Showing 33001 words to 36000 words out of 185716 words

Chapter 12 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4698

zaiyi kuka ?shine mana idan ba fushi kayi ba fad'a min abinda kayi ?shiru yayi kawai dan bai san me zai ce ba dan fushi fushin yayi dan bai ga dalilin da yasa zata dinga tura masa yarinyar da tasan yafi tsana arayuwarsa wanda shi kansa bai san dalili ba ."


maryam ta lallabo ta fito daga dakinsu ta rabe a gefen step "uhm ina sauraronka shiru ne dai ya sake biyowa baya "ina gift din din soyayyar maryam "? ya zaro ido sosai yana kallonta "haba sweetheart wai me yasa kike min haka ne ?"what did I do to you? yayi shiru yana kallonta Kmr zai yi kuka ta sake bude baki zatai magana yayi saurin dakatar daita .
"Dan girman allah sweetheart ki daina hadani da yarinyar nan kin ce na aureta naji na amince yanzu kuma zaki sake hadani da wani sabon aiki kina son na mutu ne tun kwanana bai qare ba ?tai mur mushi irin nasu na manya "mafarkinka bai kasheka ba sai mutun a zahiri ne zai kasheka?"


" adamcy wallahi ka canza rayuwa ina guje maka hakin mata akanka." yay shiru kawai yana kallonta "yanzu sweetheart fatan da kike min kenan ?me nace maka nace ka canza sai kace zaka canza ko ba shikenan ba ,ni ai kasan bazan ta'ba maka mummunar fata ba amman dan allah ka canza kaji masoyi ta riko hannunsa cikin nata shima ya daura hannunsa akan nata " naji zan canza Kiyi hakuri da duk abubuwan da nake yi wanda bakya jin dadinsa maryam ta kasa kunne sosai ko zataji abinda suke tautaunawa amman babu abinda taji dan can kasa kasa suke mgnr zai mike Hjy Zulai tace "abinci fa ?akoshe nake "me kaci dan nasan baka cin abinci a waje ? Kawai dai bana felling cin komai amman da zan samu tea mai dan kauri zan sha ya fad'a a yatsine ta girgiza masa kai alamun taji tare da kwallawa maryam kira "ya salam! ya furta yana dukar da kanshi kasa dan bai so haka ba sam baya son abinda zai shi kallon fuskarta ".a natse ta qaraso tana cewa "mami gani ."


"Dan Allah maryam hadowa wannan sarkin zuciya tea mai kauri "to mami ! ta juya a hankali ta nufi inda kayan tea yake ta hado ta dawo a natse dan tasan halinsa abu kadan Ke hassalashi bare ita data kasance makiyayiyarsa ko batayi kuskure ba zai iya maidashi tashin hankali "mami gashi ,Yauwa maryam sannu da kokari kinji mika masa" tayi Jim tana jin faduwar gaba da tsoron mai tsanani numfashi ta sauke a boye na samun sausauci tunda mami na gurin komai zai zo da sauki bazata bari wani mummunar abu ya same ba ,bazata bari ya tozartata ba no matter how zata tsawatar idan taga zai yi wani abu jiki a sanyaye ta mika masa tana cewa "yaya ga..."Banza yayi tamkar bai ji ba nan kuwa yaji haushi ne yasa bazai karba ba " maza ka karba ka shanye ka miko min cup still kin karba yayi ko kaukauran motsi dainawa ya yi a zaunen da yake ma idan ka kallesa ma zaka dauka baya numfashi ne "ka kar'ba mana "sweetheart bana sha ya fad'a yana fusrzar da iska mai zafi ran mami ya soso tasan yayi haka ne dan maryam ce ta hada "amamn kace zaka sha "yanzu na fasa babu yadda mami bata yi dashi amamn yaki ya karba ya shan akarshe ma ya mike ya mata sallama ya nufi saman dakinsa bata amsa masa ba tabi bayansa da kallo har ya bacewa ganinta gbdy mami ta rasa meke mata dadi shiru tayi tana jin bacin rai har sai datayi datasanin kiran maryam amamn ita tayi haka ne dan su dinga samun kusanci da juna, ganin yadda mami ta shiga damuwa yasa maryam ta zauna inda ya tashi ta fara shan tea tana cewa "mami tunda baya sha bari ni na sha daman cikina empty ne shiru mami tayi tana kallonta ita dai bata fushi akan komai "mami dan allah karki damu kanki akan dan wananan abun da bai ya kawo ba "dole na damu maryam mutun Kmr mai zuciyar dutse ?dan Allah kar wannan abu ya dameki nima da yayi dani ban damu ba wallahi ahankali ta dinga kwantar wa mami hankali ."


Cike da natsuwa ya tura kofar dakin ya shiga ahankali ya zauna akan daya daga cikin kujerar cushion dake dakin dafe da goshinsa yana furta oh my goodness god wai me yasa sweetheart bazata bar zuciyata ta huta da wannan yarinyar ba ?me yasa abubuwa suke faruwa dani ne komai ya zama worst a gareni ?daman har yanzu anayin auren dole ne bare shi daya kasance nmj "me yasa bazaa barshi har zuwa lokacin da yayi raayin ba ?shine tambayoyin da ya dingawa zuciyarsa ya dauki wasu mintuna zaune sannan ya fara cire kayan jikinsa ya shiga bathroom ya watsawa jikinsa ruwa ya fito ya sauya kaya zuwa na bacci ya hau gado ya kwanta shiru yana tunanin wannan auren da mahaifiyarsa ke bukatar yayi bai wani jima ba bacci ya daukesa hannuwansa duka a saman qirjinsa ."


Washegari "10am ya sauko daga bed dinsa yana mika bakinsa dauke da addua kai tsaye bathroom ya shiga yayi refreshing kansa tukuna sannan ya saka wasu hadaddun kaya wando da Riga suit duk brown colour shiru yayi lokacin dayazo saka takalminsa domin kusan lokuta dayawa adaidai wannan lokacin mami ke shigowa dakin akarshe ita Ke saka masa ya numfasa ya shan iska komai nashi tô mach yayi har glass din dake manne da idanunshi ya kwashe wayoyinsa ya sauko cikin takun isan nan nashi ya soke hannunsa daya cikin aljihun wondonsa tare da jin kai yana neman inda mami take "sweetheart ! ya kira sunanta bai ji ta amsa ba ita kuwa tajishi Sarai tayi masa banza dan haka ya nufi hanyar kitchen dan nan yafi tunanin take idanunshi suka sauka akan hjy zulaiheart cikin shiga na alfarma ."
a natse ya shiga kitchen din inda masu tayata aiki suka soma kokarin gaishesa sai dai babu wacce ya amsawa acikinsu wanda daman idan da sabo sun saba da yanayinsa ,ya qarasa ya tsaya bayan mami ya daura kanshi a kafardarta yana mai lumshe lumtsatsun idanunshi "my sweetheart good morning?


"Morning! ta fad'a atakaice tana hade rai
"Hope you had a great night? bansani ba kamar yayi murmushi amman ya maze yana cewa "sweetheart kamshin girkinki so nice tare da kai hannu zai bude kular gabanta "don't open! shiru yayi tsaye shi bai ajiye murfin ba shi bai rufe ba ya sake kokarin budewa "I said don't open "kullum aikin kenan yabon girki amman ..." bai san sanda ya tamke fuska ba ya katseta da sauri "you're worst sweetheart ! naji muje parlour'n tunda ka hanani magana dan ban san abinda ya shigo da kai kitchen ba sai ka gama batawa mutun rai kazo kana salo" ya sake hade rai sosai tamkar an aiko masa da sakon mutuwa "me nayi km ?"Bansani ba wallahi adamcy idan baka kiyayeni ba to tayi kwafa kawai bai sake cewa komai ba ya juya ya fita daga kitchen din ransa a matukar bace dan yasan akan abinda yayi jiya ne yasa tayi masa haka dining ya qarasa ya dauki cup din tea dinsa da chocolate cake yaci duk da shi din ba mai son zaki bane sosai bai jima ba mami ta shirya masa breakfast "your breakfast is ready "am okay ya fad'a ransa a hade sannan ya mike tsaye tun kafin tace wani abu ya fita zuwa haraban gidan ya nufi motar daya bada umarni yana son shiga Range Rover black color driver yajashi suka fita zuwa babban office dinsa kai tsaye ."


*******




Yauma kamar jiya maryam tana zaune akan kujerar mr ATA tare da saurayinta abbas ta tsura masa idanunta tana kallonsa tana kallon yadda yake sauke numfashinsa ,muryarsa cike da kasala ya soma fadin "ina matukar sonki maryam da'ace mutun ya Kan iya shiga zuciyar mutun ya gani hakika da kin shiga tawa kinga irin zallar soyayyar da nake miki amman ni nasan bakya sona maryam kamar yadda nake miki wahalar da kaina kawai nakeyi ."
"yaushe na furta maka bana sonka abbas ?Ko na taba furta maka haka ?ta fad'a tana hade hannuwanta wuri daya tana kallonsa" tabbas da zata tsaida mijin aure cikin masu sonta da aure to data tsaida abbas domin kuwa yafi sauran dama dama kuma ya dan kwanta mata arai "yadda tayi shiru tana kallonsa haka shima yayi shiru yana kallonta yana jin yadda zuciyarsa ke bugawa akanta "me yasa kayi tunanin bana sonka abbas ?ta katse shirun dake tsakaninsu ta hanyar fadar haka ."abbas !ta kira sunansa ya tsura mata ido kawai "kamar yadda kake sona nima ina jin wani abu akan..."


"Shiiii !"shima ya katseta "sam ban yarda da abinda zaki fad'a ba maryam zuciyar dake son mutun bata banza dashi dan haka karki fad'a min cewar kina jin wani abu akaina dan bakyasona maryam , ban ma ta'ba ganin soyayyata acikin kwayar idonki ba sau nawa zan kiraki sai kinga dama Kike dauka ?baki ta'ba tunanin ki kirani a duk tsawon lokacin da muka dauka koda kuwa zan shekara ban kiraki ba , duk wata alama ta soyayya da mutun maryam bakya nuna min hakan kawai ya ishi ne hujja amman ni nasan tabbas ina sonki dan allah karki boye min abinda Ke ran..."


Wayarsa ta soma ringing wanda sanadiyyar hakan ya katseshi ahankali ya dan zame hannu shi ya ciro ya duba dan zabura yayi ganin mai kiransa maryam ta dago ido tana dubansa ya dauki wayar ,bata ji yace komai ba sai "to gani nan ya riko hannun maryam cikin nashi adaidai lokacin da mr ATA Ke qoqarin qarasowa gurin wanda wannan ne karo na farko da hakan ya faru "ki kulamin da kanki na samu wani kiran gaugawa ne amman zanzo dawo zuwa gobe mu qarasa maganarmu ina sonki mar..."giftawar mr ATA ya katseshi tayi saurin zare hannunta dake cikin nashi jikinta na daukar rawa ,abbas ya dan bi bayan mr ATA da kallo sannan yayi mata sallama ya wuce ya bar zuciyarta cikin tashin hankali."




jiki a matukar sanyaye ta shige ciki yana zaune akan kujera kusa da mami sai dai kana kallon fuskarsa kasan yanayinsa babu alamun rahma bata tsaya ba ta nufi hanyar dakinsu mr ATA ya dago lumtsatsun idanunshi da suka canza kala wanda suka nuna tsantsar bacin ran da yake ciki ya zubawa mami sannan ya fara magana a natse sai dai mgnr tattare yake da 'bacin rai byn kmr mintuna goma sai ga maryam tare da nana hauwa'u sun shigo daskarewa tayi agun zuciyarta na rawa ,kamar ta juya saboda rawar da jikinta yake sai Kuma ta sanyawa jikinta jarumta ta cigaba da tsayuwa tana sauraronsu ,
"wallahi da tasan yana parlour'n har lokacin bai tashi ba bazata dawo ba batare da bata lokaci ba ta fahimci maganae da mami keyi akanta ne ."


cikin sanyi jiki ya mike tsaye ya soma taku da kyar fuskarsa har lokacin a murtuke take ya jingina jikinsa da bangon parlour'n yayinda idanunshi ke kallon screen din wayarsa "wa yace ki sake zama
min akan kujera da wani gardin banza har kuna taba juna dan ku din tattun yan iska ne ?tayi tsuru tsuru tana kallonsa hantar cikinta na kad'awa da jin kalmar daya jefesu dashi "wannan shine first and last karki yarda ki sake zama min akan kujeru dan ba dan ke na tanadaisu ba koni sa'anki ne ?"tayi saurin girgiza masa Kai kamar ta durkusa ta bashi hakuri dan ya bar zuciyarta ta hutu sai ta daure taki aikata hakan "ban tanadi kujeruna dan wata gardiya da garden banza su zauna suyi iskanci akai ba "adamcy ! no sweetheart bari na fad'a mata taji ko auta tayi min wannan ganganci sai na ballata wallahi bare wannan useless din ya fad'a yana nunata da babban d'an yatsa hannunsa" idan mutun ya sake min ganganci nima zan masa ganganci aikin banza kawai zuba masa ido kawai tayi tana jin wani zallar bacin rai na ratsata yayinda tuni hawaye ya soma bin kuncinta "yanzu irin mutumin daake son tayi rayuwa ta har abada kenan ? mutumin da duk duniya babu abinda ya tsana kamar ita burinsa bai wuce ya wulakantata ya tozartata ba lallai duk yadda zata gujewa wannan hadin zatayi koda kuwa zai zama sanadin rasa rayuwarta ne tun yanzu ma ya kamata tasan abun yi bazata iya ba ,zuciyarta bazata iya daukar wannan wulakancin ba ta bud'e baki da niyyar kare kanta kar mami ta dauka maganarsa gsky ce taga tuni har ya wucewarsa yana jan dogon tsaki ."




idanuwanta suka ciko da hawaye cikin rawar murya ta soma "ma..mami wallahi abinda ya fad'a ba gsky ba.."kukan da take ya hanata qarasa maganar nana hauwa'u ta matso kusa daita tare da rike kafadunta
"da Allah meye abun kuka bayan kowa ya San halinsa muje please nana hauwa'u ta janyota suka koma cikin d'akinsu tana rarrashinta "Ina ganin lokacin barina gidan nan yayi zan koma Abuja da zama duk sanda yake gidan nan bana samun sukuni"wallahi babu Inda zaki idan yayi miki ki daina nuna kina jin tsoro dan hkn da kike nunawa power kike Qara masa idan yayi miki ki rama duka shekara nawa ya bawa mutune duka fa 9 ne ..?" "naunayen ajiyar zuciya ta sauke "bazan iya daukar shawararki ba sister "manta da wannan maganar yanzu dai ya kuka kare da abbas ?wallahi ya bani tausayi gbdy na kasa fad'a masa gskiya sbd ina dan jin wani abu akansa "kenan kina son shi ?
Ta girgiza mata kai alamun a'a "ina jin wani abu akansa baya nufin ina son shi bane "tunda bakya son ya Adam shi me yasa bazaki bashi dama ba ?"


shiru tayi taki cewa komai "heeeee maryam kiyiwa kanki karatun ta natsu yanzu maza wahala suke karki ga wai iyayenmu nada arzki irinmu wahalar auruwa muke amman Kya kare a auren ya Adam din tunda baki da wanda kike so tana gama fad'ar haka ta d'auki wayarta ta shiga yanar gizo "kisa akawo mana abinci yunwa nake ji sosai ,abincin na fita ci wannan mai dacin zuciyar ya bata min rai " da idanu Maryam ta bita tana jinjina Kai ta d'auki waya ta kira layin kitchen ta bada umarni .
ko cikakken minti biyar ba'a yi ba mutun biyu suka shigo cike da girmamawa suka ajiye tiren abinci da lemun irin wanda suke sha suka juya nana hauwa'u ta bud'e kula ta zuba abinci ta soma cin mrym tana dubanta ."kici abinci mana kin tsaya tunani "jiki a sanyaye mrym ta soma tsukura tana ci tana fargaban sake haduwa da ATA gara tayi ta gudu tun sakon rashin amincewa aurensa ya Isa kunnensa ya sake damarar cin kaniyarta koma asani ne tsanar ya qaru"?


Bayan kwana biyu
Mr ATA na kwance akan kujera mai zaman mutun uku a parlour'n hjy zulaiheart ta samesa ta zauna a kusa dashi ta soma magana cikin sanyin murya "kana son ginawa kanka rayuwa na gari dole sai kayi hakuri shiyasa kullum nake bukatar naga kayi aure domin ka zama magindaci saboda hakan zai sa ka canza , mata da ya'ya zasu canzaka saboda qaunar dake tsakanin iyaye da yayansu , Adamcy ka canza Sam bana jin dadin yadda kakewa Maryam acikin gidan nan ko babu komai Maryam yar'uwaka ce Kai yanzu kana ganin da wannan zuciyar zaka samu macen da zata iya zama da Kai ?bari kaji Maryam ce kawai zata iya zama da Kai saboda tana da zurfinn hakuri sosai ,zata yi hakuri da halinka da wannan zuciyartaka ko dokin zuciya ka hau nayi Imani zata san yadda zata faranta maka ka sauko , ka tausaya min Adamcy Kai kadai Allah ya bani namiji acikin ya'yana banason na mutu na barka da wannan zuciyar ta k'arasa maganar kmr zatayi kuka yayi saurin ya mike zaune daga kwance da yake ya kamo hannuwanta cikin nashi "kiyi hakuri sweetheart karki min haka karki zubar da hawayenki akan wannan matsalar shikenan komai ya wuce ai farincikinki shine nawa inshallahu zan canza Kuma zanyi duk abinda kike so ya karasa maganar yana zamewa ya d'aura Kansa akan saman cinyarta .
Sanyayyayen ajiyar zuciya ta sauke na farinciki ta d'aura hannunta akanshi tana shafa sumar kanshi "Allah yayi maka albarka ,Allah yaye maka damuwarka Allah ya sausauta maka zuciyarka
Allah ya baka zuria masu albarka kuma ya nuna min wannan lokacin, nifa a son raina ma mata biyu naso aura maka a rana d'aya, d'aya diyar talaka d'aya diyar shararran hamshakin mai arziki ."


yayi murnushin gefen baki wanda ita kadai Ke iya ganin hakan ya lumshe lumtsatsun idanunshi yana cewa "lallai sweetheart kina ji dani "sosai kuwa Adamcy nah ai shiyasa kake min salo saboda kasan Kaine zuciyata "Nima kece zuciyata rayuwata sanyin idaniyata Ina sonki fiyye da komai " a hankali suka dinga hira mai kwantar da hankali daga karshe ta d'auke kanshi ta daura masa akan pillow kujera "thank you my sweetheart "you're welcome my happiness ta fad'a tana mikewa ".
Ko cikakken minti ashirin bata yi ba ta had'o masa abincinsa yana ganin dawowarta ya mike
yana murmushi "sannu da hidima dani sweetheart ",yanzu kam sauran kwana nawa na huta ta fad'a ta janyo karamin stood gabansa ta ajiye "bismillah kaci ya narke mata fuska "yau daya kaci da kanka ya lumshe mata lumtsatsun idanunshi kana ya soma ci a hankali "kalli cin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login