Showing 153001 words to 156000 words out of 185716 words

Chapter 52 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4701

da zai mata dan kallon yayanta take masa tunda mahaifinsa yace ta daukesa tmkr mahaifi kunga kuwa dole ta daukesa matsayin yaya agareta muryata a sanyaye tace "nima ina da tmby idan kayi naka ka gama ?ya danyi taku kadan yana shirin barin wajen domin canza waje" muje daga can ta biyosa cike da natsuwa cikin tafiyarta kamar bata son taka qasa ."


Ya tsaya tare da tsura mata idanunshi ya gyara tsayuwa hade da rungume hannunwansa a qirji "Kinsan tambayar da nake son nayi miki ?ta girgiza masa kai tana mai sake dukar da kanta "kina da saurayin da kike so ?ta dan dago idanusu suka tsarke cikin juna tayi saurin dauke nata tana cewa "acikin ranta kar dai abinda nake tunani ne zai tabbata ?kamar tace tana da mlm yahuza dan saukakawa kanta sake shiga wata rayuwa amman sai ta tsinci kanta da ce masa "a'a bani da kowa kin san kuwa kina da kyau sosai ?tace ina dai ji mutane na fad'a amman ni dai nasan bani dashi ,kiji tsoron allah yadda yayi maganar yasa tayi murmushi har fararen hakoranta da wushiryarta suka bayyana ."


"Kina da matukar kyau ,Ke rayuwarki ce kawai a irin wannan area amman siffar ki da halinki suna manyan unguwa ne kinfi dacewa da zaman acan nasha mamakin dana ganki anan ?tayi murmushi "to saboda me zakayi mamaki dan na kasance a irin wannan unguwar ?",su mutane dake rayuwa acikinsa su ba mutane bane ?ya sake tsareta da idanunsa ganin karfin halinta akan maganarta "har wani dagewa kike da tmby okay ai an kusan daukeki tunda baba ya amince ?




Shiru tayi tana nazarin maganarsa ai an kusan daukeki tunda baba ya amince domin kawar da maganar tace "dady yace zaka fahimtar dani wani abu me zaka fahimtar dani ?yayi shiru murmushi akan fuskarsa yace "matsalarki kunya ni kuma tsoro ta dan yi Jim ,a ina na zama matsala ?bai bata amsa ba sai kallon gabansa daya cigaba da yi daga bisani yace "ni baki tmbyeni ko ina da yammata ko bani dashi ba ?ta dan daga kafadanta alamun babu ruwanta da hakan domin wannan babbar maganace tama fi karfinta me ma ya kai ta ga wannan tmbyr ? "kodan saboda baki damu da yayanki ba ?


"A'a?
"Ya a'a da kin damu dani nasan zaki tmby ko yaya abinda ya shafi rayuwata mussaman Kiyi koyi da irin tmbyr danayi miki akan samari " nan da nan taji wani iri da alamun zai yi rigima da jan magana idan ba haka ita ina ruwanta da wasu yammatansa "karkiji da wai sai kin mun irin tmbyr da na miki zaki bar nan idan ba haka sai dai na tasa keyarki na wuce dake " ta zaro ido tana kallonsa da mamaki wannan shi ake kira karfin hali barawo da sallama "to shikenan bari na tmbyeka sai dai ba tmyr ka zanyi akan kana da yammata ko baka dashi ba dan nasan kana dasu aruru wata killa ma kullum sai kayi budurwa sama da hudu "dariya mai dan sauri yayi yana kallonta "lallai sai kace wani na mamajo yadda ya fadi mgnr ya bata dry dan hk daga dryr bata sake cewa komai ba sai shine ya cigaba da cewa "ni nan da kika gani matsoraci ne tsoron mata ne dani ban ta'ba cewa ina son ko mace daya ba ,ba dan kuma bana ganin wadan da nake so ba sai dan kawai dana tunkaresu da maganar sรณ sai naji gabana yana faduwa ."


Murmushi tayi "lallai ka cika matsoraci ta fad'a acikin ranta ya dan kyaleta amman gashi momy ta gaji da zamana haka ta samomin wacce zan aura "gsky kaji kunya kai yanzu mata ma kake jin tsoro a yadda zamani ya samu cigaba,sai kana yiwa mace kallon macen arziki sai kaga ashe ba haka bane ta dan yi jim ,"ina tmbyrka a ina matsalar take kace matsalarka tsoro ni kuma kunya a wani fannin kenan ?shiru ya biyo byn tmyrta har ga allah bata kawo komai ba saboda bata tunanin hadadden saurayi kamarsa zai ji wani abu akanta har ma ta burgesa sam bata kawo akanta ba haka take biyewa zancensa ."




Ya katse mata tunani da cewa "daace zuciyar kowa zata fitar da matsalarta dana tabbatar zamu samu fahimtar juna har ki fahimci dady da kuma kin gane zabin da momy ta tay min "tayi shiru a ganinta mgnrsa bata dace daita ba bata san komai akan rayuwarsa ba ya sake katse mata tunani "kin shirya cire kunyar ki ni kuma na cire tsoro dan ki samu amsar tambayoyinki .?ta dan tabe baki " ni wai waya fad'a maka ina da kunya ya zaro ido "Subhallah Au baki da kunya ?tayi murmushi "to ai kaine wallahi ni ne wallahi me ?"wai na cire kunya sai kace kunyar takalmi ce ya danyi murmushi ya tsaida idanunshi akanta ita ma shi take kallo dan tana tunanin zai fadi matsalarsa ne ganin yaki dauke idanunshi akanta yasa tayi qasa da idanunta ta fara shan jinin jikinta domin irin kallon da yake mata mai fassara ne ."






"Maryama wacce momy na ta zabar min ita ce daidai da rayuwata kuma tana kusa dani yardarta abbana yake nufin a matsayin na fahimtar daita soyayyata ya dan gyara tsayuwa "kece zabin abbana kece zabin momy sannan kece zabin kanwata ta sauke kanta ta qasa tsayuwar da kafafuwanta wata shuumar kunyarsa ta mamayeta ji take tmkr ta nitse a wajen daman manufarshi kenan agareta amman ta tsayar dashi tana ta dogon zance dashi ya qara fuskantarta "kece kadai naji duk duniya tun a kallon farko soyayyarki ta doki zuciyata da wani shauki ganinki a karon farko kaunarki ta mamaye ni yardarki itace yarda da abba yake nufi ki bani yardar soyayyarki ni kuma zan nuna miki hallacin so zan fayacce miki irin soyayyarki da take cikin raina ."




Kamar ruwa ya cinyeta haka ta koma a wajen tmkr ba itace Ke hira ba ita kanta hirar datayi a awaanin abaya datasanin yinta take ,da kyar ta daga idanunta ta kallesa ganin gbdy idanuwanshi suna kanta yasa ta sake gyara mayafinta "ki daure ki sanar dani abinda zanjewa da momy domin ta samu sukuni momy na tana matukar qaunarki kullum tana kewarki da alfahari da halinki domin tace bata ta'ba ganin diyar talakawa da irin jarumtarki ba fannin hali da tarbiya da ina ganin momy ta dauki abun da zafi amman ganinki ya tabbatar min ni kaina zanyi alfahari dake idan kika kasance mata agareni kin dace da rayuwata ."




Hakikanin gsky sai dai taki yusif saboda gudun rashin tabbacin samunsa ba dan bai cancanta ba har zuciyarta kalamansa sun dan wanke mata mikin dake daskare a zuciyarta na rashin mlm yahuza da abinda akayi mata amman duk da hk bazatai ganganci amsar wata soyayya a yanzu ba ina ma tana da tabbacin samunsa ? kinyi shiru kice min wani abu "batare dasanin ba kawai taji kalmar allah ya tabbatar mana da alkairi,kenan kin amince zaki auri matsoraci ?kai ma ka yarda zaka auri mai kunya tana gama fadar hk ta bar wajen da d'an saurinta ta boye abayan windowsu tana sauke numfashi ita ba wai tana jin sonshi bane aa ta gaji da rayuwar gidansu km tana son ta dauke mahaifiyarta daga cikin gidan suyi rayuwar farinciki kuma taga alamun zata samu a wajen Yusif ,"


Da zasu wuce aka shigo da kayan abinci masu uban yawa umma ta kara masu godiya yayinda maryama bata bari sun qara yin wata hira da Yusif ba duk da shi yaso suyi sallama amman taki duk mutanen gidan suka fito har yammatan gidan a tunaninsu zai ce yana sรณ nan kuwa basu san tuni ya gama amayar da abinda ke ransa ba, suna tsaye a tsakar gidansu daga nan maryama bata qara taku daya ba ta koma side dinsu har bakin mota suka rakasu baba gali bai saba boyewa aunty salma komai ba dan ya kwashe abinda ya faru ya fad'a mata sakina na zaune tana jinsu aunty salma tayi shiru hankalinta a matukar tashe tace kai wani irin mutun ne da bai san ciwon kanshi ba ? ga sakina bazakayi mgnrta ba gsky wannan hadin bazai yuwu ba kenan rasa yahuza ma cigaba ya kawo mata ? "to ai kece da baki ruguza mgnrsa ba ai da dole cikin yayanki zaa aura shiyasa naso ki barta dashi Ke kuma kika matsa ."


"Tรด ai sai ka nuna masu akwai wanda take so idan yaso duk abinda akayi akan mlm yahuza sai a kwance kaga dole nasan zai dauki shukura ko sakina tunda iyayensa anan suke son ya zabi matar aure baba gali yayi shiru aikin gama dai Ya gama shiyasa komai nake gaya miki ki dinga bi ahankali gashi nan da kanki kin rusa rabon yayanki dan da tuni yusif rabon yayanki ne aunty salma tayi shiru tare da cewa "yanzu ma bata baci ba nan da dan wani lokaci kadan zai fasa ya kalleta ai nasan zaki iya amman hakan zai sa iyayensa su gane akwai wata sannan mutane ma zasu zagemu ."tsaki taja kai ka damu da wannan in har kana son yayanka da arziki ya zama dole wannan karon ka bani hadin kai baba gali yayi murmushi to ai ki bada himma da haka suka kawo karshen hirarsu tรก tashi ta dauki mayafinta ta nufi gidan alfa




Tayi saa bata samu kowa ba duk abinda ya faru ta sanar dashi yayi murmushi yace "kada ki damu Ke ai mutumi yar arziki ce bakya rabuwa damu duk runtsi kuma da yarda allah zan taimaka miki ki tashi kije ko kaffara bazan yi ba wallahi sai yusif ya auri sakina ko shukuran Kike so ,cikin farinciki ta koma gida duk yadda sukai da alfa ta sheidawa baba gali ya kuma yi murna dan shi kanshi da baya son tana zuwa bin malamai dan yasan har dashi takewa amman yaji dadin na wannan karon tunda yar shi guda jininsa zata taimaka ."


duk mutanen gidan suna zaune a tsakar gida Maryama na zaune kusa da umma ganin kamar zaa tautauna akan yusif yasa ta yunkura ta mike nan kuwa taji sun fara tautaunawa akanshi tana tafiya tana tsinkayo maganarsu har tayi nisa ta daina jin komai ."da misalin karfe tara na dare sai ga kira daga baba gali bata kawo komai aranta ba sai mgnr yusif zai mata ,tana isa ta gaishesa ya amsa yana gyara zama yace "wai me ya hadaki da mlm yahuza ne ?tambayar tazo mata a bazata domin irin haka bata ta'ba hadata dashi ba, koda suka rabu bai kirata ya tmbyeta ba sai yanzu data manta dashi tace "babu komai dan ban san abinda nayi masa ba daya canza da shukura" to ai ba soyayya bace a tsakaninsu da shukura ita kanta salma rashin fahimta ne ku dawo Kmr yadda kuke dan dazu da kanshi yazo neman ki"




"Nemana kuma me kuma zai min ai ni na rigada na yafesa har abada ,aa maryama ban sanki da fushi ba Kiyi hakuri idan ya dawo ki samu ku sasanta kanku kinji bai kamata ba dama shi irin wannan sabanin ai dole yana zuwa a mijin da zaka aura ,ido kawai ta zuba masa kafin daga baya ta sunkuyar da kanta kasa ahankali ta furta to "baba ina kuma alqawarin da kayiwa abban kausar ?yayi shiru yana dan nazari "maryama da na zama qaramin mutun ta bangaren mahaifin mlm yahuza ai gara na zama ta bangaren alqasim maude domin shi zai min uzuri kuma idan na hada yusif da yaruwarki sakina ko shukura nasan komai zai wuce ."


Tayi shiru kawai hawayen takaici suka nemi zubo mata daga idanuwanta gbdy ta rasa abun yi kawai ta mike ta koma banger su ta fad'a dakinta ta kwanta ta kudundine kanta ta fara rusa kuka mara sauti dan tasan wannan ma ya zama ba rabonta ba tunda ma baba da kanshi ya furta mata haka yanzu ita hk rayuwarta zata qare cikin kunci da wahala "me ta tsare masu da basa qaunar cin gabanta? duk wani abu da suka san zai zama cigaba arayuwarta basa so ."




Mmn sudais


๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—
MAR'ADAMS
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 25


Allah sarki maryama kwana tayi kuka har sai da garin allah ya waye sakamakon haka fuskarta ta kunbura ita kanta ta rasa dalilin me yasa take kuka rashin yusif da zatayi ne ko kuwa dawowar mlm yahuza ne ?a zahirin gsky duk bbu ko daya aciki dalilin zubar hawayenta ,zubar hawayenta bai wuce na rashin qaunar da baba gali yake nuna mata kiri kiri ba, lamarinsa yana mugun daure mata kai ."




Tarasa gane kanshi ,mai hakan yake nufi da aikatawa? anya ma kuwa baba gali yana cikin haiyacinsa dan kwananan abubuwan da yake sun qara shan bambam dana da ? al'amarin ya damu maryama har yasa kwalkwaluwar kanta Ke neman tarwatsewa ,da gaske dai baba gali da sauran dangin mahaifinta basa qaunarsu sai ma a yanzu ta qara gane cewa ba dalilin haduwar iyayenta bane silar qiiyayyarsu garesu daman can basa qaunar mahaifinsu ."


Babu kuzari ajikinta haka ta tashi da safe aunty da habib suka damu sosai da ganin sauyi atattare daita idanuwansu na kanta lokaci zuwa lokaci suna lura da damuwar da take baibaye daita sai dai basu ce mata komai ba sanin ko sun tmyeta zata fad'a masu babu komai, amman ita maryama tana lura da yanayinsu nason yi mata magana ."


aikinta data saba na safe tayi bayan ta kammala ta shiga wanka wanda zuwa lokacin Auty ta gama girki ta fito cikin doguwar rigar tana zama aunty ta kawo mata nata abincin tasa abincin agaba tana tsakura yayinda zuciyarta ke mata tuni da abubuwan da suka faru jiya atsakaninta da yusif ta jisa dabam akan mlm yahuza ,ko kadan zuciyarta ta kasa daina tunaninsa ba wai dan tana sonshi ba dan gsky daga haduwarsu jiya bata ji cewar tana son shi ba ta dai amincewa aurensa ne saboda ta samu saukin rayuwa ,soyayya kuma tasa aranta bayan sunyi aure zata so shi daman ita kuma ba dabiarta bace saurin zurmawa soyayya ."


Tana tsakurar abinci sannu ahankali har taci rabi ta dauki plet din da taci abincin ta kai inda suke yin wanke wanke ta dawo ta nufi hanyar dakinta tana qoqarin shiga aunty ta kira sunanta cikin muryarta mai tsananin tausayawa agareta ta juyo a natse tare da amsawa sannan ta dawo inda take zaune ta durkusa agabanta ,aunty ta dubeta sosai ta sauke numfashi tace "yanzu princess har akwai damuwar da zata dameki ki kasa fad'a min ?


Nan da nan ta rikice domin dai bata son fad'a mata komai sannan bata son tasan ma tana cikin damuwa dan ita a ganinta gara ta boye damuwarta muryarta a matukar sanyaye tace "aunty ai bana boye miki komai kuma Kinsan idan akwai abinda Ke damuna kece mutun ta farko da zan fadawa tunda bani da wacce ta fiki ko babu komai adduarki nada matukar mahimanci agareni "yanzu zaki iya rantsewa da Allah babu abinda ke damunki ."?


Maryama tayi shiru dan bazata iya rantsewa ba kuma bazata iya sanar daita ba dan zata fita shiga damuwa ita kuma bata qaunar ganin damuwarta wallahi akan taga aunty cikin damuwa gara ita ta qare rayuwarta aciki ,duk maganar da aunty ta keyi ba tace uffan ba illa ta sunkuyar da kai kawai tana sauraronta zuciyarta na karkarwa , duk yadda aunty taso taji wani abu daga bakinta amman taki ita dai ta karbi qaddarata na rashin yusif."




Haka ta kasance acikin gidan zuciyarta babu sukuni kwana uku da faruwar abun sai ga mlm yahuza yazo gurinta har da bata hakuri yana mai jinjina abinda yayi mata ,yace shi kanshi yayi mamakin abinda yayi ,wai shine yake kin kulata kuma shine yayi soyayya da shukura ? yana magana Kmr zai yi kuka wanda ita ahalin da take ciki bata jin tausayinsa kuma bata jin zata karbe shi ta barwa duk wata mai so kai auren ma ta hakura dashi har abada ."


duk hirar da yake mata baya mata dadi wani irin tsanar shi taji yana shigarta sannan duk nacinsa haka ta wuce ta barsa ta koma cikin tana tunanin yadda alamarin zai kasance shin idan yusif yaji hukuncin baba gali ya zai yi ?."zai amince ne ko kuwa dai shima zaa kawar masa da tunaninsa ne kamar yadda akayiwa mlm yahuza? " bani da gata bani da kowa sai allah da kuma mahaifiyata ta sheidawa kanta haka ."


"mai zai hana ki fadawa mahaifiyarki gskyr lamari sannna ki tashi tsaye da addau zuciyar ta ,ta fad'a mata haka? zan dai tashi da addaua amman bazan iya fadawa aunty komai ba dan zata fini shiga damuwa gara idan maganar ta fito taji daga sama ta kwanta shiru tana kallon saman dakin hawayen na gangarowa ta gefen idanunta ."




Kuka take har da shesheka wanda bata ma san sautin muryar kukan na fita ba, cikin haka aunty ta turo kofar dakin ta shigo ganinta haka yasa taji wani gagarumin tashin hankali da sauri ta qaraso kusa daita ta zauna tana kiran ainihin sunanta "maryama !
a matukar firgice ta dawo natsuwarta ta mike ta zauna tana goge hawayenta da hannuwanta duka ,aunty ta tsura mata ido kawai tana kallonta dan gbdy rasa abinda ke mata dadi arayuwarta take idan taga maryama cikin damuwa ."


A dan fusace tace "kukan me kike yi ?wani irin bugawa qirjin maryam ya shiga yi nan take ta shiga kokuwa da numfashinta dake barazanar daukewa sakamakon kukan da take sannan ahankali ta shiga girgiza wa aunty kai alamun babu komai "babu komai kike kuka haka maryama ?"yanzu bazaki fad'a min damuwarki ba ?"Ke kenan kullum cikin damuwa cikin zubar da hawaye nasan acikin kwanakin nan akwai abinda ya faru wanda kike boye min meye shi sannan waye yazo wajenki ."?


hawayen da take kokarin maidawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login