Showing 162001 words to 165000 words out of 185716 words
Chapter 55 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
daya idan ma ta kama a daki d'aya idan damuwa yake kunsa min ni kadai zan shanye ,haka zalika idan farinciki ne ni kadai zan ji duk wani abu da zan tsinta acikin gidansa akaina zai qare kina tunanin zanyi farinciki a gidan mutumin da baya sona ?"bana jin akwai halittar da yaya adam ya tsana kamar ni, a wasu lokutan na Kan zauna nayi tunanin me yasa yake tsanata haka ?ta sauke numfashi mai hade da sheshekan kuka ya Adam yayi mugu mugun tsanata sister ."
"Na fada yanzu ma zan sake fad'a aurena dashi babu abinda zai haifar sai damuwa domin kuwa bazai yi yadda kowani magidanci yake a gidansa ba ,bazai dauki duk wani responsibility dina ba,zai watsawa mami qasa a idanunta domin zuciyarsa bata tattare da tsoron kowa ko shakkun kowa na sha jin yadda yake fadawa ya hisham da yaya bello cewar baya sona ,nima idan banki auren ba sister me kike son nayi ?ni da akwai yadda zanyi na tsaida maganar auren nan wallahi da nayi domin nafi bukata hakan ko kuma mutuwata dan wallahi zan so faruwar haka da dai na kasance a gidansa abar wulaqantawa ."
nana hauwa'u ta riko hannuwanta duka cikin tsananin damuwa tana cewa "tabbas akwai ciwo sister ciwo kuma mai zafi acikin zuciyarki nasan yaya Adam bai sonki sister amman bazan daina baki shawara akansa ba domin ina ji ajikina zai canza zaki canzasa sister ."maryam ta girgiza mata kanta alamun "a'a ! bazan iya ba sister bazan iya canzasa ba ,yaya adam yafi karfina yafi karfin hada rayuwa dani babu wanda yasan abinda Ke ransa gabadaya acikin halayensa bai gama fitowa dashi fili ba saboda babu wanda Ke rayuwar akarkashinsa ,sister zuciyata zata buga matsawar aurena ya tabbata dashi nasan nan gaba kadan zan mutu dan bazan cigaba da rayuwa mai dadi ba ".
"kiyi addua sister dayawa anyi irin aurenku karshe kuma yayi kyau kuma anyi farinciki ki hasasowa kanki haka ki daina tunanin bad things a tsakaninku ."at every step sister ta ina kike hango min jin dadi ki duba irin abubuwan da yake ta yaya kike son nayi scricfied din rayuwata akanshi ?"nasani sister amman ki bari ayi ki gani daga ranar ki fara Kirgawa day by day wata rana soyayya zata kasance a tsakaninku wallahi inada wannan tabbacin kirki zubawa mami kasa acikin idanunta domin kuwa ta yarda dake ta fad'a ta sake jadaddawa cewar zaki mata biyayya bazaki zuba mata kasa a ido ba dan allah karki karyar da yardar data tayi miki ."
"mami tayi alkwarin muddin tana raye sai anyi auren nan kuma sai kin samu farinciki a gidan yaya kuma ma shi ya Adam ya amince zai aureki har yau din nan bai ce ya fasa aurenki ba "bisa umarnin mami ba ?cewar maryam tana duban nana hauwa'u hawaye na turereniyar zubowa bisa kuncinta "ina ..!ina jin bazan .."sai kuma tayi shiru ta kasa cigaba da maganar gabanta na wani irin faduwa da karfin gaske." dan allah ki bar maganar nan haka sannan ki bar kuka nan tashi muje d'aki ki kwanta ki huta jiki a matukar sanyaye da taimakon nana hauwa'u ta mike tsaye tana jin wani irin sanyin a gabobinta tana jin kafafuwanta sun gaza daukarta nana hauwa'u ta rikota sosai ta makaleta a gefen jikinta suka nufi daki ."
ATA ya sauko tsaf cikin wata dakakkiyar gezner tamkar ranar zaa daura masa aure dinki ya balain yi masa kyau takalmin kafafunsa cover shoes ne yayi matukar dacewa da shigarsa kanshi babu hula sai agogon fata dake daure da tsintsiyar hannunsa
ahankali yake taka step yana saukowa yana duba agogon hannunsa har zai fita sai kuma ya dawo baya ya dauki hanyar dakin mami, ya tura kofar dakin a natse ya shiga ya isketa zaune hannunta rike da waya wanda ya nuna masa alamun waya ta gama tana ganinsa ta sake hade fuska tamkar bata ta'ba dariya ba dan kalamansa sun ta'bata sannan sunyi mata ciwo matuka a tunaninta ko mai aikinta bata cancanci adam yyiwa mummunar fata haka ba bare diyar danuwanta wanda su kadai iyayensu suka haifa suka bari a duniya."
cikin kankanin alokacin yaga sweetheart dinsa ta canza ganin irin kallon da yake mata yasa ta kawar da fuskarta aranshi yace "har abun ya kai haka ?."shiru yayi kawai yana dubanta a tsanake shi a ganinsa babu wani laifi acikin maganarsa dan so ba karya bane haka zalika rashin so ba karya bane , hakuri yake son ya bata amman daya tuna akan maryam ne sai yaji ya fasa ,yayinda ita mami hakurin tayi tsammanin ya shigo ya bata dan shi take bukata daga garesa amman sai taji sautin muryarsa can kasan makoshi kamar koda yaushe yana cewa "sweetheart ni zan fita amman bazan wani jima ba" bata juyo ta kallesa ba bare tace masa wani abu jiki a sanyaye ya fice daga gidan gbdy can qasan zuciyarsa cike da bakinciki da fargaban shirun sweetheart dinsa dan a duk sanda tayi shiru haka matsaloli ne zasu biyo baya ."
Daga shi sai direbansa acikin mota kira ne ya shigo wayarsa yana duba screen din wayar sunan aunty shahida ya gani bai dauka ba dan yasan kararsa mami ta kai wajenta yana kallo har kiran ya katse wani kiran ya sake shigowa sai datayi masa kira biyar bai dauka ba haka aunty khadija kiranta biyar har suka isa station kiransa suke yi amman yaki dauka ya fito daga cikin mota kai tsaye office din dpo ya nufa ya tareshi cikin farinciki ya mika masa hannu suka gaisa yana nuna masa wajen zama da hannunsa a hankali suka fara tautaunawa akan hindu."
"ranka shi dade yarinyar nan bata da mutunci ga rashin kunya ga bakinta baya mutuwa an kawo mata abinci ma ta kwafar tana zagin wanda ya kawo mata tun daaka kawota bakinta bai yi shiru ba sai tsinewa mutane take "dubansa ATA yayi yana cewa "baku ladabtar daita bane shiyasa "ai yalla'bai na dauka kamar wancar yarinyar ce da kace kar ataba lafiyar jikinta shiyasa nayi masu gargadi amman dai tasha mari a wajen inspector romoke numfashi ya sauke
"abinda ya kawoni yanzu ina son a tsanata bincike akanta fiyye da wanda akayi akan nuzla idan ta kama da duka duk ayi mata domin ta amsa laifinta ."
"bare ma wannnan yarinyar cikin sauki zata amsa laifinta dan ta tabbatarwa da jami'an da suka kamota muddin ta fito sai tayi ajalin yarinyar dakasa a bibiyeta ga dukkanin alamun itace mashekiyar da muka dade muna nema ATA ya gyada kai kawai yana saurarensa."dpo ya cigaba da magana "ko akawo maka ita ne ?ya fadi haka ne ko zai bukaci ganinta kamar yadda ya bukaci ganin nuzla."
ya girgiza masa kai kawai alamun baya bukata "abinda nake so bana son maganr kamata ta fita zuwa koina har ku gama bincikenku akanta sannnan bana son kowa yasan inda take har sai ta fad'a maku itace ta kashe mubina cikin girmamawa ya amsa masa da to "matsawar ta amsa itace ta kashe mubina ina son tasan girman laifin data aikata ku kaita kotu batare da sanin kowa ba alqali ya yanke mata hukunci daidai da laifinta a turata kurku wannan shine kawai abinda nake bukata "in sha allahu yalla'bai zaayi duk yadda kake so "tare da dpo suka fito yana sake jadaddawa dpo baya son tana tsare ya fito da kudi masu yawa kamar wancan ranar ya damkawa dpo sannan ya wuce ya tafi ."
Ahankali yake takawa har ya isa cikin dakin mami ya sameta zaune a saman abun sallah tana jan carbi kana kallon idanunta kasan kuka tayi kuma ba kadan ba ya qarasa ya zauna a gabanta ya riko hannunta daya cikin nashi yana kiran sunanta "sweetheart!"da kyar ta dago kunburarrun idanunta ta tsura masa sannan ta zare hannunta cikin nashi tana cigaba da jan casbaha jikinsa ya sake yin sanyi bai ta'ba ganin wannnan yanayin atattare daita ba sai yau duk abinda zai mata bata taba daukar zafi dashi irin haka hasalima a inda abun ya faru anan take barinsa ."
Ahankali ta mike tsaye ta koma bakin gado ta zauna shiru yayi kawai yana kallon yatsun kafafunta kafin daga bisani ya yunkura ya mike tsaye ya isa inda remut din ac yake ya dauka ya kunna saboda zafin da yake ji ya zauna kusa daita ta sake mikewa ta fito daga dakin ta barshi zaune yabi bayanta da kallo sannan ya biyo bayanta ,koda ya fito parlour'n bai ganta ba sai sautin muryarta yajiyo sama sama daga dakinsu nana hauwa'u dan haka ya haye samansa."
Tun bayan fitar hindu hajiya aljannatu Ke kwance tana bacci ,acikin baccinta ne tayi mafarkin wai ga wasu mutane sun zagaye hindu wanda batasan ko su waye ba ,macen dake cikinsu taje ta samu tana tambayarta lafiya suka zagaye ta amman tayi mata shiru tana kallonsu zasu wuce daita tace "ina zaku wuce min da yarinya ?da wannan kalmar ta farka daga mafarkinta tare da kallon sugura dake zaune akan dadduma da alamun ta idar da sallah né tace "sugura ina hindatu ?"ai tunda ta fita bata dawo gidan nan ba "ta fad'a mata haka sannan ta cigaba da laziminta bandaki umma ta shiga tayi alwala ta fito tayi sallah tana idarwa tace "wallahi duk jikina ciwo yake "sannu Atu " dake haka suke kirata ."
"yauwa sugura dauko min wayata na kira naji inda take "sugura ta mike ta dauko mata wayar ta mika mata ta fita atu ta soma neman layin hindu sai dai abu daya aka fad'a mata a karon farko "switch off ta sake maimaita kiran the same thing tayi shiru rike da wayar tana jin wani iri ajikinta da tunanin inda taje dan ita ba mai yawon leke leke bace acikin estate din bare tace a dubota koda yaushe tana gida idan kaga ta fita zata siyan abu ne ko kuma da shiga gidan hjy zulaihat ."wasa wasa har dare babu hindu ba alamunta nan fa hankalin mahaifiyarta dana yayyunta ya tashi nan da nan baba qarami ya fita nemanta tare da sauran yan'uwanta amman duk inda suka je basu ganta ba ,dan haka suka qarasa police station mafi kusa dasu sukayi report sannan suka dawo gida cikin matsanancin tashin hankali."
Har washgari baa ga hindu ba koda hjy zulai ta samu labarin abinda ya faru batayi sanya a gwiwa ba ta d'auki kafafunta taje gidan baba babba tayi masa bayani komai ,shine ya kira baba qaramin koda ya shigo ko kallon inda mami take bai yi ba sai bayan da baba babba ya sheida masa aiko cikin tashin hankali da zafin rai yake tmbyrta police station din daaka wuce daita "ina zan sani tunda daga sama allah ya kawowa maryam dauki "bangane hausar baki sani ba "iyakar abinda nasani kenan na fada sai ka bazama zuwa duk wani police station dake kusa da nesa domin nemanta idan kuma angata lokacin ni kuma zan shigar da qarar abinda ta aikata ."
wani mugun kallo ya watsa mata yana cewa "ki kalleni da kyau zulai kinga nayi miki kama da irin wadan nan mutane ?kisani ni ba wannan shashan bane da danki ya garkame masa 'ya kwana da kwanaki bai dauki mataki akai ba dan haka wulakancinki da isarki ta tsaya akansa ke kuma ki tsaya a iyakarki.." idan ba haka ba me zai kayi ?bai yi magana ba illa nunata da babban dan yatsansa da yayi alamun gargadi sannan ya juya kamar zai tashi sama naunayen ajiyar zuciya baba babba ya sauke yana cewa "kiyi hakuri kin rigada kinsan halinsa "nasani amman a haka yake son na bawa d'ana umarnin ya auri hindu ?ai wallahi dana bari adamcy Ya auri hindatu gara nuzla bancin hisham dake tsakani nan suka cigaba da tautaunawa akan matsalar ."
ATA ya sauko a natse cikin shigar suit a hankali yake takowa yana kallo koina a parlour'n har ya qarasa saukowa , babu kowa parlour'n har sweetheart dinsa bata nan ,wanda adaidai lokacin daya sauko daita yake fara cin karo agabanta zai ci abinci har sai ya bar gidan take tashi ta shiga ciki wani lokacin kuma ta cigaba da zama amman yau babu ita babu alamunta ."
kallon dining yayi da alamun an gama shirya masa breakfast numfashi ya sauke ya nufi hanyar dakinta ya shiga bai ganta ad'akin ba ,dan haka ya samu waje ya zauan a bakin gado yana jijiga kafarsa a tunaninsa ko tana ciki bayi kusan minti goma yana zaune amman shiru ,ya mike tsaye ya fito yana neman layinta kiran na shiga amman bata dauka ba, layin nana hauwa'u ya kira tana dauka yace "ina sweetheart ? okay ya fad'a takaice yasa kai ya wuce zuwa office bai tsaya bin takan abinci ba ."
Bangaren baba qarami da yayansa duk wani office din police na kusa dasu sunje amman babu labarin hindu duk inda suka je sai ace ba nan aka kawota ba dan haka suka bazama zuwa headquarters sukai report ,da yamma koda ATA ya dawo bai iske mami ba sai dai tasa an a shirya masa dining amman bata tsaya ba tunin ya gano manufar mami akanshi tashin hankali kenan wanda baa saka masa rana idan kowa zai iya barin rayuwarsa ya hakura amman banda sweetheart dinsa bazai iya ba zai iya komai akanta zai iya sadaukar da farincikinsa gareta ."
wanka ya shiga byn ya fito ya sauya kaya zuwa na shan iska ya sauko ya shiga dakin mami tana zaune tare da maryam tana shirya mata kaya a kwaba tana ganinsa ta dauke idanunta zuwa kan maryam "Yauwa maryam kwashe wannan kayan ki maida su sama, jiki a sanyaye ta dauki kayan ta ajiye kamar yadda mami ta buqata sannan ta maida murfin kwaban ta rufe ta raba ta gefensa ta fice daga dakin ."
Ya sauke numfashi "ammm sweetheart "kada kace min komai please dan banason jin komai daga bakinka yadda na zuba maka ido kaima ka zuba min ido kowa yayi tsabgar gabansa kayi abinda kaga ya fiyye maka arayuwarka mami ta fad'a tana nuna masa kofa .."sweetheart "dan allah adamcy ka bar min daki tunda ba kai ka gina min shi ba fita kafin nayi maka abinda bazai mana kyau ba "sweetheart ." ya fad'a a karo na biyu zuciyarsa cike da matsanan cin tashin hankali "ka fita adamcy ka fita bana son ganinka fita ta fad'a tana kawar da fuskarta ."
"Da gaske dai sweetheart dinsa bata son ganinsa me yayi da zafi haka ?a ganinsa shi bai yi laifin komai ba juyawa yayi ya fita yana waiwayenta yana jin kuna acikin rashi tun daga lokacin mami ta fita harkarsa shi kuwa abun ya damesa idan ya sauko yaga bata nan baya tsayawa karya wa zai wuce office washegari ya kasance weekend yana saukowa kai tsaye dakin mami ya shiga ya sameta zaune ya gaisheta cike da ladabi ta amsa tana qoqarin mikewa saboda har lokacin tana jin zafi da radadin abinda yayi mata har tayi taku biyu taji ya riko hannunta "dan girman allah sweetheart kiyi hakuri da abinda nayi ya fad'a cikin rawar murya."
wani sanyi dadi taji ya lullubeta daman abinda take bukata kenan daga garesa sai dai taki kallonsa ahankali ya dawo gabanta ya tsugunna bisa gwiwowinsa "ina mai neman afuwarki sweetheart ki yafe min nima ba yin kaina bane ki fahimceni wallahi bana jin son yarinyar nan araina ."
"amman sai kayi mata mummunar fata ?ta fad'a abun na ta'ba ranta ayi ganganci da rayuwar yarinya tankar mai fa adamcy wallahi a tunanina ko dabba na ajiye a gidan nan akayi mata haka bazaka fad'a haka ba bare mutun wacce kasan tana da mahimanci arayuwata" ta qarasa maganar adaidai lokacin da aunty shahida da aunty khadija suka turo kofar dakin suka shigo shiru kawai tayi tana dubansu ."
A natse suka qarasa shigowa cikin dakin sosai suka samu waje suka zauna mami ma ta zauna tana dubansu daya bayan daya "mami kin tashi Lfy?lafiya lau ya kwanan yaran ?"duk suna lafiya suka amsa mami ta dubi babbar diyarta tana cewa "a yau nake sa ran jama'a zasu fara sauka domin zuwa bikin adamcy da maryam amman sakamakon abinda yayi na janye maganar aurensa da maryam ya d'ago kanshi da sauri ya zuba ma mami idanunshi ."
"Ku sheida na yafe masa duniya da lahira yaje ya kawo min wacce yake son ya aura ita kuma mrym in sha allahu zan samo mata wanda zai min biyayya ya aureta" wani sanyi dadi ya lullubesa na farinciki jin maganarta ta farko amman kuma a karshe yaji wani irin tarin damuwa na shiga zuciyarsa matsowa yayi daf daita yana cewa "sweetheart ai na baki hakuri dan allah kiyi hakuri "na hakura adamcy amman da wani abu yaje ya sameta a sanadiyyarka kazo kana murna da jin dadi gara a fasa ."
Shiru yayi ya kasa cigaba da magana "mami dan darajan allah kiyi hakuri tunda yayi nadama har ya baki hakuri sannan babu abinda zai samu maryam zata cigaba da rayuwa kamar kowacce yar adam Kiyi hakuri ki yafe masa kin rigada Kinsan halin adam bai iya magana ba duk maganar data fito bakinsa haka yake cabawa inji cewar aunty khadija wani mugun kallo ya wurga ma mai hade da harara ."
"Me yasa bazai zama mutun na farko da zai ji ciwon abinda akayi mata ba? maryam fa matar da zai aura ce, matar da zai raba duk wani farinciki da akasin haka ce daita ,kuma yaruwa mafi kusanci da rayuwarsa amman ya