Showing 105001 words to 108000 words out of 129912 words

Chapter 36 - MATAR GWAMNA COMPLETE Document from Abdallah.txt

24 Nov 2024

5827

zan yi magana amai ya kufcemun na fara kelaya amai a jikinsa ina so ya sakeni ya ki sakina sai ma rungumeni ya yi jikinsa.
Tun Teemah na iya yunkurin aman har karfinta ya kare Aliyu gabaki daya hanaklinsa yayi kololuwar tashi ya rasa ina zai sa kansa.
Teemah ta fashe masa da kuka tana yunkurin wani aman ta kasa ta shiga dukansa"ka sakeni wlh bana son wannan turaran ka matsa kusana idan ba so kakee na mutu ba."a rikice Aliyu ya sake ta yana dafe kansa ya matsa gefe yana kallon yadda Teemah take birgima saman carpet tana yunkurin amai ta kasa sai kuka take.
Aliyu yace"wlh my Noor ba zan iya kallonki cikin wannan halin ba pls tsaya na temaka miki don Allah bari mun zancan mutuwa wai meye a jikina baki so"Ya fada yana nufo ta hankalinsa duk a tashe yadda take birgima k'asa...............




โœ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐ŸปYar Janafty๐Ÿ’‹




*19/February/2020*




Rahma ummu Fareesa...โœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป




*๐Ÿ‘ฐ๐ŸปMATAR๐Ÿ‘ฐ๐Ÿป*
*๐Ÿ’–๐Ÿ’–GWAMNA๐Ÿ’–๐Ÿ’–*








*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
____________________________________




*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________




*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger๐Ÿค™๐Ÿป




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf๐Ÿ‘Œ๐Ÿป๐Ÿ˜˜*








*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page 4โƒฃ3โƒฃ*




"""Aliyu yana isa gun Teemah ya sanya hannayensa ya ciccibeta, ya rungumeta ya nufi saman bene da ita.
Teemah wani aman take son yi amma babu kuzarin sake yunkurin wani aman, ga kamshin jikin Aliyu yana kara kusanto ta.
Fashe masa tayi da kuka tana cewa" dan Allah ka ajiye ni wlh bana son kamshin turaran jikin ka pls ka ajiye ni." ta karasa maganar , tana dukansa.
Aliyu bai saurari Teemah ba dan hankalinsa atashe yake, sai da ya shiga bedroom din baccin su.
Kai tsaye, bathroom ya shiga da ita, yana rungume da ita ajikinsa ya hada mata ruwa mai dumi ya cire mata kayan jikinta da ya baci da amai ya sa kata cikin bath, har yanzu kuka take.


Yace"my Noor pls kiyi hakuri yanzu zan cire kayan jikina" ya fada yana matsawa nesa da ita kasancewar toilet din katon gaske.
Sai da ya tube kayan jikinsa baki daya ya saka cikin inajin wanki ya kunna dan baya son yar babynsa ta kara jin kamshin da bata so.
Bayan ya kunna injimin wankin ya nufi gun shower ya kunna ya dauki soso da sabulu ya shiga wanka sai da ya garje jikinsa tas ya daura towel ya nufo gun Teemah.


Wacce take kwance cikin bath ta lumshe idanuta gumin ruwan na mata dadi, towel din jikinsa, Aliyu ya cire ya shiga cikin bath din ya rungumeta, ya ce "Yar Babyna sannu bude idanunki ki fada mun yanzu kinajin kamshin da baki so."ya karasa maganar yana mata wanka cikin wani salon so mai kayatarwa.
a hankali Nabude idanuna na kallesa ina zumburo baki jikina yayi lakwas babu karfi,na tura kaina kirjinsa ina sunsunawa, banji kamshin ba, na shafi kirjinsa mai yalwar gashi, ashagwabe nace"my chocolatyna babu kamshin wai ina ka samo shine? ni bana son sa karka sake sawa , my chocolatyna ka fadamun mana ina ka samo shi"? Aliyu kara rungumeta yayi jikinsa yana murjeta da sabulu cikin wani irin salon sa mai zautata yana kissing din wuyanta, yana bin sassan jikin Teemah da wani salo na musaman aransa yana cewa "Babyna ta ya zan yarda na fadi abin da zai tayar miki da hanakli kinyi amai ma a ranshin sanin ta in da na kwaso kamshinsa bare kin sani.
Haka yayi ta mata wayo cikin salonsa na daban dan ya batar da maganar turaren dan ko da wasa ba zai fadi mata ba ta birki ce masa da rigima, ya kasa shawo kanta ba.


Teemah mikis tayi tai lamo jikinsa, dan Aliyu ya gama birkita mata lissafi da salon wanka da yake mata, ta lumshe idanu ta sai sabke ajiyar zuciya take ta manne jikinsa,tana kiran sa ashagwabe.
"My chocolatyna" Aliyu ya amsa,da "Na'am yar Babyna sannu" ya fada yana dauraye mata jikinta,tas ya wanke ta ya dauki abarsa suka fito.


Agagauce ya goge mata jikinta ya shafa mata mai,ya zabo mata abaya red colour mai shegen kyau tayi mata mutikar kyau ya yane mata kanta da mayafin abayar.
Duk tana manne cikin jikinsa ya gama shiryata tsaf asalin kyanta ya fito da yarintar ta.
Bakin gado ya nufa da ita ya zunar da ita,zai matsa ta rikeshi ta kafe shi da mayan idanunta, tana kwakwab'e fuska tace"My Haidar bacci na keji" ta karasa maganar tana matsar kwalla, ta kwantar da kanta saman hannunsa.


Aliyu ya furta "Ya Salam My Noor tawan bari na saka kaya hospital zamu aduba mun lafiyar ki wannan aman da kika yi sai asaka miki drip, kalli jikinki kawas babu karfi yi hakuri bari na saka kaya kinji my yar Babyna" ya fada yana janyeta cikin siyasa ya kwantar da ita idanunta alumshe.
Har ya je ya saka kayan idanun arufe suke.
Wani rantsatsan yadi ne nasu na manya ya saka kalarsa baki ne yayi masa masifar kyau ya saka hula tasu ta manya, Aliyu yayi kyau mutika ya nufo bakin gadon.


Ya zauna ya janyo Teemah jikinsa yana shafa fuskarta, yace"Babayna na saka turare baza kiyi amai ba" ya fada ya dora bakinsa saman nata yana tsotsar lips d'inta,fitar numfashin ta yaji tana fitarwa daki daki, bakinsa ya zare anata yana cewa "Y'a Allah Babyn chocolate yau wane irin bacci ne ya sako min ke gaba gashi jikin ki zafi ma, bari na kirawo Dr Zubaida" ya fada yana kwantar da Teemah, sai yanzu ya tuna wayoyin sa suna k'asa.


Saukowa yay, ya dauki wayar yana, duba wayoyin yaga kiran jama'a babu adadi cikin wayarsa.
Zama Aliyu yayi ya lalubi number Dr Zubaida, ya kirata bugo daya ta gada tare da sallama.
Aliyu ya amsa ya ce "Dr ki zo da sauri karamar matata bata lfy amai ya sata gaba ga zazzabi yanzu ya zubo mata da hospital zanzo da kaina to ta sami bacci ne kizo ki dubamin ita yanzu pls."Dr Zubaida cike da girmamawa, tace "Ok ranka ya dade yanzu kuwa insha Allah" Aliyu bai sake magana ba ya tsinke kiran,ya mike ya nufi saman bene.


Yana zuwa ya ciccibeta yana rungume da ita ya sauko k'asa, tana sharara baccin ta.
Yana saukowa ya nufi Saman 3 seater ya kwanta da ita jikinsa, ya dora ta saman kirjinsa ya rungume abarsa yana shafa kanta zuba bayanta, ransa duk babu dadi jin zazzabi ajikinta sai tsaki yake Ja, dan yasan duk kamshin turaran Masa'uda ne ya saka ta wannan halin.


Bayan kamar 30 minute yaji ana danna ball din kofar parlon.
Aliyu kwantar da Teemah yayi zai sauka yaji, Teemah ta kara shigewa jikinsa tana turo baki.
Murmushi Aliyu ya saki ya duka ya sakar mata kiss saman lips dinta, yana shafa fuskarta, yace "My Noor tawan bari agama duba min ke sai ki hau saman kirjin mijinki kiyi kwanciyar ki." Ya fada yana banbare ta daga jikinsa,ya zauna nesa da ita ya zuba mata idanu sonta da tausayin ta na azalzalar zuciyar sa.


Nasira ce taje ta bude ma Zubaida kofar ta shigo da sallama, Nasira ta amsa ta mata jagora, har can cikin parlon.
Suna isowa wajan su Nasira ta gaishe da Aliyu ta juya, Zubaida ta gaishe dashi ya amsa cikin lumana.
Aliyu yace "Dr a atashe ta..? Zubaida tace "Yallabai a tashe saboda zan dauki jinin ta da fitsarin ta da kashin ta, na duba su" Aliyu yace"Ok ya fada yana rankwafawa ya dora bakinsa saman kunnan Teemah yana shafa kyakyawa fuskarta, yace" My zahara tashi aduba lafiyar ki "ya fada yana kissing din kunnanta.
Dole Dr Zubaida ta Kau da kanta.
Cikin dubara Aliyu ya tayar da Teemah daga bacci sai lumshe idanunta take, dan wani irin dadin baccin take ji.
Shagwab'e Teemah ta afka jikin Aliyu tana kukan sangarta, tana cewa,"My chocolatyna me yasa ka tasheni ni bazan yarda ba Allah kuwa "ta fada tana kokowar cizon sa.
Ya na Dariya yace" Baby tsaya bamu kadai bane kalli doctor tazo duba mun lafiyar ki."Ai kuwa cike da kunya na d'ago da kaina na kalli gefen da Dr take, take na sake shi na matsa gefe ina harara sa na cinno baki gaba ahankali nayi magana yadda Dr baza taji ba, nace"To ka tashi ka tafiyar ka ni ba ruwana dakai mun ba ta ma da kai" dariya Aliyu yay ya kalli Dr Zubaida, yace "Dr bismillah yi aikin ki a saka mata drip kuwa..? Dr tace"bari muga yanayin jikin nata" ta fada ta matso ta fara duba Teemah.


Sosai ta dubata tana mata tambayoyi tana bata amsa, ta bata yan robobi guda biyu tayo kashi da fitsari ta duki jininta, ta hada Allurai tasa gwamna, ya bata fresh milk tasha tayi mata Allurai, tace ma Aliyu ba sai an mata karin ruwa ba amma ya kiyaye saka turare tunda bata so taga alamar shigar ciki ne da matarsa.
Ai kuwa da daman kudi tabar cikin gidan, Aliyu yace sauran kyauta sai ta tabbatar da gaske abinda gwaji ya nuna na ciki.


Bayan tafiyar Dr Teemah tana kwance saman kinjin Aliyu, ta kalleshi ashagwab'e tace"my chocolatyna wai ina ne ka samo turaren mata mai wari... bai bari ba ta karasa maganar ya had'e bakinsu yana bata wani sansan yan hote kiss ya birkito ta ta koma k'asa, ya haye saman ta amma bai sakar mata nauyi ba, ya mur koshe ta saman kujerar. yana mata zazafan romance mai rikita kwanyar masoyi ai kuwa Teemah ta zauce ta biye masa suna romance mai tsayawa a zuciya basu tan-tan ce ba suka ji kiran sallahr magarib.
Ya dauki abarsa suka haye sama.
Ya dauro alwalla ya tafi masallaci.
Teemah bayan ta gama sallahr magarib ta sauko k'asa.
Ta saka aka soya mata wainar fulawa, taci ta dora kunun gyadar sai da taji kamar zata yi amai ta bari, ta kira Abbanta suka sha hira ta kafa musu kukan sangarta wai bata da lfy yanzu likita ta gama dubata, daket ma taci wainar fulawa da kunun gyada, sai da iyayye da Abbanta suka yi lallashin ta da wayo suna bata labarin garin sarki sai ga Teemah ta zage tana kyalkyalata dariya, sun jima sosai kafin ta musu sallama suna mata nasiha karfa ta rika ma mijinta tabarar da take musu da rigimar banza.
Dariya kawai Teemah tayi ta kashe kiran, ta mike ta nufi part din Bintu.


๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ๐ŸŒŸ


Safina ce duke gaban malam bokanta tana kuka tace "Malam komai ya lalace aure ya kan kama dan Allah ka temake ni ka lalata auran nan wlh ranar har marina yayi mutumen da idan na masa kurtu baya tsallakewa amma yanzu harda bugo na yake, ina so asaka masa tsanar ta a zuciyar sa a fasa auran wlh ko nawa zan biya." ta kai karshen maganar tana kuka.
Malam Dalhatu yace "ai kin makaro dumin yarinyar tana da karfin Addu'a, tana yi iyayan ta nayi, bari kiga wani abu" ya fada yana bude wata kwarya yayi saddabarun sa, yace ta kalla,sai ga Maheeda ta bayyana cikin parlon bakin su, taci kwalliya cikin ratsantsan less baki mai adon fari tana zaune kusan sanator Nuradeen suna kallon junansu suna sakarwa juna murmushi.
Nuradeen ya zaro wayarsa yace "sweet heart kalli irin akwatinan ki sun kusa iso wa daga Maroc "ya fada yana bata wayar.
Maheeda ta amsa ta kalla tace "wow my Honey thank u so much, wannan duk ni daya i love u my Honey" ta karasa maganar tana sakar ma wayar kiss.
Murmushi ya saki yace "sweet heart kin fi haka ma" murna tasa Maheeda ta rankwafa ta sakar ma Nuradeen kiss a goshin sa, ta koma baya tana dariya tana cewa "i love u shuga dadyna" ai Safina bata san lokacin da ta dauki kwaryar ruwan maganin ba zata rotsata da k'asa tana cewa "kinci kutumar ubanki shegiya karuwa, shikuma Nuradeen zaici kaniyar uwarsa munafuki magaribar fari ya tafi gidan su,wlh sai na raba ki da mijina, ashe iskanci kike son koya masa, zako ki shiga duniya."ta kai karshan maganar tana sakin kwarya.
Malam Dalhatu ya cafe, kwaryasa yace "ashe ke mahaukaciya ce, to wlh yau da kin raina kanki idan kwaryar nan ta fashe ahaukace zaki tafi daga nan gidan sakaryar kawai na fada miki gaskiya auranan ba fashi idan kin takura ke ce zaki kwana aciki dan haka ki tashi kiban guri tun kiluwa bata baiyana ba a gaban ki."ai Safina da tsoron tsiya tashi tayi jikinta na rawa ta fice.
Tana shiga mota direba yaja ya tafi,kai tsaye tace ma direba ya kaita gidansu amaryar mijinta.
Bai musaba ya dauki hanya, ko me ta tuna tace su koma gida zai zo ya sameta ai๐Ÿ˜‚shegiya Safina da ki je mana Aradu kisha mamaki agun sanator Nuradeen hamm.


Bangaran Teemah tana murda kofar parlon Bintu taji hayaniyar yaran, da dan gudun ta karasa shigowa parlon dauke da sallama a bakinta, tana cewa"My Antyna i miss u" idanunta suka sauka kan Asif da muneerat da mucoter suna wasan buya Rauda idanunta arufe tana neman su.
Teemah itama ta shiga aka fara da ita ta sin cewa Rauda daurin, taba Muneerat ta daure mata tace"to maza ku buya ni zan nemo ku duk in da kuka shiga,ni zan nemo ku" kuma karfin haline take jikinta ba karfi ko daya, cikin murna suka ce "momy mun yarda a kafta"dariya Teemah tayi tace"Ok Oya ku buya ai kun ga bana ganin ku hashashene zanyi"da gudu suka nufi gun bauyan su.
Teemah ta fara binsu tana neman su mucoter ta fara kamowa tana dariya"yaro kaga na kamo ka ko ai wannan aikin na ne, agarinmu"ta fada tana sakin sa ta nufi mabuyar muneerat ta damkota.
Bintu baki da hanci ta saki tana kallon Teemah duk yau kishin yarinyar ya adabi zuciyar ta duba da yadda ta rike Aliyu yau baya ganuwa ga haushin Aliyu kansa da take ji, amma haka ta daure, tana dariya harda rike ciki da maamkin ya akayi idanunta arufe amma tasan mabo yar kowa.


Bangaran Aliyu kuwa bayan anyi sallahr isha har zai tafi hospital yaji sakamako dan ya matsu yaji Babynsa na dauke da cikin sa,sai dai ya fasa dan yaji tace da zaran ta inda gwajin zata kirasa,sai ya nufi part d'in Teemah ya janyota su tafi part din Bintu dan yayi missing din yaran sa.


Yana zuwa yaga plate da cup ya nufi gun yaga ba komai aciki ta cinye, dariya yayi ya kwashe wayoyin sa ya zuba cikin aljihu d'ayar da take hannunsa yana duba irin lambobin da suka kirasa ba adadi, yaga kiran Aminullah ba adadi,kai ya dafe ya kirasa bugu daya ya d'aga yace"ina gaisuwa babban Yaya irin wannan bacewa haka ko amarci ake ci" murmushi Aliyu yayi yana shafa kansa yace"humm yaro zan kama ka ne ba wani amarci bata da lfy ne, ykk..? Aminullah yace"Ayya sannu a gaishe ta zan zo gobe na dubata"Aliyu yace"Ok mun gode zan kira ka anjima" ya fada yana kashe kiran, tuna wa yayi da Masa'udah ya lalubi number ta ya kirata, tana ta ringing ba'a daga ba, sai da ya kira sau uku bata d'aga ba, baki Aliyu ya tab'e ya d'aga kafada ya haye saman bene.


Bangaran Masa'udah kuwa lokacin da Aliyu ya kirata Suna parlo tana jikin Papi tana masa hira taga kiransa, ta mike cike da kunya iyayanta suna mata dariya ta shige bedroom ta kwanta saman gado shaukin Aliyu ya hanata sukuni tana kallon kiran taki dauka, ta saki murmushi ta tura kanta cikin pillow tace" My love ni bazan dauka ba kazo yanzu ka rungumeni na shaki daddadan kamshin ka gani cikin shaukin ka ni idan naji murya ka yanzu rikita ni zata yi sai naji kamar abin da ka fada mun d'azu yanzu zai faru amma gobe zanyi k'ok'ari mu hadu na kwanta cikin jikin ka kana nuna mun salon tattalin ka amma pls my love kar ka sake fadamun wannan maganar zan zauce maka ilove u my Gwamna much love" ta fada tana birgima saman gado.


Bangaran Aliyu kuwa ya na zuwa sama ya duba Teemah bata nan,murmushi ya saki yace " yar Babyna kinji sauki kenan"ya fada yana sauko wa, k'asa ya nufi part d'un Bintu domin ganin yaransa da Noor d'insa.


Ta kofar waje yabi, yana dab da shiga wayarsa ta dauki ringing, yana dubawa yaga Dr Zubaida.
Jikinsa yana rawa yayi picking ya kara akunnesa ya ce"Dr ya ake ciki Allah yasa naji Alheri"Dr tace "Yallabai matarka ciki ne da ita har tsawon sati uku da kwana uku cif ajikinta" wani irin farin ciki ne ya bai baye Aliyu yace"Allah ina mika godiyata gare ka da wannan kyauta da kamun tare da abar sona,Dr nagode sosai zaki ga sauran tukuici mai tsoka."Ya fada yana tsinke kiran cikin farin ciki,ya nufi kofar dan ya kosa ya shiga ya kalli Babynsa mai dauke da ciki sa, ya fada ma Bintu ta taya shi murna.
Dai-dai lokacin da Aliyu ya murda kofar, glass din ya shiga lokacin Teemah tana bin Asif da gudu ta kama kowa shi ya gudu suna zaga yan parlo suna dariya.
Asif yana hango Dadyn su ya nufi bayansa da gudu yana dariya Aliyu ya saki baki da hanci yana kallon su yana sakin murmushi ganin Teema cikin farin ciki tare da yaransa suma suna farin ciki.
Aliyu ya boye Asif a bayansa hankali yace"my son kayi shiru mana karta gane ma boyar ka."Teemah ta biyo shi in da take jin dariyar nan ta nufa, tana cewa"ni fa sai na kamo ka yau, Antyna ki fadamun wani gefe ya nufa" ta fada tana dab da isa kusan Aliyu santsi ya kwasheta tayi luuuu zata fadi tana cewa "Wayyo Allah!! Antyna"aguje Aliyu yayi kanta yana kiran ta"My Noor Allah ya tsare mun ke karki fadi ki ji ciwo, ki temake ni kar ciki na ya sake fita daga jikin ki don Allah Baby"..โœ๐Ÿป๐Ÿ˜†
Ikon Allah su Aliyu Gwamna hankali ya tashi idanusa sun rufe a gaban yara, ta Noor dinsa kawai yake๐Ÿ˜‚๐Ÿคญ๐Ÿค”
๐Ÿ’ƒ๐ŸปYar Janafty ce๐Ÿ’‹


Sai idan Allah ya kaimu Monday




Rahma ummu Fareesa ceโœ๐Ÿปโœ๐Ÿปโœ๐Ÿป


*21/February/2020*


*๐Ÿ‘ฐ๐ŸปMATAR๐Ÿ‘ฐ๐Ÿป*
*๐Ÿ’–๐Ÿ’–GWAMNA๐Ÿ’–๐Ÿ’–*








*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
____________________________________


*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________




*Written By*
Rahma AbdulNasir
Yar mutan Niger๐Ÿค™๐Ÿป




*Uwa mabada mama Janafty kaunarki gareni daban take Tun daga farkon matar gwamna har karshe Sadakarwar kice my Sweet momy Janaf๐Ÿ‘Œ๐Ÿป๐Ÿ˜˜*










*Bismillahir Rahamanir Raheem*




*Page 4โƒฃ4โƒฃ*




""""Teemah tana dab da kifewa a k'asa, Aliyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login