Showing 12001 words to 15000 words out of 129912 words

Chapter 5 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5797

tun ranar da yakira tana bacci bai sakeba itama batayi gigin kiransaba Adu'arta daya Allah yasa kar suma Haidar dinta wani Abu rigarnan kuwa ta Aminullah da ita take kwana tana shakar kamshi Mu'azzam yaji dadin yada ta maida hankalinta tana karatu tace yasaya mata waya yace ah ah sai ta gama secondary school Dole ta hakura Dama Dan taga yan ajinsu duk sunada waya da kuma kawarta maheeda Dan koda wasa bata taba gwada daukar wayar Aminullah ta tafi makaranta da ita ba


✨✨✨


Yau ta kama weekend da misalin karfe hudu na yamma zaune suke bayan sunyi sallahr la'asar Rasheed jikinta zaune Mu'azzam ya kallesu yayi dariya " su watsime manya meyasa yanzu kika zama shiru shirune ko duk girmane murmushi tayi" yaya Dan kai ne banason sunan fah dariya malika tayi takaiwa mu'azzam dukan wasa" to kaji sai ka kiyaye ramawa yayi " kuji haka kawai kitadamu gajiya dariya suka ba teema" ni dai bari natashi na tafi makaranta shuriem zukuje kai ya girgiza mik'ewa tayi tashiga bedroom ta saka hijabinta wayarta taje inda take boyewa ta dauko taga Aminullah yakira har sau biyu idanu tazaro zama tayi tana jira ko asake saida ta kwashe Rabin awa takasa tafiya islamiyyar ga lokaci ya shige kiran ya shigo saida ya kusa tsinkewa ta daga ta Kara kunne cikin nutsuwarta da zakin muryata tayi sallama ta gaishesa ashgwab'e kwanci yayi ya rufe idanusa ya sabke ajiyar zuciya inajinsa shiru nayi bansake maganaba can naji yace"My Teemana ykk? yada yayi maganar yasa naji wani iri na daure nace" lfy amma kadena cewa ni takace please sansanyan murmushi yayi " OK naji my zahara kwana biyu bana garine amma ko kinemeni ko my ashagwabe nace " yo ni ina zan nemeka meye hadina da kai da fatan My Haidar na lfy? " eh to wayasani dai idanu nazaro bakina narawa nace" me... ka... Masa? murmushi yayi mai Dan sauti " ya kin canza shawara zaki rabu dashi ko. shiru nayi " wlh duk inda kika shiga inada labari ki taka asannu duk yabi ya baibayeni da wata irin voice mai dadi shiru nayi ina sauraran sa har ya gama maganarsa harda sharuda ya gindaya mun anutse tamkar bayaso yake magana ajiyar zuciya na sabke" OK naji yanzu zan tafi islamiyya sai nadawo baimun magana ba ya tsinke kiran agagauce na shirya na boye wayar na fito


" yaya mu'azzam sai nadawo" kanwata naga fah guri ya kure" eh bari sai naje ko fatiha na samu anty sai nadawo na fadi ina ficewa, tafe nake cikin nutsuwa ba'a ganin fuskata sai idanuwana niko dama ba niyar zuwa islamiyya nayi murya Aminulllah ce ta tsumun zuciya tasa naji ina son ganin My Haidar na amso kudin hannusa nazo nashaki kamshinsa dan yau Aminullah ya tadomun tsuman son Haidar hanyar governor house na dauka dayake babu nisa cikin unguwa daya muke kaf na gama waiwayena banga uwayan jarababa naji dadi lokacin danazo ba'a fara raboba ance basuna shida iyalinsa muna zaune misalin karfe shida mukaji jiniya ta karde layin baki daya hankalina na gun har aka bude musu hamshakin get suna ta shigewa ciki gidan wulleliyar motar da tafi sauran haduwa tana tsaye kofar get din bata shigaba ko ina jami'an tsarone da sojoji suke shawagi yau duk atsorace nake wani murdadan kato nagani


Ya fito ya bude motar kafafunsa ya fara fito dasu kafin uban jikinsa idanuwana na lumshe na bude dan yau my Haidar yayi mugun yin kyau gashidai zaikai 50 year gashi ingarman namijine kyakyawa ajin karshe akyau kana ganinsa kaga bafulatanin asali gilashine baki manne kan fuskarsa saidai fuskarsa babu walwala alamar miskilancin ya motsa amma duk da haka yayi kyau sosai wata danyar shaddah ganilah ce jikinsa farace tas anzuba mata zare bleu ina cikin kallonsa naga wata mata fara yar lukuta kyakyawa saide tana dauke da ciki kyakyawace zata kai 35 year kyakyawar fuskarta dauke da murmushi tana rike da yarinya fara kyakyawa yar kimanin 7 year jami'an tsaro na kewaye dasu ya kamo hannuta suka nufo gunmu jinayi dama banzoba raina ya bacci yada yake rike da hannuta kwalla ta taru idanuna na maida kullum ka idarsuce sai ya basu sadaka ya hana akorasu saide an saka matakan tsaro akwai na'ura da take lura da su ko da akwai me niyar mugunta ya boye wani Abu ajikinsa zata gwada suna isa suka fara bamu sadaka daya bayan daya yazo daidae guna naji gabana ya tsananta faduwa zarazaran hannuwansa ya begu ya bani sadakar nashiga rudu ban saniba na hado da hannusa ina kallon kwayar idanusa da sauri ya janyen hannusa yanajan tsaki yana goge hannusa fuskarsa babu alamar rahma daket ya karasa


rabon ya tafi yaja hannu matarsa mafi soyuwa azuciyarsa kallonsa tayi " my man meya faru shiru yamata sanin halinsa bazai taba bata amsaba tayi shiru security na biye dasu Rauda na rike da hannu bintu tace"Dady angama rabamusu ne? " cikin zazakar murya yace" an gama baby motar suka shiga baby tana GABA gun direba bintu ta kwantar da kanta kafadarsa kallonta yai ya daga mata gira. yasa tattausan hannunsa yana shafar cikinta " my man wa ya tabamun kai ko masu amsar sadakane NASA ahanasu zuwa hannuta ya kamo ya saka karamar yatsarta bakinsa yana tsotsa shiru tayi dan tasan bazai taba fada mataba suna shiga gidan naga haduwarsa tamkar Aljannar duniya fitowa sukayi ya dauki baby yana rike da hannu bintu matarsa mafi soyuwa azuciyarsa baya iya hadata da kowa aduniya cikin isa da izza yake takunsa tamkar shekaru basu jaba wata hanya sukabi suka nufi wani hadaddan parlo da sallama suka shigo parlon yayi Ashe ganin dare nakeyimasa tsawa naji bintu ta dakawa wata mata " ke ban muku kashe kubar duk wani aiki mutikar my man zai shigoba kar shegiyar da ta kara tsayawa aiki? "Hajiya ayi hakuri muneerat ce tace nazo na gyara gun da suka bata " ok bacemun da gani da gudu matar tabar wajan dan shi ko kallon inda macan take baiba hannu bintu ya kamo suka karasa shigowa tafkeken parlon kyawawan matasan yara su ukku mace daya maza biyu suka tarbesu cike da murna rumgumesu sukayi suna dariya ya kalli Asif da mukutar " Oya kuje kuyi Alwalla kuzo muje masallaci lokacin sallah ya kusa my Munee keko kiyi agida keda my Raudana baki dayansu suka nufi bedroom suna dariya ya wulga ba kowa ya dauki bintu cak sai dariya takeyi ya nufi bedroom dinsa" washhhh my bintuna zaki karya Aliyun ki keda baby ya fada yana kiss din wuyanta dariya tayi " Allah my man na kara nauyi ko kai ya daga bai sake magana ba suka shige bedroom don shirin yin sallah wacce ko kiranta ba aiba Ka idarsa ce haka shirin yin sallah tare da iyalinsa tun kan Akira,


ina ganin sun shige gida na sabke ajiyar zuciya na Mike wata, namun magana ko saurarata ban ba na tafi ina farin cikin ganinsa ga kamshinsa na shaka ga ido hudu mun hada dashi ina mamakin yada masha Allah yakeda cikar halita tsarinsu zaizo daya da Aminullah har farin saide kowa kamaninsa daban har bansa wa, yafi dadin muryaba tafe nake raina fari tas na cire katon hijabin na bar karamin murmushi dauke kan fuskata cikin zazakar muryata nace" saini teema ta gwamna kudin sadakin ka kake bani da hannuka ina sonka ko bazaka soniba sauri na fara ganin magarib takusa ina dab da isa gida dan na gama gangarowa kawai naci karo da dan ladi a mashin dinsa da katon daron namansa agaban mashin din sai baki yake washewa na karkace zan wuce ya tare hanyar da mashin Dole tasa na tsaya karan motar da najine aguje yasa na waiwaya gabana na faduwa dan namanta kashedin da Aminullah ya gama mun dazu kafin na fito atosrace nake bin motar da kallo dan ladi ya tsareta da idanu sai lasar baki yakeyi dan hijabin yayi karami sosai ya bude baki zaiyi magana ne.....✍🏻


















Rahma ce ummu fareesa😘


✍🏻✍🏻✍🏻
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*






*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________


*Written By*
Real Ladingo😉
Yar mutan Niger




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*




*🙏🏻🙏🏻🙏🏻Please kudaina kirana ko turamun sakon tambaboyi Akan wanene wannan Aminullah wai. Dan Allah na fadamuku yo ina kuka taba ganin anyi haka abun da zai faru acikin labari kuma nabaku shi kafin lokaci yayi hakuri zakuyi kubiyoni cikin labarin har na warware muku zare da abawa masu cewa idan kun turo sako bana mayar muku saboda Allah tambayar kuce batada Amsa shiyasa amma duk da haka Real Ladingo Rahma ummu Fareesa yar mutun Niger 💃🏻😂🤣🤣😆Wallahi ina yinku ina sonku ina kaunarku kamar yada kuke son matar gwamna I love you🌹 irin mazga mazga dinan Ana kyawun tare😘🤝🏻🤝🏻😘*








*DEDICATED TO*
My Shafancy






*Bismillahir Rahamanir Raheem*






*Page* 6⃣




.....dan ladi na shirin magana yaga mota ta tunkarosa kamar zata takesa da sauri ya matsa har zufa ta fara keto masa shuuu motar ta fice harara motar Teemah tayi taja tsaki ta gyra tsayuwarta tana harara dan ladi dariya yayi " watsime bari kuci abunku ki more ya zage mata tsinka biyu na nama Ashe baki komaba kauye nifa ranar naga wata har zan tsaya na tuna warsu fah mai gadin gidanku yace kin koma kauye wlh warsu mugune bakin ciki yake miki dan karki aureni na rika kawo miki kashin miya kinsan mu mahauta bamu barin matanmu da kwadan nama anjima zan bullo muzanta ya bata takardar naman hanci ta done ta had'e face" amma Allah ya isa tsakanina dakai wlh tunda na tsallake shairrin su nawalu mai goro da lado mai kifi to Allah kaima nafi karfinka mugu wato ka barbado magani a nama ka kawomin naci ni mayya na rika binka ko wlh kana neman dauré kanka agarinan wai watsime to inama kasan wannan sunan ko akauye sai kace Teemah amma saboda bakin ciki kake batamun sunah miyau ta tofa masa a fuska ta zuba da gudu amma tana gaba kafin ta shige gida motar tasha


gabanta wannan katon ya fito " ke wlh Oga yace ki kiyaye yanzu ma dan baya fita wannan lokacin ne kuma na daukar masa komai acikin camera kiyi hankali da tsayawa da irin mutanan da ko baruwan Flowers oga bazai sa suba hararasa nayi na rike kuguna " wlh bari kaji ko Ogan naku bazai juyaniba tunda ba hadina dashi aniyarku ta biku kuma sai na hadaku da My Haidar kansa ya kada dan ya razanata ya nufota da gudu na tura get na shige motar suka shige suka jata da karfi saida nazo kofar parlo na tsaya ina maida numfashi nutsuwata na gyara na tura kofar na shigo da sallama yaya ma'azzam zai fito " watsime sai yanzu kin jima har ana shirin sallah "yaya nifa banason sunan nan nayi fushi dariya yayi" to yi hakuri ya fada yana ficewa, murmushi nayi na shige " Fatima sai yanzu? dariya nayi naje kusanta na zauna" Aunty yau na dade ko momy zo mugaisa Aunty kinga yaya ko? " tau meyayi ya fadi sunan ko? " hmmm Ashe kin sani Shoriem wlh sai na fara cin gidanku idan baku zuwa islamiyya " oh mama zasu fara ai " ni nashiga nayi sallah amshi momy amsarta tayi Rasheed na biye dani ina zuwa nashiga bathroom na dauro Alwalla na fito " Rasheed maza zo muyi sallah gwara ka koya tayar da sallah tayi,


tana gamawa ta gyara zamanta ta janyo Qura'an ta fara karatu Rasheed yana mata sururu bata saurareshi ba taci GABA da karatunta har saida aka kira sallah isha'i ta rufe Qura'an ta Mike ta tayar da isha'i, tana gabamawa tayi sujada tajima goshinta akasa tana kai kukanta gun Allah dan akwai abinda ya cinkushe mata azuciya gaskiya ko ni watsime ta burgeni saboda akwai ibada dagowa tayi ta daga hannuwanta nanma tajima sosai ta shafa fatiha ta Mike ta cire hijabi ta haura gado "Rasheed jeka gun Aunty yanzu zan fito kaji dan kirki " to na tafi da gudu ya bude kofar ya fice wayarta ta cire bankadan matashi aikuwa yanzu Aminullah taga kira har biyu jitayi tana son jin muryasa mai dadi dailing din lumber tayi bugo daya yayi picking shiru tayi batace komaiba sansanyin murmushi ya saki cikin amon muryasa mai dadi yace" My zahara ykk? idanu na lumshe naji kamar my Haidar dinane " hello My Teemah kiyi magana ai naga duk abinda kukayi da mai nama " to ina ruwanka ai gwamma shi idan bazai cutarmun da my haidar ba wai mene zaka bani kakirani? " love zan baki ya fadi cikin wani irin Salo da wani suna mai dadi da yafada k'asan makoshi duk diriricewa Teemah tayi ashagwabe nace "Aminullah please kafita rayuwata kana yaudarata dayawa zaka dauki alhakina ka daina mun yanayin my Aliyuna komai kayi sak shi kana ruramun wutar kaunarsa azuciyata meyasa komai naka yake satar NASA ko dan ka cutar dani nakai karshan maganar ina sakin kukan shagwaba tunda ta fara magana ya lumshe idanusa yanajin wani yanayi na daban da bai taba jiba akan diya mace jiyake sonta zai iya kasheshi kukantane ya dawo dashi haiyacinsa


"My zahara please bari kukan wlh hankalina atashe yake idan kina kuka baki kusana bare na lallabaki na shanye hawayenki Dan banaso suzama asara komai baki tsada gareshi agurina please my heartbeat yi shiru kinji to me zai hana ni ki soni tunda muna ruwa dashi wlh ina mugu mugun sonki da kaunarki tsawon shekaru biyu kenan, ki daina kukan my Rabin Raina cikin shashekar kuka nace" Aminullah ni bazan sokaba zuciyata ta mutum dayace duk bazan samesaba murmushi ya saki" ok yi shiru kuma idan bakiyi shiruba to yanzu zansa amsa, wani abun cutarwar idan kina musu ci GABA da kukan " nayi shiru ni sai anjima inada abunyi" ok Matar gwamna zan kiraki zuwa can dare kinji zahara haskena baki na turo " to naji amma dai bakada gurbi aeuciyata, kitt na kashe Kiran na boye wayar kasan pillow na sabko daga saman gadon na gyara fuskata na fito parlo " Aunty baku nemana? dariya tayi" ai Rasheed yace karatu kikeyi? " eh na gama yaya yau nasami ice cream kuwa? dariya yayi" yau bazaki samu madara mai sanyiba yarinya " Aunty kice yaya yasamun ice cream dan Allah kuma abarcewa madara mai sanyi ai yanzu kan mage ya waye na fadi ina langwabe kaina


" ni ba ruwana kunfi kusa gake gashinan dariya yai " ok zan kawo miki aban abunci naci ko kan dining muka nufa mudukanmu kowa yaci abinda yakeso dayake kullum idan yaya na gari girki kala uku Aunty takeyi bayan mun gamalane mu'azzam yace mushirya zamu tafi can gidansu zuwa nayi na shiryo cikin abaya doguwa Riga da gyalenta ina fito ni suke jira muka fito harabar gida muka shiga mota ina baya nida su shuriem sai dariya Rasheed yake sani saida muka biya aka sai mana ice cream mukasha muka more akofar gadan yayi parking muka fito ina rike da hannu yara muku shiga da sallama muka shigo parlon innah sahiya na zaune " ah maraba da baki sannunku da zuwa maraba har kasa Malika taje ta duka ta gaisheta nima nayi yada tayi na gaishe " ah Fatima yan mata idan Mu'azzam baya gari baki neman muku mik'ewa mukayi muka zauna saman kujera yaya yazo kusanta ya zauna ta zungureshi akai" innah me kuma nayi? " ba komai kaga kai Rasheed kuzo mana mu gaisa gunta suka zo ta hadasu ta rungumesu" innah ina Abba kuwa? " wlh shida malam zakari suke tare baka kirashi awaya zaku zoba ko? " eh ai jimawa zamuyi ya iskomu " Fatima ina karatu ana yi da kyau ko? " innah munayi munkusa fara jarabawa ma" to Allah ya taimaka ya bada sa'a " Amin innah " amsomun Aisha mugaisa itama naga irin na Shuriem ne ko sai rigima amsarta nayi na kaita aikuwa ta kiya ta kafa kuka Malika dariya kawai take musu Dole na maidota gun uwarta, hira mukayi sosai har abban su Mu'azzam ya dawo sai tsokanata yakeyi wai tsoho za'a auramun nayi ta dariya munjima agidan sai karfe goma da rabi muka dawo gida koda mukazo bacci yaci idanuna atsaye namusu sallama na shige bedroom dina wanka nayi agurguje nasaka rigar bacci na Haye gado wayata na duba Aminullah yace zai kirani bai kiraniba tsaki naja na kasheta gaba dayanta nayi kwanciyata ina Adu'ar bacci bajimawa barci ya saceta


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


zaune take bakin makeken royal bed d'in Mai girma Aliyu gwamna cikin wasu kayan bacci masu masifar kyau da tsada masu sulbi farare tas sai zuba kamshi takeyi tayi kyau mutika cikinta ya fito sosai game takeyi da wata hadadiyar wayar Aliyun sai murmushi takeyi dan ta kware wajan iya wannan game din kofar bathroom ya bude ya fito dauro da towel jikinsa na tsigar da ruwa hannusa daya dauke da karamun towel yana goge jikinsa ya kalleta baice mata komaiba ya murmusa kadan kallonsa tayi " my man? gira ya daga mata ya tambayeta da idanu menene dariya tayi" my man yau miskilancin yayi yawa komi sai ta idanu ta fada tana Mik'ewa taje ta rumgumeshi ta baya ta ta zuro hannuwanta tana shafa gashin kirjinsa murya can k'asa yace" my bintuna bari na shafa mai mukwanta kinga da Asubah tafiya gareni ko? " my man to ba kai bane kaki amsawa murmushi yai " my tauraruwar zuciyata na amsa na'am my bintuna ji yada kike zunguremun babyna dariya ta kyalkyale tayi masa kiss tsakiyar bayansa ta sakeshi ta koma ta zauna ta dauki wayarsa taci gaba da game dinta shiko ya goge jikinsa ya shafa mayukansa masu azabar taushi da dadi ya gyara sumar kansa gashi luf kwance sai sheki yakeyi bakikirin sumarsa mai kyau ya bude wardrobe ya ciro kayan bacci irin na bintunsa Riga da wando ya saka ya fesa shegen turaransa mai sanyin dadin kamshi ya haura saman bed d'in " my bintuna zo kiji wani zance mai dadi " my man

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login