Showing 180001 words to 183000 words out of 185716 words

Chapter 61 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4690

shi ya sha giyarsa da sigarinsa son ransa domin a halin da yake ciki su kad'ai ne abinda suke rage masa rad'ad'in damuwarsa ."






Kallonsa maryam ta cigaba da yi ko kifta idanunta bata són yi akanshi "kallonsa kad'ai ya isa ya harzikawa mutun brain dinsa ,namijin duniya ne ko daga yanayinsa ,wani murmushin farinciki na samun nasara ya subuce mata "duk Kinsa da aureta gashi dai allah ya bata sa'a a karshe ta zama mallakinsa na har abada, domin tasan muddin mami na numfashi a doron duniya bazata barshi ya wulakantata ba bare akai ga maganar saki atsakaninsu zasu rayu tare har karshen numfashinsu dan haka zata iyawarta da komai ta makallakesa har ma ta zama wani sashin na rayuwarsa ."


Duk da ba kulata yake ba bare kallota amman da kyar take iya control din kanta akanshi don kallonsa yana cikin abinda ke sata fita haiyacinta tama rasa a duniyar da take ,a duk lokacin da tayi saa ya kalleta kuwa hakan na matukar sata natsuwa ,ta lumshe idanunta acikin ranta tace "adamcy nah ni kad'ai ,komai naka yayi min ilarka dai baka son rainin da zafin zuciya uwa uba tsanar mutane na babu gaira babu dalili ."






Kamar ance ya d'ago kanshi dake risine yaga idanunta akanshi ,a zaunen da yake ransa ya fara 'baci ,zuciyarsa ta dinga tafarfasa sakamakon kallon da take masa na kurrulla irin kallon daya fi tsana arayuwarsa ,numfashi ya sauke ahankali tare da sake kau da kanshi muryarsa a tsarke ya kiran sunan da yake kiran mahaifiyarsa dashi "sweetheart !"ya'akayi adamcy nan? "ta amsa cike da tsananin kulawa "Kece wa yarinyar nan ta bar d'akin nan" a d'an firgice mami tace "wace yarinyar kuma ?"


Shiru yayi yana sake 'bata rai mami ta kalli gabadaya parlour'n babu kowa daga ita sai shi da maryam ne acikinsa "kenan dai maryam yake nufi ?"adamcy matarka ce fa ?"oh my god sweetheart ki kalli kiga irin kallon rainin hankalin da take min ." yayi mgnr a d'an tsawa ce mami ta waiga ta kalli maryam wacce tun soma maganarsa tayi saurin d'auke idanunta akanshi ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ."




"Ba nasara akayi akaina ba ni naga damar amincewa aurenta dan naga sai wani kallon gani gani take min ,wallahi tun da wuri ki ja mata kunne kar taga an d'aura min ita ta nemi ta dinga min kallon iskanci idan ma tana tunanin wani abu acikin ranta wallahi tayi maza ta cire dan hakan ba abu ne mai sauki ba ."


"Da me zan ji ?aurenta da aka min dole ,ko da kallon iskanci da take min ? amman barni da zazzafar qaddarar data rufta min shekaru goma sha .." yayi shiru yana sauke zazzafan numfashi ,ya gyara zamansa tare da kai hannuwansa duka ya rufe fuskarsa dashi yana jin kamar yayi kuka kafin daga bisani ya cigaba da sakin bakaken maganganu masu zafi da ta'ba zuciya duk magiyar da mami take masa akan yyi shiru bai yi ba har sai daya samu natsuwa sannan ya saurara inda ya kwanta akan kujera ya juyar da kanshi gefe yana sauke numfashi ."




mami ta kallesa na second biyar sannan ta juya ta kalli maryam dake tsaye gabadaya ta rasa me zata ce ."yayinda maryam Jiki a matukar sanyaye ta matsa daga kusa dasu tare da juya masu baya tana jin faduwar gaba mai tsananin , tsanarsa gareta yana matukar d'aga mata hankali sosai taji bacin rai ,taji kamar ta fice daga d'akin mummansa ganin yadda ya juya baya ko mami yaki kallo ."




mami ta qara matsowa kusa dashi tace "Adamcy ka daina zafafa kiyayyar matarka a gaban idanunta saboda ban fidda rai wata rana shakuwa mai qarfi na iya shiga tsakaninku ba dan haka ka dinga qoqarin dannewa ka barwa zuciyarka please " tana gama fadar haka ta mike tsaye ta qarasa inda maryam take tsaye tare da riko hannunta suka fito daga d'akin."




Suna fita mami ta soma qoqarin rarrashin maryam ,tayi saurin cewa mami "karki wani damu mami banji komai araina ba," idan da sabo na rigada na saba da halinsa fatana allah yasa aurenmu ya zame mana alkhairi arayuwarmu gabadaya."shiru tayi kafin ta cigaba da magana "mami ni dai ki qara tayamu da addua akan wacce kike mana duk da har yanzu yaya adam bai amince dani ba amman yau kawai naji wani sanyi da samun 'yanci a zuciyata ."




Murmushi mami tayi dan tun tuni ta fahimci wani abu akan maryam din hakan kuma yayi mata dadi domin ko babu komai zatayi hakuri da duk wani wulakanci d'anta cike da farinciki tace"na gode sosai maryam in sha allahu zan cigaba da yi maku addua allah yayiwa rayuwar aurenku albarka allah ya azurtaku da samun zuria masu albarka ko ni yau zuciyata ta rage nauyi duk da rayuwar da adamcy ya d'auko ya rage kashi sabain na farincikina amman duk da haka naji zuciyata ta rage nauyi saboda nayi imani ko bayan raina zaki kula da rayuwar dan'uwanki ."




"Maryam adamcy rayuwata ne Kiyi hakuri dashi , Kiyi hakuri da halinsa ki kular min dashi "in sha allahu mami zanyi iyakar qoqarina " na gode maryam allah yayi miki albarka "ameen na gode mami allah ya qara miki lafiya da nisan kwana mai amfani "Ameen Ameen mryam shiyasa nake qara sonki akwai ki da hakuri dasanin yakamata ."suka cigaba da takawa ahankali suna magana har suka sauko qasa fuskarsu d'auke da murmushin farinciki ."




Bayan saukowar mami ta aika akira mata hisham dan tun safe yana bangaren baba babba tare dasu salim tana zaune a d'akinta yayi sallama sai data bashi izinin shigowa sannan ya turo kofar d'akin ya shiga kanshi a risine a kasa kallo d'aya zaka masa ka fahimci jikinsa a mace yake , hisham ya rusuna ya gaishe da mami cike da girmamawa ,ta amsa masa cike da kulawa tana nuna masa kan kujera amman yaki zama ya zauna akan daddumar daya gani a shimfide akan kafet."




"Hisham ya akaji da taro ?kamar bazai amsa ba amman ya kasa ko babu komai mami tana da kima gareshi bazai ta'ba yi mata banza ba,dan haka ya bude bakinsa da kyar yace "alhamdulillah mami ya naku ?to Alhamdulillah hisham allah yayi maku albarka gabadayanku, allah kuma ya baku ikon cinye jarabawa rayuwar, kowani bawa rayuwarsa tattare take tafiya da jarabawa iri iri ."


"Kayi hakuri akan sauyin daka samu ka dauki hakan a matsayin jarabawa da kuma qaddara, auren auta yana daga cikin qaddararka wanda baka isa ka goge faruwar hakan ba ,abinda nake son ka fahimta Idan allah bai nufeka da samun wani abu arayuwarka ba sai ka gode masa domin allah sonka yake kuma duk abinda allah ya qaddara shi zaka samu, abinda allah bai qaddara zaka sameshi ba duk yadda abun ya kusantoka at end of the day bazaka sameshi ba duk kuwa son da kake yiwa abun ."




"Wannan kuma duk hukuncin ubangaji ne , idan da yau mun sanya hakan acikin zukantamu da zamuyi rayuwa cikin jin dadi cikin annashuwa batare da wata damuwa ba ,idan mun samu allah ne ,idan mun rasa allah ne" wama tasha una illa anyasha allahu rabbul alameen duk yadda kaso idan allah bai so ba bazai ta'ba yuwa ba ."




"wannan hukunci ne na allah ,allah yasa hakan shine mafi alkairi wata killan ma idan ka samu auren nuzla arayuwarka ta zame maka maseefa da tashin hankalin da sai kayi nadama ,ta zama bala'i arayuwarka yanzu rashinta sai ya zame maka alkhairi arayuwarka kayi hakuri da sauyin da allah yayi maka da sannu zaka ga irin sakayya da allah zai maka domin duk wanda ya yarda da allah allah zai isar masa ."




"idan kuma akwai alkhairi a tsakaninka da nuzla sai kaga anan gaba ka qara daita wannan duk kadan ne daga hukuncin ubangiji fatanmu allah ya zaba mana abinda yafi zama alkhairi arayuwarmu kar allah ya barmu da zabinmu "duk wannan maganar da mami take kanshi na kasa ya kasa d'ago kanshi har sai data dasa aya ta hanyar saka masa albarka sannan ya d'ago yayi mata godiya ya mike a natse ya fice daga gidan gabadaya."




Karfe biyar daidai motoci guda goma na alfarma sukai parking a kofar gidan mami domin d'aukar nana hauwa ,mutanen da suka zo gabadaya sun kasance kawaye ne ga hajiya zulfa'u ,kowacce cikin shiga ta alfarma domin kallo daya zaka masu ka fahimci kudi ya zauna ajikinsu shigar kowace tana wane na wane , sai dai mami tace hisham take son yazo ya d'auke amaryarsa da kanshi lokacin da sakon ya samesa yaji abun wani iri ranshi ya 'baci matuqa ."




"duk kawayen mumynsa da abokansa da suka tafi d'aukota basuyi ba sai shi da kanshi yaje kamar wata zinariya ?yayi wa kanshi tmbyr yana jan tsaki bana jin zan iya zuwa dan nasan nauyi kawai mami take són d'aura min ya lalubo wayarsa yana qoqarin kashewa kiran mami ya shigo "ya salam !"ya furta a fili yana mai dafe kanshi kiranta né yayita shigowa har sai daya d'auka ,yana d'auka tace "hisham d'ana kazo ka d'auki matarka " babu yadda ya iya dole ya amsa da "tô mami ganinan zuwa"ransa a matukar 'bace ya tashi ya shirya cikin wani d'anyen voyal fari sol ya shiga d'akin hjy zulfa'u ya fad'a mata inda zashi sannan ya fito ya kamo hanyar zuwa abdullahi estate."






zaune nana hauwa'u take agaban mahaifiyarta sanye da fararen kaya tun daga kan takalmi mayafi pos din dake rike a hannunta agogo komai na jikinta fari ne sol jikinta lullube cikin mayafi , shape din fuskarta kawai ake iya gani ,wani irin qamshin jikinta Ke fitarwa mai sanyin dadi da sanya natsuwa tare da kwantar da hanakali yayinda yan'uwata mata ke zaune akan kujera kowace cikin shiga iri d'aya ."


nasiha mai matukar ratsa jiki mami take mata tana tunatar daita hakin daya rataya a wuyanta cike da gamsuwa nana hauwa take gyada mata kai tana zubar da hawaye adaidai lokacin ATA ya shigo d'akin sakamakon kiransa da mami tayi bai qarasa inda suke ba ya samu waje ya tsaya ya jingina bayansa da bango d'akin ya rungume hannuwansa duka a qirjinsa yana kallon nana hauwa'u dake zubar da hawaye yayinda aunty shahida ta mike daga mazauninta tana faman rarrashinta tana goge mata hawaye ."


Ahankali hisham ya turo kofar dakin ya shigo ya tsaya yana jin wani iri a gabadaya ilahirin ajikinsa kafafuwansa sukai masa nauyi ya kalli inda ATA yake tsaye rabonshi da ganinsa yau tsawon kwana uku kenan ,numfashi ya sauke yana qoqarin danne abinda yaji yana taso masa kafin ahankali aunty shahida ta qaraso inda yake ta riko hannunsa ta zaunar dashi kusa da nana hauwa'u agaban mami ."


"hisham ga amanar nana hauwa'u nan na danqata a hannunka ba dan ina tunanin zaka cutar daita yasa na damka maka amanarta ba sai dan yanayin rayuwa da kuma yadda aurenku ya kasance, aure ne da babu wanda yayi tsamanin faruwarsa amman dake haka allah ya qaddara babu tsimi babu dabara sai ya kasance ,kema nana hauwa'u ga amanar hisham d'ana na damka miki, kisan mahimanci amana ko ban gaya miki ba aure amana ce atsakanin ma'aurata kuma duk wanda yaci amanar dan'uwansa allah bazai barshi ba."


" na tabbatar d'ana hisham bashi da matsala idan naga wata matsala daga gurin ne zaki kuma ki kuka da kanki dan bazan ta'ba d'aga miki kafa ba ko baki uzuri ba dan haka ki kiyaye "aunty shahida dake durkushe kusa dasu tace "hisham ga amanar auta nan allah ya tayaka riko "aunty khadija da zabiba ma dai abinda suka fad'a kenan "shi dai ya shiga ukunsa yanzu mumynsa ta gama damka masa amanarta kafin ya fito tana jadda masa ko rama taga nana hauwa'u tayi sai ya hadu da mummunar fushinta ,yanzu kuma ga mami dasu aunty shahida shi ya suke son yayi da rayuwarsa ?" shifa baya jin zai iya rike wata amana amman babu yadda ya iya muryarsa a sanyaye yace "in sha allahu mami zan kiyaye allah ya qara girma ya qara lafiya" Ameen Ameen hisham allah yayi maku albarka ."




Banda kuka babu abinda nana hauwa'u Ke faman yi wanda hakan Ke sake d'aga hankalin ata kwata kwata irin wannan rayuwar bata burgeshi zaa akai mutun gidan miji amman yana kuka irin haka kamar zaa kai shi kabari ,a tunaninsa wannan zalinci ne sam bai kamata a had'a irin wannan auren ba gara idan nmj ke so komai na zuwa da sauki canza rayuwar mace ba abu bane mai wahala ga d'a nmj amamn canza raayin nmj abune mai bala'i wahala ahankali yaga an mikar da nana hauwa'u tsaye shima hisham ya mike suka jero."




Kamar ance nana hauwa'u ta d'aga kanta idanunta ya sauka akanshi tsaye cike da sanyin jiki ta soma tahowa zuwa inda yake tsaye yana ganin haka ya kau da kanshi gefe yana sauke numfashi har suka qaraso inda yake bai waigo ba ,nana hauwa'u ta kasa wucesa kowa yayi mata fatan alkhairi tare da damka amanarta a hannun hisham amman banda shi tasan halinsa shirunsa yana nufin abubuwa dayawa a gareta dan haka ahankali ta dawo ta duka agabansa tana masa sallama sautin kukanta na tashi."


jikinsa yayi sanyi gayayyun idanunshi ya ware akanta still tana durkushe tana kuka yayinda tafin hannunta ke kife a saman kafarsa wani abu ya had'iye mai d'aci daya tsaya masa a makoshi bai ta'ba sanin cewar yana qaunar qaramar kanwarsa ba sai da aka samu wannan canjin ,babu yadda zai yi daita né domin itace da kanta ta amince, da tursasata akayi sai dai ayi bala'i da zaayi amman bazai yarda ba ,kukanta ya dinga ta'ba zuciyarsa bai san lokacin da ya kira sunanta ba "nana hauwa'u!"


Kanta ta d'ago wanda ke cike da ruwan hawaye ta zubawa yayanta tattausan murmushi ya sakar mata kafin ya mika mata hannunsa alamar ta kama ta mike tsaye ,da wani irin sauri ta kama hannunsa tana ganin kamar a mafarki yake mata murmushi "ina mafarkine ko kuwa ? tayi maganar a fili tana kuka " menene auta ?murmushinka yaya wannan shine karo na farko danaga irin wannan murmushin akan fuskarka" ya qarasa mikar daita tsaye ya kwantar daita akafad'arsa yana shafa bayanta " kiyi hakuri kukan ya isa haka auta "lafewa tayi sosai ajikinsa Kmr wata baby "yaya ka yafe min ban bi umarninka ba "karki damu dani ki kula da kanki ".




shi kuwa hisham zuba masu ido yayi yana jin wani zallar 'bacin rai na ratsashi "ki daina kuka auta idan kinga da matsala ki kirani babu wani uzuri da zanwa hisham shima kuma yasan halina bazai yi any thing nonsense ba "wani irin kallo hisham din yayi masa kamar yace masa "me zai yi idan aka samu matsalar sai ya duba idanun mutane dake wajen mami bazata ji dadi ba hka sauran yanuwata da suke da kima a idanunshi ,sannna idan ya fad'a haka mumynsa bazata d'aga masa kafa ba idan taji labari ."




ATA ya kamo hannunta ya saka acikin na hisham ya damke waje d'aya "ga amanar auta please ka kular min daita fiyye da yadda zaka kula da kanka" shiru hisham yayi masa yaki cewa komai, Jiki babu kwari suka fice daga d'akin, aunty shahida da aunty Khadeeyja da zabiba na biye dasu suna qarasowa parlour'n hisham ya zare hannunsa cikin nata yayi gaba shiru tayi kawai tana duban bayansa kawayen hajiya zulfa'u mutun uku da suka tsaya suka mike tsaye maryam ta qaraso ta rungume nana hauwa'u tana cewa "shikenan sister zaki tafi ki barni" ta qarasa mgnr tana fashewa da kuka "ai baku rabu ba mrym tunda duk mazajenku 'yan gidan nan ne ,kusan kullum suna nan inji cewar hjy nurriya."




Da kyar aka 'bam'bare maryam ajikin nana hauwa'u hjy sumayya ta riko hannunta suka fito zuwa haraban gidan ta bud'e mata bayan mota ta shiga ta zauna ta rufe murfin ,yayinda hisham ke qoqarin qarasawa wajen abokansa hjy summaya ta kwalla masa kira ya dawo ya tsaya gabanta "shiga"mumy kuje kawai daita zan biyoku "aa hisham ba'a yin haka shiga kawai sai wani daga cikin abokanka yajaku "kai !"ya furta a fili sannan ya shiga ya zauna ko kallon inda take bai yi ba ."


Su biyu ne zaune abayan motar sai salim a mazaunin direba hawaye yaki tsayawa a idanun nana hauwa'u,wani sabon kuka ne ya kufce mata sanda suka fito daga estate dinsu suka hau titi ,gefe tayi da kanta tana damke hannuwanta cikin juna "salim kasan wani abu ?salim dake tuki yace "aa sai ka fada "wai ATA ke bani amana" salim naji haka ya manna ipod a kunnensa ya cigaba da tuki "aikin banza sai kace shi ya iya rike amanar' yar wasu da yake son shi a rike masa amanar kanwa, mutun sai shegen son kan tsiya sai kazo kasani dole na rike maka amana."




kunnuwan nana hauwa'u ya jiyo mata maganarsa acan kasan makoshi kamar ta juyo inda yake sai kuma ta fasa ta cigaba da kallon titi ya sake motsa bakinsa kmar zai yi magan sai kuma yayi shiru ya ciro wayarsa dake ringing yanayin yadda ya amsa ta fahimci yaya amar ne "kaga amar dan allah ku barni da damuwata kowa amana amana !! wai me kuke nufi dani ne ?" me yasa bakuje kuncewa ATA ya rike amanar maryma ba sai ni zaku dameni da wata amana saboda kun rainani ?"dan girman allah ku barni na huta naji da damuwata no no!! bazan fa gane ba wayar salim ce ta d'auki qara ya danna iPod din dake makale da kunneshi yana cewa "okay mumy an gama har ya gama wayar musayar magana hisham yake akarshe dai ya kashe yana furta aikin banza kawai ."


Tafiyar mintuna ta kawosu ikeja gra atare suka qaraso gbdynsu har abokan ango sanda salim yayi parking a haraban gidan hajiya sumayya tayi parking a haraban gidan, hisham ne ya fara fitowa yayi gaba ,jiki a matukar sanyaye nana hauwa'u ta fito hjy sumayya ta qarasa da sauri ta riko hannunta cikin nata suka biyo hisham abaya cikin natsuwa har zuwa bakin kofar shiga parlour'n hajiya zulfa'u tana zaune cikin kawayenta ."


wata kawarta marry wacce ta kasance yoroba ta mike da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login