Showing 123001 words to 126000 words out of 129912 words
Chapter 42 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt
karfe takwas na dare suka shigo kauyan garin sarki, murna wajan Teema bata faduwa. Su iyayye anyi ma su Teema girke-girke mai rai da lafiya, an gyara musu bangaran da su Malika suke sauka.
Yau kauyan garin sarki kofar gidansu Teema cike da jama'a, an kewaye motocin gwamna sai cewa suke mijin watsime mai Allo yazo kawo watsime haihuwa ba inda suka k'ara shagala sai da su Boos suka fara jido kayan haihuwa wanda komai kayan haihuwar odarsu Aliyu yasa, akayi daga dubai, kursu ana tsaka da kwaso kayan ta iso mijinta ne ya kai mata labari ai kuwa aguje tazo da ita aka jide komai, sai washe baki take ganin harda su buhuhunan shinkafa da katan-katan na macaron , da jarkar mai bakinta yaki rufuwa sai cewa take abu namu zamu rak'ashe.
Bayan Aliyu sunyi sallah isha tare dasu Abba yasa Teema ta masa jagora har bedroom an gyara tsaf gadon yasha sabon zane sabo irin dan saudiya ga wani fitinanan kamshi na tashi fanka sai kadawa take sanyi mai dadi. Bayan Aliyu yay wanka Teema, ta shirya shi, cikin Riga da wando na na yadi mai shar-shar suka fito. Bayan sun gama gaisawa, iyayye ta ke cemasa" ya hakuri zama da su Zahara" murmushi Aliyu yay Abba ya ce"Auta tashi kuje ya ci abunci su su bassu suke ko an kaimusu bangaransu" Teema dariya take harda rike ciki ta mike suka nufi massukin Aliyu.
Da kanta ta bashi daddan girkin da iyayye tai musu shima ya bata ci tayi dam ta langwab'e jikinsa ta ce"My chocolate bari na tafi muyi hira da iyayye da Abba da kursu" Aliyu ya zura hannunsa cikin rigarta, yana murza nipples d'inta, ya ce"Babyna ni banji duriyar Dr Zubaida ba tana ina...? Teema tai dariya ta ce"My Haidar Dr iyayye ta boyeta bayan tayi wanka taci, abunci ta kunna mata fanka ta mata shimfida tana can dakinta, a kwance tana chart kursu tana wajanta, tana zuba mata surutu". Aliyu yay murmushi ya janye rigar Teema ya ce"My Noor nasha abuna?" Teema ta ce "Eh bari na baka" ta fada tana tallabo kansa ta saka masa nonota d'aya a baki ya ko cafke ya fara tsotsa cikin nutsuwa Teema na shafa kansa tana murmushi tanajin dadin tsotsar.
Ya jima sosai yana shan breast dinta sai da ta fara jin zafi ta cire daga bakinsa tana dariya, ta ce"My chocolate kamani na tashi" janyeta daga jikinsa yay ya mikar da ita ya ce" Babyna ni kadai zan kwana wayyo na zama maraya" Teema tayi narai-narai da idanu ta ce" Mijina zan sato jiki na dawo da zaran su iyayye sunyi bacci kaji" dariya Aliyu yay ya kamo hannunta suka fito.
Hira sosai Aliyu da su Abba da iyayye sukayi Teema na jikin iyayye tana mata tausa kursu ta fito daga dakin suka gaisa da Aliyu. Sai can dare mijinta ya biyota, suka tafi gida, Aliyu ma zuwa yay ya kwanta ya kira matansa suka sha hira, dan Teema wayo ta masa, tana can manne da iyayye tayi bacci.
***
Washegari da misalin karfe goma su Aliyu sukayi shirin komawa gombe ya k'ara jama Dr Zubaida kunne ta kula masa matarsa sosai. Teema cikin kewar mijinta suka rabu harda kuka sai da Aliyu yayi akin lallashi , kafin ya samu ta hakura ta saki ranta suyi sallama ya tafi yasha Addu'a da godiya gurinsu Abba da Hajja Nanu waccetayi ta tsokanarsa.
Bayan tafiyar su Teema a ka shiga yawo gari duk inda tayi kallonta ake cike da sha'awa ana mamakin watsime mai Allo ce ta zama haka kamar balarabiya. Su nawalu har gida akazo ma watutu sannu da zuwa hakama lado mai kifi duk sunyi auransu matansu duk da ciki.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
Washegarin komawar Aliyu Bintu ta bar girki Masa'udah ta kama Aliyu yau ba inda ya fita saboda gajiya sai yama ne ya leka Office daga can ya wuce gidan iyayansa. Masa'udah da kanta ta shiryasa Aliyu daddan girki irin wanda ya ke so ta hada masa fruit na kankana ta masa dambun nama, Bintu sai santi take, dan har suka gama cin abunci dare Aliyu bai shigo ba, yana gidansu suna hira da iyayansa ya Kira Teema sunfi awa guda suna hira take fada masa tana gidan Nanu ita da Dr Zubaida da kursu Nanu ta musu danbun shinkafa da zogale suna ci. Aliyu dadi yaji sosai ya ce tabi asannu da sun gama su koma gida.
Sai karfe tara Aliyu ya nufi gidan sa.
A parlor ya samesu suna kallon wa'azi a tashar Sunnah Tv, da sallama ya shigo yaran suka tarbe shi da murna sai da ya d'agasu d'aya bayan d'aya. Bintu ta ce"My man wai baka gajiya da daukan yaran nan" Dariya Aliyu yay ya ce"Bana gajiya wlh so nake naga gidan ya cika da yarana, na samu kaamr guda talatin, ace duk ku uku kuka haifamin" Masa'udah tayi dariya tana masa sannu da zuwa. Ajiye Rauda yay ya dauki zahara da ta numfashi tana bangala dariya, ya dauketa yana shilawa ya ce"da Masa'udah" My love rabona da abunci, tun safe fa" mik'ewa tai tana murmushi ta nufi kan dinning ya bi bayanta Bintu na masu dariya ta ce "Zahara zata barka kaci abunci anutse".
Masa'udah da kanta ta ba da Aliyu abunci, har ya k'oshi ta bashi fruit ya sha yana sanyi zahara na rungume da babanta sai yakushin sa take tana masa gwalamtunta Masa'udah tana musu dariya. Bayan Aliyu ya gama suka dawo parlo Masa'udah ta tafi bedroom din Aliyu ta hada masa ruwan wanka , ta dawo ta fada masa.
Zahara taki ta yarda ya ajiyeta ta fara kuka sai Masa'udah ta mata wayo ta amsheta tana jijigata Aliyu ya tafi yayi wanka.
Masa'udah tana jijiga zahara har tayi bacci, ta zauna tana rungume da ita suna hira da Bintu yaran suna can gun game dinsu, Bintu ta korasu su dauki karatu gun Asama'u suka nufa su dauki karatu.
Aliyu bayan ya fito ya kunna laptop yana aiki suna hira jifa-jifa da su Bintu. Sai da dare yay sosai kowa ya nemi kwancinsa, bayan Aliyu yaje yama Bintu sallama ya kira Masa'udah bangaransa. Sai da ta shirya kanta cikin kayan bacci ta saka hijabi ta tafi bedroom dinsa. Lokacin Masa'udah ta zo Aliyu yana sallah, hijabin ta cire tayi kwanciyarta.
Aliyu sai kusan karfe biyu ya gama sallah ya shirya cikin kayan bacci ya ya hauro saman gadon, ya ce"My love kinyi bacci ne...? Ya fada yana rungumeta. Dariya Masa'udah tai ta ce"Haba my love ta ya zanyi bacci baka kusana" Murmushi Aliyu yay ya shafi cikinta, da ya taso ya ce"Babyna ka ce momy ta mun tausa da fatan dai bata baka wuya ba dan naji girki yayi dadi kar aje an ba Babyna wuya" Masa'udah mak'ale Aliyu tayi tana dariya tana zabura yadda yake shafa mata cikin. Aliyu ya fara rikita mata lisafi da salonsa cikin k'ank'anin lokaci ya birkita ma Masa'udah lisafi ta shiga maida masa martani yadda ya dace sosai suke romance din junansu kafin wani lokaci sun lula duniyar ma'aurata. wani sanyi dadi dukanunsu suke ji tunda Aliyu ya shige gidan dadi ya lumshe idanu yana kai komo yana kiranta"My love tana amsawa cikin guguwar dadin da takeji sai sambatu take zuba masa tana kukan kissa harda shasheka tana k'ara zugashi, haka suka haukacema junansu suna raya sunnah. Asuba ta gari.
***
Yau kwanan Teema uku a garin sarki masha Allah tana samun kulawa gurin iyayanta da hajja Nanu kullum sai sun zagaya garin sarki ita da Kursu iyayye ta hanata amma sai cewa tayi Aliyu ya ce ta rika yawo Dr Zubaida kullum sai ta dubata duk inda zasu tana biye dasu, gudun kar nak'uda ta kamata, a yawon dan basu zama iyayye kuwa dadi take Autarta Allah ya kashe ya bata miji nagari mai sonta da kuanarta ga taimakawa yan garin da yake dalilin Fatima.
Yau ta kama asabar da misalin karfe biyar na yamma Teema ce zaune a tsakar gidansu, tana cin danwaken alkama sai santi takeyi tanama iyayye surutu, tana cikin magana sai taji wani abu ya soki bayanta sai ta cije baki abin da ya isheta ta ajiye kwanon ta fashema iyayye da kuka, tace"Wlh iyayye yaron cikina yana caka mun wuka fa haba ina dalili tun safe fa yake mun zalumci, nagaji"Iyayye ta ce"Wai Auta lafiyar ki kuwa ta ina dan cikin ki yaga wuka... maganarta ce ta tsaya lokacin da Teema ta fasa ihu ta rike marta tana cewa"Wayyo Allah wlh sai ya fito na shiga, uku" aguje iyayye ta nufi Teema ta riketa ta ce"Na shigesu Zahara karki ma, haihuwa kuka wai ya ma akayi kina nak'uda tun safe ban saniba, gashi Dr sun tafi zinder...dai-dai lokacin Dr Zubaida ta shigo da sallama da ledoji a hannunta, ganin iyayye ta kamata Teema sai matse baki take zufa ta wanka mata fuska ta rike iyayye gam ta ce"Iyayye ni kam ta Allah ta zo dan Allah ku yafe mun kiramin Abba da Aliyu na nemi gafarasu:Zubaida ta iso tana cewa"iyayye wai meke faruwa, haihuwarce"ta fada ta kama Teema sai kallamar shahada take. Zubaida ta kamata suka shiga ciki ta shiga bata temako tana dubata haihuwar ta gabato. Iyayye mayafi a hannu ta fice da gudu ta tafi kiran hajja Nanu ta biya gidan malam shehu aka mata rubutu ta nufi gida lokacin Teema tana dab da haihuwa tana jin jiki ta cema hajja nanu"Hajja dama da zaki haifi Abba haka kikaji...Bakinta, hajja Nanu ta rufe mata. Cikin ikon Allah tare da temakon Dr kan yaro ya fara badowa. Zubaida ta ce"Zahara kiyi nishi kadan" Teema cikin wahaltuwa tayi nishi sai ga kan yaron subuk ya fito Zubaida ta janyota ya idasa fitowa yaro namiji kyakyawa kamar Aliyu yayi kaki ya ajiye a take ya tsala, kuka Hajja nanu ta yanke cibiya amma sai me wata nakudar Teema ta fara Zubaida ta ce"Wlh wani d'an ne"ta fada tana duba Teema bata tan-tan ceba kai ya bado Zubaida ta temaka mata sai ga santaleliyar yarinya ta fado tana tsala kuka. Hajja nanu ta rangada guda, ta ce" kai Masaha Allah" Zubaida ta yanke cibiya ta duba Teema ta k'aru saida ta mata dinki wanda daket da jibin goshi akayi shi Dr ta ce da Hajja a dora ruwan zafi a gyarata.
Iyayye murna ta cika mata ciki sai kallon Teema ta ke wacce tayi tsuru-tsuru da idanu tana kallon ikon Allah sai maida numfashi take.
Bayan anyi ruwan gumin Hajja nanu ta gyara yaran tsaf gwanin sha'awa an saka musu kayan sanyi, Zubaida ta bude gadon jariran aka kwantar dasu saboda yana da girma. Iyayye da kanta ta gyara Teema sosai, bayan ta gyarata ta dora mata kunun kanwan ta zuba masa madara ta bata tasha daket saboda ciwon cikin da take. Bayan ta Shane hajja Nanu ta sakata gaba saida ta shayar da yaran harda kuka saboda yadda suke tsotsar mata nono zafi Kamar kan zai fadi takeji dan zafi sai hawaye take.
ABBA labari yana samun sa ya Kira Aliyu ya fada masa, karkaso kaga murna da a kace Teema ta haifar masa yara biyu mace da namiji ana take ya rika kiran yan da a bokan arziki yana fada musu lokacin suna tare da Masa'udah dan murna rasa me ma zatace tayi. fitowa tayi da gudu ta fadama Bintu nan suka lalace da murana, suna shirya yadda zasu ci bakinsu a garin sarki kowacce ta Kira iyayanta ta fada musu sukuma suka kurayi Aliyu suna masa barka. Aliyu can gidansu ya tafi ya fada musu ya Kira Safffah da marwah ya fada musu sai murna suke zasu Niger sunah.
Teema saida tayi kwan uku da haihuwa ta warke ta fara cin abunci saboda ciwon ciki da yake takurata sosai ta ke samun kulawa kullum suna waya da Aliyu itace ta hanashi zuwa tace ya zauna yayi aikin sa, ya bari sai sunah tunda tana samun kulawa ga yaranta cikin koshin lfy. Daket ya yarda sai jibi sunah za suzo, baki dayan family dinsa da matansa. Teema tayi murna sosai Maheeda ma tana tafe duk itama cikin ta ya dan fito. Malika kuwa tun washe garin haihuwa ta iso Mu'azzam sai ana gobe sunah zaizo.
Haka kuwa kayi ana sunah saura kwana biyu Aliyu suka iso tare da tawagarsa Teema dadi da murnar ganin su Bintu da Masa'udah su Anty Halima Saffah da Marwah matan su Aminullah kai gaskiya garin sarki ta kwashi jama'a, ba laifi su kursu an samu yadda a keso baki yaki rufuwa. Teema bata samu ganin Aliyu ba sai zuwa dare ai kuwa ansha tsotsar bakin juna har nonon saida ya lasa Teema sai shagwab'e take zuba masa yana lallabata yaji dadin ganin yar macan tayi kama daya da Teema tamkar an tsaga kara har fatar jikinsu iri daya namiji kuwa babu abinda ya bari na Aliyu.
Duk inda kuke tunanin sunah na yan biyu masu gata yaran Teema an musu dan kauyan garin sarki cike yake babu masayar tsinke, ko ina jama'a ce shanu biyu aka yanka raguna biyar macan aka saka mata sunan Hibatullahi Namijin Teema ta buga kai da fata tace Aliyu ta ke so, dole Aliyun aka saka hakan ya burge yan uwansa sosai, da shi kansa harama su Bintun sunji dadi sosai Teema fadin irin kyauwun da tayi bata lokacine ita da yaranta Hayyo mai ganga fa yasha liki kam su iyayye yau saida ta rasa inda zata jama'a Maheeda sosai bakin,Teema ya burgeta sai taji inama a kauye ta girma.
Alhmdllh haka akayi biki lfy aka gama lafiya su Aliyu sai washe garin sunah suka tafi baki dayansu sai Teema kadainsuka bari harda kukanta Dr Zubaida manta bisu wacce Aliyu ya ce shi kadai yasan alherin da zai mata wanda bazata manta ba har bayan ransa. Malika ko da Maheeda da Mu'azzam sai bayan suna da kwan biyu suka tafi Teema tasha kuka wai su zauna sai ta zubar da ruwa, kafin su koma tare dariya kawai suka.mata suka tafiyarsu.
******
Haka Teema ta ci gaba da wanka tana kula.da yaranta, Aliyu ya turo mata Nasira da Walida suna mata ronon Haidar da Hibatullah itako tana samun kulawa agurin Nanu da iyayye sai gyaran gargajiya Suke mata ciki da waje ta murje tayi kyau tayi yar kibarta saboda tana cin abunci sosai, gata da ruwan nono yaran kullum suna gurinsu Nasira shiyasa take samun lokaci suyi ta shart da Aliyu soyayya ba irin wacce basayi ta waya ita da chocolate d'inta da su Bintu da Masa'udah kullum sai sun gaisa.
Haka rayuwa taci gaba har Teema sukayi Arba'in sunyi mul-mul ita da yaranta Teema tasha gyara ta tsumu sai zuba take Aliyu zauwar sa biyu, yana duba yaransa. Teema zinder taje aka mata kunshi da kitso na kice raini na komawa gombe. Teema ta zama tauraruwa cikin taurari yaranta kyakyawa masu farin jini kowa sonsu yake. Su iyayye sun mata fada sosai ta zauna da yan uwanta lafiya tama mijinta biyayya sosai taji nasiyar iyayanta Boos ne yazo daukarsu Da kuka suka rabi da Abba da iyayye da Kursu da hajja Nanu suka tafi suna mata fatan alkhairi iyayye kanta saida tayi kukan rabuwa da yarta da jikokinta.
***
Nigeria gombe da misalin karfe tara na dare Teema ce taci uwar kwaliya ta kece raini Hibatullah na kuka ta sunkuya ta dauketa ta ce"Ke yarinya ni fa yau banida lokacin ki lokacin my chocolate ne"ta fada tana dorata kafadarta ta kira Nasira ta dauki Haidar suka nufi part din Bintu ta musu bazata dan basu san ta isoba.
Da sallama suka shigo parlon Bintu. Masa'udah ta mike da gudu tana cewa"Anty Bintu wlh anty Fati sun iso, zo kiga yaranmu kyawawa" ta fada tana amasar Hibatullah tana mata wasa Teema ta ce" Nagode ni baki tawa sai ta yarki ko" Dariya Masa'udah tayi Bintu ce ta fito tana murmushi ta ce" Wlh nazata sai can dare zaki iso sannu ya hanya" ta fada tana amsar Haidar a gun Nasira. Zama sukayi suna gaisawa Hibatullah ta tsala kuka Teema ta amsheta tana shayar da ita yaran suka baibayeta suna mata sannu tana amsawa. Aliyu ne ya shigo bakinsa yaki rufuwa ya kuramaTeema idanu wani irin kyau da tayi tayi yar kiba kamar ba itace ta haifi yaran ba. Bintu ta ce" Bakuwarmu ta shi muje dinning mu ciyar dake" dariya Teema tayi tana kallon Aliyu ta daga masa gira ya kashe mata idanu yana mata nuni da ta gama cin abunci ta wuce part dinta kai ta kauda. Kan dinning suka nufa har yaran sukaci suka yi, dam cikin wasa da dariya kowa ka gani cikin farin ciki yake.
Basu jima ba da gama lunch Teema ta musu.sai.da safe ta tafi part dinta tana rike da Haidar Nasira Hibatullah. Aliyu a dadafe ya kai karfe goma yama ko wacce sallama ya nufi gun Teema duk sun gano yadda Aliyu ya ke dauki dariya kawai sukayi sukaci gaba da hirasu.
Aliyu yana zuwa saida ya shirya kansa cikin.kayan bacci ya nufi dakin Teema ya isko ta shirya cikin wata riga bata maraba da tsirara, tana labe bayan kofa yana shogowa ta mak'aleshi ta baya tana dariya ta ce"Wayyo my chocolate I miss you I love you sonka ya kusa kasheni saboda kewarka, so bakwai ina suma ina farkowa My Haidar rayuwa babu kai wlh bata anfani ta karasa maganar tana sakin kukan sangarata tana cewa" My Haidar goyani naji gumin bayan ka rungumeni ka rarsheni kaji"Aliyu a rikice ya dauketa cak, yana juyo da ita yana sunsunata ya ce"My Noor don Allah bari kukan yi hakuri ba ganiba insha Allah babu a binda zai sake rabamu haba Sahiba mmn Tiwis wlh inason Hibatullah fiye da tunaninki saboda tsayar kamar da kuke da ita yi shirunki bari na goyaki" ya fada yana goyonta yana zagaya tsakiyar dakin sai dariya take tana cewa"dokin malam kayi gudu mana... Aliyu sa da ya gaji ya safke ta, yaje gadon yaransa ya daukesu daya bayan d'aya ya musu Addu'a ya kwantar dasu ya dauki Teema suka zube saman gado Teema ta bude baki zata masa magana ya cafke bakinta yana bata hot kiss, Asuba ra gari wannan budirin naku bazai