Showing 114001 words to 117000 words out of 129912 words

Chapter 39 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5822

wanke mata fuska har aka tashi taron sai da kowa ya watse kafin Safina ta cira kafafunta suka kasa daukarta sai gata ta yanke jiki ta fadi a gurin kawayanta biyu su suka ciccibeta suka kaita mota suka nufi gida da ita suna mata Allah wadai da ta yadda aka ci mata fuska cikin jama'a.


Teema da ita aka kai amarya Safina kallon arziki bata ma yan uwan Maheeda ba, ta ce bata daukar amanar kowa,Saida Teema ta kai Maheeda gidanta tikun tayi mata sallama zata tafi Aliyu yazo daukarta Maheeda ta kafa kuka Teema ba za ta tafi ba ta barta sai daket Antyn Maheeda ta banbare Teema daga jikinta ita kuka ita kuka haka Teema ta fito ta sharbar majina.
A mota ta isko Aliyu Boos ya bude mata ta shiga tana shiga jikin Aliyu ta fada ta rungumeshi tana sauke ajiyar zuciya.
Aliyu ya tallabo yana sunsuna wuyanta ya ce"Tau Babyna sannu ya gajiya Maheeda ce ta suka mun matata kuka To yi shiru yi hakuri mu je gida yanzu na miki wanka, ki ci abunci na miki tausa kiyi bacci"ya fada yana tura hannunsa rigar ta ya shafi cikin ta ya rungumeta gam yana sauke ajiyar zuciya, tausayinta ya cika masa zuciya.


Har motar tayi nisa Teema bata ma Aliyu magana ba ta dai manne jikinsa tana shakar sansanyan kamshinsa.
Aliyu ya ce"My Noor yar baby baza ki mun magana ba umm Babyna."a hankali muryata can k'asa nace "Wayyo ango ni karabu dani naki bana ma magana"Aliyu jin fitina Teema ta ke ji ya rabu da ita dan sai nukurkusasa take, tana so yayi abu kadan ta barke masa da kuka ganin hakan ya sa ya rungume a barsa gam yana shafa cikin ta yana mata sannu,ta yi banza da shi bata kula shi ba har suka iso gida.
Part din Bintu suka yada zango sun dan jima sosai Bintu ta kawo ma Teema kunun gyada da soyayen dankalin haussa ai kuwa ta ci sosai sai santi take Aliyu ya ji dadin yadda ba tai amai ba.
Sai karfe goma suka ma Bintu sallama suka nufi part d'insu.


Aliyu yana fitowa daga bathroom rungume da Teema ya mata wanka dan bacci take ji sosai har ta fara masa bacci cikin bath, wayarsa ce ta dauki ruri bakin gado ya zaunar da Teema, ya goge mata jikinta ya shafa mata mai ya dauko riga yar gutuwa ta bacci mai sulbi ko gwiwa bata kaiba, pink colour ya saka mata zaune yayi kusanta ya janyota jikinsa, yana tayarwa jelar kitson kanta yana, daure mata, wayar ta sake ringing, Aliyu ya ce"Yar Babyna kina kusan wayar bani na naga waye"Hannuna na beka ka na dauko wayar idanuna saman screen din wayar naga sunan Masa'udah na yawo baro-baro na beka masa,ya amsa amma ganin sunan ya saka Aliyu ya ki daga wayar ya kalli Teema da ta kifa kanta saman kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya, ya tallabo kanta ya ce"My yar Baby menene kar kiyi kuka kinji Amaryata, in miki tausa ko..? Kai na d'aga masa ina lumshe idanuna da suke cike da hawaye...
Wayar ta sake daukan ruri,na dago da kaina muryata na rawa nace"My chocolate ka dauka matarka ce maybe tana bukatar ka" na fada ina ke cewa da kuka na rungumeshi gam ina buga kaina kirjinsa.
A rikice Aliyu ya saki wayar ta fadi k'asa ya rungume Teema ya hauro saman gadon ya kwanta rai ran ya dorata saman kirjinsa, yana cewa"Oh my God yar Babyna tu shiru kalli ba ki da lafiya To meye na kuka yi hakuri kin ji matata bari kukan"shiru nayi na narke saman kirjinsa ya shiga lallabani da mun tausa ina zuba masa shagwaba har bacci yayi a won gaba dani.
Aliyu ganin Teema tayi bacci ya kwantar da ita ya sakar mata kiss saman goshinsa da lips dinta ya mike ya sauko daga saman gadon ya nufi bathroom.
Yana fitowa ya isko wayar na wani ringing, ya dafe goshin sa a hankali ya furta "Ya Allah gani gareka"ya nufi gun wayar ya sunkuya ya dauka Masa'udah ce dai wannan kiran shi ne na sha biyu,picking yay ya kara a kunnansa,ya ce"wai don girman Allah me kike so kuma da yamma ba naje na ganki ba muka yi sallama sai gobe idan kin shigo amma kike so tayarmun da fitina, haba Masa'udah, To fadamun me kike so..?" Shashekar kukanta ya ji tana cewa"my love ka zo yanzu wlh a kawai matsala babba in ko so kake na mutu shikenan"idanu Aliyu ya zaro ya ce"ni bazan fito ba a wannan tsohon daran meye ya sameki?" ya fada yana kashe wayar, baki dayanta yana sakin murmushi, ya nufi wardrobe ya ciro jallabiya fara tas ya saka ya fesa turare ya nufin gun sallah ya hau kan dadduma ya tayar da sallah nafila.






Bangaran Maheeda da Nuradeen kuwa bayan kowa ya watse ya hadasu domin yi musu nasiya, amma sai da suka sha dambe da Safina kafin ya nufi gun Maheeda Safina ihu take, jajir kamar mahaukaciya, shiko Nuradeen ko a jikinsa ya nufi gun Amaryarsa, Maheeda bayan duk sunyi abin da ya dace bisa koyarwa manzon Allah Nuradeen ya shiga nuna ma Maheeda salo-salo tafiya da tayi tun tana nokewa har ta bada kai bori ya hau.
Lokacin da Maheeda taji labari ya canza ta shiga dukansa da yago da cizo da kuka da neman ceton Allah tana ta fasa auran amma ina malam Nuradeen bai san inda yake ba Safina kuwa tana labe tana junsu sai kuka take ta kasa barin gurin Nuradeen kuwa sai sambatunsa yake yana cewa bai san mata ma suna suka tara ba sai yau, nan ne Safina ta fice da gudu tana kuka Asubah ta gari............✍🏻Nuradeen and Maheeda Safina a je ayi bacci tunda kin ji abinda kike son ji.


💃🏻Yar gidan Janafty ce💋




*2/March/2020*




Rahma ummu Fareesa✍🏻✍🏻✍🏻




*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*








*بسم الله الرحمن الرحيم* ____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger🤙🏻




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*










*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page 4⃣7⃣*




.....Safina yanda taga rana haka taga dare ba tai bacci ba, tsabar kishi da tashin hankalin da ta shiga baya faduwa, jin irin sambatun da Nuradeen ya ke a kan Maheeda.
Bangaran Aliyu kuwa sai karfe biyu ya gama ibadarsa, da nema kusanci gun Allah, bayan ya gama Addu'o'insa ya mike ya cire jallabiyar jikinsa, ya saka kayan bacci, ya fesa turare ya hauro saman gadon.
Ya saka Teema cikin jikinsa ya rungumeta gam jikinsa, yana tofa musu Addu'ar bacci, hannusa saman cikinta yana shafawa yana gama karanto Addu'ar ya lalubo bakinta ya fara tsotsar yaja musu blanket ya lulubesu yana kissing dinta yana shafar breast dinta.
Teema baccinta take cikin nutsuwa ta zagaye hannunwanta bayansa.
Aliyu ya jima sosai yana shan bakin Teema kafin ya saki, ya matseta gam sai bacci.
Asuba ta gari. Bangaran Masa'udah kuwa bayan Aliyu ya kashe wayarsa tayi yar dariya ta fada saman bed,tace"My love kawai tsokanar soyayya ce nake maka lfy ta lau mijina Allah kaimu jibi babu d'aga k'afa my love" ta mik'ewa ta shiga bathroom, sai wani anushuwa take.


******


Bayan kwana biyu yau a ke biki na kece raini gidansu Masa'udah wlh bakina bazai iya fadar jama'ar da Alhaji Ibrahim mai dala ya taraba bikine a ke na yar gata Masa'udah tayi kyau har ta gaji kafin safe zauwa yanzu da yamma ta saka kaya sunfi kala goma sai shige da fice take tare da kawayanta,
kallo daya zaka Masa'udah kasan lallai fa suna ji da nera duba da irin kayan da ta ke sakawa,tayi kyau na uban mamaki ta hadu sosai ba karya.
Hajiya Falmata ma sai shiga take tana fita sutura ta ke ce raini, anyi walima mai kayatarwa sosai a cikin gidansu.
karfe biyar suka tafi dinner tare da kawayanta da yan uwanta na matane zallah anci ansha anyi raye-raye abin gwanin burgewa sai dab da magarib suka tashi inda aka dawo a ka fara shirya amarya domin zuwa gidan mijinta.


***
Bangaran su Teema ma haka suka yini kowa a part d'insa tare da yan uwansa Ana basu baki.
Teema ta saki ranta ta maida komai ba komai ba wannan ko aikin hajiya Mansura ne da Malika sosai sun nusar, da ita karta yadda tayi haukan kishi tunda mijinta na sonta ta ko hakura ta saki ranta tasha kwaliyarta, abin ba karamin dadi ya ma Aliyu ba.
Bintu ma hakan ce ta watsar ta basar bata yi irin na auran Teema ba ta saki ranta da yan uwanta da kawayanta har yamma aka watse ba wanda zai ce yaga damuwarta.


Bangaran Maheeda da Nuradeen sosai taji jiki amma yadda yake bata kulawa cikin kwana biyu ta warke suna shan soyayyarsu sai dai bai kara kusantarta ba.
Safina tayi haukan ta gaji tunda Nuradeen ya barazana da saki ta ajiye hankalinta tana kula da yaranta amma ko kallon arziki basu isheta ba daga Nuradeen din har Maheedar.


Karfe tara dai-dai motocin daukan amarya suka isa gidan su Masa'udah.
Masa'udah ce rungume jikin Papi yana mata fadan ta zauna lafiya da mijinta da kishiyoyinta banda fada duk da yasan ba halinta bane, ta kiyaye duk wani abu da zai kawo sab'ani tsakaninta da mijinta ko abokan zamanta.
Kuka take sosai ta ririkeshi, shima kwalla yake.
Falmata ta banbare Masa'udah a jikin papi ta ce"Don Allah kuyi hakuri ba fa rabuwa kukayi ba, Auta maza ku tafi ana jiranki ina miki fatan Alkhairi Allah baki zaman lafiya, da kwanciyar hankali cikin gidan auranki ki rike duk a bubuwan da na fada miki zaki ci ribar rayuwa, Hajiya Yagana ku je Ana jiranku"ta fada tana sakin Masa'udah wacce take kuka wi-wi, Falmata d'aki ta shiga itama kukan take. Haka a ka fitar da Masa'udah a ka sakata mota tare da yan uwanta da babbar kawarta Nazifa, motocin suka nufi gidan Aliyu gwamna wato government house.


Har suka iso gidan Masa'udah kuka take ba yadda hajiya Firdausi batayi tayi shiru ba tako haka suka iso gidan.
Bayan sun fito daga cikin mota a ka nufi part din Masa'udah wacce mashigarta daya ce da Bintu.
Da sallama suka kutso cikin parlon.
Bintu da suke zaune daga ita sai Mamu da Farida suka amsa cikin sakin fuska suka basu gurin zama, sunji dadi sosai bayan sun gaisa
Hajiya Firdausi ta ce"To ga kanwar ki mun kawo muku dan Allah ku zauna lafiya kuyi hakuri da juna amatsayin ki na babba idan tayi kuskure kisata a hanya , ke kuma amtsayin ki na k'arama kiyi biyayya gare su."
Bintu tayi murmushi ta ce"Ba komai Allah ya bamu zaman lfy"suka masa da "Amin Firdausi ta ce"ina ne bangaran d'ayar muku kaita...? Bintu ta kwatanta musu, sai sun fita.
Haka ko sukayi suka sake fita suka nufi part din Teema, son jima suna buga kofar kafin a zo a bude Malika ce ta taresu.
Bayan sun gaisa nan ma hajiya Firdausi ta dora da nasiya tana mamakin k'aramtar Teema a she yarinya ce sosai sai dai fa sun sha mamakin madarar kyau irin na Teema da yadda ta tarbe su cikin girmamawa tako amshi amanar Masa'udah, cikin farin ciki suka baro part din Teema.


Suna dowa wa suka shiga part din Masa'udah, wow nera ta sha kashi buro uba kam dan carpet din parlon Masa'udah kadai abin kallone bare a kai ga sauran a bubuwan kai mai karatu ka Kisima haduwar dakin Masa'udah, da kanka.
Bayan sun gama sake mata nasiya hajiya Firdausi ita da yagana suka bar Nazifa tare da Masa'udah har yanzu kuka take.
Mamu bayan kawo amarya suka tafi gida ita da Farida kawar Bintu, sai ita sai yaranta suke zaune a parlor.
Sai karfe 11:00pm, Aliyu ya saka aka maida kawar Masa'udah gida daket ya banbare ta daga jikinta ya samu Nazifa ta tafi ya rarashi Masa'udah ya fito.
Teema ce tsaye gun motar su Malika zasu tafi lokacin sha biyu saura dan Aliyu ya kira Malika ya ce su lallaba mashi ita kar su tafi da wuri. Mu'azzam yana tsokanarta bata ce masa komai ba, murmushi tayi, ta ce"Yaya Mu'azzam bazaka ga kuka naba wlh"dariya suka mata Mu'azzam ya ce" Ai kuwa yau kam kin bani mamaki kanwata gaskiya naji dadi sosai Allah ya qara miki lfy"Malika ta ce "Amin"Teema tana tsaye sai da motar su Malika ta tafi, ta juya ta nufi part d'inta.


Tana dab da shiga taji an dauketa cak.
Baki ta bude zata kwarara ihu Aliyu yayi sauri kame lips d'inta yana tsotsa.
A jiyar zuciya ta sauke jin Aliyu ne Teema tayi luf jikinsa ta lumshe idanunta ta sakalo hannunta wuyansa, batayi magana ba har suka shige ciki.
Ya zare bakinsa a nata, ya nufi kujerun parlon ya zauna tana jikinsa ya wani manneta yana sunsunata.
A hankali ya kiranta"My Noor yar baby kinci abunci kuwa...? Shiru nai masa na kara shigewa jikinsa zuciyata na wani irin bugawa da karfin gaske...
Aliyu ya tallabo kanta ya kura mata idanu ya shafi cikinta, ya ce"Babyna kinci wani abu pls yi hakuri ki mun magana, dan Allah karki sakani damuwa my yar baby"D'ago da kaina nayi na danne kuka na kura masa idanu son sa da kaunar sa na ragargaza mun zuciya, nace"My chocolate karka damu naci abunci Anty Malika ta bani naci pls karka damu da damuwata ka a jiye hankalinka kaje kayi a binda ya ke gaban ka"na fada ina k'ok'arin mik'ewa, ya riko ni.
Ya ce"Oh my Noor Ok muje part din Bintu mu dawo sai kuzo na miki wanka na saki bacci" Fuska na kwakwab'e zan fara kukan sangarta ya mike dani tsaye yana jijigani kamar jaririya, ya ce"Sorry baby Haidar dinki ne ya tab'a ki ko...?kai na d'aga masa ina kara makaleshi.
Murmushi Aliyu ya saki ya rungume Teema gam yana tafiya da ita bakinsa saman kunneta ko me yake fada mata sai kyalkyalata dariya take tana wutsul-wutsul a jikinsa shi ko yaci gaba da mata radar a kunneta tana dariya.


Babbar kofa Aliyu ya bi a haka suka fito yayi hakan ne, dan ya sa Teema farin ciki.
Ko da ya shigo part din Bintu bai a jiye Teema ba sai da ya zo har kofar parlo.
Ya sauketa ya gyara mata mayafin ta ya rungumeta yana shafa bayanta ya kai bakinsa saman kunneta ya ce"My Noor ki saki ranki ina sonki babu misali kema kin sani Babyna dan haka karki damu kanki kinji Sahibata" Kara shigewa jikinsa nayi na ce"My chocolate wlh bazan damu ba, zan jure rashin ka mijina" murmushi Aliyu yay ya ce"Yauwa a bar kaunata"ya fada yana sakinta ya kamo hannunta ya danna madanin glass din kofar suka shigo hannunsu sark'e da juna suka shigo da sallama.


Lokacin Bintun har ta shige bedroom yaranta sunyi bacci dan dare yayi sosai.
Aliyu ya zaunar da Teema saman kujera ya kalleta, ya ce"Babyna bari na kirasu"idanu Teema ta lumshe ta d'aga kanta.
Aliyu da sauri ya bar gurin bayaso yaga kukanta dan yana cewa ya rarasheta kuka zata saka masa, shiyasa yake mugun tausayinta, bedroom din Bintu ya nufa.


Yana shiga ya hango Bintu saman bed kwance rungume da zahara idanunta a lumshe. Bakin gadon ya matso ya sanya hannuwansa ya zare zahara ya kwantar ya tayar da Bintu zaune.
Sai lokacin ta bude idanunta ta kallesa, murmushi ya sakar mata ya mikar da ita tsaye ya ce"Muje yanzu sai ki dawo ki kwanta kinji my Bintu matar Aliyu Damba" Murmushi Bintu tai bata musa ba ta dauki hijab ta saka ya kamo hannunta suka fito.
Suna fitowa ya saki hannunta ya nufi part din Masa'udah yana dafe da kansa har zuciyarsa mata uku sunyi masa yawa a halin yanzu amma ba yanda ya iya da kaddara ubangiji.


A nade ya isko Masa'udah cikin blanket, ya iso bakin gadon ya janye blanket din ya ce" Masa'udah taso mu tafi" mik'ewa Masa'udah tayi Aliyu ya kamo hannunta ya gyara mata lufayar jikinta mai fitar da wani sihirtaccen kamshi tayi mata kyau sosai ta fito da kyawun dirinta tsafa.


Bintu na kusa da Teema suna hira su harda dariya Teema ta dora kanta kafadar Bintu, Bintun na laluba mata kitson kanta tace"My zahara amma kitson a kwai zafi ko...? Teema zatayi magana Sallamar Aliyu ta saka bata bata amsa ba.
Kusan Bintu ya zaunar da Masa'udah shiko ya zauna kusan Teema ya ce"To Alhmdllh ina ma Allah godiya a kan kyautar da ya sake bani na karba hannu biyu don Allah ina rokon ku ku zauna lfy ku bani kwanciyar hankali kunga ba kullum nake da lokacin kaina ba so dan Allah ina so ku zauna lfy da junanku, ke Bintu kece Babba kuma inajin dadin yadda kike zaune da zahara lfy To inaso yanzu ma a dora daga inda a ka tsaya.
My zahara ke yanzu kinga kema kin zama babba dan Allah ki rike kanwar ki ku zauna lfy duk da nasan shekarun ku ba daya ba amma ta fanin wannan Allah ne ya ba ki girman zaki iya mata fada idan tayi ba dai-dai ba, ke ma Masa'udah ki bi yayunki sauda k'afa banaso rigima a gidana wlh duk kowacce ta tayar mun da hankali zan a jiye so gefe na hukantata karku ce ban gaya muku ba" Teema da Bintu suka hada baki suka ce"Haba My Gwamna namu kayi hakuri babu wani a bu da zai faru tunda muna son mijin mu dole zamu zauna lfy"suka fada suna kallon junansu suna sakin murmushi.
Aliyu ya kura musu idanu ya girgiza kai.
Masa'udah dai kunya ta cikata magana shiru tayi.
Bintu ta ce"Ah amryarmu ba magana" Masa'udah ta ce"Anty ina yini"Bintu ta amsa tana murmushi.
Teema ta kauda kai ta tab'e baki , Aliyu yana lura da ita, murmushin gefen baki Aliyu ya saki Babynsa badai kishi ba.


Teema ta mike ta ce"To Antyna amaryarmu Allah bamu Alheri bacci na keji sai da safenku"ta fada tana tafiya.
Bintu ta ce"Asabu ta gari"ta fada tana mik'ewa tama Masa'udah sallama ta nufi bedroom dinta.
Aliyu ya ce da Masa'udah"jeki ki yi shirin kwanci yau kin samu a binda kike so"idanu Masa'udah ta zaro ta mike a tsorace ta nufi bedroom gabanta na faduwa.
Aliyu ya girgiza kai ya ce"Yarinya ai baki zaro idanuna ma sai anjima ya fada yana sosa gefen kunnansa yana sakin murmushi, ya mike ya nufi bedroom dinsa saida ya gama shirin kwanciya tsaf ya dauki ledojin kajin har guda uku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login