Showing 87001 words to 90000 words out of 185716 words
Chapter 30 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
ta yaya kike tunanin zataji dadi ?"ta yaya kike tunani zan iya bata farinciki byn ga inda zata samu fiyye da nawa ."?
maryama ta kalli umma cikin sarewa ta cigaba da magana " umma abun na da matukar ciwo irin ciwon dake cin zuciya da bargo ,ciwo ne da bashi da magani da mafuta har sai ka had'u da mahad'inka , shiyasa a kullum idan na kalli aunty sai naji tamkar tana boye mana wani abu mai mahimanci ga rayuwarta , ashe gsky né hakika bakinta bazai iya furta mana komai akan rayuwarta ba matsawar ita din uwa ta gari
ce , dan allah umma Kiyi min rai ki raba zuciyarta da wannnan rayuwar idan kuma baki yi ba ni zanyi ,zan rabata da nauyin dake daskare a qirjinta ."
Tana gama fadar haka ta mike a hankali tana share hawayen idanunta da suka gagara tsayawa tana jin wani zafi a qirjinta , bazata cigaba da d'aukar wannna nauyin ba , koda aunty bata amince ta koma ga yan'uwanta ba ,lallai ita zata nemosu a duk inda suke acikin garin nan ."muryarta a sanyaye tace "umma ni zan wuce sai da safe " kai kawai ummah ta gyada mata sannan maryama ta fara tafiya umma tayi shiru tabi bayanta da kallo tana kallon yadda take d'aga zara zaran yatsun kafafunta da kyar tamkar wacce bata da laka ."
" A inda ta bar mahaifiyarta anan ta sameta tare da habib suna hira da alamun shi baya cikin damuwa kamar ita." bata tsaya ba byn tayi sallama tace "aunty sai da safe tana gama fadar haka ta wuce ta nufi d'akin baccinta bayanta suka bita da kallo , yanayinta kad'ai ya fahimtar da aunty akwai tarin damuwa atattare daita shiru kawai tayi tana tunani "har yaushe maryama zata yi farinciki arayuwarta ?".
A natse aunty ta mike tabi bayan maryama tana jin tsinkewar zuciya haka shima habib akan kujerar da take zama idan zatai zane suka isketa ta dafe kanta tana sheshekar kuka atare suka qaraso suka zauna abakin gado suna fuskantarta shigowarsu yasa ta tsaida kukanta wanda taso tayisa sosai har taji natsuwar zuciyar."
dogon numfashi aunty taja tare da cewa "na shiga uku ni bilkisu " ta furta cikin tsananin tashin hankali dan bata qaunar abinda zai d'agawa yaranta hankali shi kuwa habib hannun maryama ya kamo cikin nashi ya damke da karfi cikin tsananin tashin hankali " heartbeat meke damunki ?." muryarta a raunane tace "babu komai after dad "ya babu komai zaki shigo cikin damuwa , yanzu mun shigo mun ganiki kina kuka amman kice babu komai ki fad'a min idan akwai abinda ke damunki ."
shiru tayi tana cigaba da shesheka "ki sani bamu saba boyewa juna komai ba idan kika min haka baki min adalci ba ,ko km damuwar dazu ce ? still dai shiru tayi ,sosai suka d'aga hankalinsu ita kuma taki cewa komai sai faman ajiyar zuciya ta saukewa ." damke hannunta ya sake yi sosai yana rokonta "dan allah heartbeat karki daga mana hankali ki fad'a min kukan me kike yi ?kallonsa kawai tayi tana lumshe idanuwanta ganin yadda hankalinsa yay matukar tashi da yadda ya d'aga hankalinsa ya matukar bata tausayi daman kuma haka ne idan daya yana cikin damuwa dole ne daya shima ya tsinci kanshi cikin damuwa."
"Yanzu princess bazaki koyi dauriya akan kowacce irin damuwa bace domin ki tsira da rayuwarki da rayuwarmu gabadaya ,Ke kenan kullum cikin zubar da hawaye akan damuwa me yasa zaki dinga asarar hawayenki tare da qoqarin kashe kanki abanza ."?
"Gara dai ki fada mata gsky aunty domin ita rayuwar nan da take ganinta wani lokacin idan abubuwa suka wa mutun tsanani dole mutu ya rage wasu abubuwa domin tsira da rayuwarsa da lafiyarsa."
hawayen da take qoqarin maidawa ne suka samu nasarar gangarowa bisa kuncinta cikin sauri tashiga gogewa wasu na sake gangarowa duk yadda suka dinga kwantar da kai da murya dan suji damuwarta amman taki fad'a masu komai domin da zarar ta bude baki hawaye da sheshekan kuka Ke hanata magana dole tasa suka daga mata kafa suka fice d'aya bayan d'aya daga dakin da zumar zasu lalla'bata gobe ta fad'a masu dalilin kukan ."
tafi mintuna goma byn fitar aunty da habib zaune sannan ta yunkura ta tashi tana sauke naunayen ajiyar zuciya ta shiga bayi ta d'auro alwala ta fito ta gabatar da sallahr magariba da isha'i tare da shafa'i da wutiri byn ta idar ta koma kan katifa ta zauna tare da jingina bayanta da pillow ta rungume hannuwanta duka a qirjinta ."
ahankali ta runtse idanunta tana tariyo komai daya faru dasu tun suna yara "Kenan adalili rasa mahaifi da kaka yasa rikonsu ya dawo hannun abban sadam ."tun tana qarama yar shekara hud'u a duniya ta taso cikin so daga bangaren abban sadam da umma da mahaifiyarta amman daga bangaren aunty hassana da sauran 'yan'uwan mahaifinta kuwa saboda haushin da kiyayyar mahaifiyata yasa suka dinga nuna masu tsana da tsamgwama , sun ci wuyarsu sosai most especially Ita ganin kiyayyar dangin mahaifinsu da irin tsanar da baba gali yayi masu ya bawa aunty salma damar cin kashi akansu da mahaifiyarta ."
tun daga lokacin kuruciya har zuwa girmanta abinda yake rage mata zafin gidan shine soyayyar umma bancin ita kowa a gidan baya sonsu amman kuma wani lokaci shi kanshi baba gali ya kan tausaya masu in dai ba fad'a sukai da sakina ba ko yarshi qarama ba , idan tayi mata laifi ta d'an daketa shine zai fito da 'bacin ransa har ya fito da zallar kiyayyarsa ,kuma tun da ta lura son ya'ya ne dashi domin ba ita ba ko uwar data tsugunna ta haifesu baya raga mata akan ya'yansa ."
"yayan baba gali uku ne aliyu sakina wacce sa'artace sai mai bi mata salamatu wacce taci sunan hajiya kakarsu ana kiranta da shukura bata fi shekara sha bakwai ba a yanzu ,itama babu yabo babu fallasa suna d'an shiri daita sai dai idan taga uwarta na fushi da zagina bata hanata sai ma dai ta zugata domin itama tana nuna kishinta akainta idan taga umma tana tarairayata ko wani ."
Baba gali dinki yake ada rasuwar abban sadam yasa gidan buredi da rikonsu ya koma hannunsa alhamdulillah babu laifi ita din mai qokari ce ta kowani fanni boko da arabic ga baiwar zane da Allah ya bata ."
Alokacin baya kullum ta allah sai aunty tayi masu special lesson ita da habib kusan kokarinta ta samu ne a wajen mahaifiyarta ,duk unguwar da makarantarsu ana maganarsu akan ilimi bokon da suke dashi haka duk gidan ba masu jin turanci kamar ita da habib ko wani abu za'a tambaya ita ko habib ake tambaya mahaifiyarsu ta tsaya masu akan karatunsu shiyasa ma education dinsu yayi very fast kuma à sanadiyar qoqarinta ita da kawarta subai'a yasa gwanati ta dauki nauyin karatunsu zuwa lagos state university ".
bangaren sakina da sauran yaran gidan matsalar iyayensu ne dan basa maida hankali akan karatun yaransu gashi sam basu da isashen ilimin boko ko Arabic barin ma aunty salma karta ji labari ba arabi ba boko sai uban girman kai ,sau tari idan shukura tazo koyon wani abu a wajenta bata só sai ta nuna ai itama tasani dan me zatazo wajenta akarshe idan tayi mata zero take samu a makaranta shiyasa da yarinyar ta gane ta daina bata idan tace ta kawo kai tsaye take ce mata bataso zero zataci ."
hatta alwala ba daidai aunty salma take yi ba kuma sallah ma bata dameta ba ,tun suna yara baba gali Ke mata fad'a akan tarukun sallah din da take yi amman taki ta daina shi kansa daya gaji sai ya rabu daita ya dinga Kwa'bar yaransa da yin sallah sanin in har dan uwarsu ne sai dai kar su yi babu abinda ya dameta dan idan ma koyi zasu yi daita sai dai su koyi taruku sallah."
Su kuwa aunty bata yarda tana gama dauro alwala zata tura habib zuwa masalaci ita km ta umarceta taje tayi alwala sannan a kullum dare auty ta kan fito tsakar gidan tare dasu har sakina kasancewar tana qaunarta ta koya masu darasin lissafi , tana daukar lokaci akansu har sai taga sun gane sannan ta bukaci wanda yake da damuwa a bangaren karatunshi ko baka da matsala zatai 'yan tambayoyi ana bata amsa idan bata gamsu da amsar ba ta qara yi masu bayani , bangaren karatun alqurni kafin suyi bacci sai aunty tasa sun karanta izawaka da tabaraka kafin su kwanta da safe kuma sai sunyi murajaa alqurni sannan su shirya su wuce school ko islamiyya ."
A ranar batayi isashen bacci ba ga tsananin tunani ga kwadayin son ganin yan'uwan mahaifiyarta gargadin kanta ta shigayi akan fad'awa soyayya da ma ko waye idan kuma soyayyar ta zama dole sai dai tayi a gidan aurenta ga duk wanda ta aura har asuba tayi maryama batai wani yi baccin kirki ba shiyasa kiran sallahr farko acikin kunnenta akayi ta gyara kwanciyar ta koma ta kwanta bacci kad'an tayi ta lalubo wayarta ta duba taga biyar da rabi saura lokacin sallah yayi dan har an tada sallah a matsalacin unguwarsu ."
a hankali ta mike zuciyarta cike da damuwa bakinta dauke da adduar tashi daga bacci ta kai tafukan hannunta tana shafa fuskarta sannan a natse ta zuro kafafunta ta sauko ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito cike da sanyin jiki ta gabatar da sallah asuba byn ta idar ta d'auko alqurni ta soma karatu cikin suratul baqara anatse ta kai idanunta ga window d'akin taga gari ya fara sha tayi azkar din safe tana nan zaune tana lazimi har shida saura sannan ta koma ta kwanta akan sallaya nan da nan bacci mai nauyi ya dauketa ba ita ta tashi ba sai goma saura ."
Ta mike da kyar bakinta dauke da salati sakamakon qirjinta dake wani irin bugawa ta
gyara gadonta ta fita ta dauko tsintsiyar shara
ta share d'akin ta fito har falo ta shiga d'akin mahaifiyarta bata ganta ba tasan may be ko tana byn gida wajen yin wanki ,dan wannan kaida ne kullum safiya sai tayi wanki kayanta wani lokacin da nasu ta share d'akin tasss ta fito da sharan zuwa falo ta shiga kitchen ta hada kayan wanke wanke ta wanke atake ta goge koina ta sharo sannan ta hada da share falo tayi mopping ta koma daki ta cire kayan jikinta ta shiga wanka bata wani jima ba tayi alwala ta fito kai tsaye ta shimfida daddumar sallah ta sallacci salatul duhu byn ta idar ta shirya kanta ta kwanta lamo cikin zullumi ta kamkame jikinta waje daya wani iri take ji a duk gbdy ilahirin jikinta soyayya irin wacce iyayenta sukayi bazata ta'ba yarda ta jefa kanta cikinta ba".
Ta godewa allah daya bata kyakkyawar zuciyar da bata da lokacin maza ,bata jin soyayyar ko wani nmj ta ratsa koina ajikinta ,duk wanda yazo da sunan sonta ya dawo ya gudu bata taba jin haushi ko kewarsa bare ta damu kanta akansa ita fa gsky tafi ganin laifin mahaifiyarta akan abinda iyayenta sukai mata kuma taji dadin mutuwar mahaifinta akan rayuwarsa domin daa kalleta ace ita din diyar dan shaye shaye da neman mata ne wallahi gara mutuwarsa akan rayuwarsa, data dangwama tana masa adduar shiruya allah gara ta qare rayuwarta wajen yi masa addua samun rahmar Allah ."
Da misalin karfe goma sha d'aya da rabi daidai na safe aunty duk ta damu tun jiya rabon tasa maryama a cikin kwayar idanunta ga dai alamun ta tashi dan har tayi ayyukanta na yau da kullum data saba dan ga parlour nan a gyare tsab sai zuba kamshi yake koina tsab daga ita har habib sun kasa samun kwanciyar hankali bare su karya ,sai ma wata faduwar gaban data ziyarci zuciyarsu ."
mikewa aunty tai ta nufi dakinta shima habib ya biyota kusan atare suka shiga dakin har suka shigo maryama batasani ba tana can duniyar tunani tare da rafka uban tagumi da sauke numfashi a hankali ahankali,