Showing 1 words to 3000 words out of 129912 words
Chapter 1 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt
*👰🏻MATAR👰🏻*
*💖💖GWAMNA💖💖*
*بسم الله الرحمن الرحيم* ___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________
*Written By*
Real Ladingo😉
Yar mutan Niger
*A'UZUBILLAHI MINAL SHAIDANIR RAJEEM BISMILLAHI RAHAMANIR RAHEEM*
*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf👌🏻😘*
*Bismillahir Rahamanir Raheem*
*Page* 1⃣
Akafta.... *NIGER* Yau ta kama laraba kasuwar garin wato *garin sarki* kauyen miryah karamar hukumar damagaram garin cike yake makil da jama'a saboda kasuwar garin yau takeci kuma dama tafi cika da yamma har dare zaka ganta da jama'a maza da mata yan kauyinka nakusa da na nesa abun sai ya baka mamaki ko da yaushe suke watsewa su koma garuruwansu oho da misalin karfe biyar na yamma na hango wata kyakyawar yarinyace yar kimanin 14 year se dai ba fara bace chocolate colour ce doguwa ce saide batada jiki siririya ce kyakywace ajin farko duk da bata ida zama cikakiyar budurwa ba amma masha Allah kominta yayi ba karya saide nan da shekaru biyu za'ayi zankadediyar mace agurin duk da tana yar kauye tafe take sam hankalinta ba akwanceba dan satar hanya tai ta sadado jiki ta baro islamiyya saboda ta shiga cin kasuwa gudu gudu sauri sauri take tana rumgume da wani katon Allo Wanda yakusa rabin tsayinta😂don tasan indai malam shehu yasa aka kamota ba'ayi fatiha ba to sai ya mata bulala goma saida tayi nisa ta fara tayifa cikin nutsuwa tafe take tana waka cikin zazzakar muryata" saini Fatima zahara matar gwamna idan Allah ya yarda wani katon kara ta gani ta sunkuya ta dauka " bari na dauka saboda tsaro
Tafe take cikin dan kauyasu da bai fiye girmaba tana wakarta da katon karanta ahannu da da dirkeken Allonta Wanda babu yada ba'ayi tarabu dashiba ta dauki Qura'an don yanzu kaf kauyen *garin sarki* sai kace watisme matar gwamna mai Alllo shine cikeken sunanta agarin😆 wani dan lungu tabi dan tayi Saurin isa gida ai ko taci karo da Nawalu mai goro andau wanka cin kasuwa da tiransa na goro akai idan kaga damara da yayi abun dariya yana washe baki" ah watutuna daga ina? kuma zolayace yasan daga islamiyya take tunda ga dirkeken Allonta arumgume kai na dauke na had'e face dan ko kallonsa nayi tashin zuciya nakeyi dan Nawalu kazamine na bugawa ajarida na ci gaba da tafiya amma dan tsokana sai cewa yayi " watutuna Allah ya kaimu ranar auremun Aradun Allah duk makadan kauyukanmu sai an agaiyacesu ya fada yana washe bakinsa
Da yayi jawur da goro fuska ta kwakwab'e ta zubar da yawu " wlh Nawalu Allah ya isa ban yafema ba banza kazami Abbana ba ya rabani da kaiba yanzu zan turo iyayena su kawo kashe gidanku katon banza mai warin jab'a matar gwamna kakema iskanci wlh sai na fadawa Aunty Malika idan ta kirawo Abbana kasan ai mijinta Attajirine Alqura'an sai ya hadaka da hukuma akai ka binni can damagaram adaure ka mai tsamin baki kawai ya daga baki zaiyi magana kafin yayi magana ta gyara Allonta ta kwada masa karan hannuta saida tiran goron ya juye akasa ta zunduma da gudu " kuma gobe kamun magana haka zanma tunda bakada zuciya ta karya kwana da gudu baki ya ciza "na kamaki hegiya mai dauda in ba niba ma wa zai soki ya tsugunna yana kwashe goronsa sai tsine mata yakeyi acikin ransa
Tunda ta fara gudu bata tsayaba sai asoron gidansu ya'u na mata magana ko kallo bai ishetaba ta tsaya tana maida numfashi tayi d'am ta leka iyayye bata tsakar gida buta ta dauka ta debi ruwa a randa ta shiga bandaki ta watsa ruwa ko sabulu bata goga ba agagauce ta fito tashiga d'aki ta cacaba kwalliya Jan baki har kusan hab'a jagira ba'a maganar dabak dabak tayi ta saka dinkin,ta na sallah ta fito tana leke iyayye bata gidan aranta tace yanzu haka tana gidan haja nanu to na fasa zuwa ma ta bani nacin kasuwa salon iyayye ta hanani wuff ta fita daga gidan akofar gidansu taga ya'u da tiredarsa dan shi yafi jin dadin zama ana saboda yan cin kasuwa wasu hanyar suce nan yana samun kasuwa sosai tunba masu shan sigari ba kallonsa tayi
Taga hankalinsa gurin ba wani canji ta warci halewa ta zunduma da gudu tace"kayi lisafi gwamna na zuwa za'a biyaka ta tafiyarta sai yanga takeyi baki ya ciza" zakici gidanku Mara's kunya wani gwamna zai dauki mahaukaciya saide mai faskare, itako gidansu kursu ta ma tsinke itama ta gama shiri ta shigo da sallama kursu tace" watsime Aradu da natafi ke ranar kasuwa wayake zuwa makarantar Allo? hararata tayi " mutafi dai ai kinsan ba'a barina naci kasuwa idan ban jeba islamiyya yanzu ma gudowa nayi kuma wlh idan baki fasa fadin sunanan ba Aradu sai namiki dukan mutuwa kema kin fara zama yar bakin cikin matar gwamna idan kin fada me zai rageki irin kune ko kunje gidan wlh zan hana kar abarku kushiga saboda baku cancanci zuwaba saboda kwarmato zai kaiku " to yi hakuri kawata muje Nice fa babbar kawar Amarya
Wai gwamna na ina kikeso? baki ta turo"ko na inama ko na Saudia ko Niger kasata ko wani gari a niger ko Nigeria a ko wane gari a Nigeria ko Mali ke ko na London ne na samu nayi manage dariya kursiya tayi"mudai muna kauyan damagaram ba ruwanmu da daukar dala ba ganmo tsaki tayi "aikin banza kijira ki gani zan daukeki yar wanke wanke suna tafiya sai turo baki take suna shiga kasuwa jama'a aka fara sai matar gwamna mai Allo bakinta yaki rufuwa kursiya tace" wlh mahaukaciya suka daukeki cikin masifa tace" eh sunfi ki tunda suna fadin son raina kefa yar " Allah ya baki hakuri muje daide zasu wuce
gunri masu kifi lado mai kifi da tiran kifinsa a kai ya taresu yana washe baki" watsime zo ga kifinki da kudi dalarki arba'in tacin kasuwa fuska ta yamutsa ta matsa da baya ta rike k'ugunta tana kallon ican rumfar da take kusanta bakinta sharaf janbakin ya fara b'ata mata fuska budar bakinta sai cemasa tayi " lado wlh kajira ka gani tun kafin mukoma ga mahaliccinmu zaimun sakaiya akan ka wlh kai ko bakada zuciya maye kawai ina koraka kana bina yo ko maza sun kare mezan dakai ajinka kaja ra'ayina da wani shegen kifi da kudi ganin abinda take shirin aikatawa kursiya ta jata suka bar gurin shiko lado ko ajikinsa, dan ya saba da tijara watsime sai baki yake washewa yana binta da mayan kallo
" watsimena in Allah ya yada ke din matace zaki rika farfesun kifi kina morewa, agidana yan gurin abokan sana'arsa dariya suke masa dan sunsa borin kunya yakeyi tafiya yayi ya bar musu gurin itako suna can ana yawon kasuwa tacika tayi fam saboda lado ya bata mata rai gun kawarsu suka tafi sailuba mai kosai cikin sa'a ta sayar suka shiga yawo 🤣kai watsime akwai farin jini duk inda tayi ita samarin kauye kema caa itako ko ajikinta su kursu sunyi sunyi ta musu wayo taci kudinsu kamar yada sukewa samarinsu takiya sai gurin Abbanta taje yabasu kudin cin kasuwa sai da ana Kiran magrib suka bar kasuwa akofar gidansu watsime
sukayi sallama ta fada gidan da sallama lokacin iyayye na sallah buta ta dauka ta shiga bandaki ta fito tayi alwalla ta shiga dan dakinta tayi sallah koda ta gama tajima, tana Addu'a dan yarinyar akwai addini sosai duk da karalcin shekarunta tana gamawa. ta fito iyayye ta kalleta" wlh Zahara zakici gidanku ai na biya ta makarantarku akace kin gudo ba'ayi fatiha ba. jikinta ta fada tana kukan
sangarta" haba iyayye ta dududu mintina nawane sukayi saura kiyi hakuri uwata kinji Dole iyayye ta dara " to naji amma kibari kina amsar fatiha a makaranta " to naji iyayye Abbana bai shigoba ne? " yana masallaci Albishirinki" goro? " Malika suna tafe ranar Juma'a jibi Kenan kuma sun nemi Alfarama zasu tafi dake Gombe mijinta yace zai rikeki Amana kinsan ba zama yake agariba yana wajan aiki sai karshen wata yake zuwa to kinsan Malika da sakwarta gashi ba wani yaraba gareta masu wayo ba gashi anma kanwarsa aure satin da ya wuce dama itace agurinta shine ta tada masa hankali ya roki Abbanki Alfarama abasu ke zasu saki secondary School can tunfa haihuwar yan biyu da tazo taso ta tafi dake to kiriniyarki ce nake dubawa shiyasa na hanata to yanzu Abbanki yasa baki Dole na yarda ihuu watsime ta saki cikin farin cikin ta rumgume mahaifiyarta " iyayye na gode wlh dama bayau nakeson komawaba tun zuwan da mukayi kaita duk da ina karama yanzu shakara hudu lokacin ina da shekara goma amma naji dadin garin sosai iyayye yanzu acan zanyi makarantar" in Allah
Ya yarda ki tsaya kiyi karatu ki cika gurin mahaifinki don Allah kicire haukan da ke kanki yanzu garinan sun daukeki mahaukaciya wai matar gwamna wani gwamna ne zai auri yar kauye kuma talaka futik fatima zahara ina miki fatan Alkhairi Allah ya albarkaci rayuwarki kamar yada ya Albarkaci rayuwar Malika kizamo mai nutsuwa kibar shirme kinji? " to iyayye naji kawai dama dan ayi dariyane nakeyi amma nafasa kinji" yauwa Allah miki Albarka" Ameen Abbane ya shigo da sallama zahara ta Mike da gudu ta taresa ta ruko hannusa" Ah mama ina tsarabata ta kasuwa? dariya tayi" Abbana mun cinye fah zama sukayi iyayye tayi masa, sannu da zuwa " Aisha ya gida " Alhmdllh Abban Malika ya kasuwa " Alhmdllh " to bari muyi sallah sallahr
Isha sukayi ita da zahara iyayye ta zubo musu tuwan dawar masara da miyar kuka taji daudawa da man shanu Abba ya basu ledar balangun da ya kawo sukaci tuwansu cikin jin dadi da annashuwa dan duk shirmen watsime bata taba rena gidansu ba da abincinsu kuma duk haukan da maza keyi bisa kanta da kudi da kayan ciye ciye da suke bata har yau bata taba amsaba dan ita yarinyace da abun wani bai taba burgetaba ta dogara da gidansu da iyayanta bayan sun gama ta kwashe kayan ta kaisu madafa ta wanke hannuta ta dawo kusan Abbanta ta zauna tana washe baki" mama kinji zaki Gombe zakiyi rayuwa da yar uwarki zasu saki makaranta wlh da sam ban aminceba to kinsan yada muke da mahaifin yaron yama mahaifinsa magana yasa baki shi ba mazauni bane gashi hafsat da take gunsu anyi mata aure dama itace karamar da ta rage acan gun iyayansa to sunce zasu rikeki Amana to dan Allah ki nutsu karki rika shirmen da kikeyi
Wai ke matar gwamna anaso a maidamun yarinya mahaukaciya agari wlh abun na damuna wai sai kace watsime matar gwamna mai Allo yo ina dan dalili wlh abun na damu har cikin dare nake tashi ina sallah Allah ya rabaki da wannan shirmen dan shirmene wani gwamna zai kwashi yar kauye koda kin girmama bare dudu yanzu kikeda shekara sha hudu dan Allah ki cire wannan shirmen kinga babban birni zaki wlh sa koroki ba'a musu shiririta ki kasance tamkar yar uwarki ina miki fatan Alkhairi Allah ya baki Abunda kikeso na kirki ba shirmeba Wanda hankali ma bazai daukaba" Abbana nagode insha Allahu nabar shirme karatu zan tsaya nayi" Allah miki Albarka dariya Aisha tayi
" to Allah yasa nima tace ta bari " Allah nabari ni duk Wanda ma yace matar gwamna sai munyi fada dashi sosai iyayan nata sunji dadi suna kara dorata a akan hanya dan sunsan abin da take ba daide bane sun jima suna hira sai da dare yayi sosai ta tashi ta shiga d'akinta tayi shirin kwanciya da kudirin babu wani zancen gwamna aranta tayi kwanciyata har bacci ya kwasheta
*Nigeria Gombe* Federal lom-cost misalin karfe 12:pm Na dare wani hadadan gida tamkamemansa kana ganinsa kasan mai shi nera ta zauna kaina na kutsa cikin wani hadadan parlo Wanda ya gaji da haduwa yaji kayan Alatu wasu lumtsuma lumtsuman kujeru ne a parlon har kala biyu wata makekiyar Tv na gani wacce takusa cin rabin bangon da yake manne da wani d'aki parlon shiru ba kowa amma Tv a kunne wannan d'akin mai manne da tv na shi saida nakusa sumewa saboda wani mayan kamshin dadi da yadaki hancina ga kamshin Ac wani Royal bed ne yaci kusan rabin dakin ga wasu kujeru manya manya capet malala ko ina ashimfide kallona nakai don naga waye akwance
Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci wannan bawan nashi gashide magidancine zai kai kimanin 48 year amma jin dadi da nera sun samu zama jikinsa zaka zaci bai fi 40 year ba iya karshen haduwar namiji wannan mutum yakai idanusa, lumshe yake yayi daidai dagashi sai gajeren wando fari tas dogo mai cikar zati gashin kansa luf luf sai sheki yake yanada dogon hanci da manya idanu kirjinsa cike yake da gashi yanada kirar karfafa saide fa miskine na karshe fuskarsa ta kawatu da saja gemunsa mai mutikar kyawu ya karamasa kyawun fuska wata kyakyawar mata fara tas yar duma duma mai matsagaicin tsayi ta shigo da sallama yar kimanin 31 year saman bed d'in ta hayo ta dora kanta kirjinshi tana shafa fuskarsa" my man kayi bacci ne? idanusa ya bude saboda bacci yake amma tana tabashi ya tashi yana mamakin mafarkin da ya tisasa gaba na hasken tauraruwa mai tsananin haske ta fito tana cewa ranar da zan baiyana kasarka ranar zakaci zabe duk da bakaso amma Dole sai kaci saboda talakawa na sonka kuma nima ina sonka kaidin rayuwatane karka dubi kaskantata ba ruwan Allah idan yaso ya hada Abu to hikimarsa ce kuma shi yanada dalilinsa nayin hakan don haka ka taimaki na k'asa dakai kaji tausayin na kasa dakai ka kasance mai yawan sadaka yana jin dadin zazzakar muryata hasken tauraruwar sai ya rika mamaki tauraruwa bama mutumba amma Takeda wannan dadin murya haka tunanin ta katse masa " my man lumsassun idanuwansa
ya zuba mata ya daga mata gira murmushi tai masa janyota ya rungumeta suna kallon juna har ta sa aranta tace "yau fah ko zan kwana ina magana ba laleba ya amsamun cikin sa'a taji amon zazzakar muryasa yana mata magana tamkar bayaso yana cewa" sahibata tauraruwar zuciyata my bintuna mijinki na bacci kika tasheshi ina yarana da baby Rauda? shagwabewa tayi tana shafa fuskarsa" tayi bacci ita kamar yarinya mai shan nono shakara biyar amma idan ba ajikina ba take bazatayi bacci ba shine nazo na ganka dan nasan yanzu haka tunani ya dameka tunda naga ka killace kan kai daya my man jibi muna sa ran nasara? kiss ya mata saman lips d'inta ya tsareta da lumsassun idanusa cike da tsananin kaunarta yanaji aransa bazai iya tab'a son wata maceba kai ta langwab'e tana lumashe idanuta dan yada yake mata wani shegen kallo ya sakar mata kasala " my man gira ya daga mata ya saki dan guntun murmushi bai sake maganaba tun tambayar da yayi mata ya fara shafarta yana sakar mata kiss a cikin kunneta ya fara rikirkitata da salonsa mai tafiya da zuciyarta Wanda ta yarda mijinta ita dayace agabansa ta sani ba yau ba my man dinta baya gani' ko wacce mace sai ita ita dayace acikin zuciyarsa yan zunma ta kara tabbatarwa yada yake kallon lips d'inta ta gane kissing d'inta yake son yi bakinsu ta had'e dan ta yada da mijin nata mai tsada ne mata basa gabansa duk da mata na kawo masa hari basa gabansa sai ita daya shiyasa miskilancinsa da rashin son maganar sa baya damunta don ajininsa yake babu abinda zai canza shi tunda ta kasa hakan duk kuwa zazzafar kaunar da sukewa junansu sun jima sosai suna farantawa junansu rai cike da tsantsar
Kaunar junansu basu yi komaiba bakinsu romance sai karfe biyu suka hakura da tande tande da lashe lashen juna ya lallabata har tayi bacci ya janyeta jikinsa ya rankwafa ya mata kiss akumatunta cike da tsantsar kaunarta mik'ewa yayi ya shiga bathroom yayi wanka ya dauro Alwalla ya fito dauré da towel ya dauki jallabiyar da take saman dadduma yasaka tana wani fitinanan kamshi zuciyarsa na mamakin wannan mafarki sallah ya tayar kamar kullum, ta neman zabin Allah kan wannan shugabanci da yake tunkaroshi dan hasken tauraruwar na kara jadada masa tabbas sai yaci zabe to abin da yake damunsa da take cemasa tana dirowa kasar sa zaici zabe shine ke damunsa shiyasa ya dage da Sallah d Addu'a
*************
bayan kwana biyu tun da iyayanta sukayi mata. fada ta shiga hankalinta ta cire maganar gwamna aranta ko kace mata ta gwamna to zatace bataso idan kaki saide kaji ta zambace ta rafka maka wani Abu ta gudu to ganin haka yasa aka fasa fada mata agabanta cikin kwana biyu kacal don sunsa ita ta jiyataka babu ruwanta ta ajiye katon Allonta da Qura'an take zuwa islamiyya abun yama iyayanta dadi sosai da misalin karfe biyar da rabi na yamma tafe suke ita da kursu sun fito daga gidansu kursun zata rakata gidansu tace suke suna hirasu cikin wasa da dariya sunci uwar kwalliya fuska yababa da hoda da Jan baki da katon karanta ahannu saboda tsaro duk uban da yace mata matar gwamna taci ubansa dan yanzu tafi son karatu akan wani gwamna da
Ba samu za tayiba🤣niko nace haba Teemah ai cama ma da rikici sai munje Gombe sun biyo wata yar kwana dede kofar gidansu Nawalu mai goro yana zaune da tiransa ya washe baki " watutuna barka da yamma dariya kursu " ah Nawalu ya garin? " wlh kursiya lahiya nake keda gimbiyata Jan kursu tayi da karfi suka bar gurin tana masifa" wlh bakida hankalin da kike biyashi dariya tayi suka tafi yabisu da kallo " hegiya watutuna wlh idan ta kara warwarewa akwai kayan aiki ya fada yana lasar baki suko suna karya kwanar gidansu watsime su kaga daleliyar mota ihu ta kurma ta saki hannu kursu ta fada gidan da gudu kursu ko tsaye tayi tana kallon motar mai shegen kyau yara suna kewaye da ita sai washe baki sokeyi suna cewa" Alqura'an minjin maleku yazo