Showing 135001 words to 138000 words out of 185716 words

Chapter 46 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4712

sai ma ya dauke idanunshi akan mami ya maida kan wayarsa numfashi ta sauke da karfi ta kama bakinta ."




Bayan Kmr mintuna shabiyar ya motsa lip's dinsa da kyar" sweetheart yunwa nake ji cikina har zafi yake murmushi mami tayi allah shiryeka adamcy kullum girma kakeyi amman sai ka dinga abubuwa kamar yaro ya yatsina fuska a gaban uwata nama fi yaron goye ,allah ya shiryeka me zakaci akwai alkubus akwai rice and stew akwai sakwara "rice kawai ya isa okay maryam maza zuba masa ki daura a tray ki kawo masa nan "bana bukatar daga gareta kisa wani yayi min "




"Bangane haka ba ? yayi shiru kawai yaki cewa komai duk bakinsa mgnr yake son yi "zaka fara ko daga dawowarka?yaruwarka kuma matar da zaka aura ce kakewa haka ? Allah adamcy ka fita cikin idanuna daga zuwanka zaka fara da bata min rai kuma ya mukayi da kai ?bance ka bar duk wani mugun nufinka a inda ka baro ba ?"yi ...ha ..kuri sweetheart ya fad'a tare da dago kanshi nan take kwayar idanunshi ya shiga cikin na mrym wani mummunar faduwar gaba ya risketa saurin cire nata tayi ilahirin jikinta na daukar rawa "maryam jeki yi abinda na sakaki a tsorace muryarta na rawa tace "to! ta juya ta shige kitchen domin dauko trya




Mmn sudais


๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—
MAR'ADAMS
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 22




Saurin mikewa tsaye mr ata yayi ya haura samansa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ransa a dagule yake taka step dan idan akwai yarinyar daya tsana anan duniya to wannan maryam din ce, ji yake kamar ya kasheta ya huta da muguwar tsanar da yayi mata ,mami tabi bayansa da kallo har ya qarasa sauka akan step tana jin zallar bacin rai da bugun zuciya yana shiga d'akin ya cire rigar jikinsa da singlet ya cila kan kujera ya shige bedroom dinsa ."






koda maryam ta fito daga kitchen taga wayam babu shi babu alamunsa a inda ta barshi ta kalli nana hauwa'u ta kalli mami fuskarta da alamun tambaya "zuba masa abincin daya buqata ki bishi d'akinsa dashi maryam tai saurin zaro ido waje ,cike da matsanancin tsoro ta shiga girgiza ma mami kai yayinda yanayin bugun da zuciyarta yake ya qaru, yanayin tsoratanta kuwa sai ya baka mamaki idanuwanta ta runtse jin tashin hankalin daya kusantota ."


nana hauwa'u ta mike daga inda take zaune ta qaraso inda mrym take tsaye rike da tray mrym bata ankara ba sai jin mutun tayi tsaye kusa daita ta dafa kafad'anta ta bud'e idanuwanta da kyar akan nana hauwa'u "common sister ki sanyawa jikinki natsuwa ki rage wannan tsoron please ".ta fad'a tana riko hannunta ta fara tafiya daita."






"Sister bazaki gane bane wallahi ina matukar jin tsoronsa, na sani yanzu dai kiyi abinda mami tace babu abinda zai iya miki keda kike da mami a hannunki ai sai yadda kikayi dashi, da taimakon nana hauwa'u ta had'a komai a tray ta rakata har samansa adaidai bakin kofar shiga parlour'nsa taja ta tsaya tana cewa "ki shiga da kafar dama sannan ki sanyawa jikinki jarumta daga nan ni zan koma "haba sister mu shiga tare mana Kinsan fa bani da wannan jarumtar "rufa min asiri sister kar ya sauke fushinsa akaina gara ke idan yayi anything stupidty zai had'u da mami ni kuwa fa ? komai yayi min yaci lafiya ,kafin mrym tayi wani yunkuri yin magana har nan hauwa'u ta juya ta soma tafiya tana waiwayenta tana karfafa mata gwiwa "




Cikin natsuwa ta tura kofar parlour ta shiga bakinta d'auke da sallama taga baya parlour ta had'iye wani yawu daya tsaya mata a makoshi tana qoqarin daidaita numfashinta da natsuwarta ,ahankali ta ajiye tray hannunta akan center table din dake ajiye ta nufi kofar bedroom tayi knocking ahankali saboda tasan baya sรณn hayaniya jin shiru yasa ta sake knocking amman still shiru ".




ganin kar abincin yay sanyi ta sake qarawa kanta laifi a wajensa yasa ta murd'a kofar cike da tsananin tsoro da tashin hankali ta shiga idanunta a runtse tare da rufe kofar ta sunkuyar da kanta kasa tana jiran ya balbaleta da ruwan maseefa amman taji shiru .jin shiru yasa ta d'agowa taga baya cikin d'akin wani naunayen ajiyar zuciya ta sauke , kai tsaye kwakwaluwarta ta bata yana cikin d'ayan d'akinsa ."




Ahankali ta juya ta fito daga cikin d'akin har tayi taku uku domin isa bakin kofar d'ayan d'akin sai kofar d'akin ya bud'e ya fito daga shi sai gajeren wondon dake sanye ajikinsa a matukar tsorace take kallonsa da kallon murd'add'en jikinsa dake sheki tsabar kulawar da yake samu ."wani wulakantaccen kallo yayi mata mai had'e da harara yasa a tsorace ta d'auke kwayar idanunta akan shi tayi saurin juya masa baya tana neman afuwarsa "am really sorry mami tace na kawo maka abinci .."


Tsaki yaja a fili yana kallon bayanta daga inda yake tsaye yana iya hango tashin hankalin da take ciki ya rasa me yasa sweetheart take masa hk ?ya guji cin abinci daga hannun yarinyar amman sai da tasa aka biyosa d'akin dashi kmr dole sai yaci abincin hannu ?"yayiwa kanshi tmby yana mai sake jan wani tsakin ."




ta gefenta ya raba ya wuceta ya shige d'ayan bedroom dinsa dan ganinsa tsayawa ma inda take asara nรฉ ,kusan mintuna shabiyar ya sake fitowa a tunaninsa ta fita amman abun mamaki tana nan tsaye Kmr wata tsohuwar soja , ya ja tsaki ya zauna akan kujera ya kunna computer dinsa ya shiga yanar gizo fannin kasuwancinsa . ta cigaba da tsayuwa sai dai ta rasa yadda zatayi masa magana yaci abinci sai ta motsa labbanta zata masa magana amman tsoronsa ya hanata ."




tana tsaye aka fara kiran wayoyinsa yana amsa kira ,duk abinda yake ko ajikinsa dan babu ruwansa da tsayuwarta ya cigaba da abinda yake tana kallonsa ta kasan idanunta ya kashe computer ya kwashe wayoyinsa ya d'auki rigarsa ya rataya a kafad'ansa ya fito ya barta tsaye ya sauko kasa har lokacin mami na zaune ita kad'ai ."




Ya zauna batare da yace komai ba , mrym ba tayi fushi ba dan daman ita ba mai saurin fushi bace , kafin kaga fushinta da wahala sai dai akwai zuciya ,zuciyar ma yana dadewa bai motsa ba amman idan ya motsa babu kyau ,ta d'auki tray data shigo dashi ta fito, a parlour ta iskeshi zaune yana shan kamshi inda kasan wani jinin sarauta yana daddana waya ,har gabansa ta qaraso ta ajiye tray din akan table din dake gabansa ta bud'e masa kular abinci cike da tsoro dan kar tayi laifi ta d'auki ruwan dake kan tray ta juya a natse ta shiga kitchen ta bud'e fridge ta canza masa da wani ruwa mai dan sanyi kad'an tazo ta ajiye masa "ga abincin !


Biyayyarta na matukar burgesa domin shi din mutun ne mai tsananin son ya juya duk wanda yake karkashinsa most especially mace , yanayin tsoronsa da biyayyarta yayi ,matsalar dai baya sonta , mami dake zaune kuwa kallonta kawai take yadda take komai a natse cike da kulawa da tsoro da gudun kartayi laifi amman sam adamcy bai damu da duk abinda take ba hasalima hankalinsa da natsuwarsa basa gareta ."




duk yadda mami take sรณn mrym din ta kasance a yanzu tayi babu wani abu d'aya saura ga dukkanin alamun zata kular mata da adamcy yadda ya kamata , daman kuma irin macen data kamacesa kenan mai tsananin biyayya da hakuri da gudun 'bacin ransa saboda yanayinsa ,maryam bata tsaya ba ta nufi d'akinsu inda ta iske nana hauwa'u kwance tana chart, ita kam zama tayi shiru cike da damuwa ita kadai tasan halin damuwar da take ciki duk yadda take son waya a wannan lokacin ya d'an fara fita kanta , dan ko ta d'auki wayarta dan shiga what's app bata 'barkata komai ,hakan friend's dinta zasu yita mata mgn har su gaji su hakura ."




Mami ta tashi daga mazauninta ta dawo kusa dashi ta zauna ta riko hannunsa d'aya cikin nata tana dubansa cike da kulawa dan bazata iya fushi dashi ba , kuma tasan muddin ba itace ta tursasa masa ba haka zai kwana da yunwa, kuma ta rigada tasan bai ci komai ba dan muddin yana qasar baya ta'ba cin abincin kowa sai nata"."look at me adamcy ,ya bar abinda yake yi ya kalleta Kmr yadda ta bukata ,look at the time adamcy ta nuna masa makeken agogon dake manne a bangon parlour'n "lokaci na tafiya tunda ka shigo gidan nan ruwa kawai ka sayanwa cikinka "bai kalli agogon data nuna masa ba bare yasan lokacin daya d'auka bai sayanwa cikinsa komai ba sai ma d'auke idanunshi da yayi akanta yana hura hanci ."




"Tsawon wata biyu bamu had'u ba sai kuma tayi murmushi ganin yadda ya qara had'e girar sama data qasa kamar wani qaramin yaro , ta d'aura d'ayan hannunta akan hannunsa dake cikin nata "me yasa baza kayi abinda zai faranta ran sweetheart dinka ba ? Ta numfasa irin nasu na manya kana ta cigaba da magana "koda yake ina son wannan fushin naka ban sani ba ko dan yana qara maka kyau ne ?"




lumshe tsumammun idanunshi yayi batare da ya juyo ya kalli mami ba yace "nima ina son fushina ina son yadda Allah ya halliceni " murmushi mami ta sake yi "to ai shikenan daman ai mai hali baya gudun halinsa yanzu dai kaci abinci shine abinda nafi buqata "na koshi ".ya fad'a atakaice yana fesar da numfashi .




mami ta juyo da fuskasa gareta ta dungure masa kai tana cewa "allah baka isa ba ,duk yadda aka sha wahala akayi girkin nan kace ka koshi ,allah sai kaci idan ba haka zanyi fushi mai tsanani da kai sai da mami ta had'a da marairaicewa sannan ya fara cin abinci daga hannunta " a ranta tace hukuma sai da rarrashi ."mami girkin nan kamar ke kikayi Kmr kuma bake kikayi ba?".




"me yasa ka fad'a haka ?yayi shiru yana nazari sannan yace "yayi dadi Kmr naki but ya dan yi maggie kad'an ba kamar abincinki ba dan sam girkinki maggie baya yawa , kamar ta fad'a masa gskyr wacce tayi amman tasan halin yan kayanta sai ya birkice mata yanzu ta rasa gane kanshi dan haka tace" ni nayi kasan yau da gobe sai allah, ni kaina naji maggie ya d'an so yayi yawa amman ai yawan da yayi bazai hana a kasa ci ba ,shiru yayi ya tsura mata tsumammun idanunshi yana dubanta a tsanake bai san me yasa ba sai yake jin Kmr ba gsky sweetheart ta fad'a masa ba ,dan dai yasan wacece sweet heart dinsa a fannin girki babu karya tana da matukar kwarewa tun yana yaro ya sani suna zaune ma take had'a girkinta ta tashi ."




bayan ya gama cin abinci mami ta kallesa a natse kafin daga bisani ta kira sunansa "adamcy nah? ya tsura mata tsumammun idanunshi kawai yana kallonta da sauraronta "ya ake ciki da maganarku dasu sultan naji ko a waya baka sake ce min komai akai ba ?ya lumshe tsumammun idanunshi na second biyar sannan ya motsa labbansa yace "magana ta wuce tunda sun dawo da makudan kadaden da suka sace "ikon allah ! account dinka suka saka kud'ad'en ko kuwa account din agc ?" no Ibrahim suka kai wa cheek amman ya fad'a min fahad ne ya kai masa bayan sultan da salim sun qare masa zagi .




"Zagi kuma ?!
Ya lumshe mata ido kawai alamun "eh !
"Wannan abu gsky bai yi dadi ba Allah
sarki ibrahim bawan Allah to shi meye nashi
da zasu zagesa ? a cewarsu yayi masu munafurci alhalin ni bashi ya fad'a min ba hasalima bai sani ba a bakina yaji ,"allah sarki bawan allah ,allah dai ya kyauta kawai , Allah km ya shirye su shiri na addinin muslinci , bancin company agc ya tsaya da kyau nasan da zuwa yanzu an rufeshi kullum daga anemi kud'ad'e a rasa sai a nemi kaya arasa kuma duk masu yi suna gindinmu ."




"sosai kuwa shiyasa yanzu gbdy zan tattara hankalina zuwa agc kusan ma nan zan fi karfi a sati sau uku zan dinga shiga sauran ranakun kuma zan dinga leka wanda suka samu acikin companies dina , hakan yayi daidai allah yasa mu dace yace "ameen ! ya fad'a tare da d'aukar remut ya canza channel zuwa aljazera.


Mami tayi shiru tana kallon tv can ta waigo inda yake zaune idanunshi na kallon tv , kallonta yayi ta gefen ido kafin ya maida idanunshi sosai kanta ya dage mata girasa daya alamun tambaya ,numfasawa tayi sannan ta soma magana "nace bakaga ya kamata ka dinga d'an jan yarinyar nan mrym ajiki ba ?
"Janta ajiki kuma kamar wata yarinya qarama ? ya fad'a cike da jin mamaki " ba maganar kamar wata qaramar yarinya bane yana da kyau ka jata ajiki ta yadda zata sake da kai idan ma ta kama ka dinga kiranta hira domin ku samu fahimtar juna ?"Wani fahimtar juna kuma ya saura sweetheart ? yarinyar nan tasan halina tasan abinda nake so da wanda bana sรณ ."


"duk da haka dai ya dace ku dinga zan tawa "gsky sweetheart bana jin zan iya, akan na kirata zance gara a fasa auren kawai dan nasan bazan ta'ba iyawa ba ,taya ma zan fara ?"mami tayi murmushi irin nasu na manya tace ,idan baka san ta inda zaka fara ba ai sai ka tmbyi abokanka masu aure sa koya maka ta inda suka fara , idan kuma kana jin kunyarsu ne sai ni na koya maka ko ba shikenan ba tunda dai ni nasan baka jin kunyata ".


tunda mami ta fara magana ata ya sanya hannunsa a tsakanin hancinsa da bakinsa kawai yana kallonta "ko na kira maka ita yanzu ?"mrym ! mami ta kwalla ma mrym kira "oh my godness god , haba sweetheart wai me yasa kike min haka ne ?kai ma me yasa bakasan kayi abinda ya dace ba ?"allah sweetheart bazan iya kira kowace mace da sunan zance ba " Allah ko ?! ya dage mata girasa d'aya alamun "Eh! ai kam dole ka kasa iyawa tunda ka zama tuxuru fuskarsa a had'e yace "sweetheart ai itama yarinyar taki tsohuwa ce wallahi , baki ga duk kashin tsufa ya bayyana ajikinta ba ? mami ta dan ware idanunta sosai "akwai wani kashin tsufa ajikin mutun ne ?ta tmbyesa dry na kufce mata ."


Wani sanyi dadi yaji aransa yace "sosai ma kuwa akwai ,to kai taya akayi ka gani ? kodai adamcy ya kamu ne yana so yana kaiwa kasuwa ?bai ce mata uffan ba sai dai a zuciyarsa yace " allah ya tsareni ,ata ya kamo hannun mami cikin nashi yana marairaice murya "sweetheart ! ya kirata sunanta tana dariya tace "ina jinka adamcy nah "dan girman allah laifin me nayi miki da kika zabi ki hadani da yarinyar nan aure ?".


"taurin kanka ne ya jawo had'a zumunci "amman sweetheart baki ga rashin dacewarmu ba ni dogo ita duwaf ? ban son wulakanci adamcy yarinyar tawa ce duwaf ?ta fad'a tana had'e rai ."ai yar daidai kusa da kafad'ata kamar zata fi dacewa dani akan mace guntuwa ?," idan ta kai maka daidai kafadanka cin tsawon zakayi ?ta fad'a tana kunshe dryata yayi shiru kawai yana zare hannunsa cikin nata."abinda bakasani ba dogo nmj da mace mara tsawo sunfi dacewa , karka damu da rashin tsawon maryam nagartata zaka duba ,Kmr yadda na sha gaya maka mrym ce daidai da halinka sannan zata haifa maka ya'ya na gari zuqa zuqa ."




"Sweetheart sai da safe yayi ma mami sallama ya mike tsaye da rigarsa akafad'a dan yasan bazata barsa ya huta da maganar yarinyar ba , kai tsaye ya wuce saman d'akinsa wanka ya fad'a zuciyarsa cike da tsananin mamakin maganar mami "wai ya kiranta zance idan ya kirata yace mata me ?yaja dogon tsaki ,aikuwa muddin sai ya kirata zance sai dai a hakura da auren ,byn wasu mintuna ya fito yana goge sansar jikinsa , byn ya gama ya qarasa inda turarukansa suke ya dauki bodyspare ya feshe ilahirin jikinsa sannan ya saka gajeren wondo iya cinyarsa da riga fara sol ya kwanta yana mai jin tausayin kansa ."




"ya rasa me ya tsarewa mahaifiyarsa da take son ta had'ashi aure da wannan guntuwar yarinyar mai siffar wada yarinya sam babu fasali , yasan muddin ya auri maryam rayuwarsa da farincikinsa zasu yi kasa ,kai gbdy komai nashi zai canza kuma yasan har da walwalansa ,ya gyara kwanciyarsa tare da janyo pillow ya d'aura asaman ruwan cikinsa ya rungume tsam tsam yana jin kamar princess ce duk da yana son mantata amman duk sanda zai yi bacci sai yayi tunaninta sannan bacci mai dadi yake d'aukarsa "


a yadda yake jin felling din yarinyar yayi imani zai had'u daita sai dai yaushe ne ? a ina ne ? bai sani ba , ahankali ya dinga juyi akan katifar yana jin felling dinta mai tsanani yana sauka a sansar jikinsa ,ji yayi kamar anyi kissing din lip's dinsa ya d'an bude idanunshi yaga wayam babu kowa sai shi kad'ai a d'akin, ya sake maida idanunshi ya runtse sai dai a haka yake jinta kusa dashi kuma yake imaginetion din komai ."




sake janyo pillow yayi ya rungume tsam yana jin tamkr itace ajikinsa , ahankali bacci ya d'aukeshi cike da mafarkinta wai gata ta hau saman qirjinsa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login