Showing 78001 words to 81000 words out of 185716 words
Chapter 27 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
daita domin dai babban goro sai magogin karfe ."
Mlm yahuza ya dan ji zafin maganar malam umar dan haka ya rage farar fuskashi "wai me kake nufi ? kana nufin dan ita din yar boko ce tana da kyau na bugawa a jarida kana tunanin zata samu aiki nan gaba zai sa ta iya fin karfin halittar ubangiji "? yahuza abinda nake son ka fahimta duk wad'an nan abubuwa da kake gani fifiko ne a tsakaninka da maryama kawai abinda nake so kaji aranka tafi karfinka tafi karfin aurenka ."
"kaga dan allah mlm ka barni ka zuba min ido ba wahalar banza nake yi ba ina cikin zuciyarta kunyar da take yawon nunawa akaina ta wadatar dani cewar nayi mata , nan gaba kad'an zata fahimtar dani ."Ka dai bi a sannu kar wata rana kana zaune wani hamshakin mai kudi ya shigo har cikin unguwar nan ya aureta .".
"bari kaji babu wani mai kudin da zai aureta domin suma masu kudin sunfi son ya'yan masu kudi yanuwansu , ita maryamar da ba galihu ne daita ba ,ai ba uban da zai shigo cikin wannan rubabbiyar unguwar ya kwashta ai duk wannan kyawun nata akan irinmu zai qare "yana gama fadar haka ya juya dan baya son ya sake 'bata masa rai ."
Tafiya kawai maryama take zuciyarta cike da kunci da tunani barkatai ba kuma akan mlm yahuza ba sai sabon sauyin data gani akan fuskar sakina dan na shukura mai sauki ne idan da sabo ta saba ita da yaran aunty hassana haka suke mata amman sakina fa basu saba haka ba suna matukar qaunar junansu tun suna yara su din masoya ne na hakika ."
da wannan tunani ta qarasa cikin gidansu kai tsaye ta nufi bangaren su sakina domin tambayarta dalilin sauyawarta ashe wahala ce ta shigo daita tana sallama aunty salma tace " Yauwa maryama d'auki tsintsiyar ki share min d'akuna tas shine amsar sallamar da aunty salma tayi mata kamar tace bazatai ba amman ta kasa ta ajiye alquranin dake hannunta ta d'auko tsintsiya ta fara shara batare da wata damuwa ba ."
tana shara aunty salma na zaginta ita da shukura amman sakina na zaune batace komai ba sa'banin da da bata yarda a zageta ko sakata aiki akan idanunta ,tana shara wani gurin da simiti wani gurin babu ga kuma sakina na zaune ta d'ago idanunta a natse ta kalleta taga kurar sharar na zuwa inda take muryata a sanyaye tace "sakinata ina ganin sai kin d'an tashi kinga kurar tana zuwa inda kike ta wani watso mata harara "ai gudun ruwanki nake kallo naga zaki shareni ko kuwa ."?
maryama tayi shiru tsaye tana karantarta akwai wulakanci acikin maganarta "ke kika kyaleta aunty sakina amman banda jakanta irin nata tana kallon mutane suna zaune zatace su matsa , banza shasha kawai mai siffar mayu ." inji cewar shukara dake zaune kusa da aunty salma abun bai yiwa aunty salma dadi sosai ba domin kuwa sakina taso ta furta ma maryama haka ba shukura ba ,sakina kam tun maganar farko datai bata qara ba ta tashi cikin bacin rai ta shige daki tana jin wani zazzafan kiyayyar maryama ."
Maryama tayi shiru kawai tana bin shukura da kallo "me kuma hakan yake nufi dani ? me na yiwa sakina ni kuwa daga jiya zuwa yau take fushi daita hk ."tayi wa kanta tambayar da bata da mai bata amsa sai sakina ita zagin shukura bai dameta ba kamar sauyawar sakina ta gyada kanta ta cigaba da shara tana tunanin laifin da taiwa sakina har ta qarasa ta wanke hannunta da kafafunta ta d'auki quraninta ta shiga d'aki inda sakina take zaune akan gado tana cika tana batsewa tana ganin maryama ta sake had'e rai Kmr taga mugun abu maryama bata damu ba ta zauna kusa daita ta soma janta da mgn taso tmbyrta laifin da tayi mata amman ganin yadda take barsarwa yasa tayi shiru daga karshe ta wuce zuciyarta cike da matsanancin damuwa ."
*******
Da misalin karfe d'aya na ranar laraba wanda yayi daidai da sauran kwana uku jirgin mr ata ya tashi zuwa france amman har lokacin jikinsa sai a hankali daga matsanancin ciwon kai ya dawo masa ciwon gabobin jiki dan ko miyo baya iya had'eyewa sosai mami ta sauko daga saman d'akin mr ata tare da likitansa byn mami ta sallame doctor rafeeq ta dubi maryam da nana hauwa'u tace "yayanku fa yau tsawon kwana biyu bashi da lafiya ku shiga ku gaishesa keda maryama ,jiki sanyaye suka ce" to! suka mike atare suka hau sama ."
A natse sukai knocking wanda nana hauwa'u ce tayi mryam na bayanta ara'be kusan second goma suka d'auka tsaye sannan ya basu damar shigowa d,akin ,da sallama suka shiga parlour suka gansa kwance akan doguwar kujerar kushin ya runtse idanuwanshi yana sanye da riga fari sol da gajeren wondo iya gwiwarsa yayinda hannunsa d'aya Ke daidai saitin zuciyarsa ya d'an bud'e idanuwanshi kad'an ganinsu yasa ya maida idanuwanshi ya runtse gam."
nana hauwa'u tace "sannu yayanmu ya jikin naka kayi hakuri walllahi bamu san baka da lafiya ba sai yanzu da mami ta sauko take fad'a mana " shiru yayi bai amsa mata ba nan da nan maryam ta shiga hankalinta dan tasan ita kam sai ya had'a mata da tsaki muddin tayi masa sannu suna zaune shiru nana hauwa'u ta d'an ta'ba maryam tana mai mata alamar ta gaishesa wani abu mai d'aci daya tsaya mata a wuya ta had'iye ta bud'e baki muryarta na rawa "yaya sannu "ta fad'a atakaice ilai kuwa tunaninta ya tabbata dan kuwa bai amsa ba sai ma tsakin daya ja yana cewa "auta ya bani abun na sha a fridge da saurinta ta mike ta isa inda qaramin fridge dinsa yake ta bud'e donsimo ta d'auko masa ta had'a masa da ruwa ta ajiye masa akan table din dake gabansa ."
"gashi yaya Allah ya baka lafiya ya d'an motsa lip's dinsa alamun ya amsa ya mike zaune da kyar batare daya kalli inda mrym take ba itama bata sake kallon inda yake ba sai ma fuskarta dake kallon wani katon hotonsa dake manne da bangon falon sanye cikin kananan kaya riga da wondo milk colour touch of black ya zura hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa idanuwanshi manne da farin glass fuskar nan tashi a had'e Kmr koda yaushe "auta !
Ya kira sunan nana hauwa'u ta amsa da "na'am yaya! "shiga bedroom ki d'auko min wayoyina da sauri ta shiga wayoyin na kan katifarsa ta d'auko tana danna gefen wayar inda nan take wayar ta kawo haske screen ta duba fusakar wayar wata kyakkyawar fuska ta gani kanta babu d'ankwali gashin kanta ya zubo kad'an ya rufe mata gefen idanunta ."
ta tsurawa hoton ido sosai nan ta gane zane ne ba asalin hoto ba ahankali take tafiya tana kallon fuskar wayar duk da zane ne ,amman yarinyar tayi matukar yi mata kyau ta kai masa tana cewa "yaya zanen dake kan screen din wayarka yayi min kyau sosai wacece ?"tayi masa tmbyr tana duban mrym da hankalinta baya kansu yana can kallon mr ata , tana kallon kyaun da allah yayi masa ba abinda yafi burgeta dashi kamar sheidar sallarsa daya fito masa a saman goshinsa yayi baki tmkr tawadar Allah ."
ahankali zuciyar mr ata ta soma bugawa da karfin gaske yana jin tmkr ta kunno masa emotion's din da yake ta qoqarin dannewa acikin zuciyarsa nan da nan idanunshi suka canza kala cikin tunanin da maryam take taji yana cewa "yarinyar mafarkina ce dana zanata da hannuna, itace cikar burina ce farincikina ina matukar sonta itace mace ta farko da zuciyata take so .." jin haka yasa gaban maryam yayi wani mummunar faduwa sakamakon jin abinda ya fad'a ta juyo ahankali ta tsura masa idanunta duk da ba karon farko kenan ya ta'ba fadar haka agabanta ba amman na yau din yasa taji wani iri a gbdy ilahirin jikinta ta lura baya iya boye fellings dinsa akan zanen ."
ina ma zata ga fuskar yarinyar taga dame tafita da har zuciyarsa ta zabeta alhalin ita din ba gsky bace ?tuna zane ce yasa ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya mai had'e da zallar kishi "ina matukar sonta auta amamn na rasata a yanzu haka ina son raba rayuwata da tunaninta da duk abinda ya shafeta yana magana yana kallon screen din wayarsa wanda Ke dauke fuskarta "mun dace da juna ko ?ya tambayi nana hauwa'u yana lumshe tsumammun idanuwanshi dake cike da azaban ciwo ."
Nana hauwa'u bata bashi amsa tmyr da yayi mata ba ta kalli maryam dake tsaye tana dubansu idanuwanta cike da kishi ajiyar zuciya ta sauke tace "yaya zamu ce allah ya baka lafiya "na tambayeki baki bani amsa ba ya fad'a a mutukar fusace yana watsa mata harara "me kace ?" shiru kawai yayi tare da tsura mata idanuwanshi itama kallonsa take tasan abinda ya tsana kenan dan hk muryarta na rawa tace "kun..." kun dace sosai kawai dai matsalar ita din ba genuine bace wani dogon tsaki yaja yana cewa "nonsense !"you and this stupid girl should leave this room right now "ya fad'a yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa da sauri ta kamo hannun maryama suka fice daga d'akin ."
Bayan fitarsu kwanciya yayi yana cigaba da kallon hoton screen din wayarsa dayawa daga cikin hotunta ya konasu hatta tsarka zanenta dake wuyansa always yayi flushing dinsa ,kadan ne daga cikin zanenta suke cikin d'akinsa sai na kan screen din wayarsa suma nan kusa yana sa rai zai rabu dasu ya huta da tunaninta sosai yake kallonta "muguwa "ya furta a wahalacce "kin addabi rayuwata kin hanani zaman lafiya ke wace irin muguwa ce da zaki damun rayuwata ?ya tambayi kanshi yana mai kawar da kansa daga kallonta yana tunani "anya bazan dinga zagawa cikin anguwane anguwani ba ko allah zai sa na ganta "? wannan ai hauka ne mr ata kake shirin yi ,me yasa bazaka yarda cewar yarinyar nan ba gsky bace Kmr yadda aka Ke fad'a maka ?
shiru yayi yana jin wani irin buguwa da zuciyarsa ke yi akanta sosai yake son raba kanshi da tunaninta ."
Bangaren maryam kuwa suna taka step tana maseefa "nifa shiyasa bana son zuwa inda yake bashi da aiki sai maseefa da disga mutun sannan wulakancinsa baya qarewa akan kowa sai akaina ko ban shiga tsabgarsa ba sai ya hada dani ni wallahi bana son auren zan dai yi ne kawai dan kun dameni , dan allah ku raba ni da aurensa na huta tunda ba'ayin aure mutun daya ." murmushi nana hauwa'u tayi "na lura kishi kike da zane fa "babu wani kishi sister amman ka auri mutun zuciyarsa na mafarkin wata aljana can wannan ai sai su shafi mutun azo arasa meke damuna "hhhhhhh nana hauwa tayi dariya "yarinya kina da aiki kam dan fasa wannan auren sai dai idan daya daga cikinku ne ya mutu maryam taja tsaki ta d'auki hanyar da zata kai ta d'aki ta shige tayi kwanciyarta dan kar mami tayi amfani da zamanta a parlour tayita aikenta d'akinsa shi kuma ya samun damar ci mata mutunci ."
Mr ata na kwance akai knocking kofar falon yana daga kwance ya bawa mai yi knocking din izinin shigowa