Showing 36001 words to 39000 words out of 129912 words

Chapter 13 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5809

mata k'asa ta danyi tayi bismillah ta fara karatu cikin zazakar muryata take karatu cikin suratul Al'imran ko da malam hamisu ya shigo teemah bata fasa karatunba mamaki yayi Dan yaga tayi k'asa kai ya girgiza ya koyama Wanda zai koyama ya ficewarsa Dan yau dama karatun Qura'an ne kadai teemah saida ta kai har karshen surah tayi fatiha ta shafa yasmin ta kalleta"Fatima yau kinci sa'a malam ya barki murmushi na sakar mata zanyi magana mukaji an bushe da dariya raina ya b'aci yasmin tace"wlh duk bakin cikine karki kulasu wai saudat fa ban fada miki bane wlh mijinki take so da Sauri na kalleta gabana na faduwa nace"kibar min wasa? "wlh Teemar Gwamna da gaske nake ba karya bace Nina kamasu abayan fanfo suna gulmar tana kuka suna bata hakuri wai idan rabontane zai aureta ya hadaku zuwat teemah ta Mike jikinta na rawa ta kalli. saudat tace"da gaske kinason My Haidar mijina kallon banza ta mata "yo sai me Dan ina sonsa kema ai mijin watace kika aura kinga kuwa ai bazakiji ciwoba idan nace miki ina sonsa kema yar kauye kin waye kin samesa bareni haihuwar birni nataso cikin daula ai bata rufe baki sai ganin teemah tayi ta wanketa da Mari ajere har biyu ta makuremata wuya ta makata da bango tana bugo ta ko ina harda cizo da yago su yasmin babu yada basuyi su amshe saudat sun kasa da gudu suka fita kiran malam bayanan suka hango habu shi suka kirawo lokacin fuskar saudat bata ganuwa ko ina Sawun hakoran teemah habu ya rasa ya zaiyi saboda teemah matar aurece bazai tabataba yace" kai Dan gidanku kuzo kuyi taron dangi ku banbareta aikuwa dama tsorone suke yada sukaga tana cizo taruwa sukayi suka dauketa caka tana wutsi wutsiltu da kansa ya daga saudat bakinta da hancinta na fitar da jini"haba saudat yaushe zaki tsaya yarinyar da kinyi ukunta ta nakasa ki ko bazaki diketaba sai ki ceci kanki diba kiga fuskarki kamar anyi b'arin mota ko ina cizone da yakushi teemah da, take gefe rike k'ugunta tana girgiza tace"yo malam habu kasan me ya hadamu mijina take so wai harda cewa wai mijin wata na aura ai wlh itama shigar Sauri tamun bare wannan karamun alhakin takeson abinda nake so Kut wlh bata isaba idanu malam habu ya zaro al'amarin yarinyar yabashi mamaki Saudat kuka tafara"wlh ki jira kigani sai an ramamun dariya abin ya basu teemah tace"ai baki dakuba ma sai na kamaki akoraran guri ke kin isa kiso mijina yo da kike cewa zanga me ramamiki Aradu yanzu nafiki gata ku tabani ku gani niko NASA My Haidar yasa boos yayi barna ko atataro sojoji da jami'an tsaro kuji ruwan harsashi ya gwaraye birnin gombe Matar Gwamna cefa wlh yarinya karkiyi fatan haduwarmu ta gaba daket malam habu ya shayo kan teemah yamusu nasiya saudat ko fuskarta ta kumbura suntum danma karsu sake rigima yamusu fatiha suka fito Saudat ko inda teemah take bata kallaba teemah tayi ta mata habaici bata kulataba yan rakiyar teemah na biye da ita har kofar gidansu saida ta shige gida suka juya.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Aliyu bayan tafiyar teemah komawa yayi ya zauna yana waya da jama'a harda mahaifiyarsa tace yakai mata matarsa Fatima karama yau tanason ganinta amsa mata kawai yayi Dan baisan ya zai bullowa wannan rigimarmar babyn tasaba kiranta yayi har yagaji bata dagaba lokacin wayar bata hannuta kiran mu'azzam yayi ya masa bayanin komai yace" idan an shiryata akirasa cikin girmamawa ya amsa yace" shima yazo yau yana garin za'a shiryata kafin su samu isowa bai bar gidan ba saida yayi sallah la'asar wajan karfe biyar tukun suka nufi government house suna zuwa ya nufi bedroom dinsa ya sake wanka ya shirya cikin gizna blue wacce taci uban zubi nasu na manya sai baza kamshi yakeyi yayi wani irin kyau Sam bazaka taba cewa Aliyu yakai.50 year ba saboda tsabar jin dadi yazama tamkar Dan shekaru talatin da biyar idan baka sanshiba ya cema haka shekarunsa zaka yarda Dan ko afuska bazaka ganoba parlo ya fito ido suka hada da bintu wacce taci uwar kwalliya kamar ba mai jegoba baki ta turo gaba ta kauda kanta murmushi ya sakar mata yaran sukayo kansa" Dadymu murmushi yayi ya daukesu daya bayan daya ya rumgumesu yana musu kiss har manyan bintu batasan ya akayi dariya ta kufce mataba goyan Rauda yayi tana dariya"dady zan bika? " no baby Rauda ki zauna sauketa yayi"Asif kuje kuyi wasa mana kunsa antula muku kayan wasa bakwayi ihuu sukaye"yeeeee dady mun tafi duka suka fice suna dariya gun bintu ya iso ya zauna ya rumgumota "my bintotona bani kiss mai zafi please banza tamasa bata masa haukanba ganin haka ya tallabo kanta ya had'e bakinsu yana tsotsa cikin wani salon da ta kasa jurewa ta biye masa suna kissing din juna saida ya rikitata ya rage mata fushin ya zare bakinsa yana mata shakulkuli tana dariya"wayyo My Man kabari cikina zai murde wayyo my man na tuba shima dariya yake wayarsa ce ta dauki ringing ya saketa ya duba yaga Mu'azzam ne picking yai ya Kara akunnesa"hello mu'azzam ya dai? ko me yace masa oho yace"OK ganine ya tsinke kiran bintu tana kwance jikinsa ya janyeta yamata kiss a kumatu ya kwantar da ita gira ya daga mata baki ta turo"Aliyu tsakaninka da Allah ina zaka wlh ban yadaba ta fada tana mik'ewa zaune ai bai tsayaba ya kwashe wayoyinsa yayi hanyar fita waje da gudu yana dariya tako biyoshi tana kuka"wlh dama nasan zalumtata akeyi dariya yake sosai yana zuwa baking kofar ya janye glass din kofar ya fice ya rufo kofar yasan bazata biyo shi harabar gidanba yaransa ya hango kusan Swimming pool suna wasa wasu a yar mota wasu na shillo kai ya girgiza yana murmushi ya fice sojoji na biye dashi har har gun wasu jigbga jibgan motoci aka bude masa ya shiga baya motoci biyu kawai yace afita dasu gidan mahaifiyarsa zashi kiran boos yayi yace "abama almajirai sadaka bashida lokaci yau direba yama motar key suka nufo get kafin suke isowa an wangame get suna fitowa wata irin jiniya ta karde titin motocin anutse suke tafiya suka dauki hanyar gidansu Teemah..........✍🏻




💃🏻yar ilu ce
















Ladingo ce yar gaban goshin kainuwa🤪
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*








*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________






*Written By*
Ladingo Yar ilu😉
Yar mutan Niger




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*












*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page 1⃣7⃣*




.......bangaran teemah ko lokacin da tazo gida aparlo ta isko Mu'azzam yana jiranta sun kirata yafi akirga Ashe wayar ta bari agida tana bedroom jina jina tashigo parlon da sallamah sai zaro ido take tazo ta zauna kusan mu'azzam kallonta yayi ya danne dariyasa yace"maza tashi ki cadado wanka malika tashi ki shiryata please kallonsa tayi"yaya ina zamu? " mijinki ya kira mahaifiyarsa nason ganinki" ni ba inda zani fah ehe yo d'azu ai dan bakasan ya muka kwasheba" ah ina kika ganshi idanu ta fara cicirawa"yo yaya awaya fah Malika tazo ta tasheta "haba Autarmu ai ko baki sonsa darajar mahaifiyarsa zaici ki daure kimasa, biyaya maybe ma idan yaga kin nutsu kurabu aruwan sanyi muje yanzu zaizo ku tafi cikin dubara da lallashi suka samu ta yarda Malika tajata har d'aki ta sakata tayi wanka Wanda yasha ruwan turare ta fito sai sheki farta take ta goge jikinta ta shafa maiyuka masu taushi da kamshi Malika ta cacada mata kwaliyya amma ba canba daide misali wacce tayi masifar kyau wani dankareran less bleu color ta zabo mata Wanda mu'azzam ne ya sayo mata daga Lagos dinkin doguwar rigane yayi mata cif cif Malika ta kashe mata dauri" wow wlh kinyi mugun kyau mutika baki ta zumburo Malika ta basar da ita ta dauko mata takalmi da jaga suma bleu mayafi bleu jakar ta rataya ta saka takalmin malika ta fesheta da turaruka iya haduwa yar babyn gwamna ta hadu sai sheki take wayarta ta dauka suka fito malika na zuzuta kyan kanwar tata mu'azzam yace"iyeee lallai yau matar gwamnar kike,


Watsime baki ta bude zata fara kuka malika tace"yi hakuri haba my darling kabarta dama lallabata nakeyi. "to kuzo ku zauna ya fada yana dariya ya kira number Aliyu ya fada masa an shiryata yana gama wayar ya ba malika ledar"ki zuba mata cikin jakar turarukane ta kaiwa surukarta baki teemah ta zumbura ta kauda kanta Malika ta amshi jakar teemah ta zuba turaren ta rufe mu'azzam yace"malika kinaso kina kaiwa kasuwa teemah ta kallesa"yaya sai na hadaka da Abbana da iyayye" ah kiyi hakuri na tuba, murmushi tayi suna zaune suna koya mata yan dubarun karta nunamasa, bataso zuwa gidan mahaifiyarsa har su Aliyu ISO Kiran mu'azzam yayi ya sheda gasu akofor gida, fitowa sukayi har bakin get malika ta rakosu ta labe mu'azzam ya fito teemah na biye dashi wani irin taku yarinyar take mai cike da Jan aji wlh ko ni ta burgeni sojojine har uku akofar motar da gwamna yake ciki tun kafin su karaso aka bude mata mota Aliyu idanu ya zuba mata cike da tsantsar kaunar yarinyar yana mutikar mamakin saurin wayawarta da kamun kanta Jan ajinta na burgeshi suna isa gun motar tasa kai tashige,


Cike da yanga da yauki cikin siririyar murya mai cike da kissa da Jan hankali tace" Asslamu Alaikum My Haidar sojojin suka rufe motar mu'azzam tsaye yayi agun har motocin suka bargun murmushi dauke fuskarshi ya juya yashiga gida Aliyu kuwa suman wucin gadi yayi kafin ya dawo Normal ya amsa mata sallamar tun daga slm bata sake magana ba ta kauda kanta murmushi ya saki yasa tattausan hannayensa ya dauketa cak ya dorata cinyarsa ya rumgumeta yana sunsunata mayafinta ya cire mata ya tura hannusa k'asan wuyanta yana shafawa ya lumshe idanunsa wani irin kamshinta yakeji ji yake kamar ya hadiyeta dan so shiru teemah tai tanajin dadin yada yake shafar wuyanta kara shigewa jikinsa tayi tana sabke ajiyar zuciya tsantsar kaunarsa da take ta dawo sabuwa fil kallonsa tayi taga idanunsa alumshe karamun bakinsa ta zubawa idanu tana lasar baki sai yawu take hadiya can k'asan makoshi ta kirasa ashagwab'e"My chocolatyna kara matseta yayi ya bude idanunsa ya kalleta ta zuba masa idanunta masu mutikar haske ta kwakwab'e fuska"Na'am my Noor me kikeso shiru kukan me zakiyi ga mijinki akusa gani yayi takurawa bakinsa idanu ganin zai ganoni na janye idanuna daga kallonsa ina k'ok'arin sabka daga jikinsa kara tarairayoni yayi ya tallabo kaina ashagwab'e ya kirani"My Noor yar babyna kalleni kinji wani iri Abu naji na mun yawo ajikina kasa kallonsa nayi na tura kaina k'irjinshi ina shakar ni'imataccen kamshinsa murmushin farin ciki ya saki yana shafar wuyanta "my Fatimana"cikin muryar Jan hankali na amsa"Na'am My Haidar ni kasakeni na zauna "Ok amshi to dagowa nayi na kalleshi harshansa ya bekomun kukan shagawaba na saka masa"my chocolatyna ni banaso ka bari na fada ina shashekar kissa rudewa yayi yana kara rumgumeni "Ya Salam my Noor meye to na kuka yi shiru bazan kara ba kinji shirun tayi tana turo baki dan taji haushin da yace bazai karaba manneta yayi ajikinsa sosai yana shafar wuyanta ya tallabo kanta ya dora bakinsa saman kunnenta yana mata magana cikin nutsuwa


"My Noor ina sonki da kaunarki sosai inaji dake sonki ya dade azuciyata zan rayuwa dake kema kinasona zaki zauna dani fatima bintuna ki dauré mukwana gado daya nasaki cikin jikina muyi bacci mai dadi kinji burin zuciyata ya fada yana lasar kunneta yanayin yada yake mata duk ya dagula mata lisafi sonsa da kaunarsa ne ke mamaye duk sasan jikinta ta kasa magana "my wife zanyi miki kuka janye kanta tayi ta dago ta kallesa tana lumshe idanu fuskarsa ta kama ta kureshi da idanunta masu mutikar haske sonsa na yawo cikin jini da tsokarta bakinta takai kunnesa ahankali take magana cike da Jan hankali da kissa tamkar wata uwar mata tace"My chocolatyna duk kasa naji ina mugu mugun sonka da kaunarka bazan iya rayuwa babu kaiba Allah ya jarabeni da sonka tun ban sankaba My gwamna i love u sonka yamun yawa azuciyata bana iya hadaka da wata shiyasa nace murabu wlh ina sonka dayawa bazan jure ganinka da wataba dazuma saida nama wata shegen duka saboda kai duk wannan maganar da take cikin wata siririyar murya take masa cikin kunnesa tana shafar sumar kansa zuwa sajan fuskarsa gabaki daya gabobin jikin Aliyu sun saki yana mamakin yarinya karama da baiwa haka tasan yada zata tafiyar da Namiji cikin Salo mai zautarwa lallai ko wace mace da baiwarta da Allah ya mata "My Aliyuna ina sonka please mu rabu wlh kishinka nakeyi Allah bazan iya zama da kaiba dan Allah kafita rayuwata kaji abin sona ta fada tana fashewa da kuka hankalinsa ba karamin tashiba yayi kanta ya janye ya dagota ya rumgumeta yana buga bayanta"don Allah My Noor kiyi hakuri taya zan iya rayuwa babu ke nima ina sonki fiye da son da kikemun ki ajiye hankalinki ki rage zafin kishi komai zaizo da sauki wlh dolema zamu kwana tare yau na baki darusan da bazaki kuma cewa mu rabuba yi shiru yanzu bari kukan kar hajiyata tace na miki wani Abu kinji yar babyna kara sautin kukan tayi cikin Jan hankali ya ko kara rudewa"Ya Salam to yanzu na gane sokike murabu ko? kai na daga" ok yi shiru bari mu fito daga gidan hajiya ya fada yana shanye hawayen fuskata ya gyaramun daurin dan kwalina ya faramun shakulkuli bansa lokacin dana fara dariya ba"My Haidar kabari na tuba wayyo My chocolatyna cikina ya fara ciwo jin na fadi haka ya bari ya rumgumeni ya had'e face d'inmu yana huramun iskar bakinsa a idanuna ido na lumshe ina turo baki kamshin bakinsa na ratsa sassan jikinta dariya yamun ya janye fuskarshi wayarsa ya dauka ya shiga camera ya rika daukanta pic iri iri hasken fitilar ne yasa ta bude idanuta ganin hoto ne yake mata ta fara k'okarin amsar wayar ya hanata kokowa suka fara tana masa kukan shagwaba ta rukumkumeshi tana k'ok'arin amshe wayar"Allah ni My Haidar sai nagani idan baiba agoge tsayuwar motar sukaji yasa ta sakeshi ta zauna tana turo baki Aliyu yayi mamakin yaushe har suka ISO har aka bude get aka shiga cikin gidan bai saniba kallon teemah yayi yana murmushi ya dauki mayafinta ya ya yafa mata ya gyara mata fuskarta ya rataya mata jakarta" wow yar babyna ilove you kanta ta dora kafadarsa cikin wata irin murya tace" My Haidar kabari ni zanyi kuka "Sorry My Noor nima yi zanyi dariya tayi ta shafi fuskarsa da saman lips d'insa"my chocolatyna inajin sonka fah kaji autan maza dadine ya hanashi magana kukan sangarta ta saka masa ta makalkaleshi takai bakinta kunnesa ta cijeshi " woshhh My heartbeat yar babyna akwai zafi yi shiru bari na amsa nasan rigimar Na'am My sweet yar babyna nima inajin sonki kamar zai kasheni dariya tayi ta sakeshi ta koma ta zauna "Oya muje kalli an bude mota tun d'azu


fitowa tayi shima ya fito sojojin na tsaye kofar motar hannuta ya kamma suka nufi ciki wlh abin sha'awa sai sun burgeka yanda suke takunsu cikin nutsuwa har kofar parlon dan kansa ya bude kofar teemah ta fizge hannuta anashi murmushi ya saki ya shiga da sallama tana biye dashi itama sallama tayi wata kyakyawar dattijuwa fara jajur da ita shekaru sun ja saide jin dadi da kwanciyar hankali ya boye hakan sai wata matashiyar budurwar zaune tana waya da wasu yara kyawawa har su uku suna game jikinta TV da take manne abango cikin farin ciki da jin dadi dattijuwar ta Mike ta tarbo teemah"maraba lale da diyata sannu kunya teemah taji rumgumeta tana farin cikin ganin kyakyawar surukata yar yarinya kara Aliyune yazo ya rumgome mahaifiyar tasa"hajiyarmu kuma abun san kaine dariya Aminullah yaji ya juyo yaganshi bakin kofa yana isowa parlon sakin hajiyar yayi ya nufi gunsa sakin teemah tayi ta kamo hannuta suka nufi gun kujeru ta zaunar da ita sabka teemah tayi ta zube k'asa saman wani lallausan carpet"mummy ina yini zama tayi tana yaba tarbiyar yarinyar da nutsuwarta cikin fara'a ta amsa"lafiya lau Fatima ya yan gidanku tashi to ki zauna kin tashi tayi ta sada kanta Dole hajiyar ta tashi ta kamota ta zaunar da ita kusanta su Aliyu ne suka ISO kusan hajiyarsa ya zauna Aminullah yace da teemah"amaryarmu ina yini kai ta dago cike da kunya idanu ta zaro ganin fiskar Aminullah dariya suka mata shida Aliyu Aminu yace"kinga mai kama da mijinki ko ai fuskata yasa yayi basaja yaje neman aure kinga na fishi kyau ko kai ta girgiza dan gaskiya Aliyu yafi Aminullah kyau dariya hajiya tayi ta rumgumo teemah "haba Aminu wace mace zata yarda akushe mijinta sai yanzu budurwarnan tayi magana "kawu inata gaisheku fah gaskiya kawu amaryarka kyakyawace son kowa Aliyu yace"Sajida uwar yan rigima ya hutu kwana biyu bakije gidana ba bintu na nemanki teemah kallonsa tayi afakaice Sajida tace"kawu zanje zuwa gobe su kausar ne sukazo da gudu suka fada jikin Aliyu "Dady ina yini dagasu ya rikayi daya bayan daya yana musu kiss"lfy lau maza ku gaishe da Auntynku gun teemah suka Nufo sudaes ya riketa yana gaisheta murmushi tayi ta amsa kausar ta nuna Aminullah " Aunty kinga dadymu Mohammed yace"Aunty kirabu da ita surutune da ita dariya sukaba teemah sosai amma kunyar surukarta ya hanata tayi Sajida tace"kawu matarka akwai kunya baide cemata komaiba Aminu ya jashi gefe suna magana mai aikice ta cika table da kayan ciyeye da tande tande hajiya tace "dota maza ci abinda kikeso Sajida ce ta tsiyaya mata lemo da ruwa "Auntynmu bismillah kanta ta kara sadawa hajiya tayi dariya ta dauko cup d'in takai bakin teemah "bude bakinki nabaki"mummy kawo zansha ta amsa ta kurba ta ajiye tana wasa da yatsotsin hannuta rike hannun teemah tayi" diyata Allah ya miki Albarka wlh nutsuwarki ta burgeni kinada tarbiya da hankali Allah ya baku zaman lafiya kikuma yi hakuri da mijinki duk lokacin da miskilacnsa ya motsa idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login