Showing 81001 words to 84000 words out of 129912 words

Chapter 28 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5825

yayi koyi da fadar Annabi jin son abin cikin teemarsa yake kamar ya koma gidan ya fasa zuwa taron da gwamna bauchi ya gaiyacesu Azare" ja'iri duk murnace. mik'ewa yayi " to mu zamu tafi sai Allah ya maidomu Abba kenan acan ya kwana? " wlh acan ya kwana Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy. "Amin sajida tana school ko ni inaso na leka gidan Anty halima najima banjeba ya fada yana ficewa hajiyar tayi dariya tana rakashi da Addu'a yana.


fita ya shige mota suka fice jiniya ta karde layin anutse motocin suka jeru. Saman titi jama'a sai hannu suke dagawa suna mai bin Aliyu da Addu'a da kudirin zaben gabama shi zasu zaba shiko idanunsa alumshe yana cikin farin ciki Mara musaltuwa Teemarsa da cikinsa sai murmushi yakeyi ya tura hannuwansa cikin sumar kansa yana shafawa motocin sai sharara gudu suke safka lfy. teemah ko tana shiga taci kukan rashin chocolate ta tashi ta je ta gyara dakin haidar komai fes fes ta canza zanan gado ta kunna turaran wuta ta dauki kayansa ta wanke ta shanya ta koma dakinta ta shirya cikin doguwar Riga ta atamfa ta murza daurin dan kwali ta yafa mayafi ta dauki wayarta ta rufo dakin ta sabko k'asa ta nufi part din Bintu. tajima tana knocking Kafin abude mata Jiddah ce ta gashe da teemah tana murmushi tace" nice Karama ni ya kamata na gaisheki ta fada tana shigowa da sallama ta nufo parlon Bintu na zaune tana waya zahara nashan nono da gudu teemah ta iso ta zauna ta kwanto jikin bintu" Aunty Bintu gani ina kwana ta fada tana kokarin cire zahara ah nono Bintu ta tsinke kiran ta kalli teemah"hajiya zahara an fito. "Kai anty nida ko jirgi ban taba hawaba. Dariya Bintu tayi "aikuwa zaki hau matar gwamna kikefa hamm ai wlh ni na gaji da hawa jirgi. dariya teemah tayi ta dauki zahara tana shillawa suna hira tace"zahara zamuyi taro na matan manya da matan da Muke tallafawa da irin yada zasu koyi sana'ar hannu da irin kayayaki da Muke basu anjima za'a fara inaso kisa idanu sosai Kafin na doraki aturba dan gaba kadan nice zan zama matemakiyarki. "Kai anty nikuma dan Allah ki bari dariya bintu tayi sukaci gaba da hirasu ta duniya.


Aliyu tunda ya fita bai samu lokacin kiran mata nasaba sunkira ma bata dauka dan wayoyin basu hannunsa suna gurin boos shiko baya daukan kiran matansa sai na jama'a haka. su bintu sunyi taron mata masha Allah kowace ka kalla ji take da kanta sun hadu ba karya teemah ta ba kowa sha'awa agurin ga kyau ga tsantsar yarinta ga yada take bin bintun dan mafi yawanci ita ta rabawa matan kayan masarufin bayan an gama koya musu abubuwan fadila tazo matar Jamal tunda ba itabace ta zubarwa da teemah ciki Safinace itako Bintu ta yanke alaka da ita kowa sai tambayarta yake agurin Bintu ta sharesu wata me sunan lubna matar matemakin gwamna dan batanan akayi auran tana kasar waje ta rika zuga bintun tana wa teemah mugun kallo taso ta rainawa Teemar hankali teemah tace bata san zancanba dan taso fitsareta dan har ta daure tsatsun ta zata kirta mata rashin kunya tana cewa duk maison rabani da Auntyna wlh sai na kirta masa rashin mutumci kuma wlh mace tanaji tana gani gidanmu ya gagareta shigowa saboda nima walkice daide kugun ko wacce maras k'unya kowace daburbura mace da ba'asan asalin balbelaba sai tace daga k'asar masar take bintu ta janye teemah ta rungumeta ta lallasheta tako ji maganar bintu bata sake ko kallon matar ba har aka tashi ataron. lokacin da Aliyu suka ISO ana Kiran magarib bai shiga


gidanba yayi Alwalla ya nufi masallaci .Bayan sallah isha teemah tayi wankanta ta had'e cikin wani guntun wando iya cinyarta da yar Riga ta rufe cibi batada hannu haka take ta saki jelar kitsonta tayi kyau sosai tamkar miji na hannunta zaune take aparlo har yanzu haushin matarnan da taso raina mata waye takeji wayarta ta dauka ta kira malika bugo daya ta daga suka fara hira. Aliyu kuwa yana fitowa daga masallaci shida yaransa dan yaji dadi sosai da ya iskesu a masallaci ya nufo part din bintu bata parlo muneerat da Rauda suka taresa rungumesu yayi yana murmushi ya dagasu yana shillawa muneerat dariya takeyi Bintu fitowarta Kenan tace"my man saukar yaushe wai wanna katuwar yarinyar kake shillawa bama Rauda ba tasaka cira nama Rauda ta fara kuka ya mata ya ajiye muneerat ya dauki Rauda su Asif sukace"Dady muma ajiye Rauda yayi yana dariya"to kubari naje nayi wanka da sauri bintu ta nufi bedroom dinsa taje ta hada masa ruwan wanka ta isko ya daga mucotar "my aman don Allah karabu dasu wlh zasu jinyataka dariya yayi ya ajiye mucotar ya nufi bedroom d'insa Bintu ta nufi kan dining ta hada masa abunci yana shiga ya ajiye wayoyinsa har zai shiga bathroom ya tsaya jikin CCTV camera yana hango wani saurayi ana korasa da bakin bindiga aguje yabar gurin baki ya tab'e har zai fice ya danna yaga wacce wacce wainar yaransa suka toya can baya ya maida ranar da ya tafi Abuja yaga teemah da bintu suna rungume da juna suna kukan rashinsa da inda bintu ta lallashi teemah har tayi shiru ta rungumeta tana bata lbr dariya, taki dariya da inda zazzabi ya rufeta ta bata magani tasha yaji tana cewa teemah cikine da ita Allah yaraba lfy murmushi yasaki" my tauraruwata bintu wlh ina sonki sosai matsalarki dayace bakimun yada nakeso ashimfida maiyu din bakinsa ne ya kame lokacin da yaga Safina matar Nuradeen ta ingije Noor d'insa ta bugi table ya goce ta fado saman cikin da irin murkususun da take tana kuka jikinsa har rawa, yake yaga yada, bintun ta tada, hankalinta ta kira Dr har suka fice da dawowar bintun da zauwar malika da yada, bintun Ta kirayi safina tana mata Allah ya isa tasa, cikin Aliyu ya zube yanzu da yasan da shi ya zatayi dadinta daya bai saniba to ba ita ba ita zuface ta karyoma Aliyun ransa amutikar bace ya dauki wayarsa, ya kirayi ACP Nasir kahuta ya bashi umarnin kai tsaye ya dauki yaransa suje gidan sanator Nura su damko matarsa, umarni yake basu suji dalilin zubarmun da cikin matata da tayi da ganga har cikin gidana Kitt ya kashe wayar ransa amugun bace ya nufi kofar fita karo sukayi da bintu tana shigo kallo daya tamasa ta matsa gefe da sauri jikinta na rawa. damkota yayi cikin tsawa yace" cikin nawane aka zubar wlh ku dukan ku har fatima sai kun raina kanku agidanan tunda ni zaku munafurta ya fada yana sakinta saida ta fadi k'asa ya fito ya nufi part din teemah tundaga kwanar shigowa ya jiyota tana cewa" wlh bai ganeba ya zube dama ni banason ciki nayi karama ai baisan da cikin ba da gudu ya karaso parlon yayi tsaye a tsakiyar parlon jikinsa har tsuma yakeyi yace" inji uban waye yace bansan kinada cikiba au Kenan duk shirine kukayi keda bintu kuka zubarmun da gudan jinina Fatima Ashe yaudarata kikeyi baki kaunata nine bakison jinina zahara ya fada atsawace saboda tsabar kidima da firgici da tsoro teemah wayar ta saki ta Mike tsaye jikinta na kerrrrrma tana girgiza kanta "wlh my Haidar ina sonka bazan iya rayuwa babu kaiba ta fada tana nufo gunsa hawaye ya wanke mata fuska wata uwar tsawa ya buga mata" karya kikeyi munafuka menaji kina fada yanzu karki kuskura ki iso inda nake wlh zakiyi nadamar sanina arayuwarki cak teemah ta tsaya jikinta na rawa zufa na ketomata tayi mugun tsorata da yanayinsa hankalinta a mugun tashe yake tama nemi kukan ta rasa............✍🏻








Rahma ummu Fareesa ce😘






*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*








*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________






*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger🤙🏻




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*














*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page 3⃣5⃣*




.....kanta ak'asa asade jikinta na rawa tsoronsa ya gama lullubeta taji takunsa na dimfaro inda take tsaye da sauri ta dago kanta kallo daya teemah tama Aliyu tsoronsa ya kara linkuwa azuciyarta ta fara ja da baya tana girgiza kai ta had'e hannayenta tana bashi hakuri" uncle Haidar natuba nabi Allah nabi kayi hakuri karka dokeni don Allah kayi hakuri uncle Haidar. gadan gadan ya nufota ransa abace. Teemah naja baya jikinta na rawa ta gama tsorata da lamarinsa zubewa tayi k'asa kan gwiwarta ta had'e hannuwanta ta sada kanta, jikinta na rawa yana isowa ya damko ya mikar da ita tsaye yana janta ya gamata, da bango ya matseta, cikin tsawa, yace" Fatima nine


bakison haihuwa dani nine bakison cikina ajikinki kuka hada baki kuka zubarmun ciki saboda baki kaunata. ya fada atsawace yana kara matseta abango. arikice ta fado faffadan kirjinshi ta fashe da kuka" wayyo na mutu na lalace uncle Aliyu kamun rai karka ce zakayi mun hukuncin rashinka wlh mutuwa zanyi wlh bazan iya rayuwa ayanzu babu kaiba. "Karya kikeyi munafuka baki sona ya fada yana ingijeta daga jikinsa zata bugu da bango ya rumtse idanunsa tayi Saurin sake rikoshi ta rungumeshi ta zagayo hannuwanta k'ugunshi tana shafar bayanshi tana goga jikinta sosai ajikinsa tana tura kanta kirjinshi ta saki rikitaccen kuka. " don Allah uncle Aliyuna kamun rai kayi hakuri karka azabtar dani da rashinka bazan iya jurewaba wlh ba da gangan na zubarma da cikiba wlh bansa inda cikiba da bakanan ne ina bacci na fado daga saman akujera shine


muna zuwa hospital akace yazu be amma bamuda laifi nida Aunty Bintu kayi mana Afuwa muntuba wlh bazan sakeba inason cikin ka sakemun ko na yara gomane zan haife ma wlh inaso da na rasaka wlh gwara duk wata uku na haifoma yara uku zan jure wuyar akan rasaka uncle Haidar kayi mana Afuwa mun tuba ta fada ashgwabe tana kara shiga jikinsa tana gogar jikinsa cikin wani irin Salo ta mannesa. Aliyu kuwa tunda teemah ta mannesa tana kuka tana shafarsa ya fara sakin layi duk ya gano kuskuransu aciki kin fada masa da sukayi sai wayar da yaji teemah tanayi nutsuwarsa ya dawo ya tureta daga jikinsa cikin fada yace "karya kikeyi bakisona bakison haihuwa dani ya damko ya shafi mazaunanta yace"wannan kike cewa na sake hawanki na miki ciki ki sake zubarmun saboda baki sona shine dan yaudara kike cewa na sake miki ciki dan ki zubar dan bansan ciwon kainaba dan nine jarababbe to ki rike abunki banaso kuma dani kike maganar wlh sai kin raina kanki ya fada yana tureta ya juya zai tafi. ihu ta saki mai karfin gaske" Uncle Haidar karka barni natuba ina sonka. tana


kai karshan maganar ta tayi baya luuuu zata fadi da gudu yayi kanta ya tarota ta fado jikinsa bata motsi numfashinta ya dauke cak rungumeta yayi gam yana shafa bayanta" saboda Allah kimun laifi dan zan dauki hukunci zahara shine kika suma kinsan kina sona meyasa kike cewa bakison cikina wlh ko mai zakiyi saifa na saki ahanya saboda gaba. daukarta yayi ya nufi saman kujera ya kwantar da ita shima ya rungumeta ya shigar da Ita jikinsa ya lumshe idanunsa ransa abace yana sabke tagwayen ajiyar zuciya yana shafa kanta dagowa yayi ya tallabo kanta ya had'e bakinsu yana hura mata numfashinsa ya kamo tafin hannunta yana murzawa da karfi. kusan 10 minute yaji tana fizgar numfashi alamun ta farfado cigaba yayi da busa mata numfashinsa tana shaka har yaji bugun numfashinta ya dawo normal yaji ta fara tsotsar harshensa cikin nutsuwa ta makaleshi sosai hannunta saman wuyansa tana shafawa ahankali idanunsa ya lumshe ya kara shigar da ita jikinsa sosai yana sabke ajiyar zuciya yana shafa bayanta cikin nutsuwa sonta na azalzalar zuciyarsa gefe daya kuma haushinta


Teemah jin laulausan harshen Aliyu abakinta wani irin farin cikine ya kamata ta kara narkewa jikinsa tana tsotsar harshensa tana nishi da shashafarsa tana kara shigewa jikinsa. kamar an tsikaresa ya kantsara mata cizo aharshenta da karfi ba shiri ta saki ta fashe da kuka jikinsa ya janye anata ya sabka daga kujera yana zabga mata harara cikin tsawa yace"dallah can ima mutane shiru tashi maza ki nemi abinci kici kije ki kwanta wlh idan kika sake kuka ko ba kici abunci ba ko ki kaki yin bacci zan dinga kallonki daga can wlh karki yarda gobe mu hadu dake tashi mana ina magana kin k'ureni da idanu. jikinta na rawa ta tashi ta hadiye kukan ta nufi dining cike da tsoro bakinta na rawa tace"Uncle... Haidar... Za... Zza.. Bi.. Na.. Ke... Ji.. Jikina.. Zafi..." Allah baki lfy kinemi magani kisha ni me zan miki ya fada yana rumtes idanunsa ya bude da sauri ya kada kai ya fice daga parlon.kukane ya


kufcema teemah ta rufe bakinta ta zauna ta zubi abuncin da yace taci duk dadinsa jinsa take kamar madaci haka ta rika turawa tana goge hawayen fuskarta tana gamwa ta dawo parlo ta dauki wayarta har ta tsage ta Haye sama dakin Aliyu ta shiga ta fada saman makeken gadonsa ta fashe da kuka saida tayi iya yinta har kanta ya fara ciwo ahaka bacci ya kwasheta idanunta har sun fara kumbura tana mai nadamar furicinta duk da ba da gangan ta zubar da cikinba ta kara nadama taji tanason ciki ayanzu dan bata taba tunanin Haidar zai mata hakaba akan cikinsa da sun fada masa kuma da bata fadawa Malika ba batason ciki ahakane har baccin ya dauketa.


da sallama ya shigo parlon. Bintu na zaune hankalinta atashe ta amsa ko kallonta baiba ya nufi hanyar bedroom din Rauda ta bishi da gudu. Dadyna. daukarta yayi ya rungumeta yana sakar mata kiss agoshinta" my baby jeki dauko chocolate kici kima zahara wasa, sai na fito ya ajiyeta. da gudu ta tafi shi kuma ya nufi bedroom dinsa Bintu ta zuba masa idanu har yashige. Aliyu yana shiga kayan jikinsa ya rage ya fada bathroom ya santalo wanka yana fitowa yaga bintu zaune da sauri ta Mike ta nufi gunsa fuskarta cike da hawaye ta fada kirjinshi ta saki kuka" my man don Allah kayi hakuri mun tuba bazamu sakeba wlh tsautsayine


banyi hakaba da wata manufa sai dan nasanka da son yara kar hankalinka ya tashi shiyasa nace karmu fadama amma laifina ne Zahara tayi karama bata isashan wayon da zata bani shawara mu fadama munyi kuskure dagani har ita Kayafe mana mun tuba my man. shiru yayi mata ya janyeta jikinsa ya nufi dressing ya shafa mai ya bude wardroob dinsa ya ciro Riga da wando na bacci ya saka dan yana bukatar kwanciya ya wuta yau da wuri wayarsa ce ta dauki ringing ya nufi gunta yaga sunan Nuradeen tsaki yaja ya dauka yay picking ya kara akunne" hello." Aliyu dan Allah kayi hakuri naji duk abinda safinar tayi agidanka ACP da kanshi fah yazo kamata badan itaba danni ka janye karan wlh zan mata abunda yafi hukuncin da za'a mata dan wlh sai na bata mamaki kawar amaryarka zan auro mata wlh sai tayi nadamar duk iskancin da take shukawa agidana karshansa yazo pls Aliyu kayi hakuri ni wlh sunana ne banason ya baci. Ajiyar zuciya ya sabke" OK naji amma Nura babu matarka babu matana ba ita ba gidanz wlh duk rada ta kuma takowa gidana wlh sai NASA an daureta. " nagode Abokin kwarai shugaba mai adalci insha Allah bazata zoba nima zaman hakuri nakeyi da ita. baki Aliyu ya tab'e ya tsinke kiran.


ya kalli Bintu yace" dallah malama lfy kika sani GABA fita kibani guri bacci zanyi shiru tayi ta fice jikinta asanyaye ta koma parlo ta zauna tana goge hawaye yaranta suna wasansu. Aliyu Kiran ACP Nasir ya kira yace su baro gidan Nuradeen komai ya wuce. wayoyinsa ya kashe baki daya yayi kwanciyarsa dan agajiye yake ga bacin rai haka ya kwanta baici komaiba. Bintu ko karfe shadaya tasa yaranta kowa ya kwanta taje tayi shirin bacci ta dauki zahara ta nufi dakin Aliyu cikin sa'a tana murda kofar ta bude zahara ta ajiye agefe agadonta ta hauro gadon ta shige jikinsa ta rungumeshi ta jamusu blanket tana kuka kasa-kasa yana jinta yayi burus da ita har tagaji jinta acikin jikinsa batasan lokacin da bacci ya dauketa ba. Aliyu ya jima kafin bacci ya daukeshi da kudirin sai ya horasu da kyau yada gobe bazasu sakeba barinma teemah da yajita da kunnansa batason ciki. Asubah ta gari.


************************************


Bayan kwana biyu
Har yanzu Aliyu bai huceba baya shiga sabgarsu ko kallon arziki basu samu teemah da Bintu sun kasa sukuni hankalinsu atashe yake idan kaga Aliyu na dariya shida yaransane suke wasa jiya teemah ta kama girki da kanta ta hada masa abunci amma yaki ci lokacin bacci ta iskeshi dakinsa korota yayi yace taje dakinta bayason taje ta jika tasha baya ci haka tayi ta rusar. kuka ta koma dakinta da zazzabi ta kwana dan ta rasa ya zatayi saboda babu wata fuskar rungumarsa. gashi abukace take dashi. to haka Aliyu yake gasawa matansa gyada ahannun barinma teemah yafi azabtar da ita dan ya hana ta rabesa dan kar ya kasa control din kansa. Bangaran.


Safina da Nuradeen kiri kiri yace mata aure zai yarinya danya ai haukane batayi dan tuni nura yaje gidansu maheeda cikin hukuncin Allah ta yarda dashi dari bisa dari dan rayuwar teemarta da Aliyu tana kwadayin samun miji dan love niko nace Maheeda ki shirya zama da safina idan maganar aure ta kan kama. da misalin karfe tara na safe teemah ta shirya cikin Riga da siket na material pink colour tayi kyau sosai ta saki jelar kitsonta ta fesa turare ta dauki mayafi da wayarta ta fito dan ranta ya fara baci akan abinda gwamna yake mata kawai tana daure wane dan tasan itace batada gaskiya. anutse take taka matatakar bene har ta sabko kamshinsa taji ta tabbatar yana parlon kan dining ta tsinkayosa gunsa ta nufa ta ajiye mayafin tana zuwa ta bayansa ta rungumesa ta rankwafo da kanta ta dora bakinta akunnesa tana shafa kansa" My chocolatyna good

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login