Showing 102001 words to 105000 words out of 129912 words
Chapter 35 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt
fito da kyawun dirinta tsaf ta daure gashinta ta fesa turaruka babu adadi ta dai yi yar kwaliyarta tayi kyau sosai amma sai ta kara narkewa asaman gado ta shige cikin blanket tana jiran Aliyu.
Aliyu ko suna zuwa gidansu bayan an bude masa mota ya fito ya shiga ciki.
Da sallama ya sanyo kansa cikin parlon.
Wani gamshin dadi ya daki hancinsa.
Hajiyarsa na zaune tana gyarama Abbansu Aliyu farce Sajida ta sakasu gaba tana musu tsiya.
Atare Suka amsa sallamar.
"Abba yace "Shugaba nagari mai adalci kaine da kanka cikin rana haka."ya fada yana dariya.
Aliyu ya kurama iyayan nasa idanu yana murmushi.
Ya karasu ya zauna yana gaishesu yace"Abba ya gida wlh wai daukan yaran nazo gobe akwai school,hajiyarmu ba magana ma." ya fada yana rungumeta.
Sajida tace "Kawuna ina yini ai wannan tsafin kabarsu kawai"Aliyu yace "Sajida idan kika shiga hannuna wlh zaneki zanyi."Hajiya tace"Aliyu ya gida dasu Bintun ya jikin Fatima yaranka fa d'azu d'azu Aminullah ya tafi dasu gidansa yace da yamma zai kaisu gada."murmushi Aliyun yayi yace"Ok ba damuwa ai ban saniba duk suna lfy.
Abba yace ''ya wannan ita karamar matar taka kana kula da ita dai ko dan yarinyar tana bani tausayi dan Allah ka bata kulawa kamar sauran matanka."Aliyu Kasan ya sada k'asa yace "eh ana kula da ita yanzu ma batada lfy can zan biya na dubata."Hajiya tace "Asha Allah bata lfy"Abban yace"a To tashi ka dubota ita din abin atausaya matace."hajiya tace"lalai fa"Sajida dariya tayi.
Aliyu ya zabga mata harara,sum tabar parlon.
Aliyu ya mike"ni zan tafi sai zuwa dare zan dawo."Addu'u suka masa,hajiya tace"Mazan fama bazaka ci wani abu ba"?Kai ya sosa yace"Sai na dawo da dare."atare sukace "Allah ya kaimu.
Aliyu yana fita ya shiga mota basu zame ko ina ba sai gidansu Masa'udah.
Suna isa ya kirata awaya yace yazo...............✍🏻
Kuyi manage wlh banajin jikina k'ok'arine nayi saboda mahimmancin cika Alkawali
*17/February/2020*
Rahma ummu Fareesa ce😘
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger🤙🏻
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
Gabaki dayan wannan Pagen Sadakarwa ga yan Gidan Ladingo Yar Janafty yaba kyauta tukuici naga sharhi da comments dinku na shekaran Jiya wlh tamun dadi ya sakani nishadi sosai shiyasa na baki kyautar page kuji dadinku😍🥰🤩🤩🤩 Nagode kwarai Allah yabar zumunci🤝🏻🤝🏻🤝🏻
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page 4⃣2⃣*
Masa'udah tana jin Aliyu ya iso cikin murna ta mike,ta kara gyara fuskarta, ta kara fesa turare ta shafa humra ta dauki mayafi maras nauyi ta yafa sai baza kamshi take , ta fito parlo.
Hajiya Falmata na zaune,ta fada jikinta tace, "Mamah ya zo." Falmata ta ce "to wa zai biya sanyin jikinki ai yana parlon baki Papi ya sauke shi har ya fita, dama lokacin zai fita ne tashi maza ki je babu dadi jira" Mik'ewa Masa'udah tayi a nutse ta fito ta kama hanyar parlon bakin.
A nutse take takunta cike da aji gwanin burgewa , har ta isa kofar parlon.
Kofar ta murda ta sanyo kanta cikin parlon sallama dauke a bakinta cikin sanyin murya.
Amsawa Aliyu yayi kansa dauke a k'asa.
Gun sa ta nufo ta kura masa idanu yayi mata kyau mutika ji take kamar ta lasheshi.
Kusansa ta isa ta zube kan gwiwarta , ta ce "my love ina yini ya rana?" Amsa gaisuwar Aliyu yay, yana dago da kansa.
Ya ce "sannu ya jikinki tashi ki zauna" ya fada yana bata hannunsa.
Cikin jin kunya Masa'udah ta saka hannunta cikin na Aliyu ya kamata ya mikar da ita tsaye, ya zaunar da ita kusansa still yana rike da hannunta ya ji hannunta akwai zafi.
Ya kalleta ya ce "Ya aka yi na ji hannunki zafi kenan kinada zazzabi, bayan kin ce an saka miki drip" ya fada yana janye mayafi jikinta ya ajiyesa gefe,ya dora hannunsa saman wuyanta ya ji da zafi rau.
Masa'udah kuwa tunda ta ji Aliyu ya taba mata wuyanta yana shafawa laushin tafin hannunsa da kamshinsa ya baibayeta sai ta ji bata bukatar komai sai jinta ajikinta.
Muryasa mai amon dadi ta tsinto yana cewa "Masa'udah kin ci abuncin da nace ki ci kuwa? bare kisha magani." ya karasa maganar yana dauke hannunsa saman wuyanta.
Cikin sanyin murya Masa'udah ta ce"my love bana iya cin komai"ta fada tana kallonsa.
Sitll shima ita yake kallo,ya had'e face ya ce"Ok kin kyauta tunda bakya jin magana, to karki sake ce mun bakida lfy ni zan tafi, Allah ya baki lfy." ya fada yana mik'ewa tsaye.
Masa'udah idanunta suka ciko da kwalla ta mike tsaye ta fada saman kirjinsa ta rungumesa kam-kam ta saki kuka harda shasheka,tana cewa"my love ka yi hakuri zan ci wlh ni bansan meke damuna ba, sam bana jin dadin rayuwata idan baka kirani ba, ga shi ni ka hanani na kira ka wlh shi ne yake hanani cin abunci amma ka yi hakuri zan koyama zuciyata hakuri da kai tunda bana gabanka" ta fada tana kara shigewa jikinsa tana kuka mai cike da abin tausyi.
Aliyu kansa ya dafe da hannu daya ya zagaye bayanta da hannu dayan yana buga bayanta.
Ya furta "Ya Allah to yi shiru waye ya ce ban damu da matata ba ? ba gani na zo ba"ya fada yana janyeta daga jikinsa yana rike da hannunta ya zauna ya rungumeta jikinsa yana goge mata hawayen fuskarta.
Yace"idan kina so mu shirya kibar yawan damuwa ki sa a ranki na damu dake kuma ki bar zama da yunwa ko baki san bakida cikakar lfy ba" ya karasa maganar yana gyara mata kwanci jikinsa.
Ai kuwa Masa'udah ta ji wani irin dadi marar mustuwa.
Kwayar idanunsa take kallo cike da zallar kaunarsa, ta kara lafewa jikinsa ta dora hannunta saman fuskarsa tana shafa sajansa a hankali takai bakinta saman goshinsa ta sakar masa kiss ahankali ta furta "Mijina ina tsananin kaunarka ina jin tsoron wani abu nan kusa."
Tkarasa maganar tana had'e face dinsu,tana fitar da numfashi da sauri sauri suna shakar numfashin junansu.
Aliyu ya janye fuskarta ya tallabo kanta yana shafa fuskarta yana hura mata sakar bakinsa yace"na fada miki bana son kina damuwa ki ajiye hankalin ki kalli yada kike fitar da numfashi Oya fadamun yanzu me kikeso ayi ko zaki tare kinga sai kina ganin mijinki kullum, Oya maza sa akawo abinci da magani yanzu na baki ki ci na tafi gida."ya fada yana sakin fuskarta yana jin yada kirjinta ya tokareshi ya zuba mata idanu.
Sauka Masa'udah tayi daga jikinsa ta nufi hanyar fita.
Aliyu yace"ina zaki ba mayafi ko bakiga yada kayan suka kamaki ba."ya fada yana karama surata kallo yana tab'e baki.
Cikin jin kunya ta dawo ta dauki mayafin ta yafa ta fara tafiya a nutse.
Bata jimawa ta dawo da plate a hannu da ledojin magani ta dora plate din da maganin kan table ta zauna kusansa ta cire mayafin.
Murmushi Aliyu yayi ya matso ya bude plate din, yace"ina spoon..? Marerece fuska Masa'udah tayi ta jingina da jikin Aliyu cikin sanyinta tace"my love ka bani da hannunta pls"ta fada tana shigewa jikinsa tana jin wani irin shaukinsa na ratsata.
Aliyu yace "Ok To tashi zaune "ya fada yana saka hannunsa a plate din jalof din ta ji hadin kaya ba karya nama yaso ya fi shinkafar yawa.
Ya tsakura ya dago ta ta zauna ya kai bakinta, ta yi bismillah ta amsa tana ci tana jikinsa a rungume.
Sosai ta ci ya bata maguguna ta sha dan yayi mamakin yadda ta ci abuncin sosai hannunsa ta rike tana lashe masa tas tana tsotsar ya tsotsinsa dole sai da ya ji wani iri basarwa yayi ya kura mata lumsassun idanunsa.
Ganin ba za ta dena ba ya janye hannunsa ya ce
" baki koshi ba ne..? Dariya Masa'udah ta yi.
Tace "na koshi dam" ta fada tana mik'ewa tsaye ta kama hannu Aliyu.
Ya kalleta, ya ce"Ya dai? ko rakiya zaki mun."ya fada yana tsareta da lumsassun idanunsa.
Da sauri ta sada kanta, tace"my love hannunka zan wanke ma pls karka ki don Allah" ta karasa maganar a shagwabe mik'ewa yayi tana rike da hannunsa suka shiga toilet.
Ta kunna fanfo tana wanke masa hannunsa da sabulu mai kamshi tana gamawa tama hannun kiss tana yabon hannunsa mai taushi jajir kamar jini ya fito.
Janyota Aliyu yayi suka fito yana rike da hannunta suna zauwa tsakiyar parlo ya saki hannunta ya ce"zan tafi sai kwana biyu ki rika cin abunci kina shan magani zan rika kiranki amma idan bakida lfy ki kirani tunda ba ko da yaushe nake da time din kira ba Ok."ya fada yana kallonta tayi narai-narai da idanu.
Ido ya zaro yace"meye kuma ko baki gaji da ganina ba ne..? Ai kuwa Masa'udah ta d'aga kanta da sassarfa ta karasa ta fada kirjinsa.
Aliyu kansa ya dafe ya rungumeta yace "Masa'udah menene" ya fada yana kai bakinsa saitin kunnenta yana shafar wuyanta, ko me yace mata oho ta sake shi tana zaro idanu ta ja baya da sauri tana maijin kunya ta isa gun kujerun ta dauki mayafin ta da ledar magani a guje ta fice tana cewa"wlh ni ba ruwana my love ka gaishemun dasu Anty da yarana na shiga ciki ni ba zan kara zuwa kusan ka ba ma har na je gidanka" ta karasa maganar tana fice daga parlon da gudunta.
Murmushi Aliyu ya saki yana cewa"ai nayi maganinki kema alamar rigima zaki yi "ya kwashe wayoyinsa ya fice daga parlon.
Yana fita ya nufi farfajiyar gidan inda security dinsa suke shawagi a tafkekiyar farfajiyar gidan wacce ta k'awatu da franni masu kyau suna ganinsa suka bude masa mota ya shiga Boos ya rufa ya shiga direta ya ja suka nufi katoton get don gidan,sauran motocin suna biye dasu.
Bangaran Masa'udah kuwa ko da ta shigo parlonsu Falmata tana zaune Masa'udah ba ta bi ta kanta dariya kawai take ta rufe fuska ta nufi bedroom dinta.
Falmata tana kiranta , ina! ba ta tsayaba ta shige.
Tana shiga ta fada saman makeken gadonta tana juyo da dariya tana cewa"ni dai my love wlh ba ruwana dama haka kake ina ganinka shiru shiru da kai wayyo my love ni kam bazan kara abin da zai hadamu ba da kai wayar ma na fasa."ta fada tana dariya tana juyi saman gado tana lumshe idanunta tana sunsuna hannunta tana jin kamshin Aliyu ya baibaye mata a jikinta sai cewa take "my love ni dai ba ruwana da kai ashe haka kake.🤣😆🤭ni ko nace Masa'udah don Allah ki dan fadamun abinda Aliyun ya fada miki wanda ya girgiza ki haka lokaci daya.😂
☀☀☀☀☀☀☀☀☀☀☀☀
Bangaran Teemah tunda ta kwanta bata tashi ba sai karfe uku ko sallah azuhur batayi ba.
Cike da mamaki take kallonta a dakinsu na bacci ita ko tasan a parlon k'asa tana kwance jikin Aliyu tayi bacci.
Tashi tayi ta sauko daga saman gadon ta shiga bathroom ta cika bath da ruwa gumi ta shige ciki ta jima sai da ta ji dadin jikinta sosai ta fita ta yi wanka ta dauro alwalla ta fito tayi sallah.
Tana gamawa ta shiga shirya kanta cikin riga da siket na material bleu colour dinkin ya yi mata kyau sosai mayafi bleu ta dauka takalmi bleu ta gyara fuskarta ta fesa turare ta dauki wayarta taga Aliyu ya kirata har sai uku baki ta zumburo gaba ta fice daga dakin ta sauko k'asa.
Dan wata irin yunwa take ji kan dining ta nufa ta bude ta ga babu abin da ya mata duk da anyi girki ne mai lfy domun Aliyu.
Kitchen ta nufa cikin sa'a ta isko Nasira.
Teemah ta ce "Nasira ykk ya aiki pls dan soyamun wainar fulawa ta ji man ja, ki dan kawomun gwanda Allah yasa akwai."ta karasa maganar tana dan yamutsa fuska.
Nasira tace "Eh akwai bari yanzu zan soya miki mima ki yanka mata gwanda ki kai mata" murmushi Teemah tayi tace" yauwa Nagode bari na je nayi sallahr la'asar wlh yau wani irin bacci nayi."ta fada tana fitowa daga kitchen din ta nufi sama tayi sallah.
Bangaran Aliyu kuwa suna fitowa direct government house suka nufa yayi ta kiran Teemah ya ji ko taci abunci shiru ba ta dauka ba tunaninsa ya raja'a akan tana part din Bintu ta bar wayar gidanta.
Suna zauwa ya isko baki har mutum hudu a gagauce suka yi magana saboda lokacin sallah ya gabato.
Suna gama magana ana kiran sallah, suka masa sallama suka tafi.
alwalla Aliyu ya yi ya shiga masallaci.
Bayan an idar da sallah Aliyu yana shigowa part din Bintun ya nufa.
Da sallama ya shigo parlon.
Bai ga kowa ba,sai motsin yan aiki.
Bedroom din Bintu ya nufa. Tun daga bakin kofa Aliyu yake jiyo kukan zahara.
Da sassarfa ya karasa shiga,yaga Bintu tana sallah, zahara ya dauka yana jijigata ya dorata a kafadarsa , shiru tayi tana sabke ajiyar zuciya.
Bintu saida ta gama sallah, a nutse tayi Addu'o'inta ta mike ta cire hijabi ta kalli Aliyu tace"my Man yau kuwa lafiyar Fatima bata fito ba ko batajin dadine."?Aliyu yace" Ba ta fito ba kenan yanzu na shigo gidan bari na dubota."ya fada yana bata zahara.
Bintu ta ce"nima yanzu da tafiya ce zan yi dubota amma je ka fito da ita Allah ya sa tana lfy."ta fada tana bubbude hanci.
Ta kureshi da idanu ta ce" Amma my man ina ka samo wannan turaran matan kuma ba na Zahara bane ban taba jinsa a jikinta ba."ta fada tana kicin kicin da fuska.
Aliyu ya shafi fuskarsa yana murmushi yace "My Bintuna meye na tsare gida haka kamar za'a ba my Man kashi , hancinki ne ya jiyo ni bansa wani turare ba my Bintotona, yanzu dai ba wannan kinci abunci dai ko? yarana suna gidan Aminullah sai zuwa yamma likis za ki gan su."ya karasa maganar yana daga mata gira , ya manna mata kiss saman lips dinta.
Bintu da idanu take binsa ga kamshin turaran nan mai dadin gaske na mata ya cika wajan tana ji ya ce hanci ta ne.
Zahra ta kwantar saman gado. Ta nufoshi dan yau bata iya control din kanta daga masifar kishinsa.
Nufo sa ta yi tana cewa"Allah sai ka fadamun diyar uban wacece ta rungumeka ni ba yarinya bace wlh da zaka juyani wannan ba turaran zahara ba ne kuma ma ai naji isowarka gidan,kafin ayi kiran sallah, zahara ba ta ganka ba."Aliyu ganin Bintun masifa yau take ji kishinsa ya motsa mata yau idan ya ce ya biye mata rigima za su yi ga shi ba zai iya cemata watanta ya rungume ba kawai sai ya fice da gudu yana dariya.
Bintu tako biyo shi , har wajan parlo, amma kafin ta iso gareshi ya bude kofar mai had'e da parlon Teemah ya shige ya maida ya murza key yana dariya.
Bintu turus ta tsaya tana masifa "Wlh za mu hadu kama maida ni mahaukaciya, kenan da gaske ne ko dai Aliyu yana son amaryasa daga can gunta yake kai da wuya ya ce baya sonta ko kallon arziki ma bata ishesa ba, to diyar uban waye za ta sake shiga gonarmu dan wlh daga jin kamshin kadai kasan ba karamar yar jaraba ba ce zata iya jan ra'ayinsa da kamshi amma ai gidan ta zo ba za ta nunawa Bintu kamshi ba ko da kuwa nera million nawa ne ake siyar da turare na yi zarra daga nan na san halinsa ba lallai ba ne tayi nasara , jarababbu macizai wa inda basa gina ramin kansu sai angina su shiga wlh yau Sai ya fadamun wacece wannan."ta fada tana nufar bedroom dinta ta ba zahra nono.
Aliyu dariya sosai Bintu ta ba shi dan ya tuna lokacin da suna soyayya a London yadda take dambe da matan turawa da bala'i a kansa har ta tab'a fasawa wata baturiya kai wanda daket wutar ta mutu.
Tsagaita dariya yay ya nufi parlon.
Bangaran Teemah bayan ta je tayi sallah, ta sauko k'asa ta isko gwanda a yanke cikin katon tire jikinta har rawa yake ta iso ta zauna tana ci kafin a kawo mata wainar fulawar.
Tana cikin shan gwandar ta tuna yau fa ba ta je gun Bintu ba.
wayarta ta dauka ta kira Bintun wayar na ringing bata d'adaga ba,
Teemah ta Mike tsaya da niyar taje ta leko Bintu ta ga lfy kuwa bata daukan kiranta,sai ga Nasira da plate din wainar fulawa ai kuwa tayi zamanta ta fara ci tana sama Nasira albarka, ta ci sosai fiye da rabi shi ne daidai lokacin Aliyun ya nufo parlonta.
Ta bararaje tana cin wainar fulawa sai daga yaji take.
Sallama yay,Teema ta amsa ta dago kai tana kallonsa, murmushi ya sakar mata ya waremata hannanyensa yace"Oya yar Babyna i miss u ina kika shiga yau nayi ta kiran ki baki daga ba my Bintu tana neman ki."mik'ewa nayi na nufi gunsa da gudu na fada saman faffadan kirjinsa na rungumeshi gam"Wayyo my chocolatyna i miss u too."na fada ina kara shigewa jikinsa ashagwabe na ce"
my sweet gwamna nah ina ka shiga ka barni ina kewarki i love u my chocolatyna wlh yau na yi bacci sosai ban jima ba da tashi."Aliyu kara shigar da Teemah yayi cikin jikinsa yana juyi da ita ya tura kansa k'asan wuyanta yana sunsunata yana shakar ni'imataccen kamshinta yana sakar mata kiss.
Yace" i love u too my Noor yar Babyna my duniyata me kike ci ne? haka babu bismillah Oya muje na baki a baki ki ci."ya fada yana daukarta cak ya rungumeta yana lasar bakinta da ya ɓaci da man ja.
Dariya na yi na sakalo hannunwana wuyansa ina kara makaleshi da turo masa bakina ya cafke yana tsotsar labbana ina dariya ni ma na riko kansa na tura bakina cikin nasa na kamo harshensa na fara tsotsa ina jin wani zaki da gardi.
Zama Aliyu yayi da Teemah jikinsa ya rungumeta sosai suna tsotsar bakin junansu.
Sun jima kafin Aliyu ya zare bakinsa a nata suna maida numfashi.
Ya janyo plate, kaina na tura cikin kirjinsa a shagwabe na ce"My chocolatyna na koshi wlh na ci da yawa ko za ka ci ne? na baka"na fada ina shakar kamshinsa,amma sai me wani irin kamshine ya daki hancina nan take naji kaina ya Sara dama dauriya nake d'ago da kaina nayi ina kallonsa zuciyata na mugun tashi nace"My chocolatyna wannan kamshin fa ina ka samoshi wannan ai turaran matane"na kara maganar ina k'ok'arin sauka daga jikinsa saboda aman da yake son kufcemun,na ji ya rikoni ya maidani jikinsa