Showing 72001 words to 75000 words out of 227321 words

Chapter 25 - TAKI ZAMAN AURE BOOK COMPLETE BY CANDY.doc

30 Aug 2025

1558

ni bachi idan baya bangarena saboda na rage kadaici kamar yadda ita ma kanwarta Ni'ima take tayata kwana, na yi ta jiran tsammanin ko ko Hafiz zai leko bangare ya duba lafiya kamar yadda yake duba lafiyar Aisha kullum amman shiru ko da yake ni idan yana nawa bangaren yaransa ne suke tashinmu daga bachin safe da muke komawa, yau kuma yana bangaresu wata kila shiyasa be leko nan ba, ko kuma dai fushi yake ne har yanzu be sauko ba? Domin jiyan nan na bata masa rai sosai, to me ya kamata na yi na bashi hakuri? Ko kuma na share shi idan ya gaji ya zo? Ni kadai nake ta sake sake na na rasa makama. Shiru shiru be shigo ba matarsa ma bata leko ni har azahar gashi yunwa sai cini take daman na kwana da ita. Sai kusan uku na rana sannan ya fita ina ganin haka na jikina ya mutu kuma na gane kuskuren abun da na aikata. Falon na dawo na zauna ina jin wata azzababiyar yunwa gashi babu kudi hannuna balle na siya wani abu kuma kitchen da rufe balle na saffara wani abu. A wani taimako na Allah sai ga matarsa ta shigo da sauri bangarena da far'ata kamar kullum ni kuma na dube irin duba na yar'uwa.

 Kanwata ya kike?

 Lafiya kalau

Ta yi fuskar tausayi.

 Wallahi ina can amman zuciyata na tare da ke ina tausayinki sosai, na san kin sha yunwa yau ko?

Na daga mata kai.

 Ya ji haushina jiya ko? Ina son na bashi hakuri amman ban san ya zan yi ba, na ga har ya rufe kitchen din ya tafi da key din haka na kwana da yunwa

 Allah sarki, gashi ya rantse kar na baki abincin da na dafa, saboda na fada masa da ke zan dafa

Na ji babu dadi kamar na yi kuka kuma dai na daure kar na zubar da hawaye a gabanta.

 Aisha ki ce yayi hakuri

 Zan fada masa amman ke karki yi saurin ba shi hakuri ki zubar da ajinki, yanzu kin san yadda zamu yi ga kudi 5k ki tafi ki siyo abinci a waje ki dawo ki ci

Na zaro ido da sauri gabana na faduwa.

 Aa ba zan iya ba, jiya fa a gabanki na ce zan fita kin ga yadda yake fada shi ne sanadin ma duk wannan abun balle kuma ace na fita be sani ba

 To zaunawa zaki yi yunwa ta kashe ki Noor? Ya tafi da keys din kuma ya rantse kar na baki abincinsa kuma ya fita ya fada min sai bayan Isha'i zai dawo saboda gurin Hajiyarsa zai tafi na bashi abinci ya tafi mata da shi

Na kalli kudin sannan na girgiza mata kai.

 Ba zan iya ba, be kamata na fita be sani ba balle kuma ace siyen abinci zai yi fada idan ya ji

 Taya zai ji? Ba zan fada masa ba

Na girgiza kai na lake kafada.

 Ni dai ba zan je ba

 Shikenan ni daman saboda ina tausayinki ne, bari na aje kudin

 Sai idan ba a bawa mai gadi ya siyo min

 Maigadin kuma? Ai ba zai yiyu ki aike shi ba, ba zai ma tafi ba saboda gadi yake yi kuma zai iya fadawa Barrister

 Ni dai ba zan iya tafiya ba, sai dai ko ke idan zaki siyo min

 Ni kuma? Da ciki dako dako na tafi siyo miki abinci.? Ina laifina na tausaya miki Allah ya baki hakuri

Ta mayarda kudinta ya fice daga falon, ni kuma na koma na kwanta ina jin yunwar na min yawo a cikin, haka na kwana da wahala da kuka da bakinciki wata zuciyar na cewa na tafi na karbi kudin na siyo abinci domin ba ni da wata mafita bayan wannan, wata zuciyar kuma na fada min na tafi kawai na bashi hakuri kuma na fada masa ina jin yunwa ya ba ni key na dafa abinci domin alama ta nuna ba zai shigo bangaren nawa ba ya duba ni tun da gashi har dare yayi be shigo ba kuma ya dawo. Na tashi ina jin jiri na fita daga bangaren nawa ina sanye da atamfa riga da zane na shiga bangaren Aisha na samu yaranta suna ta wasa a falon ita kuma tana bare gia. Da far'a ta tarbe ni ta dakawa yaranta tsawa wai su gaishe ni haka suka gaishe ni jikinsu na rawa na amsa ina zaunawa, kana ganina ka san yunwa ta ci ni har ta gaji.

 Lafiya Amarya?

 Hafiz yana nan?

Yaransa duk suka kalleni jin na fadi sunan mahaifinsu kai tsaye.

 Eh yana nan? A kira Miki shi?

 Eh ina son na yi magana da shi

 Toh

Ta aje plate din giar ta tashi ta shiga dakinta, bata wani jima ba ta fito ta ce min.

 Yace ki jira shi zai yi wanka

 Tohm

Na amsa idanuwana kamar za su yi magana tsabar yunwa dake matsa min lamba. Haka suka bar ni a gurin tun ina jiran fitowarsa har na fara bachi....
Ko da na farka babu kowa a falon sai ni kadai, tashi na yi na kamar zan fadi na fice daga falon na dawo bangarena ina kuka. Indai har horo ne Hafiz ne Wallahi na horu daga jiya zuwa yau kawai...




**** **** ****

Yusura na kokarin aje remote din hannunta akan Center table ta dago tana amsa sallamar da Safeena take yi.

 Wa'alaikusalam

 Sannu da gida

 Yauwa sannu dai

Safeena ta maida kofar falon ta rufe ta shigo cikin falon ba tare da an yi mata izini ba ta zauna a kujera.

 Kin gane ni kuwa?

Yusura ta yi murmushi yake.

 Ta ina fuskarki zata bace min? Safeena Right

Safeena ta yi murmushi.

 Haka ne, na ga kamar ba jiya ba ne abun, ya gida ya karin hakuri? Na zo gaisuwar Momy ne

 Gaisuwa...? Ko dai murna?

Cewar Yusura babu alamar wasa a maganarta.

 Ah haba Subhanallahi ana murnar mutuwa ne? Hana dai Yusura sai kace wata kafura

 Na ga abubuwa sun yi ta faruwa ba ki taba zuwa ba, kamar haihuwata sau biyu ina haihuwa da Kareem amman baki zo mana barka ba, sai yanzu?

 Ban ji ba ne, amman ita mutuwa kin san ba a sanarwarta ni fa gaisuwa kawai na zo, ba fada ba ina tunanin yanzu duk mun girma mun zama manya har da yara

Yusura ta yi murmushi.

 Haka ne, baya gida amman ki jira shi ba jimawa zai shigo sai ku gaisa

Ta mike tsaye ta haye dama Safeena ta bita da harara tana jin wani masifaffin kishi na cinta. Yusura na shiga dakinta ta fara safa da marwa tana cizon bakinta gaba daya ta ma rasa gane hikimar zuwan Safeena gidan, ko bata rantse ba ta san Safeena ta yi farinciki da mutuwar Momy domin tana cikin manyan makiyanta da suka hana Kareem aurenta. Kasa zama ta yi har sai da ta hango tsayawar motar Kareem a gurin da ya saba tsayuwa sannan ta nufi kofar dakin ta fita, ta san be kamata ta nuna kishi ba domin ba son Kareem take ba, but abun da Safeena ta yi a yanzu kamar cin fuska ne da mutuncinta, kuma idan har Momy zata tsani Safeena ita kuwa bata san dalilinta na kaunarta ba, zuwanta kuma ya nuna ta jidadin mutuwar Momy if not ai tana da number wayarsa sai ta kira shi ta yi masa gaisuwa ko kuma ta same shi a wani gurin.



KAREEM POV.

A lokacin da ya faka motarsa ya lura da wata bakuwar mota fake a kusa da Entrance din shiga falonsu. Be raba dayan biyu ba ko dai yar'uwarsa ko kuma yan'uwan Yusura ta bangaren uba ne suka zo gaisuwa ko ziyara, ba tare da fargabar komai ba ya shiga falon. Yana rufe kofar Falon Yusura na saukowa ta karaso gurinsa ta karbi Keys din hannunsa da ledar hannunsa tana murmushi kamar ba ita ba, sai kuma ta sumbanci bakinsa.

 Sannu da zuwa...

Safeena na kallonsu ta ji kamar ta kama da wuta, Kareem kam be lura da Safeena sai kallon matarsa yake yana mamakin inda wannan ya samo asali.

 Ga Safeena ta zo gaisuwa

Ya juya ya kalli saitin da Safeena take zaune tana ci da wuta. Ya tako ya karaso gurin da take zaune da mamaki a fuskarsa.

 Safeena? Me kika zo yi nan?

 Gaisuwa...

Ta amsa daker numfashinta na gargada. Ya kalli Yusura sannan ya sake kallon Safeena

 Ashe Momy lokaci yayi

 Haka Allah ya so

 Allah ya mata rahama, ya bada hakuri zan tafi

Ta dauki jakarta ta mike tsaye ta fara tafiya kamar wadda ta rikice.

 Ka rakata mata, amman karka dade ka ji Babyna... Bari na hada maka ruwan wanka

Kareem ya kalleta sai ta sakar masa murmushi tana masa alama da ya amsa da gira.

 Okay...

Ya amsa With so many questions da yake bukatar amsarsu. Sannan ya juya ya bi bayan Safeena da ke tsaye jikin kofar tana jin komai. Rufe kofar falon yayi suka sauka kasa.

 Wannan ya zama na farko kuma na karshe da zaki sake tako kafarki a gidana, ba zan daukar miki wannan ba

 Me yasa ka yi min karya? Kace kai da Yusura baku zaman lafiya, kalli yadda ta tarbeka a gaban idona? Da far'a da soyayya, shiyasa gaba daya ka canja min, tun kamin Momy ta rasu daker na samu kanka yanzu kuma baka amsa kirana baka mayar min da amsar sakona

 Safeena ina cikin jimami na rashin Momy a yanzu, bana bukatar wata maganar, abu na biyu kuma ki natsu ki fara tunanin yayanki da mijinki ki cire ni a rayuwarki... Na gane baki da hankali shiyasa har kika tunanin kashe aurenki ki bar yaranki ki dawo gareni, yanzu kuma abun ya wuce da har kin kai ki tako kafarki a gida? Ba zan daukar miki wannan ba, ban hada iyalina da kowa ba

 Idan na ce zan aikata wani abu akanka Kareem baka ganewa, baka amsa kirana kana ta kokarin kauce min a lokacin da nake da tsananin bukatar saka ka farinciki, da kana kula ni da ban zo gidan nan ba, na riga na sabu da kai, na cutu da soyayyarka ba zan oya warkewa ba amman a haka a mahaukaciya kake kallona?

 Taya mahaifiyata zata hane ni da abu na aikata? Taya tana raye zata hana ni aurenki yanzu kuma bayan ta mutu kike tunanin zan iya cigaba da wani mu'amala da ke? Safeena wake-up ki cireni a rayuwarki and i mean it....

Ya bar ta tsaye a gurin ya rufe kofar falon ya shige ciki.

 Aurenta ya mutu ne?

Ita ce tambayar da Yusura ta fara yi masa a lokacin da ya shigo falon. Be tunanin ta yi labe ta saurari abun da suke tattaunawa sai idan zuwanta a gidan ne ya bata mamaki.

 Me ye ma'anar abun da kika yi?

Ta mike tsaye tana kallonsa.

 Irin abun da muka saba yi ne, a duk lokacin da baki suka zo, nuna cewar muna cikin soyayya da kaunar juna. Aurenta ya mutu ne ko kuma kashewa zata yi ta aureka saboda macen da ta yi mata karan tsaye ta bar mata duniyar?

 Miye matsalarki da hakan?

 Kana tunanin zan so abun da Momy ta ki? Har abada...! Ka fada mata kar ta sake zuwa gidan nan ba saboda ni ba saboda yaranka

Ta aje masa keys dinsa da ledar dake hannunta a kujera ta nufi stairs, binta yayi da kallo har ta haye sannan ya zauna yana kai hannunsa ya taba hancinsa.

 Kai Mata kuna da wuyar sha'ani

Ya sauke ajiyar zuciya ya mike tsaye ya dauki ledarsa da keys din ya haura sama ya shiga dakinsa...



#KhadeejaCandy
https://chat.whatsapp.com/Jd2OwsAcXE7EjI7NHeFQV0

Assalamu Alaikum...
Ina talata muku
KHADEEJA CANDY STORE >?p?=?L?
Muna siyar da Atamfa, Laces, Mayafai, Talkami da Jaka, Akwaituna, Kayan Kitchen, Zanen Gado, da kuma kayan kawata gida ko falo.

''&' 5???5??? ?5??? 5???5???5???5???5??? 5???5???5???5??? &'''


5???5?? 5???5???5???5???5???5???5???5??? 5???5???5???5???5??


*Book 2 - Last free Chapter*



KAREEM POV.

Misalin karfe goma sha daya na dare ya sauko da kafafuwansa daga kan gadon yana kallon dakin kamar bakonsa. Kamin ya juya ya kalli Safeena da ta fara bachi, ya samu gamsuwa sosai sai dai kuma jindadin ya wuce zunubin yana nan, ya sake komawa ruwa, daman abu ne mai wahala idan namiji ya fara aron hannu ya daina, ko da kuwa yana samun kulawa a gurin matarsa balle kuma shi. Mikewa yayi tsaye ya nufi bandaki, sai da yayi wanka sannan ya fito ya mayarda tufafin da ya cire ya dauki wayarsa dake ta ringing a dazun amman shaidanci ya dauke masa hankali ya kasa duba wayar ma balle ya amsa. Ganin Miss calls daga Daddy da Khadija da kuma Aryam ya daga masa hankali sosai.

 Lafiya?

Ya tambaye kanshi, Safeena ta dago ta kalleshi.

 Me ya faru?

Kamin ya amsa mata kiran Hafix ya shigo wayarsa, ya amsa da sauri ya kara a kunne.

 Hello...

 Kareem na dauka ba zaka sake komawa ruwa ba?

 Kamar ya?

 Saboda me zaka yi karya da ni ka je ka aikata alfasha? Kai da bakinka ka fada min yanzu babu ruwanka da Safeena saboda me zaka koma?

 Ka yi hasashenka akan kuskure bana tare da Safeena yanzu

 Ita kadai ce ta kai ka kebe da ita a irin wannan lokacin Kareem na san waye kai

 Shi kenan kuma idan na kebe da ita sai zuciya ta raya maka wani abun muke aikatawa?

 Muryarta ma haramun ne a gareka, idan kuma lada zaka samu sai ka fada min

Kareem yayi shiru yana kallon Safeena wadda ta tashi zaune tana kallonsa ba tare da ta rufe jikinta ba.

 Momy bata da lafiya kuma jikin yayi tsanani tana asibiti, an kira wayarka baka daga ba sun kira suka tambaye kana ina nace ina tare da kai, ka zo ka dauke ni mu je

Jikin Kareem yayi sanyi gabansa ya hau duka tashin hankali kuma ya baibaye shi jin cewar jikin Momy yayi tsanani.

 Okay

Ya furta da sauri sannan ya saka wayar aljihu ya nufi Wallet dinsa da keys din mota ya dauka ya dauko agogonsa be tsaya sakawa ba ya rike a hannu.

 Lafiya? Na ga hankalinka kamar ya tashi...

Ya juyo ya kalleta a wani yanayi da ya fi kama da bacin rai ko damuwa. Sai kuma ya hade yawu ya juya zai tafi.

 Hankalinka fa a tashe yake Kareem

Ta sake fada sai ya juyo ya fuskance ta.

 Kullum hankalina a tashe yake Safeena, tun daga lokacin da muka fada a ramen wuta ni da ke, nake tsoro da fargabar kar na mutu a haka, kullum burin Hafiz na kauce daga wannan hanyar da na dora kaina kuma he's right, ba abu ne mai kyau ba, yanzu gashi saboda ke an kai Momy Asibiti ba tare da ni ba, ina kokarin ganin na kauce daga sabo amman yau kin rusa wannan kudin na wa, kina amfani da weakness dina kina jefa kanki da kai a halaka, baki tunanin future dinki da yaranki da makomarki?

 My future is You...

Ta amsa da karfi sannan ta sauko daga kan gadon ta dauki tawul ta daura.

 Yarana mijina ba su ne a gabana ba, burina nake son samu muradina nake ta hasashe, kuma kai ne, Idan ma ka gaji da wannan rayuwar da muke yi toh mu yi aure mana, daman ai ba son Yusura kake ba, toh mu yi aure ni da kai muna son junanmu

Da mamaki yake kallonta.

 Auren da yake kanki fa?

 Zan cire na aje, na auri Abdull ne saboda rashinka, auren farko ka bi umarnin Momy ka yi yadda take so ita ma yanzu ai ya kamata ta so abun da kake so

Ya matsa kusa da ita.

 Saboda ita ta haifeni ba ni na haife ta, Karki sake fadin sunan Momy da wani abun a bakinki

Yana kaiwa nan ya fice daga dakin ya fito da gaggawa ya shiga motarsa maigadinsa har ya fara bachi ya tashi ya bude masa gate. Kareem ya fice da sauri gidan Hafiz ya nufo a bakin gate ya tsaya ya kira shi a waya ya sanar masa yana waje. Babu bata lokaci Hafiz ya fito daga gidansa take ta kamshin sabon fentin da aka yi yau ya bude motar Kareem ya shiga.

 Muna daf da samun matsala da kai Kareem, matukar baka rabu da Safeena ba, ba zan iya cigaba da zama da abokin da zai kansa wuta ba

 Barrister...

Hafix ya daga masa hannu yana rufe da fada rai a bace.

 Babu wani reason da zaka fada min, duk abun da kake ta son zuciya kake aikata shi, babu yadda ban yi ba saboda ka auri Noor, abun da nake maka hange rabuwa da Safeena da samu salama ta bangaren Yusura, amman ka watsa min kasa a ido, ka daure ni ka daure yarinyar nan a gurin ubanta, gobe za a daura auren nan amman idan na tuna da yarinyar nan bata so na hakan yana daga min hankali

Kareem be sake yunkurin sake furta komai ba, yana da tabbacin Hafiz ba zai fahimce shi ba nacewar baya son auren macen da bata sonshi kuma ba zai fahimci irin halin da yake ciki ba da har saka shi komawa ruwa tare da Safeena.

 Idan kuma ita Safeena kake so ta kashe aurenta ka aureta ya fi ku yi ta aikata alfasha haka nan

Wannan karon Kareem ya amsa with full confidence.

 Ba zan iya auren macen da ba zata iya tsare kanta da mutuncinta ba, ba zan auri macen da yarana za su zama b damuwarta ba, bana son mace mai irin tunani da zuciyar Safeena yanzu, ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login