Showing 147001 words to 150000 words out of 185716 words
Chapter 50 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
tsaya ta kallesu daya byn daya cikin tashin hankali kafin ta kai ga bude bakinta duk suka fito mata da ID card dinsu daga gaban aljihu suka nuna mata daya daga cikinsu yana cewa "sunana inspector Almustapha hasan umar da fatan kece nuzla ?
Mmn sudais
๐๐๐๐๐๐
MAR'ADAMS
๐๐๐๐
๐๐๐๐๐๐
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 24
Qoqarin cire tsoro da fargaban dake tattare da jikinta tayi ta aro jarumta ta sanyawa jikinta tace "Eh yes nice nuzla fatan dai lafiya kuka tsayar dani ? "Ki adana tambayarki tukunna muna gayatarki zuwa office dinmu yanzu ."akan wani dalili kenan kuke gayyatata ? idan munje zaki ji komai ,kamar tayi musu taurin kai amman sai taga d'aya daga cikin 'yansanda na qoqarin fito da handcuff daga cikin aljihu yana cewa "zaki wuce muje ta girma da arziki ko kuma sai mu saka miki handcuff mu wuce dake ta karfin tsiya ."
ba tayi mutsu ba dan ta rigada tasan da komai dan tun tuni take jiraye dasu saboda dama tasan hakan na zuwa saboda tun rabuwarsu da yaya adam tasan ya zuba tsaro sosai akanta ta yadda duk wani motsinta arayuwarta yana sane dashi ,haka ma yansanda, dan tayi imani anan din ya bada umarnin aka mata dan da suna son kamata cikin tonon silili da har ciki zasu biyota ,ba tayi ma tunanin zata wuce lokacin daya bata batare da ta shiga hannun hukuma ba." sosai zuciyarta ta shiga rudani taji wani gagarumin bakinciki ya rufe mata kahon zuciya kuma tayi imani matukar tayi gardama dasu haka zasu da'ba mata handcuff su wuce daita , ta ma godewa Allah da ba har cikin estate dinsu suka shigo suka tafi daita ba ai da kuwa ta shiga ukunta ."
Ahankali ta soma daga kafafunta domin isa inda motarsu take jikinta na karkarwa a duniyarta idan akwai abinda ke firgitata shine hukuma tana tsanani tsoron shiga hannun yansanda, duk da tasan ba wani laifi tayi ba ,dan abinda har yasa suka gayyace din akanshi bata aikata ba ."tafiya take tana tunani da mamakin wanda ya aiko su "me ta yiwa yaya adam da zafi har haka daya kasa yafe mata ? shin laifi ne dan tace tana son shi?dan dai tasan hukuncin zafin furta masa kalmar sรณ ne ya janyo mata wannan tashin hankali, tayi masa runtsuwa da Allah bata aikata abinda yake zarginta akanshi ba amman ya kasa yarda daita "shin tayi masa kama da wacce zata iya kisan kai ko yunkurin kisa ne ? zuciyarta ta dinga mata zafi tana mai sake tabbatarwa kanta lallai yaya adam baya sonta, bayan soyayya ta aure har da soyayya ta yanuwantaka ma baya mata gashi ita duk duniya babu wanda take so sai shi ."
"anya bazata rushe wannan wahallalliyar soyayyar ba ta dawo qiyayya da tsana mai tsanani ba "? ji tayi jikinta yayi sanyi matuqa dan bata jin zata iya wannan aika aikan ,jikin nuzla a sanyaye yansanda suka sakata a bayan mota tare da wasu jami'an tsaro mutun biyu inda zuciyarta ke wani irin bugawa da karfin gaske sakamakon bakincikin sakata a tsakiyarsu da sukayi tun anan idanuwanta suka canza kala tana kallon tafkeken get din estate dinsu aka wuce daita ,tafiya kadan sukayi suka iso police station."direban motar yayi parking ya kashe motar sannan suka firfito suka shiga ciki suka karbi duka kayanta sannan aka bude wani daki wanda babu kowa aciki suka sakata ciki suka maida kofar suka rufe kukan bakinciki ne ya kufce mata ,ta soma rera kuka tana jin wani irin zafi acikin ranta saboda ta duba hagu da dama babu inda zata zauna duk inda ta kalla qazanta ne da zarnin fitsari uwa uba duhu ."
Aqalla ta kusan awa biyu tsaye tana jiran azo a fara tuhumarta domin a tunaninta da sunzo zasu fara jeho mata tamabayoyi tana basu amsa idan sun gano bata da laifi su saketa ta kama gabanta batare da sanin kowa ba sai taga sun shareta sun ma shiga wata tsabgar dabam har wata awa daya tazo ta wuce basuyi lokacinta ba ,wanda zuwa wannnan lokacin kafafunwanta sun fara sandarewa da tsayuwa ahankali tayi qasa ta tsuguna a cimintig dakin tana hawaye yayinda bakinta ya soma furta adduar neman dauki ."
Shi kuwa ATA lokacin da sakon samun nasarar kamata ya isar masa yana zaune a parlour'n mami tare daita dan bai jima da shigowa ba lumshe tsumammun idanunshi yayi sannan ya motsa labbansa da kyar "ina fatan babu wanda yaga lokacin da kuka wuce daita ?okay sai nazo ya fad'a tare da jan boyayyan numfashi ya sauke ,okay zaku iya fara aikinku kafin na shigo amman karku ta'ba lafiyar jikinta ,sun dauki Kmr minti goma suna magana yana gama waya ya ajiye wayar a gefensa yana jijjiga kafarsa daya mami wacce kwayar idanunta Ke kanshi a tun sanda ya fara wayar yace ."
"Yaakayi adamcy nah naga kayi wani iri ko akwai damuwa ne ?cikin kwantar da murya yace "no sweetheart yunwa nake ji ,bari nasa aka ..."haba sweetheart karki saka kowa please ni ban san me yasa kike yawon sako wasu cikin lamarina ba" to sarkin korafi ,kai dai da wannan halin naka Allah yasa ka canza ,kullm kai kenan cikin bakin hali naga ranar da zaka canza bazaka barni naji da tsufana ba tun kana yaro nake hidima da kai har gashi ka tsufa ta qarashe mgnr cikin salon tsokona tana hade rai ."
Ya dago a sukwane ya tsura mata idanuwanshi "yanzu ni ne na tsufa sweetheart?sosai kuwa kai yanzu tunaninka baka tsufa ba ?haba haba !!sweetheart allah idan ba fad'a akayi ba babu mai cewa na wuce 40,dan ni wallahi jina ma nake Kmr .." "kai dan Allah kama mana baki shima gyara ne ,da babu gyara da kasan kai ba yaro bane "wel ko babu gyara zan zama Kmr yaro dan gadon jikin mai kyau nayi "
"A wajen kenan ?
Ya sake tsaita idanunshi akanta sosai yace "wajenki mana! shakiyi kawai ya dai kamata ka rage wadan nan abubuwan dan ka kusan zama baba nan da wani lokaci ,nan da nan ya hade rai Kmr wanda aka fadawa sakon mutuwa duk da tsananin son haihuwa da yake amman kwata kwata baya qaunar haihuwa daga mrym ya gwamaci ya qare rayuwarsa babu haihu akan ya haihu daita ".
Ahankali ya bude bakinsa zaiyi magana mami ta katseshi dan tasan ba alkhairi zai fad'a ba "ina son zuwa yanzu ka bawa mrym matsayi mai girma acikin zuciyarka ,ya sake kallonta cikin rashin fahimtarta "Eh !nasan abinda nake yau idan ka runtse idanunka da zumar bacci ka matso daita kusa da zuciyarka zaka ga abubuwa masu yawa akanta" ya dage girarsa daya yana dubanta dan ya fara gano rikicin tsufa ya fara kama mahaifiyarsa idan ba hk ba ina shi ina wani kusantota da zuciyarsa yaji me ?bai gama mgnr zuci ba ya sake jiyo sautin muryarta ".
"tunda ta zama mahadin rayuwarka dole zuciyarka zata dinga bibiyarta " numfashi ya sauke da karfi dan yasan ba abune mai yuwuwa ba shirunsa ne ya bata amsa mgnrta "ta gyara zama kai dai kayi qoqarin yau kawai ka kusantota da zuciyarka idan Allah ya kaimu gobe zan tmb..."sweetheart yunwa !"Okay bari na tashi sarkin korafi "thank you my sweetheart Kiyi sauri please dan yunwa nake ji sosai har cikina ya fara zafi "dariya ma ya bata a duk sanda taji ya fadi haka sai taganshi tmkr yana yaro ,adamcy kenan ko yaushe zai san ya girma ? kullum idan yana gabanta tmkr qaramin yaro yake dawowa ."
Jallof din kuskus wanda yaji hanta da nama da ugu ta kawo masa ta ajiye agabansa tace "bismillah sarkin korafi kallonta kawai yayi yana girgiza kai sannan ya fara ci a natse ta zauna a kujerar dake fuskantarsa tana kallonsa hatta cin abincinsa dabam ne ,yana ci tana yi masa hirar yadda take son bikinsa ya kasance shi dai bai ce uffan ba ya cigaba da kwasar abinsa bayan ya gama cin ya mike ya haura saman d'akinsa wanka yayi ya canza kaya marasa nauyi ya zauna abakin gadonsa ya kunna system ,ahankali sakonnin abokan kasuwancinsa ke shigowa wasu ya amsa wasu kuma ya wuce ."
Washegari yana zaune akan daya daga cikin kujerun dinning sanye da wondo da riga long sleeve sai dai ya dan nade hanuna rigar kadan ta yadda zaa iya ganin hadadden agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ,yayinda mami ke tsaye a gefensa tana qoqarin saving dinsa ,ta kallesa zaune shiru ya hade hannunwansa waje daya tace "jiya da nace ka rufe idanunka tare da kusanto mrym da zuciyarka , fad'a min daka rufe idanunka me ka gani ."Kai sweetheart "nasan mrym ka gani alokacin daka rufe idanunka ko ba haka ba ?" ni ba wata mrym dana gani sai princes dina na gani ."
" kada kayi min karya dan nasan baka iya karya ba "tunda Kinsan bana karya ya kamata ki yarda dani wallahi ni banganta ba Kinsan wani abu a duk sanda na runtse idanuna princess dina nake gani wata rana cikin farinciki wata rana cikin damuwa nifa jikina yana bani yarinyar nan ba karya bace gsky ce km ba aljana bace tana nan acikin duniyarmu sai dai a ina take? " yaushe ne zan ganta ?shine bansani ba amman nasan zamu hadu shiyasa nake jin Kmr a fasa wannan auren "kai sakarai menene ya kawo batun a fasa aure kuma daga magana ?"
Kamar yayi dariya ganin yadda magaarsa ta d'aga mata hankali "wannan auren fa sai an daurashi babu makawa zaku rayu tare har ma wata rana zaka amince daita tare da furta wa mrym kalmar so na tabbatar maka da haka "tunda ya fara cin abinci bai sake cewa uhm ba bare uhm uhm har ya gama ya goge bakinsa da tissue ya mike tsaye yana qoqarin yi mata sallama suka jiyo sallamar baba babba fuska cike da damuwa mami ta bar ATA ta qaraso wajensa a inda yake tsaye dan ko zama bai samu damar yi ba kallo daya mami tayi masa ta fahimci yana cikin damuwa suka gaisa adaidai lokacin da ATA ya qaraso ya gaishesa cike da girmamawa sukai shiru mami ta dubesa tace "baba babba ka zauna mana bari akawo maka breakfast ."
Yace " zulai ba sai na zauna ba nazo ne na sheidawa adamu tun jiya baa ga halimatu ba daga zuwa siyaya nan da nan hankali mami ya tashi "baa ganta ba to ina taje ?kuma an kira layinta bata d'auka ba ?wallahi kwana mukayi kiran layukanta guda biyu shiru abinda yafi daga min hankali bata saba irin haka ba ,kuma duk runtsi ka kira wayarta zaka sameta "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun mami ta furta tana cewa "Allah ya cecemu " ATA ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa yaga lokaci ya fara tafiya ya bude bakinsa da kyar yace "baba babba muje daga waje yana gama fadar haka ya nufi kofar fita suka bar mami cikin tsananin damuwa ."
tare suka jera har haraban estate din baba babba yana sake masa bayanin tashin hankali da suke ciki "ka kwantar da hankalinka baba nasan inda take "wani irin naunayen ajiyar zuciya baba babba ya sauke yana dubansa a tsanake tare da neman qarin bayani ."wani dan bincike zaayi akanta da zarar an kammala zata dawo gida "shiru baba babba yayi yayinda zuciyar tsohon ya shiga bugawa fiyye da kaida domin kai tsaye kwakwaluwarsa ta hasko masa binciken da zaayi akanta muryar tsohon a sanyaye yace "to allah yasa muji alkhairi" ameen !ATA ya furta atakaice anan suka rabu yayi masa sallama ya nufi inda motacinsa Ke jiransa dan tun fitowarsa aka gyara tsayuwar su , tun kafin ya qaraso escort dinsa dake tsaye tmkr mashi suka yo kanshi cike da girmamawa ya shiga mota suka bar gidan ."
Bangaren nuzla kuwa gaba daya duniyar ce ta cakude mata waje daya bata ta'ba sanin haka tashin hankalin irin wanda take ciki yake da ciwo ba"ta dauka zafi da ciwon rashin son da yaya adam ya nuna mata shine damuwa mafi tsayi arayuwarta a she qaramin abu ne damin kwana daya tal da tayi acikin dakin kurkun da take ciki ya ninkashi sau babu adadi ,tana durkushe bisa gwiwowinta tare da rufe fuskarta da tafukan hannunta taji motsin ana bude qaramin kofa ,bata bude idanunta ba bare taga masu shirin budewa ,wata murya taji ta doki dodon kunnenta cikin tsawa tana bata umarnin ta fito sai lokacin ta bude idanunta da suka kumbura tsabar kukan data kwana tanayi ."
Koda ta motsa qafafuwanta dan mikewa sai taji ta kasa yunkurawa dan sun qara sandarewa kamar dotse ,hannunta ta kai ta rike karfen kofar sannan ta kai dayan hannunta ta riko kafarta daya ta yunkura da kyar ta mike tsaye ,ahankali ta fito wani qaramin daki aka nufa daita, babu laifi yafi wanda ta fito tsafta kujeru biyu tagani sai table dake tsakiyarsu ."tun kafin abata umarnin zama ta zauna dan kafafuwanta bazasu iya cigaba da daukarta ba ,mutumin daya shigo daita ya fita byn second biyar wata police mace ta shigo fuskarta a hade
har tafi na farko ban tsoro da razanarwa duk da bata aikata komai ba amman zuciyarta ta cika da tsoro mai tsanani ."
Idanunta na kan nuzla ta ajiye wukake har guda uku akan table din gabanta sannan ta zauna tana fuskantarta ,nan nuzla ta sake tsurewa hankalinta ya sake tashi wasu hawaye masu zafi suka samu nasarar gangarowa daga kwarnin idanunta ."
Bayan mintuna goma police ta soma da tmbyr sunanta ta dago idanunta dake zubar da hawaye ta bata amsa sannan ta cigaba "yanzu dai sheidar da muka samu daga bakin danuwanki ya kore duk wata hujjar da muke nema akan masu amfani da wannan wukar wajen kisa da fari ko zamu san dakilinki nayi kisan ?
Nuzla tayi shiru dan bata da amsar da zata bata sai dai ta dago ta zuba mata idanunta tana kallonta hawaye na zuba daga kwarnin idanunta ,ganin yadda matar ta soma huci tana fito da jajayen idanunta yasanya hankalin nuzla qara tashi ba shiri ta soma mgn cikin rawar murya "ni ..ni ban kashe kowa da wannan wukar ba, hasalima ni a yanzu na fara ganinta "amman ai kin ta'ba turawa yayanki adam sakon zaki ga bayan matar da zai aura ko me zaki iya cewa akan haka ?babu abinda zan iya cewa akan haka baya ga qaddara , kuma nasan tana iya fadawa akan kowa ,a garin na tsoratar dashi akan tsananin soyayyar da nake masa wannan matsalar ta faru dani ."
"kenan kin tura masa sakon cewar zaki ga bayan matar da zai aura ? ta runtse idanunta wasu ruwan hawaye masu zafi suka zubo mata ta gyada mata kai "Eh! na tura masa amman ban aikata komai ba"karya kike karki wahalar da hukuma domin yin hakan yana qarawa mai laifi laifinsa dan haka ki fad'a mana gsky domin kawowa rayuwarki sauki "
Nuzla ta girgiza mata kai jikinta na rawa "Allah ki yarda dani ban san komai ba "da fari kin kashe mubina wacce ta kasance yar uwa agareki kin kashe sadiya dake aiki tare da yayarki shahida yanzu kuma kinyi yunkurin kashe mrym shiru tayi kawai tana tunani wacece sadiya kuma ?ta dai san mubina da maryam amman sadiya kam bata santa ba ."
"Kin kashe mubina yaruwarki dan ta furta tana son adam haka zalika kun hadu da sadiya a hospital kafin rasuwarta itama ta furta tana son adam kin yunkuro kan mrym ita kuma dan ta amince zata auresa kin kashe mutun biyu din nan adalilin sun furta suna son abinda kike so ko ba haka ba ?
Ji tayi zuciyarta ta tsaya CAk ta daina aiki na wani lokacin kafin daga baya taci gaba da bugawa ji take magaarta ba'a kunneta kadai ya tsaya ba har cikin zuciyar ta take jin komai saboda dacin kalmar ."
"kuka ta saki mai cin rai meke shirin faruwa dani ?ta furta a fili cikin tashin hankali da firgice ,wai ita ake zargi da laifin da ba taji ba bata gani ba kallonta tayi da idanunta da suka koma kmr an diga jini acikinsu , tace "me zakice akan haka ?daga kalmominsa komai ya sauya mata ta gane ita din ba kowa bace sannan ta soma fahimtar bata isa tace zata ma kaddarata wayo ba ,yau din taxo mata da tashin hankalin da rudani ya zatayi da kaddara da ta fada mata " ?duk yadda yarsanda taso ta amsa laifinta amman taki dan haka ta mike ta fice ta bada umarnin a canza mata daki zuwa wani dakin dabam ."
Ai tana shiga dakin hawaye nadamar furucinta ya kufce mata domin har gara dakin farko daaka sakata dan wannan bashi da maraba da kabari yayinda zarninsa da warinsa da duhunsa ya zarta duk wani wari da mutun ya ta'ba ji tana kuka tana istigifari" Allah na tuba Allah ni bawar ka ce ya Allah kasani ban aikata laifi mai muni hk ba amman na kudurta yinsa ka gafartamin ban isa na maka wayo na hana faruwar kadarata ba " Allah ka kawomin sauki cikin wannna tashin hankali".
kuka tayi sosai ,sai dai duk rintse bazata taba karban laifin da bata aikata ba ."Ahankali kwakwaluwarta ke son tuno mata wacce sadiya dake aiki da aunty shahida da tunanin wanda zai iya aikata wannan taadanci acikin danginsu a daura mata , sai dai duk tunaninta kwakwaluwarta ta kasa gano kowacee sadiya da kuma wanda yayi amfani da damarta yayi mata haka ,hakika bata da makiyi kamar shi kuma ya cutar daita ya zalinceta ba kuma zata ta'ba yafe masa ba ,wajen bazai isheta zama ba dan hk ta gwamaci ta kwana acikin zarni da kazantar waje tana kwance taci kuka ta koshi idonta sunyi lulu dasu ."
Qarfe biyu daidai na rana ya fito daga