Showing 27001 words to 30000 words out of 129912 words
Chapter 10 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt
kuje kuyi Alwalla muneerat tace"muyi ai Kiran sallah Muke jira zarema yarinyar nono tayi"Muneerat riketa na shiga bathroom na fito wlh karki kuskura kiba Rauda yata cikin farin cikin ta amsheta yarinya masha Allah kyakyawa sak Aliyu ta fito mik'ewa tayi ta nufi bedroom wayarta ta zage daga chaji ta kira wata number bugo daya aka daga"kuka ta saki wlh Mummy ni bazan iya hada mijina da wataba jinake zuciyata kamar ta fashe inada mugun kishi akan My Man DINA wlh jinake kamar nayi hauka yazanyi dan Allah ko na barmasa gidansa kai wlh bazan barma wata dusa mijinaba daga can naji ance"haba Fatima bintu kiyi hakuri bawa baya wuce kaddarasa ni yanzu amatsayina na mahaifiyarki zanso na fito da yar cikina agidan mijinta Wanda ta fi so uban 'ya'yanta don Allah ki ajiye hankalinki ki tuna Aliyu na kaunarki baiyi aure dan ya tozarta kiba kiyi hakuri zan turo mamu har gida ta kara nusar dake wlh karki kuskura ki biya kawayan gwamnatoci kice zaki bijirewa mijinki kimarki ta zube abanza ina fada miki gaskiyane amatsayi na na mahaifiyarki kiyi hakuri fatima cikin kuka tace"mummy naji insha Allah sallama sukayi ta tsinke Kiran ta fada saman gado tana wani irin kuka" ya zan iya ganin My Man dina da wata mace Allah ya soni macan yar kauyece marar aji mara wayewa kucaka wai asirine suka masa komai wlh zataci kutumar ubanta la'ada waje da kafarta zatabar
gidan Aliyu Muhammad Damba Kowa,naka wlh yarinya kinyi kadan banda ke ko mai ajima wayaya wacce Takeda ilimi Aliyuna yafi karfinta bare kucaka mace irinki wlh kinyi kuskuran hada miji dani zaki gane bakida wayo tayama zai hada jiki da yar kauye yanzu haka garin yawan kyautarsa da Alherinsane ya temakesu iyayanta suka bashi sadaka shiko ya amsa wlh yar kauye kucaka Dole kibarmun mijina duk cikin kuka take magana kanta ta daga sama ta shiga tunanin rayuwarsu ta farko shin wai
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
jama'a wai waye Aliyu gwamna *Asalinsu* Aliyu Muhammad Abdullahi Damba kowa,naka shine cikeken sunansa Aliyu haifafan garin Damba ne nan kauyan Gombe fulanin asaline gaba da baya Muhammad Abdullahi Damba cikake bafulatanine d'a daya tilo gun Abdullah Damba Allah yayi musu Arzikin shanu da gonakai na uban mamaki kasancewar shidayane gun iyayansa ya samu gata da ilimi Addini da boko har yakai munzalin aure aka masa aure da yar kawunsa jallo hurairatu yarinya mai hankali da nutsuwa bayan aura'su da shekara daya ya gama karatunsa ya samu aikinsa acikin garin Gombe duk ba wani albashi bane mai tsoka kasancewar shidayane gun iyayansa sukace bazai zauna gidan hayaba suka sayar da shanu suka saya masa gida mai dakuna biyu da kitchen da makewaya atsakar gida suka tare da matarsa haka rayuwa taci GABA bayan shekara daya da tare warsu ta haifi yarta mace taci sunan kakarta mahaifiyar Muhammad wato Halimatu suna kula da ita sosai duk suna nuna mata faranci bayan haihuwarta da shekaru hudu hurairatu ta sake haihuwar d'a namiji zankadede fari kyakyawa ajin farko Wanda tun ranar da aka haifesa Allah ke musu budi ta ko ina yaron kawai farin jini makota ta ko ina shigowa kallonsa sukeyi yan Damba ko kusan kwansu da kwarkwatarsu
suna Gombe gidan kasa amshesu yayi kunsa dai fulani🤭ranar sunah yaro yaci sunan Aliyu Haidar, bayan haihuwarsa so biyu tana haihuwa yaran barai shiyasa yake zuba sangartasa son ransa saida ya shekara bakwai aka haifo k'anansa Aminullahi kamarsu daya da Aliyu saide shi bakine Alyu ko farine tas bayanan sai Habibullah sai yan mata biyu tagwaye saffah da marwa Aliyu tun yana yaro miskiline na gaske sam fara'a bata damesa ba sabanin k'annesa masu fara'a tundaga haihuwar yan biyu haihuwa ta tsayama hurairatu badan takaiba Allah dai ya tsayar da ita idan ka kalleta bazaka tab'a cewa ita ta haifi yara shidaba alokacin haka sukaci gaba da renon yaransu guda shida maza uku mata uku sun taso cikin gata da tarbiya dukansu makarantar gwamnati sukeyi amma kaf cikinsu Aliyu ya fisu ilimi nesa ba kusaba tudaga Primary har zuwa secondary school Aliyu yake zuwa na farko bai tab'a yin k'asaba yana samun kyau tutuka sosai harda kudade Wanda iyayan suke Tarawa basa kashewa gashi da farin jini gun malamai da dalibai baya shiga harakar kowa amma idan anyi ba daidai ba zaiyi magana tun lokacin kyawunsa ya baiyana duk bayada sakin fuska ga miskilanci idan zaka shekara kana masa magana to fah bazai kallekaba sai yayi ra'ayi sabanin k'annesa Aminu akwai fara'a habibu ma haka yan matan ma ba ruwansu to dama dama halimatu itama akwai miskilanci haka tafiya ta tafi Aliyu ya shiga Federal University kashere Wanda tsabar miskilancin sa duk da haka duk Wanda yayi ba daide ba koda malamaine a lokacin zai fadama gaskiya kuma baya barin acuci mutum shine kaf marantar aka dasa masa suna shugaba yan mata ko suka Adabi rayuwarsa Wanda shiko basa gabansa dan yanada burin karatu mai zurrfi saide Abu daya Aliyu bashida rowa duk rabin alherin da zai samu zai
rabasane ga mutane da basuda shi duk suma bawai arzikin bane dasu sosai Dan ya hana kakanninsa yawan sayar da dabobinsu suna kawo musu dukiya saboda ba laifi hanya ta budewa Muhammad har ya sauya gida mai dakuna biyar shida yaransa suna watayawa amma Aliyu Allah yayisa da tausayi duk abin da zai samu rabas dashi yakeyi ga Wanda bashida cinyau bare na gobe Aliyu kyakywane ajin farko fari dogo mai manyan idanuwa ingarma namiji kirasa ta karfaface kirjinshi abode yake ko ina gashine jikinsa yanada dogon hanci idanunsa alumshe suke idan ya kalleka zakayi zaton bacci yakeji bai fiye maganaba gashi miskinin gaske abokinsa daya har yau da yazama wani bai canzaba wato Jamil shi yaci maganin zama dashi ahaka har ya gama karatunsa dan ya karanci fannin business ne dan kasuwanci na burgeshi bayason aikin gwamnati yafison kasuwanci bayan kammala karatunsa da wata hudune ranar kamar amafarki aka kawo masa takarda wai zai tafi k'asar waje karo ilimi akan business gwamnatice ta biya masa yaunin karatunsa saboda kwazonsa har ya tubure baza shiba dan Aliyu juyayen mutumne ra'ayinsa yake bayabin ra'ayin wani sai Muhammad yasa baki da kakansa Abdullahi ya yada ya tafi Amerika
Wanda zuwan NASA ba karamun anfana yayi da hakanba kara goge aharakar business da sani rayuwa acanne suka hadu da bintu wacce daga temakonta da yayine awani gidan cin abunci saura kadan anyi mata fade Allah ya kawoshi ai kuwa tasha fada agunsa da takaicin iyayan da suke turo 'ya'yansu kasashan waje karatu babu wani matakan tsaro suna yawo inda sukaga dama daket da yarakata gidansu ta shawo kansa ta masa bayanin abun da ya faru tace wani baturene ya takura mata itako tayima iyayanta alkawali zata rike mutumcinta baza saurari kowaba saide ko dan k'asarta idan ta hadu da mutumin kirki kamarsa ta nunasa tsaki yaja ya tafiyasa bayansa tabi Ashe kusan juna suke to shine mafarin haduwarsu da binta tundaga ranar bintu ta nacema Aliyu sam baya kulata amma da yake wayayace gata shagwab'ab'a da abin dariya haka zata iskoshi gidansa ranar da babu karatu tayi ta masa shirme ta dora masa girki tun baya kulata yana mata korar kare har ya fara kulata saboda dariya da take sasa duk ba yayi agabanta sai ta fita haka shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninsu bintu tana mugun son Aliyu da kishinsa shima ya kamu da sonta duk bai gaya mataba kasa daurewa tayi ta fada masa bai musaba suka kulla soyayya mai karfi bintu akwai mugun kishi har makarantar su Aliyu take zuwa aboyé taga ko mata sunyi masa magana tasha danbe da mata tasha fasa kan 'ya'yan turawa da bakar fata saida Aliyu yamata Jan ido ta sasauta dan tasan halinsa bashida dadi zai watsar da lamarinta shiyasa take takawa asannu ahaka har tagama karatunta tace bazata tafiba sai Aliyu ya gama saida
yamata Jan ido yace wlh zai fasa auranta tukun ta koma Nigeria, kullum cikin waya suke har Allah yayi shima ya dawo Fatima bintu y'ace ga Alhaji Taheer mai kudi su ukune gun iyayansu mussadeeq ne babba sai nana barirah wacce suke cewa mamu sai bintu auta sun taso cikin gata da kulawa sun samu tarbiya sunyi karatun Addini da Na boko mahaifinsu Allah yamasa arziki yanada dukiya sosai bintu shagwababiyace ga fadan masifa da b'aci kuma sunfi sonta shiyasa takeda rashin kunya bayan ta gama secondary school tace bazata cigaba da karatu a Nigeria ba Dole mahaifinta ya kaita America har Allah ya hadasu da, Aliyu bintu farace tas yar duma duma mai matsagaicin tsayi kyakyawace tanada hanci da idanu matsagaita bata fiye gashiba amma ba laifi tsabtarta da yawan kwaliyarta ya kara mata kyau akwaita da jiji dakai saide bata cika wullakanta talakaba fagen iya tafiya da daukan dressing ba'a cewa komai akwai ta aji tanada farin jinin samari sauranyita daya Jafar sun so juna tafiyata karatu ne sanadin rabuwarsu bayansa bata so kowaba sai haduwarsu da Aliyu
bayan dawowar Aliyu da wata ukku iyayansa suka tsaya masa ya fara business da kadan kadan Allah yake ma kudin albarka har kwangilar gidaje yake soyayyasu da bintu tayi karfi sosai bintu ta Rigada ta karanci Aliyu Dan haka idan yana mata miskilancinsa ko ya basar da ita bata damuwa tunda abin ajininsane millions biyu ta basa kan ya amsa suyi aure yace Allah ya kiyaye masa daga karshema ya mata kwakwaran kashedi karta kuskura ta sake masa haka lokacin ya tura iyayansa neman auranta aka samusu ranar aure kuma lukacin business din Aliyu ya fara bunkasa mahaifin bintu ya basu kankarenan gida indan anyi biki su zauna Aliyu ya kiya yace idan tana sonsa to ta zauna inda yake meye ya nema ya rasa aduniya da har za'a bashi gudun muwa daga gidan mace bayaso
Dole tacewa babanta abarshi yayarsu Aliyu tayi aure harda yaranta yan biyuma duk an musu aure yanzu dagashi sai Aminu da Habib agidan Aliyun suke dan madedecin gidane mai masifar kyau da tsari d'kuna ukune kowane da toilet aciki kitchen dinsu mai kyau nan su Aminullah suke da zama suna karatunsu, haka akayi auren Aliyu da bintu ansha biki Dan auransa yayi armashi sosai daga kowane bangare su Jamil babban aboki ya taka rawar gani sosai abikin dama shi yayi aurensa tun aliyu na waje karatu komai cikin dattaku Aliyu yayi rawar gani ba laifi bintu Tasha akwatuna da kaya tamkar wani hamshaki kowa ya yabawa Aliyu shugaba sunan da yabishi tun makaranta anan gidansa ta tare suna son juna kamar zasuci junansu yaji dadin samunta cikakiyar budurwa Wanda yasha raki ba kadan ba haka yayi ta lallabata har ta warke sukaci gaba da budirinsu matsalarta daya bata masa yada yakeso agado saide shi yamata da ya takura tasa masa kuka Dole zai hakura yana lallashinta dan yana mugun sonta mutika saide idan miskilancinsa ya motsa Dole itace mai bibiyarsa da lallashi shiko tunaninsa duk haka mata suke agado saide abokinsa Jamil yaji yana zuga matarsa to dayake shi ba ma'abucin magana bane bai tsaya ya fuskanci inda zancan ya dosaba haka sukaci GABA da rayuwa har ta samu ciki murna ba'a maganar har cikinta ya isa haihuwa ranar wata Alhamis ta tashi da nakuda ba bata lokaci suka tafi hospital ta haifo Danta namiji kyakyawa mai kama da Abdullahi sak ranar naga murna gun dangi uwa dana uba kuma lokacin Aliyu lamura sun bude masa ta ko ina........... ✍🏻
Sai next page zamu gama labarinsun da irin rayuwar da sukayi kafin Aliyu yazama gwamna🌹
Rahma ce ummu Fareesa😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*Written By*
Ladingo Yar ilu😉
Yar mutan Niger
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page 1⃣3⃣*
......ranar sunah yaro yaci sunan Muhammad mahaifin Aliyu suna kiransa da Asif haka sukaci GABA da rayuwa cikin so da kaunar juna Asifa har yayi wayo Aliyu zuwa yanzu Allah ya bunkasa dukiyarsa sosai bayan Shakaru uku bintu ta sake haihuwa wani d'a namiji mai sunan Taheer mahaifin bintu suke cemasa mukhtar Aliyu dan murna kamar yayi hauka dan Allah yayi masa mugun son yara baiki duk shekara ta haihuba itace dai take kiyawa mahaifin bintu yaji dadin karar da Aliyu yamasa yaron yanashan gata lokacin aka ida Gina kamfanin Aliyu mai Suna *AB Sauki Kamfani* Wanda ake sarafa kayan zamani iri iri Wanda ya samu daukaka sosai ga business d'in motoci yanayi da harakar kwangilar gidaje Aliyu yayi suna agarin Gombe saboda komai NASA mai saukine ga yawan kyauta da sadaka da sauransu haihuwar bintu ta uku ce wato haihuwar muneerat ya tamfatsa gida a unguwar NEW GRA wlh fadin ginin gidan b'ata kokacine dan wlh babu abinda baisaba najin dadin duniya tamkar gidan shugan k'asa dan yanason matarsa da yaransa suji dadin rayuwa sosai haka iyayansa ma ya tamfatsa musu gida lokacin Aminullah yayi aure shida habibullah haka sukaci GABA da rayuwa soyayyarsa da bintu ko babu abinda ya rage duk da bata masa yada yakeso agado wani sa'inma idan ba tasoba bata yada suyi sex amma idanbtaso ta kafa masa fitina iri iri idan yan miskilancin na kansa ko kallo bata ishesaba bayan tare warsu da shekara daya yan siyasa sukayi masa taron dangi da karfi suka sakasa siyasa sunce irinsu talakawa keso shiko ya kiya sun jima suna bin kansa kusan shekaru hudu kafin ya yarda ya shiga siyasar amma yace bazaiyi mulkiba da wayo da wayo suke jansa jikinsu har yasaki jiki bayan haihuwar Rauda ne dai ya shiga siyasar ruwa tsumdum yada yaga talakawa nashan wuya sai ayimusu alkawali idan sunyi zabe za'a musu Abu kaza amma shiru kakeji malam yaci shirwa haka tafiya tayi tafi yawan kyautatawa jama'a da yakeyine Jama'ar gari kuwa sukace atsayar da Aliyu takara gwamna suna so tun bayaso har yaji sha'awar abun a ransa amma zaben farko makiyansa manyan yan siyasa da basuson cigaban talakawa suka shiga suka fita sukayi murdiya akace baiciba shi ko ajikinsa talakawan garine da masu goyan bayansa cikin manya aka fara tashin hankali saida ya shiga gidan radio da TV yayi magana ya basu hakuri ya nuna masu lokacine baiba idan lokacin yazo to fah babu Wanda ya isa ya hana dan haka suyi hakuri daganan ne komai ya lafa shima yaji babu dadi amma saboda Noor d'insa da take karfafa masa gwiwa cewar yayi hakuri lokacinsa na tafe amma hakan bazata faruba sai ta kusantosa yanzu lokaci baiyiba tukun na mulkinsa to haka akaci GABA da rayuwa Noor na k'asan zuciyarsa yanaso yaga ranar wannan da tace sai ta baiyana k'asarsa zaici mulki yana mamakin wanna Al'amari duk yanajin ba mutum bace amma yana sonta bai taba manceta cikin Addu'ar saba haka ko akaci gaba da rayuwa har Allah ya kawo lokacin da Aliyu ya hau kujera gwamna cike da nasarori masu yawa talakawa najin dadin mulkinsa sosai har zuwa wannan lokaci da bintunsa ta haifo masa Fatima bintu Zahra ya kuma aure Noor d'insa rabin ransa yar babynasa Wanda ita dashi suke mugun son junansu tun basu gaba junansu labarin yanda ya ganeta da yada ya saka fuskar Aminullah to nima jira nakeyi sai yaba Noor d'insa labari sai na dauko muku rahoto, labarin rayuwarsu ya k'are sai kuma kafce yanzu bintu da Teemah
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Bintu tana nan kwance har akayi sallahr isha zahara take kuka muneerat ta kawo mata ita amsarta tayi suka fito parlo ta zauna tana shayar da ita har Aliyu suka dawo daga masallaci ko kallonsa bata yiba shima ko yan miskilancin sun motsa masa baice mata k'alaba sai dai idan sun gama ido ya daga mata gira kiransa akayi ya daga waya hayaniyar yaransa tasa ya Mike ya nufi wani Hadaddan parlo ya zauna yana waya da mutanansa yan siyasa bintu ta cika tayi fam jinta ko dawa yake waya ya keb'e oho sai tsaki take ja Dan dai tasan halinsa Idan ya kebe yana waya ba'a kawo masa raini har ta mike taje ta masa tijara ta fasa ta daukin kodirin yau bazata barshi ya rumtsaba oh bintu arage kishi fah😆
*Niger* tun bayan fitarsu iyayye watsime kuka take kirtawa ahanya daket iyayye tasha kanta tayi shiru har suka isa gidan haja Nanu da sallama suka shigo haja Nanu na gindin murhu ta amsa"Aisha ya dai Fatima bintu meyene ake kuka sakin iyayye tayi ta rugu gun haja Nanu ta rumgumeta tana kuka"haja Nanuta da ranki kika bari su Abba sukamun auran Dole"asha Fati yi hakuri ta raketa ta kalli iyayye"Aisha jeki gida barni da kawata ajiye hankalinki zata bar kukan murmushi iyayye tayi ta juya ta koma gida haja Nanu taja hannu watsime suka koma saman tabarma har yanzu kuka takeyi harda shasheka"haba Fatima kiyi hakuri bari kukan goge fuskarki kiji wani labari kuma na fada miki yada za'ayi yanzu dai kina son gwamna mijinki ko bakiso kuka nasaki mai sauti"Nanu kubar cewa mijina ni banaso" to naji amma ai sonake na koya miki wayo irin namu na manya yanzu yaushe zaku gama Hutu? "da saura fah amma naji aunty tace tare zamu koma wai akwai gyaran da za'amun na meye? nanu tace" ai shine zan baki shawara gyarane za'a miki Wanda idan gwamna ya ganki zai rabu dake amma da sharadi sai kin daina koke koke kin fasa cewa bakya sonsa ai da kansa zai rabu dake inji ni nake miki wannan zance farin ciki ya kama Teemah ta rumgume Nanu tana dariya"yau kakar kwarai naji dadi ni Dan ina sonsa haka kawai sai na zauna da kishiya matarsa masifafiya tab ai wlh gwarama arabu yaushe "Nima dai shi nagani gwara kiyi shiru da kansane zai nemeki karki k'ara kuka ki ajiye hankalinki Ana gama gyaraki zai rabu dake, haka haja Nanu tayi tama Teemah wayo itako sakara tahau ta zauna sai fadi take gwarama suyi sutafi gombe amata gyaran ko ya rabu da ita tana gidan haja nanu har bayan isha, zaune suke suna cin abunci ita da haja Nanu sai labari take bata na dariya teemah sai kyakyatar dariya takeyi"wayyo cikina Dan Allah haja