Showing 45001 words to 48000 words out of 129912 words

Chapter 16 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5804

wasu manyan manyan kujeru akatafareran aparlon lallausan carpet ne ko ina malale kayan alatu sunji a parlon ba karya makekiyar Tv yar bango kai ya jinjina daga kofar da take hade da parlon bintu yana jiyo haniyar yaransa kai ya girgiza ya haye saman bene parlon teemah na sama ma ya hadu nanne yaga haduwar bedroom din teemah royal bed dinta ya hadu ba karya carpet malale ko ina bedroom dinsa ya wuce nanma ya yaba tsarin wannan kamfani sun iya tsara daki saide kudi komai yayi ba karya fitowa yayi yana murmushi ya rufe ko ina daga ciki ya rufo ya nufi wata kofa key ajikinta ya bude sai gashi aparlonsu ya murzawa kofar key ya zare key din yasa aljihu ya nufo parlon bintu na zaune tana shayar da zahara tana gyarama Rauda gashinta Aliyu ya shigo da sallama adakile ta amsa Dan tanada labarin irin uban kudin da ya kashe yama amaryasa kayan daki amma da ta tuna fuskar amarya sai ta bushe da dariya " welcome my man murmushi yayi ya zauna kusanta ya dauki zahara ya rumgumeta yabata lips dinsa tako wawura tana tsotsa Bintu kallonsa take tana dariya" my man ango banza yamata zahara na tsotsar lips dinsa Rauda tayi dariya" Dadyna karfa tacijeka bakinsa ya cire ya kalli Bintu"my bintuna yau kin samu wani abune wai kike dariya haka ne?


baki ta tab'e tayi burus dashi shima bai sake magana ba" baby Rauda ina muneerat? " Dadyna tana Swimming pool suna wanka mik'ewa yayi rumgume da zahara ya fice ya nufi gun yaran NASA Bintu ta bishi da harara taja tsaki "an girma baasan angirma ba sai rawar kafa yake Akan wannan kucakar wada daket idan zai hadiye yawo agabanta Rauda ta rike Bintu"umma da Dadyna kikeko Allah sai na fada masa baki ta buge mata"wlh Rauda zakici uwarki tashi kije ki fada masa tsoronsa nakene jiddah mai aikice tazo tana kwashe kayan dasu Asif suka bata bintu shiru tayi tabar maganar tana harara jiddah taja tsaki" iyayan gulma saura akoma gun kucaka kafin ta Kara gaba jiddah kala batace ba tayi abunda ya kawota tafi ita daya tana masifarta, Rauda kukanta ta hadiye gudun kar doketa Dadynta take jira ta fadamasa umma ta doketa ya rama mata


Su teemah Ana kiran magariba suka shigo garin Sarki tayi bacci har ta gaji mota na tsayawa ya'u zashi masallaci ya fasa ya nufi gunsu yana washe baki suna fitowa da yaga teemah saida ya tsorata Dan Sam bai ganetaba tayi kyau ga bakar abayace jikinta badan yaga daga motar ta fitoba da gudu zaiyi teemah ta shige gida da gudu tana kwalama iyayye kira kursu da tun bayan la'asar take zaune tana jiransu ta Mike da gudu amma ganin teemah taja bata atsorace tana ihu dariya teemah tayi "dallah can nice kawarki Aunty mansurah ce ta sauyani da gudu kursu tazo suka rumgume juna suna murnar ganin junansu iyayye tana sallame salllah ta Mike"tace Autata da gudu ta nufi iyayye ta rumgumeta tana dariya iyayye da kursu kallon mamaki sukewa teemah Dan Sam ta canza idan basu da suka mata farin sani bazaka ganetaba mu'zzam me suka shigo da sallama iyayye ta amsa cikin fara'a taname sannu da zuwa malika taje ta rumgume iyayye kursu sai taba jikin teemah take mu'azzam alwalla yayi ya nufi masallaci haja Nanu ce ta shigo da sallama Teemah da gudu ta nufi gunta tana dariya idanu nanu ta zaro aikuwa ta Ari takare ta kwasa aguje tana ihu haba me teemah zatayi idan ba dariya tako bita suka fara tsere suna karya kwana nawalu ya fito daga masallaci yaga haja Nanu na gudu tana ihu nawalu ya hango kamar aljana daga bayanta uban me nawalu zai idan ba ihu ba ya kurma ihu yana zanzana ya zuba dagudu fitsari nabinsa aikuwa teemah tabi banyasa" sarkin Aljanan duniya kurikeme gun fitsarinsa yama autar aljanai fitsari abaki haba ai Nawalu ya Kara gudu haja Nanu tuni ta tayi nisa itama kara man tayi............ ✍🏻


Abubuwa sunmun yawa kuyi manage














💃🏻Yar lelen Janaf ce😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*








*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________






*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger🤙🏻




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*














*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page 2⃣1⃣*




.....Teemah ganin zasu bata wahala ta tsaya tana dariya harda rike Nawalu tuni yasha saida ta gaji da dariya ta dauki hanyar gidan haja Nanu kofar soron ta tura ta shigo tana dariya talatu na zaune taga teemah itama aguje ta fada d'aki tana ihu" Dan Allah baba talatu meye wai natsoron ajikina watsimenku ce fa ta zama haka Nanu ce ta shigo da takalminta ahannu tanaga teemah zatayi baya tabita da gudun tsiya ta rikota"haba Nanuta watsimenki ce fah kwalliya ce nasha ajiyar zuciya haja Nanu ta sabke" ai wlh ban gane kiba irin wannan kyau haka ke talatu ina kika shiga zo kiga Fatima fitowa tayi tana dariya" lallai kuwa munzo biki asa'a yo wannan bakida banbanci da indiyawa farine zasu Nuna miki buta teemah ta dauka ta shiga bayi ta fito ta daura Alwalla ta shige daki tayi sallah haja nanu ko teemah na gama sallah ta dauko wata kwarya mai tsumi ta ba teemah daket Tasha harda su kuka haja Nanu tana gama banka mata magani ta Mike" nanuta ni natafi gida daga zauwa duk kin cika mun ciki da magani aikuwa taga Nanu ta miki ta dauko kasko ta kwaso garwashin uwata ba kadanba" zahara matar wata ai dama kiranki ne zani taho haba babu lokaci baki yau da gobene jibi zaki gidanki hannuta ta kama suka shiga daki talatu na musu dariya ganyen tumfafiyane guda bakwai ta dauko Wanda akasha shafe jijiyoyunsu da man kadanya ta fara turara mata akasanta kakaf saida suka kare teemah kuka harda majina tsayuwa ta gagareta hajijiya take daukarta jikinta sai kaurin hayakim yake kasanta ko ya gasu tafi 30 minute akwance kafin take mik'ewa ta fito" ni natafi mun bata haja nanu tace" tafi can anaso agyaraki kina shegantaka gida da


kishiya ai Dole mugyara miki rayuwa wlh gobema sai anyi ja'ira baki ta tura ta tafiyarta jikinta duk yasaki gabanta sai motsi yake mata tana lumshe idanu daket ta isa gida gidan cike yake da mutane baki yan zauwa biki da yan sannu da zuwa teemah ba Wanda ta kula ta nufi kitchen ta kunna gas ta Dora ruwan zafi ta shige cikin daki ta dauko bokiti duk inda tayi kallonta ake yarinya duk ta canza tayi kyau ta zama fara iyayye tace"Auta babu magana ruwan ta juye ta fito tana kumbure kumbure" yo iyayye kinsa irin wuyar da haja Nanu ta bani kuwa ta fada tana shigewa daki dariya suka Mata Malika ta Mike ta bita har tashiga toilet zama tayi har ta fito Dan ba karamun gurza tama jikinta ba Malika tace" wai me haja Nanu tayi miki ne? baki ta turo batace komai tasaka Riga ta Dora hijabi "mijinki ya kira Mu'azzam yace ki buda wayarki da Sauri ta kalli malika" anki baza'a budeba yaushe Robon da ya nemeni shi me wayo yaga akusa kaini ko hahaha wlh ni nafisa wayo Tab Allah bazan kunna wayarba kuma ko yakira ata Abba ko ta yaya mu'azzam bazan daukaba baruwana dashi kowa yayi sabgar gabansa ta fada tana hawa saman darduma


ta tayar da sallah isha'i Malika tace wlh bakida wayo" ai sarara mikine yayi ki samu nutsuwa agyara masa ke da kyau kuma ai ko godiya kin masa yada ya hutar dasu Abba bayason komai sai matarsa shinefa yamiki komai na d'aki teemah masifa nacinta Allah Allah take ta gama sallah tama malika tana gama tahiya tayi sallama ko Addu'a bata yiba ta Mike" yo waye yasakasa Dole ai niya yayi Dan haka naki nayi godiyar ke nifa wlh ban wani matsuba yanzu ayau yace ya fasa ina murna yo auran mai mata dadine kinko ga yada suke manne junusu Tab ai wlh nide baza'amun iskanci ba nayi hakuri Ana wani rumgumemun mijina agabana Tab wlh tsaf zan koyawa mace hankali idanu Malika ta zaro🤔"wlh Fatima kitaka


asannu bazaki ja da babbar mace mai ji da komai irin Binta matar gwamna bana" taci abinda ba aso aikin banza aikin hofi yo matar gwamna ni matar wacece ai sai kifito ki fadi gaskiya kice abayan uwar gidan Haidar kike ba kina kwana kwana Allah sai na hadaki da Abbana ta fashe da kuka tayi waje baki malika ta rike ta fito iyayye na rumgume da teemah malika yace" iyayye kinsan wai me akayi? " ba sai kin bata bakinki ba Auta ki koyi hakuri kinji banda rashin kunya Abbane da mu'azzam suka shigo tare teemah ta Mike tayi gun Abba "Abbana ka ga Aunty ko? dariya yayi ya riko hannuta" kibarta Auta basai kin fadaba mu'azzam yace"hajiya watsime barka da dare ya amarci banza ta masa wayarsa ce ta dauki ringing yana dubawa yaga sunan Aliyu picking yayi ya Kara akunnensa yayi sallama ko me yace ma mu'azzam oho yace"eh tana kusa gata yaba Teemah wayar ganin Abbanta na kallonta ta amsa akunyace ta nufi daki ta Kara akunne cikin zazakar muryata tace"Assalamu alaikum batajira ya amsaba tace"yo meye ake wani bin didigina ni wlh babu ruwana dakai kuma wayar naki bazan kunnaba meye zakacemun ni fah na ma manta dakai kamar yada ka manta dani daga can bangaran Aliyu tunda


teemah ta fara masa tijara ya lumshe idanunsa saboda yada muryata ta Kara dadi tamkar sarewa haka yakeji shiru baice komaiba sauraronta yake yada take masa tsiwa kai tsaye har take cewa bazata kunna wayaba batason jin muryasa babu wani dadi murmushin gefen baki yayi can k'asa makoshi cikin wata irin murya yace" my Noor nagode zaki raina kanki idan kin shigo hannuna yanzu dai tambayarki zanyi zaki shiga jirgi azo daukarki aciki Dan nasan halinki zan iya turowa azo airport kice bazaki shigaba Oya bani amsa Bintu na jirana zatamun tausa dif na dauke numfashi dabas na zauna akasa Abu biyu zuwa uku sun dimautani dadin muryar my haidar da yada yake huromun iskar bakinsa akunnena tacikin wata yana sabkemun numfashinsa da salon maganarsa tamkar bayaso duk jikina ya Saki sai bakin cikin wai Bintu zatame tausa fashe masa nayi da kuka" wlh banason jirgin bazan shigaba Allah banaso bintun taka ta shiga akaita duk inda take so idan kunaso ma kucinye juna ina ruwana ko ajikina dama ni nasani bakuda aiki sai jaraba ni nama fasa auran na fada ina shashekar kuka idanu ya zaro k'asa yayi da murya "OK zan turo motoci zan kamaki ne ya fada yana sakar mun kiss ta wayar" I love you my noor yar babyna kitt ya tsinke kiran saida naci kukana na koshi na Mike na fito naba mu'azzam wayarsa


gun Abba na nufa na zauna"Auta amarya ya gajiyar hanya"Abba nifa dama an fasa bikin baki ya rufemun"Auta zamu bata dake dariya mu'azzam yayi mik'ewa Nayi na shiga daki iyayye ta Mike ta zubi abunci ta bita dakin Malika ta tashi ta zuboma su mu'azzam abunci shida Abba iyayye nacan tana lallashin Auta tana bata abunci abaki saida ta koshi tana mata wayo ai da zaran ango ya ganta da kansane zai rabu da ita tafa gano wayo suke mata shiyasa ta basar bayan ta gama cin abuncin ta dauko ruwan tsuminta Tasha suka fito Ana hira mareku na tsokanarta wai tazama kamar aljana Dan kyau sai karfe goma kowa ya kwanta teemah na jikin iyayye har tayi bacci da haushin gwamna aranta tana kisima yada bintu zata masa tausa su mu'azzam da Abba sun raba dare suna hira Abba yanata sama mijin watsime albarka yada ya temakeso yamusu komai na dakin yarsu samu shugaba irinsa zaiyi wuya haka sukayi ta hirasu har bacci ya daukesu,


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Nigeria karfe goma shabiyu na dare Aliyu kwance saman makeken gadonsa sanye yake da kayan bacci idanunsa lumshe bintu yake jira tundazu tazo tamasa tausa masifa nacinta taki zuwa har yagaji da jira shiko tunda yaji muryar Noor dinsa da shagwabar da tazuba masa da zallar kishinsa dake dawainiya da ita ga yarinta duk sai jikinsa yasaki yaji yana bukatar kasancewa da Noor dinsa yajita cikin jikinsa kansa ya dafe ko me ya tuna ya Saki murmushi da sallama ta shigo tana turo baki amsawa yayi idanunsa arufe zama tayi"gani bai bude idanunsa ba yace"sai yanzu kika ga damar zuwa to banaso tashi ki tafiyarki banza ta masa taki fita ta hauro saman gadon ta kwanta jikinsa tana masa tausar duk da yanaso ya basar" banaso bintu ki bari tashi ki koma wajan yarki kin dagashi tayi tana danna masa dan tasan mutikar ya nemi tausa yanajin ciwon jiki tureta tayi ya had'e face"wlh banaso awa biyu ina jiranki kinsan irin aiyukan da nayi cikin laptop tashi kiban guri duk sai nayi maganinku ganin ya burkice mata babu wasa a fuskarsa ta sabko ta tsaya daga kofar daki "Aliyu dan kayi aurene kake cimun fuska yo ni ina jegona ko wanka ban gama zubarwaba zaka takurani mik'ewa, taga yayi wuf ta fice da gudu murmushi ya saki yaja blanket ya rufe jikinsa yana Addu'ar bacci Bintu na shige room dinta ta murza key tana sabke numfashi ta haura gadon tasa Rauda da zahara tsakiyarta"wlh ina tausaya maki yarinya shegiya kucaka zaki zo kisameni baka bakar banza mijin bintu yafi karfinki haka tayi ta shirmanta da haukan kishi har bacci ya saceta Asubah ta gari,


**********************************


*Bayan kwana biyu*


Duk inda kake tunanin kyau din da teemah tayi to fah abun ya wuce haka dan ta dora daga inda hajiya mansurah ta koya mata da temakon Malika ga gyaran gargajiya da tsumi da haja Nanu da iyayye suke mata wlh teemah sai ta burgeka takuma baka tausayi dan ta tsumu sai zuba take tunba turaran tumfafiyar da haja nanu take mataba gaskiya babu laifi malika da iyayye da nanu sun gyara teemah tayi kyau iya kyau ita da kursiya babbar kawa suke iya shegensu cikin kayan lefenta saida taba kursiya less da su atamfa da dogayan riguna har kala biyar itace ta gyara kursiya dan da ita za'a rakiya Gombe jiya teemah taci kuka da, aka samata l'alle harda su dora hannu akai abin abun dariya kursiya tako biye mata sukayi tayi ai kamar daga sama sukaga Maheeda teemah murna kamar ta kasheta tabar kukan tashiga murna ai ranar kursiya nan ta kwana suka kwana suna hira teemah dariya kawai take basu idan tace batason auran amma bakinta sai kiran Haidar dinta take wai zata kamashine sai ya fadamata bintu tayi masa tausar ko bata masaba su Malika kirjin biki an kasa an tsare dan so take kanwarta itama taciri tuta wajan mijinta kamar yada itama tacira wajan mu'azzam d'inta


yau tin safe ake shagali kauyen garin sarki acike yake da yan kauyika kowa cewa yake Aradu bazai bar kalloba watsime mai Allo take auran governer din Nigeria aikuwa gari yacika su lado an dauki wanka nawalu ma yaci damara da tiran goronsa akofar gidansu watsime hayyo makadi tun da safe yakecin uwar ganga kida ake mata na casu yanzuma cikin kidan ake lado sai barin kudin kifi ake Teemah na hango cikin uwar daka taci uwar kwalliya fadar kyau ba'a cewa komai dakin cike yake maheeda anci uwar kwalliya su hanne anyi adon kauyawa teemah ta yatsina fuska" wlh hanne kina bamu matsala hakane zaki gaban hayyo makadin yan mata dallah malama jeki ki sauya kaya ko muje mucashe babu ke dariya maheeda tayi" don Allah my teemah kibari muje mu fansheki ai kursu nake jira tazo muje mucashe kar azo daukar amarya ban moreba hararata teemah tayi" Kut nifa yau bazan tafi ko inaba ehe Malika ce tashigo " wai ina kursiya hayyo mai kalangu yana jiran kawayen amarya, fa mucashe kursiya ce tashigo anci uwar kwalliya janbakin nan har hab'a da kudi ahannuta tana murna Malika tace"wai ina kika shiga babbar kawa baki ta washe"Aradu uwar garke naje kara dakaina na siyar yo Abu namu liki zanma hayyo makadi teemah dariya harda rike ciki ta kamo hannu kursu "bakida hankali duk nima banida kudin amma da na baki muje inga shegen da ya sayi uwar garke mu maida masa kudinsa yabaki akuyarki haka kawai tajata suka fice Malika na hanata ko sauraranta bata yiba gidan cike da jama'a kowa sai zuzuta kyaudin teemah akeyi dan wani dankareran material ne milk colour dinkin Riga da siket zatonsu gun hayyo zasu ai suna fitowa kofar hayyo ya kara cin uwar ganga yana wake teemah maheeda ta biyosu da gudu tana Kiran teemah amma bata sauraretaba hayyo yanaga zata wuce yako nufosa yana buga gangan sai wasa teemah yakeyi......... ✍🏻💃🏻Ladingo Yar Janaf ce🌹
















✍🏻...Ummu Fareesa ce😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*








*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________






*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger🤙🏻




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*














*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page2⃣2⃣*




......Teemah jin yada kida ke shigarta hayyo na kara nufosu kawai ta amshe kudin kursu na uwar garke ta shiga watsama hayyo kursu dadi kamar ya kasheta gurin ya kaure da ihu hayyo jin ana zuba masa cefa sai waketa yake" uwargida agun Aliyu gwamna kuma Amarya yarinya mai zubin indiya Teemah kai ya dauki zafi sai kada kai take Malika ce da maheeda suka ISO suka janyeta daga filin tana turo baki " ni kusakeni ta fada cikin tsiwa" wlh kirufawa kanki asiri labari ya iske mijinki mu'azzam ne yakiran maza, ajanyeki afilin kuma yace atashi taron kidan Malika ta fada suna shigewa cikin gida nawalu sai hawaye yakeyi yana ciza baki baisan watutunsa haka ta koma ba indiyaba hadi


Ne dangidan maigari yazo gaban hayyo mai kalangu yace" wasa yakare hayyo wlh kayi ta kanka meya kaika zuwa gaban matar gwamna kana yabon kyawunta maza atashi ga dakarunsa nan suna bakin gari zasu shigo daukar amarya ai tuni hayyo yabar kida ya kwashi ayarinsa sunbar gurin Teemah kuwa gida aka shige da ita sai tsiwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login