Showing 90001 words to 93000 words out of 185716 words

Chapter 31 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4699

da sauri suka qarasa gareta dan yadda suka ganta ya matsifar daga masu hankali fiyye da jiya dan har wani doguwar rama tayi atare suka kira sunanta suna tmbyrta "wai maryama menene damuwarki ne ?"


"heartbeat banason ganinki cikin damuwa saboda duk duniya babu wanda nake so byn Allah da aunty sai ke karki bari tunani yasa mu rasaki ya fad'a idanuwanshi na kanta "bansan me yasa kike son kashe kanki akan damuwa ba wanda ni a tunani kowace irin damuwa ce zaki iya hadiyeta". aunty ta qarasa maganar tana furzar da iska me zafi daga bakinta a hankali ta mike ta koma kan kujerar aikinta ta dauko farar takardar daya ta ajiye akan table domin samun damar cigaba da aikinta ta zaro pencil har kala uku ta fara zane sai dai zuciyarta rawa take nan da nan idanunta suka cika da ruwan hawaye tarasa dalili daga jiya zuwa yau ta sake rasa sukuni da farincikinta, bata jin shaawar komai babu abinda take so da bukata kamar ta kadaice kanta ."


Aunty ta dakatar daita daga abinda take tana dubanta zuciyarta na mata wani irin suya a game da halin da take ganin maryama din ciki wanda bata san silar faruwar haka ba maryama bata dago ta kalleta ba ta cigaba da abinda take gbdy kamaninta ya canza ,ahankali habib ya shiga rarrashinta da nasiha mai kashe jiki gbdy fuskarsa ta canza Kmr zai yi kuka , Ita kam aunty kasa furta komai tayi ta zuba masu idanunta tana jin tarin damuwa ganin hk yasa maryama ta soma magana kamar bata son yi "abinda muka bukaci Auny ta fada mana taki jiya umma ta fada min babu abinda ta boye min sai wanda batasani ba." ta karasa mgnr tana dago kanta Tare da sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ta sakin wani sabon kuka lokaci daya shima kwayar idanunshi suka kada suka canza nan take yaji tsanar dangin aunty ya shigesa kasamcewarsa nmj kuma duk nmj dole yayi kishin mahaifinsa nan take ya yanke cewar a zuciyarsa bazai furtawa aunty komai akan yanuwanta ba koda kuwa ita kanta uwar gayya ta amince zata koma garesu amman shi babu shi babu su har abada ."


"Tô princes kinji kadan daga cikin tarihin rayuwata kuma ina fatan kin gamsu ?shiru kawai maryama tayi tana kallonta tare gyada mata kai "good my princess kinga rana ya fara ki tashi kici abinci ki kwanta ki dan huta kafin lokacin sallah yayi ta fada tare da mikewa tsaye "yanzu aunty haka rayuwa zata cigaba da tafiya ?tayi maganr cikin raunin murya aunty taja ta tsaya tana dubanta tare da nazarin maganarta "ina nufin haka zamu cigaba da rayuwa batare da kin san matsayinki a wajen iyayenki ba ?


"karki damu dan ni har yanzu bana bukatarsu arayuwata ina ganin kuma ku ciresu acikin zuciyarku "ni daman a yanzu dana gama jin komai na ciresu araina dan basu da wani amfani a wajenmu gara mu qarasa rayuwarmu haka batare dasu ba "haba habib me yasa zaka fadi haka shikenan ita aunty haka zata qare rayuwarta ? kai yanzu zaka iya rayuwa babu ita da kake goya mata baya ?"tayi maganr cikin tsananin fushi "kai daya kamata mu taru mu shawo kanta shine zaka ce haka .?"


guntun numfashi ya sauke yana cewa "lallai heartbeat kina da aiki mutanen da suka wulaqanta mana mahaifi dan kawai talaka ne shine zamu tashi muje wajensu alhalin bamu da komai muna nan dai a yadda suka san mahaifinmu babu wani cigaba da muka samu gsky ni bazanje inda suke ba kuma har abada "gsky habib ya kamata ka tsaya kayi tunani da kyau abinda ubanka yayi bai kyauta ma iyayen aunty ba, ni nan naji dadin dana girma baya raye wallahi da cigaba da ganin rayuwarsa gara mutuwarsa a wajena ."kallonta habib yayi yadda ta zuba masa idanunta cikin bacin rai tana fidda numfashi da kyar "ni babu wani tunani da zanyi akan wannan matsalar ke ma kuma ki bar magana a iya nan dan banga abinda zai sa naje gurin makiyanmu ba kuma ni banga abinda mahaifinmu yayi ba daya cancanci tozarci irin wanda akayi masa ba tun kafin ya qarasa maganar qirjin aunty yayi wani irin bugawa da karfi duk da bata bukatar iyayenta arayuwarta amman bataji dadin kalmar habib din ba ."


"wallahi wallahi habib idan ka sake furta wannna kalmar zan balain baka mamaki "kinga ni tafiyata ya nufi kofar fita yana cewa "allah dai ya baki hakuri amman babu abinda zai kai mu gurin makiyanmu ya qarasa fita ,jikin aunty yayi sanyi ta bude baki zata yi magana sai kuma ta kasa cewa komai "aunty !.
maryama ta kira suannata ,a hankali aunty ta motsa lip's dinta "naam !"karki dauki maganar habib da mahimmanci domin shi yaro ne ke uwa ce da muke kallo muke koyi daita kuma kece malamammu dake nuna mana daidai da ba daidai ba ,ki natsu aunty da kyau ke mai ilimi ce allah subuhanahu wata ala yace acikin suratul ahkhaf aya ta arabin da biyar وَوَصَّيْنَا الْإِنْسَانَ بِوَالِدَيْهِ إِحْسَانًا ۖ حَمَلَتْهُ أُمُّهُ كُرْهًا وَوَضَعَتْهُ كُرْهًا ۖ وَحَمْلُهُ وَفِصَالُهُ ثَلَاثُونَ شَهْرًا ۚ حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُ وَبَلَغَ أَرْبَعِينَ سَنَةً قَالَ رَبِّ أَوْزِعْنِي أَنْ أَشْكُرَ نِعْمَتَكَ الَّتِي أَنْعَمْتَ عَلَيَّ وَعَلَىٰ وَالِدَيَّ وَأَنْ أَعْمَلَ صَالِحًا تَرْضَاهُ وَأَصْلِحْ لِي فِي ذُرِّيَّتِي ۖ إِنِّي تُبْتُ إِلَيْكَ وَإِنِّي مِنَ الْمُسْلِمِينَ
Allah yana yiwa mutane wasiha ne akan su kyautatawa iyayensu , mahaifiya ta d'auki cikin mutun ,tana mai shan wahala ,kuma ta sauke shi cikin wahala ,da daukar cikin da yaye d'a na tsawon wata talatin har lokacin da karfin mutun zai kai girma yasan ciwon kansa har zuwa karshen ayar ,cikin girmamawa ta cigaba da magana "kiyi min wannnan alfarmar aunty , wallahi dan kinje garesu a halin yanzu ba kasawa bane bugu da qari iyayenki suna da hakki akanki babu ruwan allah da abinda sukai miki ".


"maryama mu bar maganar nan ta wuce dan allah sannan ki fito ki karya kar abincinki yayi sanyi tana gama fad'ar hk ta juya ta fice daga dakin shiru tayi kawai tare da bin kofar dakin da kallo idanunta na kawo ruwan hawayen tana tausayin mahaifiyarta bata san meke damun mahaifiyarta ba akan iyayenta sam sam bata son ana mata maganarsu tamkar wanda akayiwa farra'u amman tasan abinda zatai zata janye jikinta tare da tsananta addua akan lamarin allah ya daidaita da iyayenta da yanuwanta ,yinin ranar a daki ta yini taki fitowa taci komai ."






*****




Tun karfe takwas na safe maryam da mami da masu aikinta ke faman kai kawo a kitchen suna qoqarin had'awa mr ATA breakfast sosai mami take lura da yadda maryam take gudanar da aikinta , babu laifi tafi da kokari sosai sannan ta rage son jikin da take dashi wajen girki suna girki suna hira mami ta cigaba da nuna mata wasu abubuwa suna cikin aiki sai ga sallamar hindu ta shigo maryam ta amsa tare da lekawa tace "hindu ce ki shigo muna kitchen muna aiki ne."


wani irin kallon tayi mata wanda yasa maryam taji wani iri ajikinta ,hindu ta tsaya bata shiga kitchen din ba kamar yadda maryam tace ta samu waje ta kame akan daya daga cikin kujerun falon ,mami ta dawo inda maryam take tsaye tana kallonta "sannuki maryam gsky kinyi kokari sosai yau kin aikatu da kyau haka ake so, maryam tayi murmushi kawai tana jin dadin yabon da mami tayi mata "na gode sosai ai nan gaba zan kware na zama professional ta bangaren girki bazan ta'ba baki kunya ba ."


mami tayi murmushi tace "da alama zaki wanke zuciyar mamnki ta gyada mata kai alamun "eh !"
"To ni zan hau sama na dubo adamcy Idan kin kammala komai ki shirya dinnig kije kiyi sauri Kiyi wanka ki shirya ki dawo Kiyi saving din sarkin zuciyar Kiyi komai a natse kin dai san halinsa dan oya oya ne yafi son komai cikin sauri sauri bare yau din nan sai ahankali ."mami dan allah ki zuba masa da kanki mana"idan kunyi aure nice zan dinga zuwa gidanku ina zuba masa ?"dakewa zakiyi maryam ai ya kamata ace kin saba da halinsa "wallahi mani babu mai iya sabawa da halinsa sai ke nifa mugun tsoro yake bani idan na gansa hatta kayan cikina karkarwa suke mami tayi murmushi tana cewa ni na wuce "To mami sai kin fito ta fad'a cikin murmushi mami ta fito zuwa parlour'n."


hindu na ganinta ta saki fuskarta sosai tare da gaishe da mami cike da sakin fuska mami ta masa tana tmbyrta mutanen gidansu ta amsa da lafiya lau kowa yake "mami ina ya adam ne ko har yanzu bai tashi ba ?"eh!hindatu ina tunanin bai tashi ba amman yanzu haka ma samansa zani na taso shi dan yace idan ya wuce tara bai tashi ba na tashesa rausayar da kwayar idanunta tayi tana jin wani zazzafan sonshi ."


Mami ta nufi saman dakinsa tana mamakin hindu su dai yaran zamani basu da ta ido akan nmj so na mugun rufe masu ido shiyasa har kullum take ganin girma da kimar maryam, a dai barta da son social media dinta amman rawan kai akan maza sam bata dashi dan tasan bancin itace ta hadata da adam to har abada bazata iya bude baki tace tana son shi ba ."


Maryam ta kammala komai a natse ta fito a yatsine hindu ke binta da kallo tana shirya dining ,ita kuma tana tunanin yadda zasu buga kishi daita idan tai nasara shigar gidan ya adam dinta dan dole ta fita ta bar mata gidan ta zauan ita kadai ,dan idan bata kaita lahira ba lallai zata raunatata dan irin son da takewa ya adam ba na wasa ba so ne wanda bazata iya sharing dinsa da kowa ba ."


Marayam ta sha jinin jikinta da irin kallon wulakancin da hindu Ke mata dan duk lokacin data kallo bangarenta sai taga kamar hararata take wanda ta rasa dalilin faruwar hakan ,sai da maryam ta tabbatar da komai yayi neat babu abinda mr ATA zai gani yayi complain sannan ta wuce ta nufi dakinsu cikin sauri still tana mamakin hindu ."


tana shiga dakin bathroom ta shiga ta fara wanka sai dai matsalarta bata iya wanka cikin sauri ba idan ta shiga wanka a qalla tana daukar awa daya a bayi amman kasamcewar zatayi saving din mr ATA yasa ta tsakaita tayi wanka ta fito ta dauki man shafa warta wanda shima shafa man kanshi aiki ne domin tana daukar a qalla mintuna talati bare aje ga make up ta shirya cikin doguwar rigar shadda bazin har kasa bata gama kammala shiri ba taji sautin muryar mami na kiranta da d'an sauri ta fito zuciyarta na rawa kuma har lokacin hindu na zaune a parlour'n tayi shiru tana yi masa kallon tsab komai nashi yayi mata irin wanda take so nmj ne sai kallonsa take yayinda mami ke qoqarin jawa mr ATA kujera baya"


Wani abu mai mugun daci ya hadiye tare da zama yana mai runtse idanunshi ganin mami na son bawa maryam umarnin saving din mr ATA hindu tayi sauri ta mike tsaye tana cewa "mami bari nayi saving din yayana ta fad'a tana mai sunkuyar da kanta alamun kunya "amm...! "Sweetheart bari tayi kawai ya fad'a atakaice mami ta kallesa na second biyu dan sam bataji dadin hukuncinsa ba dan tasan da wata manufa hindu ta fadi hk shi kuma gudun karyaci daga hannun maryam ya fadi haka dan tasan shi tasan halinsa baayi masa gwaninta ranta ya baci sai dai danne damuwarta ."


Madadin mami ta zauna kusa dashi kamar yadda ta saba sai ta koma kan kujera ta hankince ta nunawa maryam kusa daita"maryam zauna anan kinji yar albarka ta maida hankalinta kan tv mr ATA yaji babu dadin yadda mami taja jikinta amman sanin dan maryam tayi haka yasa ya share ya dauki wayarsa yana duba sakonin dake shigowa yayinda hindu ke zuba masa abinci acikin wani haddaden plet ta matso daf dashi Sannan ta ajiye plet din a gabansa."


cike da girmamawa ta kira sunansa"ya adamccccyy...!yadda ta kira sunan cikin slow voice yasa daga maryam har mami suka waigo suna dubanta murmushi ta sakar masu wanda ke nuna tana cikin farinciki sannan ta dauke kanta ta maida kanshi wanda shi gogan har lokacin bai daina abinda yake ba bare ya dago ya kalleta sai faman ciza lips din yake yana kallon screen din waya ."


kira ne ya shigo wayarsa ya dauka a natse "ok but I think kasan nan da 1week zan wuce france ya aikin gunka ina fatan akwai nasara ya hade rai sosai haba hisham you should know me by now ka ta'ba ganin inda akayi haka ?kawai dan na tattara hankalina zuwa wani waje kawai su kamawa yiwa mutane barna ,ka kuwa san adadin kudaden da mukayi asara kuwa ?kowa acikinsu kanshi kawai yasani ba cigaba AGC bane agabansu well sai na shigo dai hindu ta marairaice murya sosai tace "ya adamcy ga abincin ka dan ajiye waya kaci abinci ".


Banza yayi mata ya cigaba da wayarsa "a lokacin zuwa office muke gashi naji ya sultan yace yau kuna da zama na mussaman "bai kalli inda take ba bare ma ta samu matsayin ya bata amsa hakan kuwa yayi wa maryam dadi sosai ,sauran kadan ta fashe da dariya amman ta danne ,ta kalli mami wacce itama ita take kallo suka sakarwa juna murmushin jin dadi sai daya gama wayarsa ya ajiye sannan ya fara cin abinci babu irin kwarkwasan da batayi masa ba da jansa da magana amman bai ce uhmm ba bare uhmm uhm ba illa ma mikewa da yayi tsaye yana gyara yar saman suit dinsa ya dan qarasa kusa da mami muryarsa a dake yace "ni zan wuce kuma kai tsaye daga nan AGC zani "to Allah ya tsaye sai ka dawo yace" Ameen!
"har ya juya ta kirasa "adamcy ! ya dan tsaya yana saurareta "kabi komai a hankali dan Allah karka dauki zafi dayawa ahankali ake bin komai ka tsaya ku fahimci juna da yanunwaka".


Kai kawai ya gyada mata ba dan zai yi abinda tace din ba dan yau kusan sai ya tashi rabin mutanen kamfanin kuma daga aiki wanda dayawa yanuwa ne a natse ya juya ya fice yana fita hindu tabi bayansa har tayi taku biyu mami tace "amm...hindu yau yayanku baya cikin moon mai kyau ba kin kuma san halinsa bare idan yana jin miskilancinsa idan kika nemi ki tsaida shi komai zai iya faruwa ko kina son wani abu ya faru ne ?"


Hindu ta girgiza mata kai alamun a'a daman ba tsaida shi zanyi ba gida zan wuce "to shikenan sai anjima sai data fice mami ta dawo da kallonta kan maryam "mami me kika karanta akan hindu ni yau gani nayi tana wasu abubuwa kamar son ya adam take mami ta tabe baki "wai son shi take amman shi har yanzu bai sani ba dan dayasani bazai bari tayi saving dinsa ba" maryam ta dan ware kananun idanunta sanna tasa dariya tana cikin dariya sai ga nana hauwa'u "sister yi sauri kizo kije wani sabon rigima da sauri ta qaraso tana cewa "bani na sha matar yayana "wai hindu Ke son ya adam wace hindu kuma ?"


Wacce hindu mike dashi a gidan nan data wuce ta gidan baba qarami wallahi har na tausaya mata dan idan ya kirani guntuwa ita km fa me zai kirata ?"
gabdaya suka sa dariya har mami "wanna kam gsky ne ina zai kaita ? ga wani cream na organic tasha duk ya canza skin dinta ta dawo farar karfi da yaji ,shi daaka bashi farar mace sol yace bai so ina ga mai shafa cream? ni wallahi da zai karbeta ma ya barni da naji dadi anan ne mami tasa baki "kar na qara jin kin fadi haka ai babu wacce zaki barwa shi da sannu zai koyi sonki dan nasan you are so different daga sauran mata ai shiyasa nace a saka sati uku ayita ta qare burina ki rage media ki janyo hankalinsa cikin kankanin lokaci ku zo juna ."


"mami kina ganin komai zanyi ya adam zai soni ?"
Mai zai hana maryam zai soki mana aure nawa akayi irin naku km a karshe ya zama soyayya mai karfi ,ni dai ina ji ajikina aurensa zai sa ku rasani da wuri tun lokacina bai yi ba." maryam ta fad'a idanuwanta na kan Mami "ki daina irin wannan tunani babu abinda zai faru sai alkhairi zai soki ki so shi babu abinda zai rabaku sai mutuwa shiru maryam tayi tana jin mami ."


Motocinsa na tsayawa a haraban AGC escout dinsa suka firfito daga cikin motocinsu mutun biyu na qoqarin bude masa murfin mota ya bud'e ya fito fuskar nan tashi sam babu annuri yana miqawa na hannun hangunsa wayoyinsa ya nufi cikin kamfanin kallo daya zaka yi masa zaka qara jin tsoronsa fiyye da yadda kake ji ."


tunda ya samu information barnar daake yi a kamfanin walwalarsa ta ragu sosai babu inda zaka kalla a fuskarsa kaga rahma ganinsa yasa kowa ya shiga hankalinsa domin a irin wannan ziyarar da yake kawowa yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login