Showing 60001 words to 63000 words out of 185716 words

Chapter 21 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4689

mgnr yana d'aga hannunsa sama sannan ya dungule ya naushi bangon falon sai da gurin ya tsage ya tsaya yana huci da kallon wani bangare ."


Baba babba ya tsaya abayansa hankalinsa a matukar tashe " maganarka gaskiya yayanmu suka fi dacewa da aurensa sai dai kayi hakuri dan'uwana bana tunanin da wata manufa zulaiheart ta had'a wannan auren ,idan baka manta ba shekara nawa ana fama da yaron nan akan ya fitar da mata yayi aure bana tunanin zata ki had'a zuria da daya daga cikinmu sannan da kasan kana da wannan burin me yasa baka fito dashi ba ?


Baba qarami bai ce uffan ba illa numfashi da yake sauke da sauri sauri gumi na karyo masa "dan haka kayi hakuri karka bari wannan matsalar ta zamo Silar da za'a samu matsala ka bar wannan burin bayan anyi wannan auren sai ayi maganar a had'ashi da daya daga cikin yaran".
"Kai kare idan ka sake yin min wannan maganar banzar sai na datseka gbdy Komai naka banga ta yadda nawa burin zai zama daga baya ba muddin d'aya daga cikin yarana basu yi nasarar shiga sawun farko ba babu wacce ta Isa ...."
"kayi hakuri ka yafe min ban fad'i haka dan quntata maka ba ya fadi hk kasancewarsa me saukin Kai sannan marason tashin hankali yafi son yayi rayuwarsa cikin salama duk maganar da baba babba yake sam baba qarami bai juyo ba ",shi wannan Karen zai wuce sai kaji daga garesa sai dai ya kamata ka sakin ranka dan wata rana ....saurin d'aga masa hannu baba qarami yayi still bai juyo ba sai dai qirjinsa sai faman bugawa yake Uncle Umar ya juya cike da matsanacin firgici da yanayin dan'uwan nasa ."


sai lokacin baba qarami ya juyo yabi bayansa da wani irin mugun Kallo Idanunsa a waje har sanda takunsa ya kai uku bai juyo ba haka shima baba qarami bai daina kallonsa ba .a sanyaye fahad dansa yabi bayan baba babba zuciyarsa na rawa dan shi kansa ya koka da abinda mahaifinsa yayi ya raka uncle Umar sai dai bai Kai shi har bakin get ba a tsakiyar hanya ya barshi yana bashi hakuri "karka damu fahad na gode allah yayi maku albarka ya amsa da Ameen ya dawo part dinsu da sauri .


falon ya d'auki shiru na tsawon lokaci yana tsaye yana tunanin bayanin daya samu daga bakin dan'uwansa a yanzu wanda yake jinsa tamkar dalma acikin zuciyarsa , "uhmmmm yanzu dai ta nuna mana cewa itace uwar Adam Kuma ita kadai ke da iko akan shi ?sai mugani idan shi din d'an mace ne Baba qarami yay maganar yana jan tsaki a fili tare da watsa katuwar harara da mugun kallo kamar tana gabansa fahad ya d'auki farin glass cup ya tsiyaya masa tattacen ruwan inibi ya mika masa "kasha baba kaji sanyi a ranka yasa hannu ya Kar'ba ya rike shi gam a hannunsa sai dai bai sha ba haka zalika bai ajiye ba."


"zan iya kasheki akan wannan haukan da kika yi zulaiheart domin Ina da tanadi da buri akan adam ya karasa maganar yana filinging da cup din hannunsa a fusace Wanda yasa take yaransa maza da mata tare da matarsa suka sake shiga rud'ani cike da matsanacin firgici suna kallonsa gabansu na faduwa ban da Hindu data samu guri ta kame akan kujerar da mahaifinta ya tashi zuciyarta tafi ta kowa zafi da tuttukin bakinciki tare da shiga tashin hankali" Fahad ...." !
ya kira sunan dansa Wanda aka kira da hkn ya d'ago ya kallesa a matukar tsorace batare da yace komai ba "abinda na fada Ina nufi har cikin zuciyata gara ta bar duniya ko ita yarinyar ta bar duniya akan rasa burina yayi maganar yana nuna sa da d'an yatsansa "wannan shine Karo na sau babu adadi da take kawo mana tashin hankali tun dan'uwanmu na raye dan haka Ina son kasheta na huta da ganinta a doron duniya muddin ba daya daga cikin ya'yana adam zai aura ba ."


daya bayan daya suka shiga kallon junansu cike da mamakin jin furunci mahaifinsu hatta hindu wannan karon atsorace take kallon mahaifinta ta gigita kwarai da gaske "a kullum kokarina naga na kawar daita a duniya darajan halakar da nake son qullawa adam yasa na barta ya karasa maganar a kausashe .yayi taku daya biyu ya tsaya gaban hindu yana kallonta "kece ya kamata ace kin auri adam ba wannan yarinyar ba kije kiyi rayuwa tamkar sauraniya a gidansa ki taka kowa yadda kike so sannan ki juya duk Wanda kika ga dama wannan hannun nawa babu abinda yasani a halin yanzu kamar ya wahalar da zulaiheart ya gigita ta hanyar azabtuwa mai muni ,ya matso kusa da hindu Sosai suna fuskantar juna "wannan karon fuskarsa da murmushin mugunta akanta "ke hindu ko zakiyi iya karfin halin kashe min zulaiheart?


Wani sanyayyayen murmushi ne ya bayyana akan fuskarta wanda mahaifinta ne kawai ya fahimci manufarsa ganin yadda ahlinta suke kallonta a tsorace yasa tayi saurin waskewa tace "baba me yasa kake mgn fiyye da kaida ?gsky sam sam hakan bai dace ba tayi maganar tana kawar da idanunta gefe al'amun bata ji dadi ba gumin da ya tsatsafowa sauran yanuwanta suka shiga gogewa suna sauke numfashi da ajiyar zuciya atare Jin abinda tace daman km ita kad'ai ke iya fadawa mahaifisu mgn kai tsaye batare da shayi komai ba , a hankali ya juya yana taku cikin tsananin damuwa da tashin hankali suka juya gbdy suna kallon bayansa har ya shige bedroom dinsa yana shirya yadda zai kawar da hjy zulaiheart ko mrym daga doron duniya .."


Mmn sudais


๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—
MAR'ADAMS
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.



Page 13




"Baba qarami na kwance har kusan tsakiyar dare ya kasa runtsawa dan sam bacci yaki zuwan masa sai faman juyi yake akan makeken katifarsa ,yayinda matarsa hjy aljannatu ke d'akinta kwance tana sharar bacci amman shi kuwa baba qarami sai tufka yake yana warwara ya d'an zabura ya mike zaune daga kwanciyar da yay, ya had'e hannunwansa duka waje d'aya "babu tantama hjy zulai tana da manufar had'a wannan auren yasan tayi haka ne dan kar wani acikinsu yaci arzikin d'anta , kunga idan ta had'asu aure da diyar d'anuwanta dole dai arzikinsa yana tare daita , dan da zarar mrym ta haihu dashi komai na adam zai dawo nata gbdy zuwa yanzu dai bai san abinda ya kamata yayi ba ko hanyar da zai bullo masu a maida auren Kan diyarsa ."




Sosai kwakwaluwarsa tayi zurfi cikin tunani neman mafuta har bai san sanda hindu ta shigo d'akin ba , ta matso kusa dashi ta tsaya tana jijjiga baba qarami wanda yayi nisa cikin duniyar tunani "baba baba !! " ta kira sunansa har sau biyu ajere sannan yayi firgigib ya dawo haiyacinsa " wai meye haka baba?" me yasa zaka damu kanka akan wannan 'yar qanqanuwar matsalar ?" baba qarami bai iya amsa wa ba sai zuba mata rinannun idanunshi da yayi yana dubanta har lokacin yana maimaita abinda ta fad'a " ai a wajensa wannan ya wuce gagarumin matsala ba qanqanuwa ba ko ita kanta tasan da zaman haka ta dai fad'a ne dan kwantar masa da hankali shi kuwa hankalinsa bazai ta'ba kwanciya ba matukar ba ganinta yayi a matsayin matar adamu ba ."


"Dan girman Allah baba ka kwantar da hankalinka mubi komai a hankali idan muka bari suka fahimci wani abu attare damu bazamu iya nasara akansu ba " cikin wani irin murya mai gyaraye da tashin hankali had'e da rud'ani yake furta "bazan iya ba hindatu , bazan iya kwantar da hankalina ba muddin ba ganinki a gidan adamu nayi a matsayin matarsa ba ,maganar aurensa da mrym ta dokeni fiyye da tunaninki ,Allah Allah nake gari ya waye naje ga zulai ayita ta qare domin kece kika fi dacewa da Adam ba wannan yarinyar ba dan wannan tsantsar muguta ne kawai take son nunawa"kai dai baba ka dan boye damuwarka baba" .




D'akin ya d'auki shiru tamkar babu wasu halitta acikinsa sai na qara ac dake aiki da kuma saukar numfashinsu haka zalika baka jin motsin komai daga sai na tsuntsaye dake shawagi kasancewar a gra suke hindu ta sauke numfashi tana mai kamo hannunta mahaifinta cikin nata "idan kaje me zaka cewa mami akaina ? " zan so nasan abinda zakace baba idan ma hali kaje tare dani ayi komai akan idanuna shekaru sha biyar kenan , tun inada shekaru sha shida nake dakon soyayyarsa bazan iya jurar rasashi ba, bazan zuba idanu wata ta mallakesa ba "zan fad'a mata komai akan soyayyarki ni ko ta biyu ce kizo bazan damu ba burina ki kasance matsayin mata acikin gidansa , ki zama tmkr sauraniya, ki yi yadda kike so nima nayi yadda nake sรณ da kamfanunuwansa ."" nan take ta had'e fuska tamkar dariya ba muryarta a kausashe ta cigaba da mgn "muddin a ta biyu zanzo nasan bazai ta'ba aurena ba , ya adam fa yana da tsari acikin rayuwarsa shi din ba mutun bane kamar sauran mutane bashi da raayin tara mata "wa yace miki bashi da raayin haka ? zai yi raayi dan uwarsa Allah dai ya kai mu gobe tare zamu wajen uwarsa kafata kafarki ."


Baba qarami ya mike tsaye ya goya hannunwansa abaya yana girgiza kai yana duban hindu kafin daga bisani ya matso kusa daita sosai ya soma mgn can kasa kasa kusan mintuna goma yana mata mgn murmushin jin dadi nรฉ ya bayyana akan fuskarta " idan bata yarda ni na zama matarsa ba I will killed mrym idan ni ban samesa ba to babu wacce zata mallakesa anan gidan duniya yadda take mgnr zaka fahimci da gaske take kuma har cikin ranta abinda take nufi kenan ganin byn maryam ."


Washegari da misalin karfe goma na safiya a kofar shiga bangaren hjy zulaiheart tayi masu kai tsaye a babban falon gidan suka iske mami zaune yayinda d'aya daga cikin masu aikinta ke zaune tana mammatsa mata yatsun kafafunta sallamarsu baba qarami tasa mami dauke idanunta daga Kan tv ta maida kansu tana sakin fuska sai dai kallo d'aya tayi masa ta fahimci akwai damuwa atattare dashi ,aranta tayi addua allah yasa ba wata matsalar bace ta taso , ta amsa sallamarsu tana cewa "sannuku da zuwa !" baba qarami ya samu waje ya zauna akan kujerar dake fuskantarta yayinda hindatu ta zauna a kasa kan kafet a gaban mami ta sunkuyar da kanta kasa tmkr mai neman gafara tare da gaishe da mami cike da ladabi ta amsa tana mami ta maida hankalinta ga baba qarami tana nazarin fuskarsa sannan ta kalli yarinyar dake zaune a gabanta tace "salaha tashi kije Ki bamu guri cikin sauri yarinyar ta mike tare da fadin "tรด !"


Mami ta sake maida hankalinta sosai garesu sannan ta fara magana a natse "baba qarami fatan dai lafiya dan naga yanayinka ba kamar yadda na saba ganinka ba yace "lafiyar dai da sauki "ta gyara zamanta cikin tsananin damuwa "daman dai na lura da hakan dan ba haka yanayinka yake ba kai din mutun ne mai faram faram duk sanda za'a ga fuskarka cikin murmushi take tรด ina jinka fad'a abinda ke tafe da kai ."


Naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana sake gyara zama yace "zulai jiya baba babba yazo min da wata magana akan hukuncinki akan Adam" ta gyada kai tana sauke numfashi "haka ne nasan zaka fi kowa jin dadi "tabbas naji dadi sai dai wani hanzari ba gudu ba nima na dade ina son had'asu aure da hindatu "mami tayi shiru tana dubansa da hindu dake zaune tana nazarinta tana son gano wani abu atattare da hindu domin dai ita din macece mai tsananin baseera tare da saurin karantar mutun sai data numfasa sannan tace "ita hindatu tana son shi ne ?


"tabbas tana tsananin sonshi na tsawon shekaru tunda tashi da soyayyarsa ta tashi ni ne mutun na farko data fara sheidawa da fari na nuna mata illar rayuwar data jefa kanta na afkawa soyayya da qarancin shekarunta alokacin na tmbyeta meye dalilinta na son shi ? me ya dauki hankalinta akanshi ? tace ba dan yana dukiya da kyau ba ,yau da zai wayi gari bashi da komai bashi da hannu bashi da kafa koda akan titi zasu rayu zatai rayuwa dashi kawai son shi ta keyi dan Allah alokacin shekarunta shashida nรฉ kawai wanda ni nake ganin bata san ma me take ba bama tasan meye soyayyar ba yasa take fadin haka ahankali baba qarami ya fayyacewa mami komai akan soyayyar da hindu ke ma ATA babu abinda ya rage numfashi mami tayi ta saukewa tana girgiza kai cikin tausayawa tana kallon hindu data sake dukar da kanta kasa sosai ."




"Masha allah naji dadin wannan abu sosai soyayya mai hade da zumunci allah ya bamu ikon sada zumunci dan allah ba dan kwadayin ko neman wata biyan bukata ba ". ta sake numfasawa ta cigaba da magana "nima daman tun farko burina kenan adamcy yayi aure biyu" ahankali baba qarami ya kalli inda hindu take wacce mgnr mami yasa ta dan dago kanta mami ta cigaba da magana "zan yi iya kokarina hindu na kawo karshen damuwarki duk da adamcy baya da raayin ajiye mata biyu amman zanyi convincing dinsa domin kawo farinciki arayuwarki da yarda allah ."


da sauri hindu ta kalli mahaifinta shima din ita yake kallo domin dai yasan diyarsa da tsananin kishi zata fi bukatar ganin ita kadai ta mallakesa Kmr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login