Showing 30001 words to 33000 words out of 129912 words
Chapter 11 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt
nanuta kibarni haka ai da nazo da wayata da na dauki hiranan na turawa haseem yasha dariya"ke wlh ahir dinki kirabani da hauka kibari har Aliyu ya ganki tukun "to nabari ai ni haushinsa nakeji waifa Nanuta kinsan wani abun haushi? " ina fa nasani idan ba kin fadamun ba watarana naje amsar sadaka ya wani rike hannuta suna yawo cikin jama'a Dan tsabar iyayi wai nice ma zan firgitata saboda tsabar munina "dan Allah ki sharesu ai kawai kiyi shiru abunki inace mun gama magana kince baki sonsa amma kinmun hiranan tafi so dari to ina ruwanki dasu tunda baki so "baki ta zumburo gaba "eh banaso shikenan ta tashi ta wanko hannuta ta dawo ta zauna" wai kin koshine? "nakoshi Nanu idasa bani labarin Abbane ya shigo da sallama Teemah ta Mike da gudu ta riko hannusa
"Abbana yau ban gankaba shine kamun auran Dole ko? " Haba Auta waneni yi hakuri dariya haja Nanu tayi hannuta ya kamo suka zauna ya gaishe da mahaifiyar tasa"haja Ashe kinata famar lallashi "to yazamuyi ai mun kashe magana kuka ya k'are ko? " eh ya kare Abba Nanu ta koyamun wayo da an gyarani da kansa zai rabu dani "Auta wannan wani irin haukane Nanuce tayi masa yaren fulatanci ta yada bazata ganeba dayake ta iya amma ba sosaiba yace "oh hakane Auta yanzu dai kinbar kuka ko? " nabari Abba hira sukayi sosai sun jima saida dare yayi sosai Abba zai tafi ta bishi gida nanu tayi tayi su kwana ta kiya Dole tabarta suka tafi, lokacin da sukazo su Mu'azzam da su iyayye har sun gaji da hira kowa ya kwanta Mu'azzam da yaransa suna tare Malika da yarta nagun iyayye suna daga kwance suna hira da malika d'akin ta fado sai kumbure kumbure take Malika ta kalleta wayarta ta dauko ta kunna gun iyayye ta nufa ta kwanta ta rumgumeta"Auta an dawo ai na zata acan zaki kwana" iyayye kalli ta Nuna mata wayarta"ai munada labarinta mijin kine ya siya miki kuka ta sakama iyayye tayi wurgi da wayar Malika ta bushe da dariya iyayye ta rumgumeta"yi hakuri Auta ai na mantane Ashe bakyaso ko? Kai ta daga" iyayye kice Malika tabarmun dariya "ke Malika barimata dariya "to Allah ya bata hakuri iyayyen ma dariyar take kumshewa mik'ewa teemah tayi taje tayi wanka tayi shirin kwanciya ta dauki wayarta ta kwanta jikin iyayye tana danna wayar taga har yanzu bai kiraba tsaki taja"yo karka kirama yo da wa zai dauka suna jinta suka mata shiru tunda idan sunyi dariya kuka zatayi pic d'in da sukayi tare ta zubama idanu tana kallo wani mugun kyau sukayi sai yanzu ta tabtar da Haidar ne fuskace kawai ya saka kuma fuskarma me kamarsane sak ahaka tana kallon pic har bacci ya fara fizgarta ta rumgume wayar tayi bacci iyayye ta janye wayar ta ajiyeta gefe tana dariya "yarinya sai fitina Wanda ba asone za'arika kallon hotonsa har ayi bacci lokacin Malika ma tayi bacci iyayyen ce ta jima kafin tayi bacci, Asubah ta gari,
****************
*Bayan kwana biyar*
Yau su teemah zasu koma gombe saboda abubuwan da za'a fara koya mata da tsumin da za'a fara mata da gyaran jiki agidansu Mu'azzam da sauran abubuwa dai dan shiga gidan gwamnati Dole sai mace ta amsa sunan mace Dole su gyarata kafin aure yada shima zaisan mace mai daraja ya aura bangaran teemah ansamu an mata wayo cewar da an gyrata Aliyu zai rabu da ita tahau kai ta zauna ta Saki ranta kullum sai Aliyu ya kirata duk da yanada haushinta haduwarsu yake jira ya gyara mata zama amma idan ya kira bata dauka ko so daya shi mutumne da baison raini shiyasa kwana biyu ya daina kiranta kuma takama masifa harda su kuka tayi ta kallon wayar tana cewa matarsa ce ta hanashi kiranta su iyayye idanu suke zuba mata suna kallon ikon Allah abun yana basu mamaki tace bata sonsa amma bur ta ishesu da rigima tana fushi Haidar yakita saboda matarsa, shiko Aliyu abubuwan sun masa yawa ga rigimar bintunsa danma ta Dan rage kwana biyu yayarta mamu tayi ta mata nasiya to da Dan sauki haushinsa daya baya jin murya Noor d'insa dan yace bazai k'ara kiran taba har ta dawo Gombe yasan sai tunaninsa ya adabeta ta rasa sukuni ita bintu da tafara rigima yake zautata da salonsa sai masifar ta ragu kafin dare nace lalai Aliyu namijin duniyane, tun jiya ya tafi Abuja wani baban tarono akeyi gidan shugaban k'asa Wanda za'a kwashe tsawon kwana biyar anayi Wanda ya hada manya manyan shuwagabani na k'asa k'asa shine da ya kira bintu ta adabeshi wai yanzu haka gun amaryasa ya tafi kauye shiru ya mata Dan shima miskilancin na kansa ko kallo bata isheshiba,ya tsinke Kiran Dan yadauki niyar su dukansu biyun da babbar da k'aramar zai sharesu ya zuba musu idanu yaga iya gudunsu yasan halin kowace yasan irin son da kowace take masa da yada shima yake son kowace cikinsu da salon son kowace daban daban azuciyarsa Dole zai basar dasu ko ya huta kwana biyu bayason hayaniya da rigima to sun sakashi a gaba Dan haka yayi watsi da lamarunsu yana harakokin gabansa,
tun safe teemah take yawon ban kwana gidan yan uwa da makwabta misalin karfe biyu na rana su Malika da yaranta cikin shiri suka fito har anshigar da kayansu mota kursiya kawar watsime harda kuka tunda tazo sama da wata guda kullum tare suke teemah tana gidanta ko ita tana gidansu teemar rumgumeta teemar tayi itama tana kuka saida iyayye ta janyeta mu'azzam dariya suka bashi sai darawa yake "haba Watsime kiyi hakuri ai zaki dawo itace babbar kawa kuma da ita za'a rakaki"iyayye kima yaya magana Abba yace"yi hakuri auta wasane yake miki kursu kema yi hakuri ai bazata jimaba zata dawo karki damu kukan ta daina sukayi sallama cikin walwala tana karama teema godiya dan kaya ta bata tafi kala biyar Wanda bata taba tunanin zatasa irinsuba haja Nanu taja teemah gefe guda ta kara mata wayo harda su dariya take ta rumgumeta"wlh shiyasa nake sonki kakata dariya akayi ta musu nawalu nacan gefe aboye sai matsar kwalla yake yana kallon teemah amma bai isoba lado ko kin zuwa yayi tunda mai gari yayi musu kwakwaran kashedi akan wlh za'a dauresu idan suna ma matar manya magana shiyasa ya hakura dan akwaishi tsoron iko mota suka shiga cike da begen kauyansu da iyayyensu shuriem harda kuka abarshi gun iyayye sai daket mu'azzam ya lallabashi yayi shiru yace gobe zai maidoshi teemah na rike da hannusa iyayye saida mu'azzam ya tashi mota ta saki tana kwalla suka rarasheta ita da Abba saida tayi dariya dukayi sallama Malika na musu dariya"yo ni bazaku lallasheniba zungurata mu'azzam yayi yama motar key sai hannu ake daga musu har suyi nisa "my darling harda zun gura ai Dole nayi kishi sai ita daya ake riritawa" nifa wlh baruwana daku kukasa akamun auran Dole shiru suka mata gudun kar suyi dariya tayi kuka gudu mu'azzam yake sosai har yafita akauyen garin sarki watsime sai raraba idanu ake ana kallon hanya ana matsar kwalla......✍🏻
💃🏻Yar ilu ce🤪
Rahma ce ummu Fareesa😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*Written By*
Ladingo Yar ilu😉
Yar mutan Niger
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page 1⃣4⃣*
......tunda Teemah suka
Kama hanyar gombe Mu'azzam bai tsayaba idan kaga ya tsaya sallah za suyi su Teemah yauma ansha madara mai sanyi har angaji amma yau idanunta kyam bata rumtsaba har suka shigo garin gombe yau da wuri suka shigo shadaya na dare saura suka shogo garin gombe suna zuwa kowa ya nemi makwancinsa saboda gajiya da bacci teemah tana shiga bedroom d'inta wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci ta cire zanin gado ta canza wani Dan akwaita kynkymi saman bed ta fada ta shige cikin blanket wayarta ta duba tana zumburo baki ta k'urama pic d'in Aliyu idanu"Allah babu ruwana dakai My haidar ni sai mun rabu shine Dan bana daukan kiranka sai kafasa kirana ai hakkina ne ka kirani ko bana daukaba yi tayi kamar zata kirasa ta fasa ta ajiye wayar tana karanto Addu'o'in bacci bata wani jimaba bacci ya dauketa, bangaran Malika da mu'azzam bayan sun kwantar da yaransu suka shiga bathroom sukayi wanka tare suka fito sukayi shirin bacci suka zube saman bed saida suka garji junansu San ransu yo akwana biyu ba'a haduba sama da sati sai can tsakiyar dare suka sararama juna akaje akayo wanka aka bingire sai barci Asubah, ta gari,
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
zaune Bintu take a Katafareran parlonsu Wanda ya gaji da haduwa yasha kayan alatu yaranta duka sunyi bacci sai zahara itako kukan dare gareta bata barin bintu bacci k'urawa wayar hannuta idanu tayi Aliyu tun jiya yaki kiranta tarasa dalili tsaye ta Mike ta nufi makekiyar TV dake manne jikin bango ta kashe kai komo ta fara tsakiyar katoton parlon nasu"wallahi dolene My Man ya rabu da kucakar yarinyar nan tun Kafin ta shigo gidan tanason hadani da mijina Wanda Muke da shekaru goma sha shida da aure yarinyar da aka Haifa ashekara aurena Dan ubanta shine zata rabani da mijina to daga yau na ajiye fitina dashi zan sasauta masa keko yar kauye kucaka zaki raina kanki wlh zahara ce ta fasa kuka gunta ta isa ta zauna ta dauketa tana shayar da ita kiran numbersa tayi bata shiga duk numbobinsa da ta kira basa shiga hankalinta ya Kara tashi amma tunawa haka yakeyi duk dare ajiyar azuciya ta sabke tana zubar da hawaye mik'ewa tayi rumgume da yarta ta nufi bedroom kwanciya tayi ta rumgume yarta itako sai harbe harbe take batada almun bacci bintu hawaye shafe shafe a fuskarta har bacci ya dauketa asuba ta gari
**********
bayan sati daya yau su Teemah suka cika sati daya da dawowa daga Niger Mu'azzam ya komabakin aiki sai su Teemah suke rayuwarsu da el uwata da yaranta teemah na zuwa islamiyya hutunsu na karshe haryanzu bai kareba Aliyu har yayi kwanakinsa biyar a Abuja ya dawo gombe har yau babu wacce yakira cikinsu harakokin gabansa yake yayi watsi da lamuransu har ya dawo teemah tin bata damuwa abin ya fara damunta harda su kuka take daga baya tayi watsi saboda batada lokaci saboda gyaran da ake mata da fara koya mata salon tafiya da magana da iya kwalliya da Jan aji kullum idan an kaita gidansu mu'azzam sai yamma take dawowo gida. tayi shirin tafiya islamiyya abinda yasa ko ta maida hankalinta kan abinda hajiya mansura take koya mata saboda rigimar da take musu ita bata sonsa tunda mata gareshi sai sun rabu shine suka mata wayo idan ta tsaya ta koyi komai atsari tayi kyau da iya magana da shagwab'a Aliyu daga ya ganta zai rabu da ita amma ba yanzuba sai angama shiryata jin haka ta tsaya ta maida hankali Ana koya mata sai an gamasu su kwaliya da iya magana da kwarkwasa da iya tafiya da iya dress za'a fara na jiki da tsumi Dan yanzu yayi wuri, suko wa innan sunsa Dole mijinta zaiso ganin matarsa suyi zance, bangaran bintu kuwa tunda taga Aliyu yayi watsi da ita Dole take kiransa tana masa Mita baide kulata har yadawo zuwa lokacin tayi laushi Dan bata jure rashinsa amma da ya dawo saida tayi masa tas miskilancin na kansa bazan ya mata ta gaji ta fada samansa tana rusar kuka tausayi ta bashi Dole ya kulata ya lallasheta yanuna mata salonsa har taji sanyi aranta to shine fa yanzu ya Dan sami kan bintu ta Dan sabko amma ba dukaba idan kishin ya motsa gaba take sakashi da fitina teemah ko har yanzu baibi ta kantaba itama bata kirasaba yasa dai Ana kula masa shiga da fitarta saide baisan gyara ake kaita gidansu mu'azzam ba tunaninsa dan babu makarantane take zuwa yini shima tunda yazo bai samu isashan lokaci ba ya huta
da misalin karfe biyu da Rabi hajiyar mu'azzam zaune take a parlo tana sauraren redio BBC Teemah ce ta fito daga wani d'aki ita da wata mace ta hade cikin Riga da siket na shadda colour green dinki ya mata cif saide rigar ta matseta kirjinta yawa zasu fasa rigar su fito kuma hannu rigar karamine agaskia teemah tayi mugun yin kyau sosai fatarta sai uban sheki takeyi ga kwalliyar da mansurah ta koya mata yau bata gogetaba tayi mata kyau mutika haka suka fito sai wani shegen taku take tana baza uban kamshi gun innah ta nufa ta zauna"ah Fatima zara'u ya dai mansura tace"bamu gamaba ba fah wai kawartace babu lfy shine tace zata ganinta amatse take? " asha Allah bata lfy cikin yanayin yada ake koya mata salon magana tace"innah na tafi ko?? ta fada tana langwabe kai alamun shagwaba dariya hajiya tayi "to ai rashin lfy ce jeki amma ki kira mijinki ki fada masa"ai na fada masa"to amma kuma wannan kaya Dan iya koyan daukan dress ne sun kamaki sosai danma bakida jiki "hajiya hijab zan saka fah har k'asa gaskiya gwara ayi A ida gyaran ko ya rabu dani nashakata innah na tafi" sai kin dawo ko nace sai gobe mik'ewa tayi"innah sai gobe dai zan jima mata ta fada tana dakar hijabinta mai niqab da hannu ta saka shima green color ne sai uban kamshe takeyi ta fito da hannuta waje tare suka fito da hajiya mansura wacce ta kware agyaran jiki da tsuma mace da iya kwalliya da tafiya koyan magana da shagwaba da kwanciyar aure da sauran abubuwa dai na mace tazama shalelen miji sunanta yayi fice kaf fadin Nigeria Dan aikinta akwai kwarewa, sosai saide tsada yanzu duka abubuwan da zata koyama teemah har zuwa aurenta saida aka tisa mata nera million guda kash duka kudin sadakin teemah ne suka bayar mu'azzam neko da wannan aiki, yace yanaso kanwarsa ta zama itama sha kallo gidan gwamna kudinta zai maida mata arone yayi yace shine ya dauki yaunin gyaran suna fitowa. direban hajiya mansura yazo daukarta"yauwa muje sai mu ajiyeki wacce unguwace?" Buba shago" to ai muma nan
Muke ai bazamu bar matar manya ta shiga adaidaita ba baki teemah ta tab'e suka shiga motar direba yaja suka tafi, mansura na Kara mata fada tafa rike duk abunda take koya mata shiru tayi tana gyada kai kwatance ta rika ma direba har kofar gidansu Maheeda ta bude motar ta fito tayi mata godiya kofar get na nufa ina dab da shiga gidan naji tsayuwar motar Boos da Sauri na juyo na kallesa ya fito ya nufoni"hajiya oga na kira maza kizo tsayuwa na gyara cikin tsiwa nace" baza'a zoba anki ba'a zuwa na fada cikin sanyin murya Dan Sam mansura ta hanani daga murya wayar Aliyu ya kira bugo daya ya daga lokacin yana zaune akatafareran parlonsa na saukar baki dan yanzu yagama da jama'a acikin nutsuwa yayi magana yana lumlumshe idanu"Boos ya akayi?"Oga wlh matarka ce mukaga tazo gidansu kawarta idan gayan nan yake amma na tabbatar baya gari yana bauchi mik'ewa yayi zaune ransa ab'ace "maza kayi mata wayo ka kaimun ita gidana na NEW GRA wlh zata sani kitt ya kashe wayar ya kira wata number bugo daya aka daga "inason fita yanzu kitt ya kashe kiran ya Mike dama cikin shiri yake shadda ce green colour jikinsa yayi masifar kyau sai baza kamshi yake yana fitowa yayi Karo da bintu rukumkumeshi tayi tana kuka"wlh Aliyu ba idan zaka ai naji kana waya wai ashirya tafiya niger yanzu "bintu please kibarni na dawo karki karamun zafi wai meye nufinku akaina wlh duk zanyi maganinku sakeni kinji my zahara na kuka kije ki bata mama janyeta yayi ya kamo hannuta tana tirjewa ya nufi parlonta da ita kicin kicin yayi da fuska ya zaunar da ita "wlh my bintu zaku sani kiyi hakuri naje na dawo babu niger din da zani zahara ya dauko da kansa ya samata nono abaki bintu sai hararasa takeyi ganin babu fuska yasa tayi shiru kiss ya mata agoshi ya fice haka kawai taji bata yada da fitarsa ba ji take kamar tabi bayansa Dan dai tasan halinsa yau da takwana gidansu bangaran Boos kuwa jin Oga ya kashe wayarsa ya fara magana yada zataji "Oga tace bazata zoba wai wayone zaka mata Dan karabu da ita tace Dan Allah kayi hakuri ka rike mata igiyar aurenta tana Sonka bazata iya rabuwa dakaiba abarta ko? har NASA Kafa zan shiga gidan da Sauri na juyo "Kut kai ni yaushe na fadama haka nida nake neman maraba dashi to wlh sai nashiga motar muyita ta kare na nufi motar da Sauri dariya taba Boos gun motar ya ISO ya budemun na shiga motar
boos ya shiga driver yaja muka kama hanya dube dube na fara" Boos kake kowa ina Ogan naku ai baya motar? " ranki shidade yana gidansa na hutawa mana ai can zamu kaiki daganan yayi shiru bai sake magana ba"wlh babu inda zanje ku saukeni babu Wanda ya kulani dole nayi shiru ina ciza bakina ina tuna yada zan masa wayo ya sakeni da irin abubuwan da hajiya mansura ta koyamun cikin sati guda dariya nayi ta farin ciki"ai My Haidar idan kasan wata ai bakasan wataba inama abubuwan da aka fara koyamun da yada nayi kwalliya yau wlh nasan da takardata zani gida dan na kara baka tsoro Allah har hijabina zan cire ina karai raya da salon shagwab'a Allah da kafarka zaka gudu kana cewa kumaidata gidan su na fasa auranta ni ko na fito cikin farin ciki na rabu da mijin masifafiya uwar yan jaraba can ku karata da ita yaushe ma gari cike da samari zan zauna da mai mata wayartace ta dauki ringing tana dubawa taga Maheeda picking tayi ta kara akunne"my mahee kiyi hakuri yanzu zanzo ina hanyar kaso aurenane cikin maganar rashin lfy tace"ke my teemah ban ganeba dan Allah kinmun bayani yada zan gane please kimun hausa daide lokacin motar