi, ina masu neman kayan Lagos kaya masu kyau da inganci Ummu Ahmad got you covered tana da kaya masu kyau da inganki order Lagos cikin sauki da rahursa. Ku yi join grp dinta domin siyen daya daya ko sari.*

*Ko kuma ku tuntube ta ta wannan line +234 803 235 0261*




*** *** ***

Gaba daya na rikice babu abun da nake sai ihu kai kace ba dare ba ne, na manta a halin yanzu babu wanda zai iya fitowa ya kawo maka dauki, balle kuma irin unguwar da muke zaune gidanje suna nesa da juna wasu ma ba a gama ba wasu kuma babu kowa a a cikin. Faduwa na yi ita ta haki jikina na rawa sosai gani nake kamar dawowa za su yi.

Daker na iya nufar gurin da wayata take na dauka sai kuma na rasa wa zan kira da tsohon daren nan. Can dai dabara ta fada domin na kira Mama two miss calls bata daga ba, na kira line Yaya Nabil na Nigeria shi ma be daga ba. Bayansu ban san waye zan kira ya kawo mana dauki da wuri ba. Na gwada kiran line Anty Larai ita kuma sai na ji wayarta a kashe, ban san kowa cikin abokan Zafeer ba, ba ni da number kowa balle na ce zan kira.

A familynsa ma babu wanda nake waya ko chat dashi balle na kira, wayarsa na nufa na dauka sai na samu tana da key, bandakin na nufa cikin tsoro da tashin hankalin da ban saba gani ba na karasa kusa da shi na daga hannunsa na taba thumb print na cire key din, na duba wayarsa na dauki number wayar mahaifiyarta na kira ita bata daga ba. Na kira duka kanensa nan ma babu wanda ya daga.

Fashewa na kara yi da kuka domin babu abun da Zafeer yake sai nishi irin na marar lafiyar da yayi nisa, ga jini na fita bakinsa da kansa, ga kuma yankuwa a hannunsa, har number da aka rubutawa Babyna da nake kyautata zaton number Fanna ce sai da na kira ita ma ba a daga ba. Na kira number wasu mutum biyu da nake zaton abokansa su na kamar hadin baki babu wanda ya amsa.

 Innalillahi Wa'inna Illaihirraji'un

Shi nake ta maimaitawa gaba daya na rasa me zan yi, zaunawa na yi abakin kofar bandakin ina kallonsa, sakarci da shashanci irin nawa zuciyata sai raya min take Zafeer mutuwa zai yi. Sy waye ma mutanen nan ma? Me yayi musu? Ko dai Fanna ce ta turo ayi masa duka? Wata kila kuma mahaifinta ne, saboda ya boye musu cewar yayi aure da ni. Shi ne abin da zuciyata ta fi raya min, sai idan kuma fada yayi da wani kamin ya iso gidan ya turo a masa duka ko kuma suka yi masa.

Da ace wani abu suka zo nema za su bukaci kudi ko abun kudi amman ba su tsaya daukar koma???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i ba suka masa duka suka tafi, kuma ni ba su taba ni ba, gaskiya da alama akwai abun da ya aikatawa wani ko kuma mahaifin Fanna ne, domin bana jin ita din kanta zata iya aikowa ayi ma mijinta wannan mummunan raunin da ya sauya kamaninsa. Dankwalin atamfa ta na saka na daure masa kai, na saka tissue na tare jinin dake fita bakinsa, na zauna a gurin ina ta Kallonsa tsorona daya kar ya mutu, gaba daya ma na manta da nawa dukan zugin jikin da nake ji da komai ya bace min.

Sai asuba aka fara maido mana da kira, daga kan Mama har Ya Nabil, ta wayarsa ma ana ta kira idan na daga na fada musu abun da ya faru da kuma halin da yake ciki sai hankalinsu ya tashi, domin a lokacin ya daina nishin da yake, sai na taba hancinsa kawai nake iya jin numfashinsa. Mahaifiyarsa ce mutum na farko da ya fara dira gidanmu tare da wasu maza biyu da ban san su waye ba suka dauke shi suka saka a Napep tana ta kuka, bayanta na bi sai na fita sai na ga irin barnar da aka yi na lalata gate din gidan, Mai gadin ma ban san a ina ya gudu ba domin babu shi babu labarinsa.


Aa tare muka isa babban titi amman babu abun hawa domin yanzu ake saukowa daga sallah azuba. Umarni ta yi min da na koma ita kuma ta kama hanyar tana ta tafiya tana kiran wani a waya. Ban yarda na koma ba domin ganin nake kamar dawowa zasu yi su min duka. Ina gurin Yaya ya kira ni na fada masa gurin da nake ashe yana gidan ma sai ganinsa na yi da police tare da Mama, da sauri na rumgume Mama ina kuka. Ya Nabil ya shiga haske jikina da wayarsa police din ma suka haska ni.

 Ke ma sun miki duka ko?

 Aa ba su min duka ba Wallahi ba su taba ni ba

 Ga fuskarki ya kumbura idonki ma haka

 Wallahi ba su taba ni ba

 To miye a fuskarki?

Mama ta tambaya na kasa amsawa.

 Akwai abun da kike boyewa ne Noor?

 Zafeer ne yayi min duka jiya

Na fada cikin kuka. Mama ta saka salati

 Shi Zafeer din ne yayi miki duka?

 Eh

 Me kika masa?

 Saboda na tafi gidan matarsa, ya ji haushin haka saboda be fada mata yayi aure ba

 What?

Cewar Yaya Nabil, police din da suke tare da shi suka ce.

 Ku yi hakuri dan Allah sawun giwa ya take ba rakumi, bari mu karasa gurin na duba kuma a tabbatar yana raye duk abun da zai biyo baya sai ya biyo

Su suka kawar da komai, muka dunguma gaba daya muka isa gidah.

 Ni ba su min komai ba, cewa suka yi ba gurina suka zo ba?

Na bawa police din amsa bayan sun gama duba gidan. Har haske ya fara fitowa tambayoyi suke min yadda mutane suka shigo da kuma irin kamamin da suke dauke da shi, har tambayar suke ko zan iya gane fuskarsu, na amsa da aa ko da na ga fuskar ba zan fada ba su ce ni na fada balle ma ba zan iya shaidar fuskar kowa a cikinsu ba domin sun rufe fuskokinsu gaba daya.

Ni da Mama da Yaya a gidan muka yi sallah asuba, Mama sai kallon fuskata take da hannayena da suke da jan duka har lokacin.

 Wai yanzu duk wannan raunin dake jikinki Zafeer ya ji miki shi?

Na sauke kaina kasa.

 Me kika masa? Tun yaushe ya fara dukanki?

 Jiya ne kawai...

Na labarta musu abun da ya faru ban boye komai ba.


 Meyasa baki fada min ba? Shegiya ce ke da zai boye aurenki? Ko kuma ita wanda yake aure ta fiki ne? Ko kuma ke ya maida yar talakawa marar gata? Miyasa baki fada min ba tuna ranar farko da ya mareki?

 Na san ko na fada ba zaki yarda da ni ba, zaki ce laifi na ne

 Dole a inda kike da laifi a baki laifi, amman gurin da kike da gaskiya dole a fada, babu kalar dukan da ubanku be yi min ba, amman ni ba zan yarda ayi ta azabarta da ke da duka ba, zan baki shawarar yin hakuri ko wane kala ban ce da duka ba, mu da muka haife ki kadai muka isa miki wannan

Police din da suke falo dayan ya leko yana bawa Mama hakuri wai ta sassauta muryata daga fadan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login