Showing 48001 words to 51000 words out of 129912 words

Chapter 17 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5808

takema Malika ta hanata rawar gaban hantsi ciki suka shiga da ita teemah ta zauna bakin gado tana harara maheeda"sai ki zubar da ruwa ak'asa kisha dariya maheeda tayi" Allah ya baki hakuri bani nakai zomonba rataya aka bani gashi kinja mana an fasa kidan baki daya kursu zama tayi ta rabka tagumi dan tayi takaicin rashin kwasar shoki gaban hayyo Malika tace" kursiya tashi kije kuyi sallama da mijinki da iyayanki ki dauko kayanki da na danki yan daukan amarya sun kusa shigowa gari ai cikin farin ciki kursiya ta Mike tana dariya ta fice teemah ta tab'e baki Malika tace da maheeda


"ki sata a hanya dan naga har yanzu da saura ta fada tana ficewa daga dakin teemah tace" ni wlh banji tafiyar yau my mahee kuyi gaba zanzo ta fada, tana lumshe idanu dariya maheeda tayi hanne tace" wai da gaske baza'aje daniba haba watsime wlh ba'a kyautamun ba banza teemah tayi da ita tayi kwance rigingine tana tunanin Haidar d'inta Malika tana fita gun iyayye ta nufa iyayye ancakare cikin wani uban less matan kauye ankewaye caa sai nan nan ake da ita danginta kamar zasu goyata itako sai washe baki take Malika ta ISO" iyayye zo kiji tashi tayi suka kebe" Malika wai yanaji hayyo baya kida ko baya samun likine?"iyayye yada zakuji shi wlh wannan yarinyar taki sai kun kebe kin nusar da ita wlh fitinarta tayi yawa yanzufa gaban hayyo makadi na fito da ita labari yaje gun mijinta yama hana kidan shiyasa kukaji shiru gasunan yan daukar amarya suna dabda shigowa cikin garin dariya iyayye tayi"


to naji kuje ashiryata zanzo na mata fada auta bataji batada hakurine kuma batason raini ne" haba iyayye ina gayamiki sai kin tsawatar mata kina kara zugata wlh idan taji kai zata hau ta zauna bazatayi abun arzikiba dariya iyayye tayi" to umma Malika, zanje nama zahara fada, zata dauka insha Allah kuje maza ku fara shiryata haja Nanu ta ISO" ke malikatu ina zahara ne hannu haja Nanu taja suka nufi daki mata sai kallon iyayye da yarta suke yanda Allah ya musu bude cikin lokaci daya daki suka shiga gun teemah tana kwance malika tace" watsime atashi idanu ta bude tanaga haja Nanu ta kwab'e fuska" wlh haja nanuta nifa nagaji da wannan dure duren wlh babu abinda zan kara sha dakuwa tamata" kinci nan ja'ira banza uwar iya shege saboda na gama gyaraki shine zakimun shegantaka ko maza tashi wanka l'alle zan miki malika tace " yauwa gurjeta dakyau tashi teemah tayi tana gunguni malika da maheeda sukaje suka duko ruwan l'alle. da yaji turare da maguguna teemah tana cika tana batsewa haka haja Nanu ta garjeta tas


Malika ta shiryata kwalliya ta kece raini wani uban material ne milk colour ta saka ta nadeta da lufaya itama milk colour sai uban kamshi take zubawa goshinta na kyalli kunshin kafarta da hannuta kadai abun sha'awane teemah tayi wani irin kyawu maheeda sai kodata takeyi baki ko sun ISO Halimace kawai ta biyu yan daukar amarya saboda garin ya burgeta tanason sake zuwa kauyen an karama baki an basu abunci Abba ya karamasu sosai mu'azzam sai nan yakeyi dasu malika tama halimatu jagora har gun iyayye tasamu tarba ta musamman taji dadin hada zuri'a dasu saida taci abunci ta huta iyayye ta kaita har gun teemah tana zaune suka shigo halimatu ta kara yabawa kanan nata zabar mace irin teemah sai mai rabo duk da tasan ba kyau ta fisaba kusanta ta zauna"cikin girmamawa teemah ta gaisheta ganin tsantsar kamar da take da Haidar dinta rikota tayi" lfy lau Fatimarmu masha Allahu Allah yabaku zaman lfy Nice nazo da kaina na kaiki har dakin mijinki kai teemah ta sada k'asa iyayye ta fice tana farin ciki maras mustuwa haka akaci da gudanar da biki cikin farin ciki da annushuwa kidane iyalin maigari suka hana saboda gwamna yace abar kidan mawaki yana yabon kyan matarsa karfe biyu daide aka gama shirin tafiya da Teemah gidan mijinta su kursiya, anyi shirin tafiya binni babu laifi anci kwalliya yan rakiya mutum hudu ne da kursiya kawar amarya sai inna talatu sai lubabatu kanwar iyayye sai mareku sune zasu tafi su dawo su malika da, maheeda, yan canne


Teemah ce jikin iyayye sai kuka, suke daga iyayyen har teemar daket ta iya mata nasiyar kuka kawai suke duk saida suka ba jama'a tausayi Abbane yazo dakansa ya banbare teemah jikin iyayye yaja hannun teemah tana kuka tana Kiran iyayye malika ta rumgume iyayye tana bata hakuri Abba har mota yakaita wata jibgegiyar Jeep ce fara itace ta amarya Halimace ta bude masa yasaka teemah shima idanunsa sunyi jajur daurewa kawai yakeyi"Auta dan Allah kiyi aiki da nasiyyar da muka miki idan kinyi haka to kin burgeni kin cikimun burina zanyi alfahari dake cikin kuka tace" Abba insha Allah zanyi aiki da abunda kukacemun ko dan kuyi alfahari dani" yauwa Allah yamiki albarka Allah ya kaiku lfy Allah yabaku zaman lfy keda mijinki kishiyarki" Abba Kumar har kishiyar?" oh Auta duk ina nasiyar da muka miki Kenan baki daukaba" Abba na dauka " to Allah yamiki Albarka "Ameen Abba ta fada cikin kuka ficewa yayi maheeda ta shigo ta rumgumeta halima ta shigo tana bata hakuri shiru tayi kusiya ta gama sallama da kowa mijinta harda kwallasa itama motar teemah aka sakata suka SATA tsakiya halima ta koma gaba sauran kuwa suna sauran motocin dan motocine guda biyar na kece raini bois uban gaiyya uban tafiya wasu babu kowama aciki yanda sukazo haka zasu koma dan Abba yace baza'a kwashi mutane kamar haukaba aje musu mutum hudu ya isa su haja Nanu kuka wiwi daket malika ta lallasheta tayi hakuri
Mu'azzam ne ya ISO motarsu teemah ya bude yagama tsokanarta ya rufe malika sun gama sallama da iyayye suma da kukan suka rabu mu'azzam yajata ya shigar da ita mota da yaransa kofar gidansu teemah babu masayar haki ko ina jama'a ne har


motocin suka tashi hanne sai kirtar kuka take an hanata zuwa haka iyayye naji na gani motar su teemah ta daga tabar gurin teemah wani irin kukane take na fitar hankali haka motocin suka daga sukabar kauyen garin sarki direbobine kwararu gudu kawai suke shararwa mintina talatin ya kawosu birnin damagaram basu ko tsayaba suka kama hanyar Kano daket maheeda ta lallaba teemah tayi shiru ta rumgumeta lamo tayi jikin maheeda kursu ko sai washe baki takeyi tana kallon titi ta saka danta cikin hijabi saboda sanyin Ac su mu'azzam da malika suna biye da motar su teemah dan yace haka zasuyi har su isa insha Allahu Aliyu kuwa duk bayan awa sai ya kirayi mu'azzam da Auntynsa halima da Boos yaji inda suke, to sai muce teemah Allah ya kawoku Nigeria garin Gombe lafiya,


******
Nigeria Gombe governement house misalin karfe takwas na dare bedroom din bintu cike yake da kawayanta manya manyan matane sai shewa akeyi anzo dannar cinya ana jiran isowar kucaka yar kauye dan tabi ta yayata yar kauyace aka bashi sadaka sai tofar da yawu sukeyi Bintu na hango taci ubansu ado ta narka wata danyar shaddah gizna baka wacce dinkinta kawai zaka kalla kasan nera tayi kuka tayi masifar kyau kasancewarta farar mace tayi masifar yin kyau sai zugata suke ta saki jikinta tana sha'aninta dan tasan yau ido hudu kawai zasuyi da kucakar amarya ta tsorata tasan nan gidan Aliyu yafi karfin zamanta safina matar sanata Nuradeen ce tace" wlh Bintu Aliyu kinyi zarra kin wuce ajin yar birni ma bare yar kauye far tayi da idanu ta bata hannu suka tafa Bintu tace" nide don Allah kutemaka kuyi hakuri karkuyi amai ko toshe hanci bare suce mun rainasu mu barsu da bakin cikin da my man zai kumsa mata, dariya sukasa, suna shewa, Rauda ce ta shigo yarinya anyi mata ado tayi kyau sosai kamarta da, Aliyu ta, fito sosai gun bintu ta nufa"momy Dadyna yace kikawo zahara, na kimasa, ita" Tab Rauda Nice zan baki yata muje na kaimasa, ita dariya, suka mata ta dauki zahara, wace tasha kayan kanti Riga da wando farara tayi kyau saffah tace "Auntyna kina wuta wlh kin hadu ba karya Bintu sai fadi take ta dauki zahara "Rauda ina dadyn nakine? " yana parlon baki momy ahaka zaki mayafin safina ta amasa ta yafa suka fito cike da nutsuwa take takunta har suka zo kofar parlo ta danna dan Madani kofar ta bude suka fito Rauda na zuba mata surutu suna zuwa ta murda kofar shima ya fito sukayi karo "Wow mijina haka kayi kyau l'alle angwanci kakeji idanu ya zaro"my bintuna yauko zaki sani haka kika ratso kika fito da dan guntun gyale dinki ya matseki gida cike da jami'an tsaro kuma kike kokarin shiga parlon baki da mutane aciki ya damkota yabi wata kofa da ita Rauda sai dariya take"yauwa Dadyna ramamin ta dokeni jiya"my man tsaya kaji mana............... โœ๐Ÿป
๐Ÿ’ƒ๐ŸปLadingo Yar Janaf ce๐Ÿ˜˜












โœ๐Ÿป.....Rahma ummu Fareesa๐Ÿ˜˜


*๐Ÿ‘ฐ๐ŸปMATAR๐Ÿ‘ฐ๐Ÿป*
*๐Ÿ’–๐Ÿ’–GWAMNA๐Ÿ’–๐Ÿ’–*








*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
____________________________________




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________






*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger๐Ÿค™๐Ÿป




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf๐Ÿ‘Œ๐Ÿป๐Ÿ˜˜*














*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page 2โƒฃ3โƒฃ*






.....Wlh bansan akwai mutane ba daide lokacin wannan ka cikeni na koma matse mata hannu yayi yabi wata yar kofa suna karya kwana sai ga wata kofar ya murda yajata ciki Rauda ko tuni tabi babbar hanya ta tafi gun yan uwanta tana dariya za'a doki momynta Dan Dadynasu ya hanata idan suna tare ummasu sozo gunsu suna shiga Aliyu ya rufo kofar yajata har bedroom d'insa ya rufo kofar amshe zahara ya shimfideta saman bed.idanu Bintu ta fara cicirawa tana yarfa hannu" wai my man meye zakamun saboda Allah meye nayi maka ta fada tanaja da baya harara ya zafga mata ya nufota" au baki san me kikayi ba neman gun guduwa take taku biyu yayi ya damkota ya matseta da bango ya tsareta da lumsassun idanunsa"nace waye ya baki damar fitowa ahaka gida cike da karti ya fada ya kamo fuskarta yana


murmushin mugunta dukansa ta fara"dallah malam sakeni haka kawai zakazo ka matseni yo tsirara kaga na fita matse mata bakinta yayi da karfi ta Saki ihu ya rankwafo ya kame bakinta yana mata tsotsar mugunta lebanta yake tsotsa cikin mugunta zafi takeji sosai dukansa take tana kuka amma yaki sakar mata baki saida ya yaga sun fara kumbura ya saki bakin nata ya matseta da bango daket take Numfashi "wlh gobe ma ki fito ahaka kiga yada zan miki hannusa ta wawura ta gantsara Masa cizo Kara matseta yayi ko numfashin bata iyawa wani irin kuka ta Saki saida yaga ta jigata ya saketa yana murmushi nan ta zube k'asa saman carpet tana maida numfashi saboda ya azabtar da ita cikin kuka tace"wlh Aliyu Allah ne zai sakamun akan zalumcin da kakemun murmushi ya sakar mata ya daga mata gira ya dauki zahara ya bude d'akin ya barta zaune tana kuka saida tayi mai isarta ta Mike ta shiga bathroom ta wanko fuskata ta fito gaban dressing mirror ta kalli bakinta yada ya kumburo ranta ya baci sai Allah ya isa take janyo masa fuskarta ta gyara ta dauki gyalenta ta fito


gun kawaye ta ta dawo sai sunne sunne
Kai takeyi tarata sukayi Safina tace" kaga uwar gidan Aliyu ya naga bakinki ya kumbura me yasa meki ne? " ni bana cikin iskanci ban saniba dariya sukayi da shewa Saffah tace" Aunty Bintu wai yanaga kinyi sanyi haba Dan Allah yo meye zaki damu kanki kici gaba da gashi ki Saki ranki murmushi tayi"kanwata kina wuta ina godiya da goyon bayanki gareni Farida tace" ai muna tare dake mamu tace" Bintu zo nayi magana dake tashi tayi suka kebe tana kallon mamu" Aunty meye gani"


wlh ki shiga hankalinki banason kizo kiyi aikin da nasani fah wlh ki ajiye hankalinki kibar biya yan yarima asha kida zasu Saki aikin da nasani ni el uwarkice bazanso naga kin tozartaba saboda bakisan irin wacce ya auro mikiba hasashene kukeyi wlh dan hakin da ka raina shine ke tsonema idanu dariya Bintu tayi "haba Aunty ai ba zuga bace ba gaskiya suka fadi amma naji zanyi aiki da abunda kikace mun shikenan ko ai kin tsaya kucakar kauye tazo ko?" Fatima ina rabaki fah wlh zan fadawa hajiya baki sauyaba rumgume mamu tayi" na sauya yi hakuri murmushi mamu tayi taja hannu Bintu suka dawo Safina tace" hajiya Fatima Aliyu kina wuta murmushi tayi" yanzun dai ruwa nakeyi dariya sukayi akaci GABA da hira Bintu ko ta matsu Amarya, tazo, bangaran Aliyu babban parlon baki ya koma rumgume da zahara Jamil yace" bani zaharamu na ganta" Jamil gata ka matsa ankawota murmushi yayi ya amsheta yana murmushi" kaga yar gata wlh kuma kama kuke sosai zama Aliyu yayi yana murmushi ya tura hannunsa cikin sumar kansa yana shafawa yana lumshe lumsassun idanunsa Nuradeen ya bushe da dariya yana nuna Aliyu" wlh Abokina jarabace take cikinka Tab kako ga yada kake lumshewa banza ya masa, ya dauki wayarsa yana latsawa Jamil yace" uhumm yau mulkin akeji ko kai ya dago ya kalli Jamil ya daga masa gira can kamar bazai magana ba yace" Jamil


zaka biya wannan dan rainin hankalin bakaji sharrin da yake kullamun ba Jamil gintsen dariyarsa yayi dan shida kansa ya gano abokinsa zumudine ke cinsa ya matsu matarsa tazo" Abokina karka damu zolayarka yakeyi banza ya musu bai sake magana ba Nuradeen da Jamil suke hirasu har karfe goma Amarya bata isoba suka kirawo matansu awaya suka tafi Aliyu ya koma bangaransu ya kaiwa Bintu yarta da harara tabishi ko aka bai kawota ba dan har yanzu bakinta akumbure yake kawayan Bintu ma suka sun watse dan dare yayi sai su biyu suka rage ita da yayarta mamu sai babbar kawarta Farida parlo suka dawo suna jira yaranta ko nagun TV suna game sai karfe goma shadaya motocin su Amarya Teemar Gwamna suka shigo garin Gombe direct government house suka nufo har jiniya mitocin suke gari ya dauka Matar gwamna Aliyu Muhammad Damba ta ISO dan yan garin suna da labari sai Addu'ar zaman lafiya jama'ar gari suke masa Adalin gwamna ya kara aure jiniyar ta farkar da teemah daga baccin da takeyi idanu ta bude tana kallon gari har aka ISO kofar gidan Aliyu gwmna sojojine ko ina burjik abakin get


get aka wamgame musu motocin suka shige aikuwa su mareku su innah talatu sai guda suke shekawa boos ne ya bude ma Amarya mota maheeda ta fito taba teemah hannu ta kama ta fito da kafarta ta dama halimatu ta kama hannuta su malika suka ISO boos ya musu jagora har part din teemah abude suka shigo da sallama duk abinda ake Aliyu yana kallonsu ta CCTV camera haba ai tsaye ya miki yana karewa teemah kallo yarinya ta wucce tunaninsa GABA daya ya dimauce wani irin murmushi yake saki ya kasa zaune ya kasa tsaye su teemah suna shiga yan rakiya kowa suman tsaye yayi malika kanta bata taba tunanin zata shigo irin wannan daulaba kursu sai washe baki take tana juye juye"oh ni kursiya Allah mai iko mukam tun aduniya munga makomarmu yasin nasan ko yau na mutu nayi shawada malika ana parlo suka sake gyarama teemah fuskarta halimatu tace" muyi mu kaita gun uwar gida dare yayi fah inaso na tafi gida fitowa sukayi halima sanin tasan gidan ciki da bai ta musu jagora har part d'in Bintun da sallama suka shigo bintu na zaune su uku suka amsa ganin harda, halima tarbasu sukayi suka zazauna kursu sai washe baki takeyi gaisawa, sukayi cikin girmamawa bintu sai wani mugun kallo take musu dan ba haka tayi tunaniba wasu k'azammai taso ta gani halima tace" ga uwar gidan ta zahara dan haka ku bata amana innah talatu da malika suka kama hannu teemah su kawota gaban bintu suka zaunar da ita bintu koda bataga fuskar yarinyar ba irin dirin jikin yarinyar ya tsorata saboda lufayar jikinta tayi mata mugun kyau jikinta na rawa ta nuna kursu" bake bace amaryar talatu ta bude fuskar teemah tana murmushi " ah ah gatanan kanwar taki mun mubaki amana don Allah kuyi hakuri da juna Allah ya kade fitina tsakaninku kallon teemah bintu tayi arikice ta tashi tsaye" kan buro uba wannan zankadediyar itace amarya, aikuwa zakici ubanki bakida gun zama agidanan azabure teemah ta Mike "wallahi badai ubana ba Abbana yafi karfin zagi gun kowace lukutar mace mai gabjejen baki asama Kut tabdijam yo waye ba dan iskaba daga kauyen garin sarki fah nazo jeki can kiji wacece watsime mai Allo da sauri halima ta ISO ta rufema teemah baki ta zaunar da ita " haba zahara kefa karama ce kiyi hakuri Malika kunyace ta lulubeta bintun jikinta ko ina rawa yakeyi jin zazakar muryar Teemah da irin rashin kunyar da take mata ta nuna halima" Aunty dake aka hada baki aka auromun wannan Aljanar tana fadin haka ta zube ak'asa asumammiya da gudu sukayi kanta.............. โœ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐ŸปLadingo Yar Janaf ce


Kuyi manage ina busy ne












Rahma ummu Fareesa ce๐Ÿ˜˜


*๐Ÿ‘ฐ๐ŸปMATAR๐Ÿ‘ฐ๐Ÿป*
*๐Ÿ’–๐Ÿ’–GWAMNA๐Ÿ’–๐Ÿ’–*








*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
____________________________________




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________






*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger๐Ÿค™๐Ÿป




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf๐Ÿ‘Œ๐Ÿป๐Ÿ˜˜*




*๐Ÿ•ŒJama'at Mubarak๐Ÿ•Œ* Yan uwa Musulman Duniya ina muku barka da sallahr Juma'ah ๐Ÿคฒ๐ŸปYa Allah ka yafe mana kura kuranmu Albarkacin wannan rana Ta Juma'ah mai Albarka


๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐ŸปMasoyana dolane yau na baku farin ciki kamar yada nake farin ciki Asha karatu lafiya๐Ÿฅฐ๐Ÿค๐Ÿป๐Ÿค๐Ÿป๐Ÿ˜˜


*Migidana Sulaiman Abban Shuriem da Fareesa ina mutikar godiya gareka Allah ya bar so da kauna su oh o ba haka aka soba๐Ÿคฃ๐Ÿ˜‚ yo Allah natuba shiga tsakanin Rahma AbdulNaseer da My bugun zuciyarta Alhaji sulaiman Abdullah ai sai Allah ba mutum ba๐Ÿ˜†๐Ÿ˜๐Ÿคช*


*My habibtyna Zainab ilove you mazga mazga kiji dadinki ta wajena iya wuya muna tare my zeey babyna๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜*


My brother Ibrahim AbdulNaseer Bro Muhammad AbdulNaseer Aunty Nusaiba AbdulNaseer Munneera AbdulNaseer Jameela AbdulNaseer Abdulmutallab AbdulNaseer Halima AbdulNaseer Hadeeza AbdulNaseer auta Aisha AbdulNaseer ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login