Showing 126001 words to 129000 words out of 129912 words

Chapter 43 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5801

faduba Alqura'an yau bushashace za'a tafkaπŸ˜‚


**********
Rayuwa mai cike da jin dadi take faruwa gidan Aliyu ga soyayya mai tsaf Masa'udah cikinta ya tsufa sosai ta kumbara sosai su Teema sun bar mata Aliyu ya koma wajanta da kwanciya har ta haihu yaran Teema sunyi wayo sosai suna zama sai dai Hibatullah a kwai kuka Teema abin na damunta sosai amma Haidar ba ruwansa ba yada kuka kowa nashine sab'anin Hibatullah bata yarda da kowa sai Teema da babanta da Masa'udah suka dai zasu dauketa a zauna lfy.
Masa'udah tun jiya take hospital nak'uda take, amma har yanzu shiru ance lokaci bai ba, da saura Aliyu hankalinsa a tashe yake haka iyayanta da su Bintu.
Aliyu suna tsaye da Teema a jikin motar da Aliyu zai shiga Teema ta ce"My Haidar ko a mata aiki a ciro yaron wlh shiyasa na kasa zama hospital tausayi take bani... wayar Aliyu ta katse ma Teema magana. Yana dagawa ya kara a kunne Dr ya ce"Yallabai abinda yafi sauki kazo yanzu k'asa hannu a mata aiki, a fito mata da abin cikinta"A rikice Aliyu ya ce"Ok ganinan yanzu"ya fada yana shiga mota ya ce ma Teema"Baby koma ciki" ya shiga motar direba ya ja suka nufi get. Kai Teema ta d'aga ta shiga ciki ta fara shirin zuwa hospital din dan yadda taga Aliyun hankalinta ya tashi.
Aliyu ya zuwa hospital suka shiga Office din Dr ya saka hannu a kan amma Masa'udah aiki. Ya fito ya shiga dakin da Masa'udah take ya rungumeta yana shafa cikinta yana mata Addu'a Allah ya sa ayi aki a sa'a Iyayanta ma Addu'ar suka mata suka fita suna zaune a waje. Aliyu ya kama bakinta ya tsotsa yana shafa kanta yana ma rada a kunne har a ka zo fita da ita sai lokacin ta kallesa tana murmushi, shima murmushi yake mata ya ce"i love u my love Allah yasa ayi a sa'a" Masa'udah zatayi magana ta bashi hannunta ya kamo da sauki ya rike gam idanunsa sun tara kwalla ya ce"My love ina jiranki kinji" kai ta d'aga masa lokitici suka turata suna cewa"Yallabai lokaci na wucewa kayi hakuri har ta fito sai ku zanta dole Aliyu ya saki hannun Masa'udah aka tafi da ita tana waiwayansa tana sakin murmushi, shima yana sakar mata zufa duk ta wanka masa fuska ya rasa ko ta mecece ga faduwar gaba toilet ya nufa da sauri ya dauro alwalla, Bintu ce ta shigo itama alwalla ta daure ta zo tabi Aliyu suna sallah nafila...............✍🏻Yar Janafty ce










Ummu Fareesa ce...✍🏻✍🏻✍🏻




*πŸ‘°πŸ»MATARπŸ‘°πŸ»*
*πŸ’–πŸ’–GWAMNAπŸ’–πŸ’–*








*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan NigerπŸ€™πŸ»




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy JanafπŸ‘ŒπŸ»πŸ˜˜*




πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š
*ALHAMDULILLAH ALLAH ABIN GODIYAπŸ‘πŸ»*




*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*End*


*Page 5️⃣0️⃣*




....Aliyu da Bintu sun jima suna sallah tsawon awa guda, cur, suna nema ma, Masa'udah sauki wajan Ubangiji. Lokacin da Teema ta iso hospital, yayi dai-dai da fitowar doctor, yana neman Aliyu. Falmata da Ibrahim da Teema suka tarbi doctor, Ibrahim ya ce" Doctor ya dai Allah yasa anyi a sa'a" Doctor ya ce" Alhmdllh ina mijinta...? Falmata ta kalli Teema ta ce"Zahara ki shiga suna cikin room din can, ki kirasa" Da gudu Teema ta nufi room din. Ta murda kofar ta shiga , Aliyu yana zaune yana jan casbi. Teema tace" Sannu ku kazo Dr yana kiran ka" Ai da sauri Aliyu ya mike yana kallon Teema ya fice, su Teema suka biyu bayansa.


Aliyu yana fitowa Dr ya ce"yallabai muje Kaga yaranka"Aliyu ya ce"Dr uwar yaran fa...? Dr ya ce" Bata farfado ba tukun sai zuwa dare". Aliyu ya safke ajiyar zuciya, gabaki d'aya suka bi Dr a baya.


Wani daki suka shiga na Musamma wanda duk yaran da aka ciro su ta hanyar operation , nan suke kawo su, a gyarasu a shiryasu tsaf, kafin iyayan su su farka. Suna shigowa nurse biyu na kula dasu yarane guda uku kyawawa mata biyu namiji daya.


Dr ya ce" To ga yaran da aka ciro mata cikin koshin lfy" Aliyu saboda tsabar farin ciki k'asa ya zube ya rike k'afafun Dr ya ce"Allah da gaske yarana ne" ya fada yana kai goshinsa k'asa yana Sujada, ta godiyar Ubangiji. Falmata da Teema da Bintu rigai-rigai sukayi gurin dauko yaran da suka sha kayan sanyi farare harda wula, wacce Bintu ta dauka kamata d'aya da Masa'udah , tamkar an tsaga kara ta wajan Teema kuwa tamkar anyi copy din Hajiyar su, Aliyu sak har farin babu abinda ta bari namijin kuwa wanda Falmata ta dauka, Aliyu sak ba banbanci.


Sosai suke cikin murna wannan kyauta da Allah ya basu, Aliyu sai Ibrahim ya kamashi ya mike ya amshi yaran d'aya bayan d'aya ya musu Addu'a yana zubar da hawayen farin ciki kyautar yara uku rana daya.


Su hajiyar Aliyu da zuwansu kenan suka ga wannan abun alheri farin, ciki ba'a cewa komai sai kiran yan uwa a ke da abokan arziki, haka ma Aliyu sai bayan sun gama murna Aliyun ya nufi gurin Dr ya nemi a kaishi yaga matarsa Dr ya ce bata farfado ba yanzu bazai bar kowa ya shiga inda take ba, dole suka hakura kuma aka koma Addu'ar Allah ya tashe ta lfy ta ga yaranta.


Kafin zuwa bayan sallah isha hospital ta cika dam da jama'a yan uwan su Masa'udah da na Aliyu. Zuwa yanzu da Masa'udah bata farka ba hankalin Aliyu ya fara tashi babu abinda yake son gani sama da Masa'udah. Bangaran iyayanta ma hankalinsu a tashe ya ke duk da Dr ya ce lfy lau zata tashi, yaranta sun fara kuka dole aka kawo madara awaki mai kyau hajiyarsu Aliyu ta basu da kanta suka sha, sukayi dam sai bacci kowane cikinsu yatsarsa abaki, abinda yasa Aliyu yakejin tausayin yaran kenan ya saka su gaba yana kallo haka kawai yakejin faduwar gaba.


Wasa-wasa sai Masa'udah bata farka ba har washe garin da aka mata aiki an kwana an yini wlh fadar tashin hankalin family biyu su ke ciki baya faduwa a baki ga yaranta da kuka dole sai Teema da Bintun, suke shayar dasu tunda yaran Teema sunfu ma shan madara akan nono. Aliyu duk ya susu ce ya hana Dr sakat shidai a kaishi ya ga Masa'udah ya mata magana da amincewar Allah zata tashi.


To yanzu ma haka ce ta faru Aliyu yana Office Dr yanzu cikin masifa yake fada ya ce" Wlh Dr idan baka kaini naga matata ba yanzu , wlh sai na baka mamaki yau a garinan zan fara rashin adalci a kanka kai wani irin mutum ne, idan mutuwa tayi ka fada mana gaskiya mana" Dr ganin yadda Aliyun ransa ya b'aci ya ce"yallabai muje ka ganta.


Haka suka nufi dakin da Masa'udah ta ke. Lokacin da suka shiga sukayi karo da nurse zata kiran doctor, cikin gagawa doctor ya nufi gadon da Masa'udah take ya shiga dubata. Idanu Masa'udah ta bude karaf suka hada idanu da Aliyu, ta saki murmushi da gudu Aliyun ya karasa bakin gadon, ya zauna ya rungumeta ya had'e face d'insu hawaye na fita daga idanunsa , ya ce"My love tun jiya nake jiranki sai yanzu kika tashi sannu wlh rabo na da naci wani abu tun jiya, Allah ya bamu kyautar yara har uku har da mai kamarki bari a kawo miki su ki gansu" ya fada yana d'ago da kansa ya ce"Dr pls aje a zo da yaran mahaifiyarsu ta gansu" Dr baiyi magana ba ya fita.


Masa'udah ta shafi fuskar Aliyu ta ce"My love zaka kulamun da yarana sosai, na yarda da Antys Fati da Bintu yarana baza suyi maraici ba my love ina sonka zan barka, amma wlh zan tafi da farin ciki na auri wanda nakeso har na haifa masa yara ba ma daya ba biyu ko...? Aliyu ya ce" My love wai me kike haka ne ina zaki muna tare wlh Allah ina sonki ke macace da tasan darajar mutum tunda muke dake wlh baki tab'a batamun raina ba, wani lokacin har mamaki nake" murmushi ta saki ta damke hannunsa ta ce" My love na baka amanar yarana ka kulasu naji dadin yabon da kamun" da sauri Aliyun ya had'e bakinsu yana kissing dinta sosai Masa'udah ta ke taya shi ta dage sai tsotsar harshansa take tana rike da fuskarsa suna kallon junsu. Shigowar jama'a ce ta saka suka saki juna suna maida numfashi. Su Bintu gunta suka nufa har iyayanta.


Murmushi Masa'udah tai tana kallon su daya bayan daya, ta ce"Alhmdllh naji dadin sake ganawa daku don Allah a zaman da mukayi idan na b'ata muku ku yafeni, Papi kaida mummy ku yafemun don Allah" Falmata ta zauna kusanta ta ce" Mu baki mana komai ba, mun yafe miki" Aliyu ya janyo yaran ya runguma mata su.
Bintu ta ce" mummy ta shayar dasu ko" Hajiyarsu Aliyu ta ce" Aliyu d'agota ta basu su sha"


Zai kamata ta girgiza kai ta rike hannunsa tana murmushi ta ce" My love na baka Amanar yarana kaida su Anty da mummy pls kar bari suyi, rashin uwa pls" gabaki daya kowa yay tsaye kanta hankalinsu a tashe. Aliyu bai damu da mutanan ba ya rungumeta ya kwashi yaran dukansu ya runguma mata, tako rungumesu, gam tana lumshe idanu.


Aliyu ya ce" bari na gyaraki su sha nono" Masa'udah batayi musuba Aliyu ya gyarata ya fara shayar da yaran sosai suke shan nono Masa'udah ta daure dan tanajin zafi, amma haka suke hira da jama'a dakin cike yake da jama'a iyayanta hankalinsu a tashe ya ke amma ganin tana hira da mutane hankalinsu ya kwanta.


Duka yaran sai da suka sha nono sukayi dam sai da za'a saka mata drip Aliyu ya kwashe yaran ya kwantar dasu kowa kagani farin ciki yake ganin Masa'udah tayi sauki.
Aliyu saida yaga tayi bacci cikin nutsuwa tana rike da hannunsa lokacin dakin ba kowa.
Ya janye hannunsa ya mata sumba ya nufi gun yaran sai baccin su Suke.


Da dare misalin karfe goma Masa'udah jikinta yayi tsanani Dr na tsaye a kanta Aliyu yana rike da ita haka iyayanta tana so tayi magana , ta kasa sai kallon Aliyu take tana murmushi karfin hali, ta fara shakuwa Ibrahim ya ce" Aliyu fada mata kalmar shahada" ya fada kuka na kufce masa yabar dakin da gudu.


Cikin kidima Aliyu ya ce"My love meye haka" damkeshi tayi" ganin halin da take ya fada mata kalmar shahada wanda daket ta iya fadi tana kallonsa, tana kai karshe idanunta suka kafe, k'af.


Cikin mugun tashin hankali Aliyu ya fada mata yana kiranta" My love meye nufinki amma ba mutuwa kikayi ba" Matata ina sonki" Dr ya dafa Aliyu ya ce" Kayi hakuri shafe mata idanunta" jin abinda ya ce Teema da Bintu suka nufi gurin jikinsu na rawa, ganin da gaske Masa'udah ta mutu bata motsi atare suka saki ihu suka zube k'asa a sume, Dr da gudu ya fita ya kirawo jama'arsu Falmata wacce ta fara fitowa da gudu suka shiga.


Lokacin Aliyu ya shafema Masa'udah idanu ya rungumeta yana kuka kamar karamin yaro sam bai san ba ma su Teema sun suma, har an kwashesu an kaisu dakin da za'abasu temakon gafawa.


Hajiyar Aliyu ta janye Aliyu daga saman Masa'udah Falmata ma ganin gwara Masa'udah daket ta iya furta "Autarmu kuma yar farko mun yafe miki.... daganan diff ta fadi k'asa sumammiya.


Innalillahi wainnahilaihur rajiun.
Wallahi duk inda kuke tunanin tashin hankali to family Masa'udah da Aliyu sun shiga mutuwar Masa'udah ta girgiza mutane dayawa zuwa sha binyun dare, mutuwar matar gwamna ta baza birnin gombe da kauyi kanta.


Su Bintu sun farfado bandan kuka babu abinda suke.
Aliyu idan ka ganshi ya zama kamar zararre abin ba'a cewa komai. Dan iyayanta ba'a maganar tashin hankalin da mutuwar Masa'udah ta sakasu.


Washe gari da misalin karfe tara na safe aka kai Masa'udah gidanta na gaskiya wlh fadar irin jama'ar da suka ciki gidan gwamna da na iyayanta abin baya faduwa Aliyu yayi kuka sosai sai ma da za'a sakata makwancinta wlh kusan zaucewe yayi saida Abba ya rikeshi. Kai duk inda zan fada maka abin ya wuce nan dan si Teema ma daket aka Barbara hagar jikinsu aka fice da gawar.


Yaranta Teema da Bintu suke shayar dasu basuda aiki sai kuka baci ba sha. A haka har akayi sakar bakwai , amma kullum gidan cike da jama'a su iyayye da Abba da hajja Nanu sun zo kwanansu uku suka koma. Ranar sadakar bakwai aka radawa yara sunah Aliyu ya sakama mai kama da Masa'udah Masa'udah mai kama da mamarmu ya saka mata sonan ta Furairatu ya ce ace mata ummi, sai namijin sunan mahaifin Masa'udah Ibrahim.


iyayanta suka koma gida suka roki Aliyu alfaramar a basu yarinya guda Aliyu ya basu ummi dan ya ce bazai iya basu my love ba.
Haka sukayi godiya sunji dadi sosai.
Sauran biyun daya Teema daya Bintu sunce zasu rike Amana saboda Bintu ta yaye Zahara yaran Teema kuwa renon su na gurin su Nasira kuma sunfi shan madara a kan nono.


********
Haka rayuwar taci gaba har akama Masa'udah sadakar arba'in har yanzu Aliyu bai saki ba, ya zama wani iri kullum yana tare da yaran sunyi mul-mul dasu Masa'udah tsabar kama da uwarta babu abinda ta baro shiyasa Aliyu baya iya hadata da kowa Teema ma tana k'ok'arinta. Ummi ma tayi mul-mul tayi wayo gashi batada kuka Aliyu ya dauki son duniya ya dorama yaran yana kaf-kaf dasu.


*******
Kwanci tashi asara mai rai yau har Masa'udah ta shekara a k'asa yaranta sunyi girma suna gudun su ko ina, sunyi mugun shakuwa da Aliyu my love ya ke cewa Masa'udah yarinya akwai kyau ga wayo yaran Teema ta yayesu amma tana shayar da my love har yanzu Aliyu daket Teema da Bintu suka janyosa jikinsu ya dawo dai-dai saboda yadda suke tarai rayarsa da bashi kulawa ga wata irin riritawa da Teema take masa, da salonta na soyayya da shagwab'a idan kaga yaran Teema uku abin gwanin sha'awa bazaka tab'a cewa ba ita ce ta haifi Masa'udah ba dan tafi sonta fiye da Hibbatullah da Haidar.


Zab'e ya gabato Aliyu fur yaki ya ce bayaso amma magiyar da jama'ar gombe suke, masa ya fitowa zasu zabeshi daket da sa bakin Bintu da Teema, ya yarda kwana biyu baya samun zama a gari abubuwa sun masa yawa sai a hankali. Cikin ikon Allah Aliyu ya sake cinye zab'en gwamna jama'ar gombe sai murna da farin ciki, baya faduwa. Aliyu sai bayan da aka rantse dashi ya samu nutsuwa abubuwa suma sa yawa.


Bangaran Teema bayan ta yaye Masa'udah da ta roki Aliyu ya barta tashiga jami'a amma yaki fur ya ce ta hakura ta kula masa da yaranta dan ya gano Teema shigar cikine da ita amma bata saniba. Teema ba laifi tana temakawa yan uwanta da iyayanta dan yanzu haka ana Gina babbar secondary school a garin sarki da wani tafkeken masallaci da islamiyya wanda Aliyu ne ya dauko nauyin yin komai ya saka sunan Teemah.


🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Da misalin karfe goma na dare su Teema suna part din Bintu ita da yaranta suna hira sai gyangyadi take. Bintu ta bushe da dariya ta ce"my zahara aje a kwanta wannan da bacci yazo ko"Teema ta kalli gefen Aliyu da yake waya my love tana saman sa, tana masa jagwal-gwalon gwarancinta yana shafa kanta yana magana. Teema ta ce"My Haidar kaji Anty fa wai ciki gareni" Gira Aliyu ya d'aga mata yana murmushi. Baki Teema ta turo ta ce"Anty wlh bacci nakeji sai da safe ta janye Hibbatullah daga jikinta, ta kama hannunta.
Haidar ya rugo daga gurin su Asif yana dagama Teema hannu, daukarsa Teema tayi ta hadasu su biyu ta ce" my love wai kun zo da dady ai nasan baza ki tafi ba" hannu Masa'udah ta d'aga ma Teema. Dariya Teema tayi tace " Haidar sauka na dauki 'yata" ta fada tana ajiye Haidar saman ciyar Aliyu ta dauki my love sai dariya take Teema tayi k'asa da murya tace" My chocolate ina jiranka Allah in ka dade kuka zanyi" ta fada tana d'agowa, ta rike yaranta suka fice, tanacewa"Anty good night" Bintu ta ce" Night.


Teema tana zuwa saida ta masu wanka ta shirya su cikin kayan bacci, ta basu madara suka sha dan har yanzu suna sha sai da sukayi bacci ta kwantar dasu ita mata tayi wanka ta shirya cikin kayan bacci ta sakko k'asa tasha fresh milk tana zaune, ta ga Aliyu ya shigo da sallama. Da gudu Teema ta ruga ta fada jikinsa ta makalkaleshi ta ce"My chocolate ina My Haidar...? Aliyu ya daga cak ya goyata yana dariya ya ce"Bituna ta rikeshi wai tare za su kwana zahara take rigima a barmata kaninta" Teema tayi luf bayan Aliyu ta dora bakinta kunnansa tana tsotsar fatar kunnesa, a haka suka haye saman bene.
Bayan ta shirya Aliyu cikin kayan bacci sun kwanta manne da juna yana shafa cikinta ya ce"Babyna ciki fa gyaraki wlh" Teeema ta narke jikinsa tana shafarsa a shagwab'e ta ce"Wlh my chocolate na sani fa yau kwan uku da na sani, har tsawon wata biyu" Aliyu ya ce "Allah yasa ki haife mun yan uku" Teema ta ce"Ameen my Haidar tunda kanaso... bakinta ya kame ya fara bata zazafar sumba, nan take suka haukata junsu da rikita junansu har aka fada haraka. Asubah ta gari.


*****
Agurguje Bayan shekaru goma
Wanna shekaru da suka shude a bubuwane dayawa sun faru , harda saukar Aliyu kan mulki ya koma gidansa wanda ya so yafi gidan gwamnati kyau da tsari yaran sa duk sun girma sun zama samari muneerat an mata aure, har Rauda Asif da mucotar ko karatu suke amma suna duk an saka musu Rana yanzu sai zahara da Masa'udah da Hibbatullah yan kimanin shekaru sha biyu zahara tana da sha uku da watanin rayuwar gidan Aliyu rayuwace mai cike da tsafta, Teema tanada yara bakwai cif.


Bintu tana da takwas dan yan biyu ta haifa, sai auta Mujaheed. Teema kuwa ta sake haihuwar yara biyar bayan yan biyu Hassana da husaina sai Ahmed da halimatu sadiya, da Samha yanzu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login