Showing 51001 words to 54000 words out of 129912 words

Chapter 18 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5802

Mika muku godiyata da jajircewarku har Allah ya fito muku da yarku lfy yan uwana wlh ina muku son so Fisabilillah😘😘


*My uwar kwarai momyna Jamila Janafty i love u ina miki son so Fisabilillahi kedin ta dabance agareni banida bakin yimiki godiya😘😘😘😘*


My mom Aishi Alto wlh kema bazan manta dakeba Allah yabiyaki ina sonki domun Allah😘😘


My mom Hafnasy aminyar Janaf nagode da. Kulawarki da irin Kiran da kika rika mini nagode ina sonki ina kaunarki😘😘


*My Aminiyar kwarai uwar dakina kuma malamata mum Sayyeed&Noor kisani ina sonki domin Allah halinki na daban ne iya wuya muna tare🤝🏻😘*


*DEDICATED TO*
Masoyana da kuka sako bakunanku cikin Addu'o'i har Allah ya fito mun da Fareesata😘😘😘 lafiya dan haka duk Wanda yasan yayi Addu'a ko jimamin bacewar Fareesa jikar Janafty😘 to kudauka wannan Sadakarwar takuce kuyi yada kukeso da shafin wannan na yau💃🏻💃🏻💃


*Assalamu alaikum Agaskiya yan uwa musulumai babu abinda zance muku sai Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi wallahi ban taba zaton ni Rahma Ladingo yar gidan Janafty sunana ya fita haka ba hakika naga ruwan masoya wlh basu faduwa harda Wanda baka taba zatoba dan wlh har yanzu akawai sakonin da ban bude ba inaba duk Wanda suka kirani hakuri ban dagaba da masu turo sakoninku ban budeba kuyi hakuri ayanzu Nagano asalin masoyana Wanda sun nunamun ba litafin da nake rubutawaba kade ba suke so har dani dan wlh duk Wanda masifa zata sameka ya shigo lamarinka wlh babban masoyin kane na hakika Wallahi ni nasan karfin Addu'ar bakunan yan uwa musulumaine ya fitomun da Fareesa lokacin da muka gama sarewa da lamarin nagode nagode Allah yasaka da Alkhairinsa jinjina da mika godiya ga dukan k'ungiyoyin marubuta Wanda suka tayamu jaje lokacin kuka da kuma nunamana farin cikinsu lokacin da fareesa ta dawo wlh bazan taba mantawa dakuba Allah yabar kauna yan uwana marubuta da makaranta ina godiya Hakika Allah shine abin godiya Allah nagode maka da kafitomun da Fareesa lafiya bayan mun cire tsamanin samunta abun kawai al'ajabi saida ta kwana ta yini karfe uku da rabi na yamma aka jiyo kukanta akofar get abun ya girgizamu wlh har yanzu ban daina kukan farin cikin samuntaba da kukan tausayinta yarinya karama maishan nono ta bata tun karfe tara nasafa sai washe gari karfe uku da rabi na yamma kuma har yanzu ba'asan ko su wayeba😭😭😭 🤲🏻Ya Allah kabinmun hakkina ka toni asirinsu*


Kuma bazan taba mantawa da kuba *80K Hassan ATK* *Mu'az Prince Abdul* *Ibrahim Bross Abu Sameer Fast Class its B Y* *Ibrahim Abdul Nakowa* *Abu Hisham*👏🏻👏🏻👏🏻ina mika godiyata gareku mutika naji dadin yada kuka nuna damuwarku da goyan bayanku da Addu'arku gareni Allah yasaka muku da Alkhairi Allah kadai zai biyaku ba mutumba Nagode Ana tare🥰🤝🏻🤝🏻😘




*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page 2⃣4⃣*




......da gudu Mamu tayi kan Bintu ita da Farida mamu tace"Bintu bakiji saida nasaki har daki na gargadeki ki kama mutumcinki amma kika ki yanzu wa gari ya waya Halimatu ce ta dauko ruwan gora a fridge ta kawo ta bude ta yayafa mata afuskarta ta sabke ajiyar zuciya ta bude idanu ta kalli mamu da Farida da Aunty halimatu tace"don Allah Aunty kucemun mafarki nakeyi ba dagaske bane wannan yarinyar bace Aliyu ya auromun dariya Teemah sukaji cikin wani shegen salo mai dauke da Jan hankali muryarta tamkar Ana busa sarewa tayi dariyar ta bude baki zatayi magana da Sauri Malika ta buge mata baki tana hararata cikin shagwaba da wani irin salo murya can k'asa tace"wlh Aunty sai na fadawa My Aliyu Haidar kin dokar masa Amaryasa ta fada tana bubbuga Kafa gabaki daya kunyace ta cinye jama'ar gurin kowa da idanu yake binta Bintu ta kalli Mamu idanunta sharkaf da hawaye tace"Aunty wannan karuwar zan zauna da ita


da karfi Mamu ta buge mata baki Teemah tanaso tayi magana Malika da innah talatuwa da maheeda sun taushe mata baki Halimatu ta zauna ta riko hannun Bintu fuskarta babu wasa tace" haba Bintu ki nutsu mana kishi ai ba hauka bane yaushe zaki damu kanki kiyi hakuri ai ko wacce halinta nagari shi ke fitar da ita Dan haka ki ajiye hankalinki kiyi hakuri kuma bai kamata kicemata karuwaba kija girmanki saboda gudun raina kiduba kiga farawa da iyawa ma don Allah kuyi hakuri ku ajiye hankalinki mijinku fah shugabane na Al'ummah kwantar masa da hankali zakuyi ba ku tasa masaba kiyi hakuri bintu nasani kishi akwai ciwo amma idan ka daure ka kauda kanka komai zaizo da sauki ta kalli teemah Zahara zo nan Malika ta kawota kusan Bintu Aunty halima ta zaunar da ita ta kamo hannun teemah ta damka acikin na Bintu da Sauri Bintun ta kalli hannun Teemar yada taji wani irin laushi tamkar na jarirai ga wani irin kunshi mai masifar kyau ga fitinanan kamshi na tashi jikinta jitake kamar ta shaketa ta kasheta amma ta dake saboda tasan Halima bata daukan raina tamkar Aliyu Teemah ko kallon Bintu take tana danne dariyarta yada bakinta yayi gabjeje ganin bintu na hararata yasa ta sada kanta cike da kissa tace"Aunty kiyi hakuri


Halimatu tace" yauwa Fatima yar kirki innah da mareku kuzo ku. Bada Amanar da aka Baku gabansu sukazo suka zauna innah talatuwa tace"Bintu Dan Allah kiyi hakuri lalle kishi akwai ciwo amma idan ka daure komai mai wucewane Dan haka ga amanar kanwarki nan yarinyace idan tayi ba daideba kisata ahanya kuyi hakurin zama da juna Dan Allah kekuma zahara kibi yayarki sau da Kafa banda rashin kunya kiyi aiki da Abinda Abbanki da iyayye suka fada miki banda rashin kunya Allah ya kauda shaiden tsakanunku Teemah ta fashe da kukan kissa ta rungume Bintu"Aunty kiyi hakuri da sbinda namiki zan biki sau da Kafa nayi ta miki biyayya sai kince tayi yada ai bin nagaba bin Allah rungumeta tayi da haushi haushi tana buga bayanta"kiyi shiru komai ya wuce nima ki yafemun? " babu komai Aunty Bintu tafa masu sukayi suka hada baki"Alhmdllh munji dadi sosai Allah yabaku zaman lafiya Mamu tafi kowa farin ciki ta hadasu tayi musu fada halimatu tace"to ku tashi muje ni gida zan tafi tashi sukayi Bintu da kanta ta mikar da Teemah tsaye tana rike da hannunta suka jero har kofar parlon da zata fitar dasu su shiga part d'in Teemah saida suka fice Bintu ta dawo Fareeda tace "Bintu nifa inaga kiyi hakuri kawai ku zauna lfy murmushi ta Saki Mamu tace" wlh naji Dadi sosai da kika gane gaskiya duk da haka kinbadamu suma haba Bintu kishi fah ba hauka


bane kiri ka hakuri dama na fada miki taya za'ace babban mutum mai daraja kamar Aliyu ya auro kucaka murmushi tayi"Aunty komai ya wuce zamu zauna lfy insha Allah"yauwa naji dadi mu zamu tafi Allah kade fitina Allah yabaku zaman lfy tare suka fito da Farida da Mamu suna kara bata hakuri har kofar parlo ta rakosu saida suka fita ta, dawo hawaye sun wanke mata fuska bedroom d'insu mucotar ta shiga har sunyi bacci shida Asif Addu'a ta tofa musu ta rage gudun Ac ta fito ta shiga bedroom d'insu muneera suma sunyi bacci ita da Raudat suma Addu'ar ta musu tana shashekar kuka ta fito ta nufi bedroom d'inta zahara na bacci agadonta na yara bathroom ta shige, duk binda ya gudana Aliyu yana daga cikin bedroom d'insa ya baje saman makeken gadonsa yana kallonsu har sumar Bintu da irin tijara da tama teemah da ramuwar da tayi duk ya gansu wani yayi dariya wani ya gintse fuska yanzuma kallonsu yake sun haura, saman bene da teemah murmushi yayi yana shafa sumar kansa yana lumshe idanunsa ya Mike ya shiga bathroom, yayi wanka ya fito daure da towel ya goge jikinsa ya shafa maiyuka masu kamshin gaske ya bude wardrobe ya ciro kayan bacci masu kyau milk color Riga da wando ya saka ya fesa turare ya kashe wayoyinsa daya ya bari akunne ya dauketa ya fito d'akin


bintu ya nufa tana kwance saman gado tana kirtar kuka"ah Ya Salam waye ya tabomun my Bintuna zo muji da sauri ta d'ago ta d'aga masa hannu"Aliyu karka iso gareni banason ganinka? murmushi ya saki"Allah ko Bintu to sai anzo din mik'ewa tayi zata sabko cikin masifa tace" wlh bazaka tabani ba bari ni nabarma d'akin banason ganinka yayi azamar isa ya rikot dukansa ta fara tana rusar kuka"wlh Aliyu sai ka sakeni ni bazan zauna da kishiya ba ko ita ka saketa wlh bazan yardaba rungumeta yayi gam ya kwantar da ita ya Haye samanta ya tallabo kanta ya zuba mata lumsassun idanunsa yana murmushi "my Bintu yau ni kike cewa na sakeki saboda idanunki sun rufe akishi? " eh na fada din ka zaba ni ko ita ta fadi tana kokowar turesa daga jikinta" anki baza'a sakeki ba ina sonki" to ka saketa ni bazan zauna da itaba" itama ina sonta bazan saketaba ihu ta kurma tana wawurasa da cizo da yago kanta ya kara rikewa ya danneta ya sakar mata nauyinsa ya fara rikita mata lisafi da wani shegen Salo ya had'e bakinsu yana mata wata irin sumbata sai yamutsata yake tun tana hauka da kufce kufce har ta saddako tayi lakwas ta sakar masa jiki tana lumshe idanu har bacci ya dauketa yanajin sabkar numgashinta ya zare bakinsa yana murmushi ya dagata ya gira mata kwanciyarta ya tofeta da Addu'a ya dauko zahara ya runguma mata itama ya mata Addu'a ya lulubesu da blanket ya Mike"wannan matan nawa wlh sai nayi da gaske kowace zafin kishi yake dawainiya da ita wai na saketa sai kace ina hauka jinki bana sonkine na kara aure ai Bintu Aliyu mutu ka Raba ya fada yana murmushi ya kashe wutar dakin ya fita ya janyo mata kofa d'akuna yaransu ya nufa ya tofesu da Addu'a ya fito ya nufi part d'in Teemah,


bangaransu Teemah suna zuwa part d'inta Halima ta musu jagora har saman bene dakin teemah suka shiga wani tamfatsetsan bedroom ne da yaji tamfatestsan gado da carpet. malale tsakiyar dakin wlh tsawa fadin tsaruwar dakin bata lokacine bakin gado halima ta zaunar da ita"Fatima ni zan tafi Allah yabaku zaman lfy
kurika hakuri da juna na tafi kukane ya kufcewa teemar dan ta saba da halimar yau daya" kiyi hakuri zan dawo ma yan uwanki sallama ta fice su malika da maheeda ma sukace zasu tafi tace batasan zancanba ta tada rigima daket Malika ta samu ta gudu maheeda sai hakura tayi zasu kwana dan tasan mijinta bazai zoba akwai baki su innah talatu wani d'aki suma maheeda ta kaisu akawai komai aciki suka kwanta kursiya ko tana tare da su teemah Maheeda tayi shirin kwanciya kursiya ma ta kwanta tana rungume da d'anta maheeda ta shimfida mata wani lallausan bargo" Teemah ki tashi ki cire lufayar ki saka kayan bacci? baki ta turo ta juya"ni fah ki barni maheeda raina abace yake ahaka zan kwanta bargo maheeda ta shimfida ta dauko follow tayi kwanciyarta teemah tace"yo meye kowa ya ware aka barni akan wannan makeken gadon ni daya saikace mayya banza maheeda ta mata dan kawai neman fitinace take"wai badaku nakeba? " haba my teemah ya fah zan kwanta Mika agadon mijinki kiyi hakuri tsaki teemah taja ta sabko ta cire lufayar ta shiga bathroom idanu ta rika rabawa irin tsaruwar bandakin kadai abin kallone tubewa tayi ta kunna shower tana mamakin haduwarsa dan ba irin na gidan malika bane wanka tayi ta dauro towel ta fito dan ba sallah ba take ta goge jikinta ta bude karamar Jakarta ta ciro rigar barci ta saka tafada saman. Katon gadonta tana juyi sai tsaki takeja maheeda na jinta tayi burus da ita wayartace ta


Dauki ringing dubawa tayi taga Haidar ne baki ta turo ta janyo wayar tana kallo har Kiran ya katse wani ya shigo jinayi inason jin muryasa picking nayi na kara akunne amma banyi magana ba iskar bakinsa ya rika huromun ta wayar yana sabke numfashi saida tsikar jikina ta tashi gashin jikina ya mimmike na lumshe idanuna na saka masa kukan sangarta arikice cikin amon muryasa mai Dadi yace"Ya Salam my Noor meye na kukan me nayi miki ke ko dan tausayina bakyaji yaushe rabon mu hadu cikin shashekar kuka nace"yo ba kaibane ka daina sona ni gobe gidama zan koma" Ya Salam yanzu yi shiru my Noor yar babyna zo na ganki 2 minute? " bazan zoba ba ruwana dan matarka ta bugeni ai bansan inda kakeba" bude kofa kifito zaki ganni akofar da take kallon taki yi dam karki bari aganki mu gaisa ki koma kiyi sauri ina jiranki kitt ya kashe wayar idanu na zaro taya zan fita amma jin yace minti biyu ne na sabko na nada lufayar kan rigar barcin nayi dam na fesa turare na leka fuskar maheeda tana bacci kursiya ma haka sadaf naje na bude kofar na leka yana tsaye jikin kofar dakinsa karaf muka hada idanu murmushi ya sakar mun da sassarfa ya nufo guna sai jinayi ya daukeni cak yana juyi dani ya nufi dakinsa yana shiga ya murza key ajiyeni ya warware lufayar " wow tsarki ya tabbata ga ubangijin da yayi wannan halita my yar babyna ya fada yana sunsunani yana lasar wuyana ya rungumeni tsamtsam yana jujuyani atsakiyar bedroom d'in ahankali duk ya susuce jin taushin fatar jikina da wani irin sihirtattacan kamashi ahankali naji ya kirani"my Noor yar babyna kimun magana narkewa nayi jikinsa na rungumesa na saki kukan shagwaba


"Ya Salam daukata yayi cak ya nufi gado dani ya zauna ya sakani cikin jikinsa sosai ya zubamun lumsassun idanunsa ya kamo hannuna yana shafa kunshin hannuna" my babyna yi hakuri kukan me kikeyi kina tayarmun da hankali my Noor jikinki laushi ga wani irin kamshi kinyi kyau dayawa duk kin canza ga muryarki kamar sarewa dan dadi ya fada yana saka yatsata bakinsa yana tsotsa ya riko hannu gida yana murzawa ahankali yana lumshe idanu kallonsa nayi ina lumshe idanu cikin fisgo numfashi hade da shagwaba nace" My Haidar DINA? "yatsar ya cire a bakinsa ya tallabo kaina"Na'am My Fatimana menene kaina na boye kirjinsa" to ba kace mu gaisaba na tafi murmushi ya saki ya kwantar dani a tamfatestsan gadonsa shima ya kwanta ya beka hannu ya kashe wutar dakin ya daukeni cak ya dora kirjinshi yana shafa bayana bakinsa. Ya kai kunena cikin wata irin murya mai dadi yace mun" yar babyn haidar kwanta kirjin mijinki kiyi bacci mai dadi kinji ya idasa maganar ashagwab'e yana sakarmun kiss akunnena wani iri naji. na narke saman kirjinsa na kifa fuskata saman tashi ina gogawa cikin kissa, da shagwaba nace"wayyo ni My chocolatyna bazan kwana ba ajikinka ka maidani inda ka daukoni kaida kace Aunty tama tausa dan naji ahaushi na saka masa kukan shagwaba yanayinta da dadin muryata da, shagwabarta sun dimautashi ya susuce ya kara rungumota ya kamo fuskarta shima ashagwab'e yace"wayyo my Noor yar babyna kiyi hakuri idan baki kwanaba ajikina mutuwa zanyi wayyo yar babyna bata sona ya fada cikin shashekar kukan wasan da ya saba mata dan ya batar da zancan Bintu itako har yau ta kasa gano ba kukan gaske yake ba jin shashekar kukansa, yasa ta rikice tana kara rungumesa ta fashe da kuka" my haidar yi hakuri bazan sakeba bari kukan kaji mijina wlh ina sonka bari kukan zan kwana cikin shasheka yace"to kiyi shiru kema kuma kibani bakinki nasha sai nabar kukan ya fada yana shashekar kuka bakinta na rawa tana shashekar kuka tace" to my chocolatyna yi shiru amshi kasha. ta fada tana tallabo kansa ta dora bakinta anashi da sauri ya cafke ya fara tsotsa cikin wani irin yanayi da kwarewa tsotsar bakinta yake yana gamawa da k'asan lips d'inta duk ya kashe mata jiki harshensa ta kamo ahankali take masa wani irin tsotsa tana shafa


sumar kansa tana hadawa harda hakoransa tana tsotsa Aliyu jiyake duniyar na yawo dashi yada Noor d'insa ta iya sarrafa harshensa itama dadin yada yake sarrafa harshenta takeji ta kara narkewa jikinsa tana fitar da numfashi tare da yar shasheka abinda ya haukata Aliyun Kenan yaji kamar yacire bakin nata zare bakinta tayi zatayi magana ya sake cafke bakin nata ya shiga dura mata yawunsa tana shanyewa yana shashafata laushin jikinta ya gigitashi cikin wani irin Salo ya dora hannusa saman breast d'inta saida ya saki dan kara hannunsa ta rike gam sun manne juna gam suna musayar yawu sai kawai sukaji karan bindiga daram amutikar kidime Aliyu ya zare bakinsa ana Teemah ya janyeta jikinsa wani Harbin aka sake agigice ya sabko ya ya dzuko bindiga inda yake ajiyewa teemah ta diro ta biyo Aliyu da gudu zai bude kofa ta fada jikinsa ta rungumeshi ta fashe da kuka" wallahi babu inda zaka akashemun kai wlh baza ka fitaba hankalinsa atashe ya juyo da ita ya rike kafadunta" my Noor ki bari naga abinda ke faru baza'a kasheniba inaso na tsiratar da rayuwarku keda bintu da yarana ko ni zan rasa tawa rayuwar wani irin kuka tasaki ta bure samsa ta makalkaleshi" wayyo nashiga uku wallahi Aliyu bazan bari akashemun kaiba wlh saide ni nafita akasheni ta fada tana sakinsa tana kokarin yada zata bude kofar ta fice fisgota yayi ta fada kirjinta ya rungumeta gam zuciyarsa na bugawa da karfi "Please my zahara kiyi hakuri karki kara tayarmun da hankali ina sonki banaso wani Abu ya sameki ya fada yana kara matesata jikinsa kuka take sosai"Wayyo Allah My Haidar karka tafi ka barni wlh zan mutu idan wani Abu ya sameka ta fada ta ririkeshi tana rusar kuka hankalinsa yayi mugun tashi yana rungume da ita gam yana buga bayanta ya lumshe idanunsa" my Noor kiyi hakuri zanje nagano yarana da bintu daide lokacin sukaji Harbi na uku kusan part d'insu akidime ya dauki teemah cak yana rungume da ita ya bude kofar ya fito..............✍🏻
💃🏻Real Ladingo yar gidan Janafty😘
















Daga Alkalamin Rahma ummi Fareesa😘


*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*








*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________






*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger🤙🏻




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*






*Sadakarwa ga masoyan My Fareesa shafin na yau duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login