Showing 6001 words to 9000 words out of 129912 words

Chapter 3 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5796

shiru yamata yana murmushi kan gado ya direta " ko zakimun wanka? " my man nide jekayi kazo bathroom ya shige ya jima kadan kafin ya fito daure da towel yana goge jikinsa Window ya daga yana leken harabar gidan ko ina ya wadatu da haske jami'an tsaro ta ko ina sai shawagi sukeyi kai ya girgiza gun CC Tv camera yaje yana dubawa haka wajan gidanma ko ina da matakan tsaro kai ya


jinjina agaguce ya shirya ya saka jallabiya ya tayar da sallah raka'a biyu yayi Yajima yana Addu'a muryashi can k'asa yake magana " my noor Dina Allah ya Kara daga haskenki a fadin duniya zan kasance mai farin ciki idan haka ta kasance muryasa ta Kara yin kasa banji me yaceba Yajima sosai kafin ya tashi ya cire jallabiyar yasaka kayan bacci ya fesa turare mai masifar dadi ya haye gado ya kwanta ya kashe wutar d'akin duhu ya baiyyana " my bintuna kinyi bacci shirun da yajine yagane ita kam akwai saurin bacci rumgumeta yayi gam jikinsa ya tura harshensa kunneta sai ta kyalkyale da dariya " my man ka bari shiru bai cemata komaiba ya shiga sauya mata lisafi cikin zazafar soyayyarta soka fara farantawa junansu rai Asubah ta gari bintu Aliyu,


****************************************


*Bayan shekara biyu*
Rayuwa kenan yau da gobe mai maida yaro babba rayu taja sosai yau Aliyu Mohammed Damba ya cika shekaru biyu kan mulki Wanda abun Alkhairin da yayiwa garinsa da jaharsa ya baxa ko ina kullum kimarsa karuwa takeyi aidanun duniya farin jininsa kullum gaba yakeyi kyatu da sadaka ta zame masa jiki da temakon nakasassu shiyasa abokan gaba suka tisasa gaba Wanda basusun k'asa taci gaba


Amma haryau Allah bai basu sa'ar cin galaba akansaba Teemah tun abinda ya faru ta fita harakar gwamna ta rufe babinsa arayuwarta saide sonsa na manne cikin zuciyarta ta binne tunda ta gane babu wani Fa'idar yin hankan ta maida hankali wajan karatunta yanzu ta shiga JSS 3 masha Allah ta goge ta zama cikakuyar budurwa kyawunta ya fito ta murmure kirjinta ya ciko saide bata fiye manyan breast ba kuma ba kananu baneba tsaka tsakiya suke wlh idan ka ganta akacema abaya tayi wannan shegiyar kwalliya zakasha mamaki ta nutsu yanzu bata fiye hayaniya ba idan ba tana tare da Maheeda ba ko malika Abu biyu ke damunta ayanzu irin daga masu sayar da ruwan jarka abaro sai mahauta masu nama ko yan yawan zamana gari banza sun adabeta da soyayya itako Allah yanagani tunda ta rasa gwamna har yau bata taba jin son wani mutumba aranta dan haka take fakewa zuwa gidan gwamna aboyé amsar sadaka kawai dan tagansa taji dadi kuma tunda take zuwa cikin ikon Allah shine yake bata da hannusa gun jerin Almajirai amma rufe fuskarta take da hijab mai niqab bayaganin fuskarta bare yasa,akorata ko akaita gidan mahaukata tunda take amsar kudin bata taba kashewaba saide tayi ta sunsunawa tanajin kamshinsa tana farin cikin akwai wani mutum mai kudi kwanaki ya matsa mata saida tayi kwana biyu bataje school ba haka zai rika turomata kudade sama da dubu dari da wayoyi masu masifar tsada da kayan ciye ciye bata taba amma saba ita dan tsoronsa matakeyi abun da ya isheta tunda har yanzu bata da waya ta fadawa, Malika itako Ta kirayi Mu'azzam ta fada masa yana cikin aiki ya bari yazo dan yaji tsoron yada sukace yana bata makudan kudi bata amsa


Tsoro yake a yaudari yar mutane da yaje ya dauko amana da rana tsaka yazo cikin sa'akuwa ya hadu da mutumin yace yana sontane da aure da aka tuntubeta tace bataso ya shafa mata lafiya karatu zatayi Dole ya rabu da ita amma sai me kullum duk inda zata ko makaranta ko islamiyya sai taga wata jibgegiyar mota na binta ko taganta jikin gidansu to abin ya dameta amma ba'a taba mata magana ba sai dai tana ganin masu motar su biyune har cikin makarantar suke shiga suna zagaye amma babu Wanda ya taba musu magana ta fadawa Malika tace kawai itace take ganin binta sukeyi harakarsu daban tafita bayansu shine tayi watsi dasu ko suna binsu abaya idan direbanta zai kaita makaranta ta fasa damuwa tunda Malika tace ba itaba sukebi hakade rayuwar ke tafi masha Allah teema akwai farin jinin har masu shayi da biredi😆


***
Misalin karfe Shida na yamma ta fito daga islamiyya cikin Nutsuwa take tafiya da sauri sauri saboda hadirin da ya gangamu ga iska duk atsorace take saboda motar na biye da ita wata yar kwana Ta karya sukaci karo da dantani mai ruwa ya turo baro ya washe baki " ah Fadima daga ina kiyi sauri kar afara ruwa fuska ta kwakwabe " dan Allah meyasa kuke takuramun me na tsare mukune ruwan da ya fara zubowane yasa bata ida maganar ba dantani ya saki baron ruwan tana tafiya ya bita da gudu " muje na rakaki karki jike zazzzabi ya kamaki na shiga uku dan kudin auran da nake tara mana ya kare amagani hannusa ya beka zai rike mata hannu yaji shi akasa a shmfida wani murdeden mutum yamasa bugu daya atake ya suma ihu ta kwara ta gigice ta rasa hanyar bi mutumin daya ya daga dantani ya sauye masa robar ruwa ya farfado ai da gudu yayi gun baronsa tana cikin gudu mota ta sha gabanta Dole ta tsaya tana zaro idanu motar da take biye da ita kullum ta tsaya dab da ita wannan Wanda ya sumar da dan tani ya fito yana, zaro mata idanu " ke maza, shiga, wannan motar duk da, tana tsoro amma ta dake cikin dauriya tace" naki bana shiga ku kasheni idan kasheni zakuyi me na mukune wai? bindiga taga ya zaro ga uban ruwan da akeyi jitayi fitsari nason kwace mata, ta faraja baya yana binta har taje jikinta motor da yakeso tashiga arashin sani Ashe murfin abude kawai sai ji tayi tayi luuuu zata fadi taji an tarota anjanyo an shigar da ita motar daga waje aka rufo motar saman kujera aka zaunar da ita jikinta na tsiyaya ruwa harda dan guntun fitasrinna iya tsorata ta tsorata jikinta kerrrma yake daket na bude baki zan kurma ihu naji wani tattausan hannu ya rufe mun bakina akaja motar guje......✍🏻


To fah wanene wannan mai kasadar daukar watsime😆😆😆
















Rahma ce ummu Fareesa😘
✍🏻✍🏻✍🏻
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*






*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________


*Written By*
Real Ladingo😉
Yar mutan Niger






*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*




*wannan shafin Sadaukarwa gareku comments dinku na burgeni sosai My umaimah Aliyu my ummiee zaria my Shafancy mum Sayyeed malamata🤪 my Aishana💋 ummu Nabeel mmn Teemah Nafeesat mareega mmn nanah Firdausi Naimcy my Hadeeza kawata😘 my khadija🌹 Sa'arbukar Rabi'u Fadilatu salihu mmn Wasila maryam habibu my Aisha idris duk wannan shafin nakune malakinkune sai kunso akaranta kuji dadinku kuna manne cikin zuciyata i love you lodi lodi🌹🌹🌹*






*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page* 4⃣




....wani daddadan kamshine acikin tafin hannusa da ya rufemun baki ya baibaiyeni hannun taushi tamkar na jarirai Wanda yasa nakusa manta da satoni akayi cikin dauriya na gantsara masa cizo atafin hannusa amma ko gezo bai ba saima wani sansanyan murmushi naji an sakarmu Kara cizonsa nayi akaro na biyu amma baiyi ko gezauba jin taushin hannu ya tsoratani karfa jini ya fito amma tuna satoni akayi cikin Kara harzuka na Dora hannuna kan nashi ina kuka na Kara masa wani uban cizo saida fata ta tashi wata zazakar murya naji yace" Ashhhh my Teemah kinjimun ciwo ko bakisan hakori dafi bane? da Sauri na dago kai na kalleshi wani haddadan mutumne mai kamala manyan kayane jikinsa farin jajir dashi ingarman namiji gabana naji ya yanke ya fadi Dan zatona wannan mutumin ne yasa aka satoni to bashibane wannan ban sanshi ba tsoro ya Kara kami jikina na rawa ga sanyin da nakeji ruwa sai digo yake ajikina ganin tana rawar saniya tausayinta ya kamashi gefensa ya duba ya dauko wata jibgegiyar rigar sanyi mai masifar kyau bai tsaya wata wataba ya fuskanceta ya zai saka mata ta kiya ta buge hannusa face ya had'e tam ba wasa a kaushashe yace" ke tsaya na saka miki banson raini ko bakiga yada kike rawar sanyiba ganin yada ya tsare gida yasa na tsaya ya sakamun rigar saman jikeken hijab Dina hannusa Wanda na jiza har nafitar masa da fata na kalla murmushi ya saki" Oya kiciza ko kin gaji ne? harara na zabga masa duk atsorace nake bansan inda zai kainiba kuma da ganinsa ba karamin mutim baneba tsayar da kukan nayi ina zubar da hawaye Dan tunda ya shigar dani motar ban daina kukaba nace


" Dan girman Allah mai nayi makane meye hadina dakai da kasa aka satuni ina zaka kai dama kaine kake bibiyar rayuwata ka adabeni tunda na fara magana ya zubamun idanusa masu kamar zaiyi bacci tsadaddan murmushi dauke kan fuskarsa wannan mutum da ganinsa akwai jiji da kai abinda ya Kara harzukani ina magana yanamun dariya cikin jin haushin dariya najanyo gefen hijabina Wanda ya Dora min rigar sanyinsa asama yana tsiyayar da ruwa na lafta mishi ajikin sai dukansa nake raina ya gama baci Dan ko ina yarinya babu abinda na tsana in ma mutum magana yana dariya tsayar da dariyar yayi saboda ruwan hijabin duk ya bata mishi fuska rike hannuwana yayi " yi hakuri my Teemah na daina wai Ashe fitinar na nan zansha fama jin dadin muryasa yasa na daina dukansa Dan yanzu cikin wani irin salo yayi maganar Jin na daina dukansa ya Sakar mun hannuna yana goge


ruwan fuskarsa nayi mamakin yada baiji tsantsanin ruwan da na yarfa masa afuskarsa ba motar naji ta tsaya dagowar da nake na ganmu kofar gidanmu cikin farin na rinka kiciniyar bude motar na kasa juyowa nayi na kwakwabe fuska " ni budemun mota na futa barayin yara ta Allah ba takuba wlh ina shiga gida zan fadawa Addata ta fadawa yayana sai an bincikoku duk dariya ta kamasa ya gintse ya had'e face "My Teemah zo zauna zamuyi magana ta fahimta ganim yada ya sauya lokaci daya yasa ta Kara tsorata amma ta dake saboda bata fiye ma babba rashin kunya ba ta dawo ta zauna wani kwali naga ya janyo ya bata " amshi wannan wayace zan rika kiranki muna hira tsarinki yana burgeni inaso muyi abota dake najima a gombe sunana Aminullah Mujaheed mai jama'a Nine babban duk wani Dan sanda dake cikin garin gombe yanzu shekara biyu kenan ina ganinki duk tsaron da ake baki nine nasaka saboda kina burgeni ko wannan mutumin da ya takuraki nine nan na masa kashedin ya barki tunda bakison sa yanzu insha Allah zan tsaya miki har sai kinsamu wanda kikes o abinda nakeso dake yanzu inaso ki maida hankali gun karatunki kinga kin kusa sauranku wata ukku ku karasa secondary school so kiyi qokari kuma duk Wanda ya nemi zai takura ki fadamun amshi wayar? fuska na yamutsa duk da muryasa namun azabar dadi duk ta kashemun jikina amma na dake nace " banaso ka barshi ni bana amsar abin mutum kuma banayin qawance da namiji ina ka taba jin hakan ka fadi gaskiya kawai kace kanason cutar dani sai na sakankance ka yaudareni to bari kaji karka ganni yar karama kamar kurciya ka daukeni jahila inada ilimin Addini da boko dan haka aje anemi wata ayaudara ba niba naki banason wayar karike abinka karka kara nuna ka sanin ko ahanya kuma sai na fada agida


murmushi ya saki kafin ya hade fuska tam ya kamo hannuta ya dora mata kwalin wayar ya saka idanusa cikin kwayar idanunta jikinta ya saki ta farajin kasala dan idanusa tamkar wani sinadari na kawayar bacci ne acikinsa kanta ta sada " kinsa Allah my Teema idan baki amshi wayarnan ba sai nayi mugun baki mamaki ga in da ake son ceto rayuwarki kinacan kina fama da son Wanda baima san kinayiba to wlh idan baki amasaba sai nasaka ancutar da mai girma governor sai na wulakantashi sabode ke dan munsan komai shine kike so baki kola kowane namiji da sauri na kallesa idanuna suna zubar da hawaye na rike wayar na rungumeta kirjina " kayi hakuri Aminullahi wlh zan rike wayar koda yaushe ka kirani zan dauka karka cutarmun dashi ina sonsa har nabar duniya amma bazai taba saniba saboda ya tozartani yacimun mutumci yasa ankaini gidan mahaukata Allah ne yasoni yanzu da inda takardar hauka abin


Na batamun rai amma kuma sonsa ajinina yake babu Wanda ya isa yasa na fasa, sonsa kayi hakuri karka cutar dashi please? " ok kina nufin bazaki kula kowani namiji haka zakiyi tazama saboda shirmen ki " ni banceba yanzu dai mubar maganar badai waya bace kawai kake bukata muyi da abuta naji na yarda mutuikar bazaka cutarmun da My Haidar ba " tsaki yaja " karki karmun zancansa mutikar bani namiki inada kishi ki kiyaye wannan abunda kikeyi zai saka na kara tsanar governor wani har nacutar dashi kuka ta fara ta riko hannusa " don Allah karka cutar dashi naji idan dai bazaka saka acutar dashiba wlh naji bazan kara sonsa ba zan yakiceshi azuciyata har Allah ya bani wani kaji Aminullahi? miskilin murmushi ya saki kafin ya hade face " ok naji amma da sharadi? " da sauri nace" naji fadi sharadin? " karki kuskura ki nunawa wani wayar ko kifadawa yayarki ko iyayan mijin yayarki ko kawarki maheeda kuma inaso ki cireshi aranki mutikar kikayi haka to bazan cutar dashiba zabi ya rage naki tunani nayi naga so azuci yake ba gani zayiba nafasa ko ban fasaba " OK na yarda duk zanyi abinda kace kaima kuma kasa adaina bibiyata tunda ga waya" shiru yamata miskilacin ya motsa bai sake magana ba yabeka hannnu ya bude mata mota bata jira komaiba ta fice da gudu ta nufi ciki kai ya girgiza yana sakin murmushi direba yaja motar suka tafi wayarsa ta dau ringing bai dagaba ya dauki wata ya danna wata number buga daya aka dauka murmushi yasaki yace" aiki na kyau da alama buri zai ciki Dan naga alamun nasara kitt ya tsinke kiran wayoyi har biyu suna ringing yaki dagawa tsaki yaja ya lumshe idanusa yana shafa sumar kansa mai yalwar gashi yana tuna ta inda zai fara Dan yasan da yarinyar burinsa zai cika murmushi kwance kan kyakyawar fuskarshi idanusa ya bude ya kalli gun da ta zauna duk lemace ta ruwan da ya jikata tsaki yaja yana Kara matsawa nace daga baya kenan malam Aminullahi ka manta kaine ka dauketa cak ka zaunar da ita a motar kuma har ruwan saida ta gogama afuska😂


✨✨✨✨✨✨✨✨✨


ko da ta shiga gida duk arikice take ta tsorata da wannan kyakyawan mutumin mai cike kwarjini kwalin wayar ta boye ajikinta bata tsaya parlo ba ta shige bedroom d'inta ta boye wayar tacire rigarsa tana sunsunawa ta ajiyeta bakin gado ta cire jikakun kayanta ta shiga bathroom tayi wanka ta dauro Alwalla ta fito tasaka doguwar Riga Mara's yauni ta fito parlo kenan taji kiran sallah magarib malika na zaune tana shayar da yarta ta kalleta"Fatima ina kika tsaya har ruwa ya jikaki haka naga ficewarki ko kallonmu bakiyiba ? zama tayi ta Dora kanta kafadar malika " ban tsaya ko inaba Aunty lokacin da na fito aka fara ruwan kallonta tayi taga kamar da damu aranta cire yar tayi daga shayarwar ta kwantar da ita gefenta ta rumgumo Teemah tana buga bayanta " ki fadamun damuwarki ko kinada wacce zaki fadawa murmushi ta kakalo" wlh Aunty ba komai kawai dan dai ruwa ya jikanine sanyine nakeji fah ta fadi tana dariya ajiyar zuciya ta sabke" wlh har naji dadi nazata ko wannan mutanan da kikace suna binkine suka tareki amma rigar waye ajikinki mai shegen kyau daganinta ba takarmun mutumba daga ina kika samu" gabanta yayi mugun faduwa tsoranta ya baiyyana cikin in ina tace" Aunty da... Ma... Malam ne..Yabani wai nasaka tunda gidan da dan nisa kar ruwa ya jikani? " amma Allah ya saka masa da Alkhairi shikuwa ina yasami irin wannan Riga mai tsada maganar na basar na saketa" Aunty muyi sallah dariya tayi " wlh kisan na dan rudene nazata cikin damuwa kike yayanki ya kira yace agaisheki yananan tafe cikin satinan murna sosai nayi " Allah ya kawoshi lafiya bari nayi sallah nazo ki kiramun shi mu gaisa jiya banji muryashi ba na fada ina shiga bedroom dina, sallah nayi ban tashiba saida aka kira isha nayi,


najima ina Addu'a Allah ya kare gwamna kar kyakyawan mutuminan ya cutar dashi akaina mikewa nayi Dana tuna kashedin da yamun mutikar ban kunna wayarba zuwa nayi na daukota na cirota daga kwalinta naga iPhone ce kuma karshan kudin jikinane ya dauki rawa " wlh bazan kunna wayar nan mai uban kudiba ba ruwana dan naga ta hannu yaya Mu'azzam bata kai kudin rabin wannan ba jikina na rawa na maida wayar kwali na boyeta naji Malika, na kirana nutsuwata na saita dan ni yanzu nafi tunanin kyakyawa dan yankan kaine dan natuna kusan inda na zauna dauri dauri. uban kudin da nagani fitowa nayi har ta hado mana abunci saman carpet muka zauna bamu je kan dining ba Rasheeda na saman cinyata ina bashi munaci muna hira da Aunty har muka gama ta kirawo yaya Mu'azzam tabani mukasha hira yana tambayata da matsala ko wani mai takurani nace babu munjima sosai muna hira kafin muyi sallama, yau munjima sosai muna hira da Aunty kafin naji barci Rahseed yace yau gurina zai kwana najashi muka tafi, kwance nake sai juyi nakeyi tunanin ya zanyi na cire son gwamna azuciyata dan kar mai kyau ya cutar dashi jinayi ko za'a rabani da raina bazan iyaba amma zanyi kokarin dannewa sadakarma zan daina zuwa amsa sai jifa jifa dan kar aje ya gano yasa acutarmun da gwamna Addu'ar bacci nayi na rungume rigar mai kyau saboda kamshinsa yayi shige da na My Haidar duk akwai banbbanci amma sai nasaka akamshin My

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login