Showing 108001 words to 111000 words out of 129912 words

Chapter 37 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5814

yayi wani irin sauri, ya taro ta ta fada saman kirjinsa male-male, ya rungumeta sosai ya ce "Baby Sannu ki rika bi ahankali"ya fada yana kunce mata daurin fuska ta.
Teemah kuwa jinta ajikin Aliyu ta safke numfashi ta rukumkume shi gam ta cusa kanta kirjinsa duk ta tsorata, zaton ta faduwa zatayi.
Ashagwabe ta ce"My chocolatyna naji tsoro ashe garkuwata yana kusa dan, wayyo my Haidar nawan i love you"ta fada tana kara shigewa jikinsa ta zagaye hannayenta ak'ugunsa.
Aliyu ya kunce mata idanunta yana sakin murmushi, ya janyeta daga jikinsa, yana fadin"Baby Noor dawo haiyacin ki bamu kadai bane" ya fada,kunya duk ta cika sa gaban yaransa dan sam da farko ya manta da inda suke, Teemah ita ma kunya taji bata kalli Aliyu ba, ta kalli yaran suna dariya ta nufi gun Asif tace "Asif na bika bashi yanzu na tsorata bazan yi ba." Ta fada tana dariya.


Shima dariya yayi yace" Momy nafi ki wayo baza ki kama ni ba" ya fada yana cewa" dady i miss u"ai kuwa gaba ki daya yaran hankalinsu yayo kan mahaifinsu da gudu su hudun duka suka nufesa ya ware masu hannuwansa, yace" i miss u too yaran Albarka kuka kusa saka momy ta fadi ko." Suna isowa suka fada jikinsa suna dariya ya rungumesu baki dayan su yana musu kiss, sun makaleshi suna dariya.
Teemah ta iso gurinsu tana dariya tace"kar ku kayar da dady mana ni baza ku min ba ko To nayi fushi bari na tafi gun Antyna"Teemah ta karasa maganar ta nufin gun Bintu. Rauda da muneerat suka biyu Teemah da gudu suka, rungumeta suna dariya Rauda tace "momy kin fiye tsoro" Murmushi ta saki ta ce" ba dole ba" Aliyu ya kamo hannun mucotar da Asif suka nufo gun Bintu.


wacce takai ci da bakin ciki da wani mugun kishi ya ke cinta ranta amugun bace ta ajiye zahara, wacce take bangala dariya ta mike, tana mik'ewa zahara ta fashe da kuka, Bintu ko ta kanta bata bi ba ta nufi bedroom, Teemah ta saki yaran ta nufi gun zahara tana cewa"Anty kuka fa take" ko kallonta Bintu bata yi ba ta ci gaba da tafiya, Aliyu yace" My Bintuna dawo ki dauke ta mana" juyowa Bintu tayi ganin yaran basa kallonta ta watsa ma Aliyu wani mugun kallo ta juya ta shige bedroom d'inta ta murza key.
Sororo nayi cike da mamakin kallon da Anty ta watso ma Haidar, amma na basar na dauki zahara ina jijigata na dora ta akafada tayi shiru tana safke ajiyar zuciya, Muneerat ta ce"wai zahara tasan momy"
Aliyu bai yi magana ba ya zauna yace"my zahara kawo ta mu gaisa"Teemah bata yi musu ba ta bashi zahara ta zauna nesa dashi, yaran suka bai baye shi suna ma zahara wasa tana bangala dariya Aliyun ma dariya yake.


Teemah kuwa da idanu take binsu ta mike tsam bata yi magana ta nufi bedroom din Bintu dan sam bata ji dadin yadda Bintu tayi ba sai take ganin kamar ita ce ta bata mata rai.
Bintu kuwa tana shiga dakinta bathroom ta shiga, bayan ta fito ta zube saman bed ta saki kukan takai ci wai Aliyu yau agaban ta ya ke cewa wata Baby Noor dinsa kenan ita, duhun sa ce ko? ranta a mugun bace yau yake dan Teemah da Aliyu sun kaita bango iskancin su ya isheta tunani take ko ta dawo musu Bintu ta sak, dan taji ciwon abin da suka mata jiya da yau, juyi ta fara tana ciza baki tana kukan ta.


jin Teemah na bugun kofa tana kiranta, yasa ta mike ta je, ta wanko fuskata ta nufi dressing mirror ta gyara fuskata ta zo , ta bude sam fuskata ba wal wala.
Teemah zata shigo tana cewa Anty lfy kika bar zahara tana kuka kuwa" Bintu ta yamutsa fuska tace" lau me kika gani" Teemah tayi murmushi tace" naga duk kin can za ne." Bintu ta kamo hannunta suka fito.
Tace" ni ban can za ba kam Fatima sannu ya jikin ki..? Teemah ta ce "da sauki" zama suka yi suna tab'a hira sama sama Aliyu ya ba Bintu zahra tana shayar da ita.


yaran kuwa Aliyu ya korasu su dauki karatu gobe akwai school, idan suna magana da Teemah Aliyu yana saka baki Bintu zata bar maganar, shiyasa ya sharesu ya dauko laptop ya kunna yana abinda zai k'ara shi gefe daya yana amsa waya da jama'a.
Teemah ta kalli agogon bango taga karfe 11:00 pm na dare.
Teemah ta zaro idanu ta mike ta kalli Bintu tace "Anty mu kwana lfy wlh zazzabi na keji sai da safe"ta fada tana tafiya.
Bintu tace "Allah ya kaimu"ta fada tana mik'ewa tsaye ta nufi bedroom, cikin zafin nama, Aliyu ya mike ya bita aguje dan yasan rufe kofa zata yi.
Bintu cikin sassarfa ta karasa, kofar ta murda ta shige, amma kafin ta murza key, Aliyu ya shigo ya matse ta a bango.


Ya ce "Wai my Bintuna me na miki kike wani shareni bakya min magana nayi miki laifi ne..? Cikin da jin haushinsa Bintu tace"Dallah malam sake ni ka matseni ko baka ga yarinya bace a hannuna"ta fada tana kokowar ya sake ta.
Ya kara matse ta, yace"Baza a sake ki ba me aka miki kike kumbure-kumbure"ya fada yana daukar ta cak ita da zahara ya nufi bakin gado ya ajiyeta, ya kwantar da zahara ya rungume Bintu ta fara kiciniyar amshe jikinta tana kuka tace"ni fa na fita sabgar ka kaje kayi duk abinda zaka yi wlh babu abinda ya dameni duk wata rawar kafa da rawar kai da kake wanne ne ban ganiba Aliyu idan kana so ka karo wata macan daya ka cike hudu ai ba akai zasu zauna ba aikin banza aikin hofi sauran da suka samu, meye na d'agawa"ta fada tana kokowar ya saketa.
Aliyu murmushi ya saki dan yan zu ya gano yau Bintun sa kishin ya motsa dole ya lallaba abarsa, kara rungumeta yayi gam ya fara lallashinta da kalamai masu dadi amma fur yau Bintu ta kiye masa dan asama take sosai babu yadda bai ba ya shawo kanta taki dole sai hakura yayi bayan yayi kissing dinta shi ya mata wanka ya saka mata kayan bacci ya kwantar da ita ya rungume mata zahara ya mata sai da safe, ko kallo bai isheta ba haka ya bar dakin ransa babu dadi dan yasan taji ciwon abinda ya ma Teemah gaban ta lokacin sam ya manta da kowa da komai dole zai lallasheta har ta safko tunda shi ya bata mata dama ga na turare.


Aliyu yana fita dakin yaran sa ya je lokacin har sunyi bacci dan sha biyu ta gota, Addu'a ya musu ya rufo kofar ya fito ya shiga na su muneerat, suma sunyi bacci Muneerat tana rungume da Rauda, Addu'a ya tofa musu, ya rufe kofar ya fito.
Ya je ya rufe kofar babban parlo ya dawo ya bude karamar kofa mai had'e da parlon Teema ya shiga ya rufe ya je ya rufe kofar parlon ya haye saman bene.


Teemah kuwa tana zauwa saida ta shiga kitchen ta dafa indomie taci tasha lemo tayi dam ta haye saman bene tayi wanka ta shirya tsaf cikin wata rigar bacci milk colour iya gwiwa tana da kyau mutika, ta yi kwanciyarta saman makeken royal bed dinsu, na bacci, tana latsa wayarta tana jiran Aliyu, shiru bai zo ba ta cika tayi fam ta wur gar da wayar ta shige cikin blanket tana sauke numfashi tana juyi wani mugun bacci take ji amma ta kasa sai juyi take.


Ahaka Aliyu ya iskota yaga sai birgima take tana nade cikin blanket.
Baiyi magana dam ya shige bathroom yayi wanka agagauce ya fito.
ya goge jikinsa ya murza mai hankalinsa gurin Teemah yadda yaga tana birgima daga farko gado zuwa karshen gado tana nishi da shashekar kuka.
Akidime gwamna ya saka kayan bacci, ko da wasa bai fesa turare ba,ya hauro saman gadon ya janye blanket din ya ciccibeta yana fadin"yar Babyna menene? me ya sa miki pls yi hakuri fadamun my Noor tawan."ya karasa maganar ya rungumeta.


Yana sunsunata ya had'e face d'insu yana hura mata iskar bakinsa, yace"Babyna menene ya saka min autar mata kuka wlh kukan ki yana saka ni Cikin tashin hankali mamar Babyna yi shiru ki fadamun me nayi" ya fada yana shafa k'asan wunyata yana hura mata iskar bakinsa, suna shakar numfashin juna.
Teemah tayi tsit da kukan ta narke ajikin Aliyu ta zagaye hannuwanta abayansa, tana safke ajiyar zuciya, ashagwabe tace"my chocolatyna ina sonka ina kaunar ka wayyo my Haidar nawa bana son rashin ka, akusa dani duk sai na zauce na ahaukace na gigice na dimauce na susuce hankali na ya tashi na rasa nutsuwa ta My Gwamna na i love you pls karka barni idan amaryarka tazo hauka zanyi My Haidar mutuwa zanyi idan babu kai rayuwata sonka nake kishin ka na azalzalar zuciyata Mijina ka rungumeni sosai ka rarasheni kaji My chocolatyna" ta fada ta kara rungume Aliyu tana kara,
shigewa jikinsa tana safke tagwayen ajiyar zuciya.


Aliyu kuwa da ya gama mutuwar zaune Teemah ta kasheshi da kala manta ta fasa masa kai ta gama zuzu tashi, matseta yayi jikinsa sosai yana shashafata ya kai bakinsa saman kunnanta cikin wani irin yanayi na shaukin kauna ya ce" wayyo my duniyar dadina my yar Babyna noor i love you My Teemah wlh kina dab da haukata ni da kalaman ki, sonki da kaunar ki ajinina yake my Noor wlh kece duniyata kece rayuwata My Fatina wlh babu wacce ta isa tasa na juya miki baya, da izinin Allah ki kwantar da hankalin ki Tawan zuciya Haidar dinki taki ce" ya fada yana sakar mata kiss akunneta, yana murza k'asan wuyanta zuwa fuskata da kitson kanta, cikin wani irin salon love.


Teemah ta wani narke ta manne jikin Aliyu tana jin dadin yada yake lasar kunnanta da shafarta, cikin sangarta da shagwaba Teemah ta kirasa, "My chocolatyna"Aliyu yace"Na'am yar Babyna mijin kine ya saka ki kuka ya jima bai zo ba gurin Babynsa, to kiyi hakuri kinji Babyna , kina son Mijinki dayawa ko..? Babyna." Cikin shaukin kaunarsa Teemah ta dago da kanta ta kamo fuskar Aliyu ta kura masa idanu tana shafa kyakyawar fuskarsa, tace"my Haidar ina sonka sosai wayyo my chocolatyna yan zu itama matar kace kana sonta ko Aliyu wayyo kishin ka zai kasheni yau kishinka nake Allah kuwa." Teemah ta karasa maganar tana barke ma Aliyu da kuka ta dora bakinta anashi ta fara tsotsa tana kuka.
Arikece Aliyun ya tallabo kanta ya kamo harshen ta ya na tsotsa, amma Teema taki daina kuka, dole Aliyu ya zare bakinsa ya kwantar da ita ya mata rumfa da kirjinsa, duk yabi ya susuce, ya ce "My Noor don Allah ki yafe ni pls bari kuka wlh ni ke na ke so yar Babyna shiru abin ki Aliyun ki ke ya ke so zan sauke mata hakkin da Allah ya dora mun kawai zan safke akanta domin na tsira agobe kiyama... cikin ihu da d'aga murya,Teema tace" to kabar fada mun wlh zan haukace maka to ina ruwana...bakinta Aliyu ya kame yana tsotsa yana murzata cikin wani irin salo,ya saki bakinta yace"Wayyo Yar Baby sweet yawunki baya isata, yauzu dai bari damuwa ko baki san kina da ciki na ba Baby kin yi ciki yau sati uku da kwana uku wlh shiyasa nake kara kaunar ki saboda akwai ki daukan seti ni da Yar Babyn Matata bama wasa, Oya yi dariyar murna mun samu Baby."ya fada ya maida kansa saman cikin, Teema ya since igiyar gaban rigar ta ya dora bakin sa, saman cikinta yana kissing dinta da shafa cikin da, murza k'asan marata ya zura harshesa ramin cibiyarta yana lasa yana mata kiss hannunsa daya yana mata chakulkulo sai ga Teema ta zage tana kyalkyalata dariya.


Cikin wuyata tace'' Abbun Babyna ka bari wayyo ciki zai kulle" da sauri Aliyu ya d'ago yana dariya ya haye samanta ya had'e face d'insu yace"Sorry My Ruhina amma ni dai ki ce mun chocolatyna yafi dadi, kinji Antyna."haba me Teemah za tayi idan ba dariya ba ta makale Aliyu tana kyalkyatar dariya tana dukansa cikin wasan soyayya tace" To Bari na ba dan gidan Anty Teemah kashi" haka suka lalace suna kokoyi suna dariya sai da yaga Teema ta manta duk wani bacin ranta sai murnar ciki da take ya rabo da ita ya dorata kirjinsa yana mata tausa tana zuba masa sangarta iri-iri da dan kokoyin su.


Kwance take saman kirjin Aliyu suna hira yana shafarta, bayan sun gama kokoyin, Teemah ta shagwab'e tana nan nagar Aliyu tace"My chocolate Abbun Baby Allah kuwa, kasan me..?caraf ya kame bakinta ya fara bata hote kiss, babu bata lokaci ta biye masa suna shan yawu da murza junansu, cikin shaukin kaunar juna.
Wani irin romance sukewa juna mai tsayawa azuciya baki dayan sun zauce sun zauta juna sai safkar numfashin su akeji. Teema an lola wata duniya, bata tan-tan ce ba ta juyo Aliyu yana Addu'ar saduwa da iyali kafin ta dawo haiyacin ta taji shi cikin jikinta har ya shiga, lumshe idanu tayi tana safke ajiyar zuciya, Asubah ta gari Aliyu and Teema asha bidiri lfy.


**************************************
*Agurguje bayan wata daya da sati daya*


Bayan wannan lokacin laulayi ya saka Teemah gaba dan ba karamar wuya ba take sha, gashi Aliyu bai cika zama agari ba shiyasa da zaiyi tafiya har tsawon kwana goma ya kai Babynsa gidan Malika ake kula masa da ita har ya dawo. bangaran Bintu da Aliyu an kai, ruwa rana kafin ya samu kanta ta safko ya kuma gane me ya bata mata rai itama ta ta fadama mamu matsalarta dan ta gaji da jan tsakin da Aliyu yake mata idan yana saduwa da ita, mamu ta sakata ahanya tayi mata fada me yasa duk zaman da tayi da mijinta shekaru sha biyar bata tab'a fada ba to ba laifi duk da Aliyu baya zama sau uku suka sadu tayi iya kokarin ta wajan yi masa yadda yake so ba lai fi kuwa ansami canji wani abun ta ajiye ne sai amarya tazo.


Bangaran Masa'udah kuwa sau biyu rak suka hadu da Aliyu, shima ko da wasa bata yadda ta zauna kusansa dan har yanzu kunyar sa take duk da tana so ta rungumesa shiko dadi yake ji da bata rungumarsa, bare Noor dinsa taji kamshinta tayi amai.
Aliyu ya ba Masa'udah kudin akwatina 2million su hado komai.
Masha Allah kuwa dubai suka tafi da iyayanta sun mata odar gadaje guda biyu masu masifar tsada da kayan kitchen, da na daki akwatina set hudu Masa'udah ta hado na kece raini masu tsadar gaske, saida suka kwashe sati daya cif à dubai suka dawo gida yau kwana su biyu da zuwa shi kuma Aliyu baya gari suna waya, dai yace idan ya dawo zai zo ya dauka ya kai gidan Antynsa.
Masa'udah sun fito da anko masu kyau da tsada ita da kawayanta dan biki ne na kece raini za'ayi Agidan Alhaji Ibrahim mai dala, ba laifi Falmata tana gyara diyarta cikinta da wajanta.


Nuradeen da Maheeda soyayya babu kama hannun yaro yayin da aure yake kara gaba towa, Maheeda sai shirye-shirye ake ita da Teemah duk ba lfy bace da ita haka take daurewa su tsara yadda Abun zai tafi sun fito da anko Teemah ta kira Aliyu ya bata izini su tafi kasuwa aikuwa tasha masifa ya haukace mata ta waya daket ta samu kansa ta bashi hakuri, ya safko daga fushi Malika dariya kawai take musu.
Bangaran Safina tabi malaman har tagaji babu sauyi dan har wani kauye taje gun wani k'asurgumin boka yace sai yayi anfani da ita bukatarta zata biya taki dan Safina ta tsani zina, dole ta hakura ta dawo amma da kudirin kafin auran sai ta wargaza komai.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Yau ta kama weekend ne tun safe Bintu ta kwashi yaran ta suka tafi can gidansu suka yini aka yi musu kunshi da kitso.
Zaune Bintu take tana ba zahara nono, mahaifiyarta ta kalleta tace" Fatima Bintu wai bazaku gida ba sai dare yayi ba kince yau ya ke zauwa ba." Bintu ta yamutsa fuska tace"Mamah fada kawai yayi ba laila ba ya zo, amma bari na kira direba ya zo mu tafi"mamah tayi murmushi ta girgiza kai tace"Fatima ina fada miki ki kama kanki ki kama girman ki duk da naga kuna zaune lfy ya jikin Zahara din..? Bintu tace taji sauki tana gidansu ai"ta fada tana dailing din number direba, bugu daya ya daga, tace ya zo ya maida su gida yamma tayi sosai.
Su ko yaran sai wasan su suke, Bintu ta kallesu tace" Muneerat Oya ku nutsu maza hada kayamu mu tafi gida mamah ta koramu"Rauda tace "Ni dai ana zan kwana gobe babu school" Mamah tace"ai kuwa dai yi zaman ki, amma mijina kwalelanki" Asif ya ce"Mamah nima nan zan kwana"Bintu tace"Baza ka kwana ba dadinku na hanya bari Raudah ta kwana ita daya" mucotar cikin jin dadi yace "ni Dadyna zani na gani nayi missing d'insa" Mamah ta bashi duka abaya suna dariya.


Direba na zuwa ya kira Bintu ta tarkata yaranta sukama Mamah sallama dan Alhajin baya gari tun jiya, Rauda kadai suka bari su suka tafiyarsu gida.


Bayan sallah magarib ina kwance cikin parlo na gama amai kenan, ina maida numfashi komai baya mun dadi ga rashin Haidar ga ciwo ya sakani gaba ko ruwa nasha sai na amaryar... Inajin Anty Malika na mun sannu nayi shiru,
Idanuna na lumshe ban kulata ba, kaina naji na sara mun komai baya mun dadi...
Malika tace"zahara me zaki ci ai baza ki zauna haka ba kalli yadda kika rame dama abu ba abun kirki ba" fashe mata nayi da kuka nace"wayyo Anty ni na gaji wlh bazan iya ba ina dalilin jaraba haka kawai ina neman mutuwa dan Allah anty acuremun cikin bana so...baki Malika ta rufe mata, tace "haba Fatima kiyi abu na hankali mana ke jikin ki yadda gwamna yake son cikinsa idan kika zubar da gan-gan zai zauna dake ko zai zauna dake sai ya hukun taki, dan Allah kiyi hakuri ko wacce uwa haka take ji, ba yau ya ke zauwa ba ai gwara yazo ya tarkata abarsa yaje ya lallabaki da jinya nasan harda kewarsa ake zubamun shagwaba" ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login