Showing 174001 words to 177000 words out of 185716 words

Chapter 59 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4709

laifinmu kake kallo idan bamu taya mahaifiyarmu kukan ahalin da take ciki ba me zamuyi ?" Inji cewar amina "shikenan mun rasa nuzla shi kuma hisham an bashi wata amadadinta yarinyar nan fa bata son shi aka takura mata gashi ta gudu an barmu da matsalarmu nasan ko mutuwa tayi basu da asara "zainab ta qarasa mgnr tana zubar da hawaye."


Zainab tasa gefen mayafinta ta goge hawayenta kana ta cigaba da magana "kai ma yaya kasan ba'a kyauta mana ba kuma koda wani lokaci baba abayansu yake baka san abinda hajiyarmu take ji acikin zuciyaarta ba , wallahi matsawar baa ga nuzla a rayuwarmu a haka zata qare ,tabbas raywarmu zata qare cikin damuwa amman wallahi kowa sai ya d'and'ani kud'arsa dan wallahi i bazamu yarda ba wannan d'aurin auren bazaa d'aurashi ba sai an nemo mana nuzla zumunci ya dade bai lalace ba kowa yayi ta kansa kawai .."




"Kada kuyi haka amina gara mu mika komai
zuwa ga allah "yaya Ibrahim ya fad'a yana kamo hannuwansu ya zaunar dasu akan kujera suka zauna suna zubar da ruwan hawaye ,ya kamo hajiya salema itama ya zaunar daita yana dubansu ,kallo daya yayi masu ya gano cewar gabadayansu basa cikin haiyacinsu "sam sam kalmanku basu min dadi ba kuma kun bani mamaki dan banyi tsamanin wadan nan kalaman zasu iya fitowa daga bakunanku ba ,kun kuwa san yadda naji da kuka fadi lalacewar zumunci ? dan allah ku dawo hankalinku sam baba bazai ji dadin duk wani abu da zaku kunno kai dashi cikin ahlinsa ba ."




Ya maida hankalinsa sosai ga hajiya salem yace "hajiya Kiyi hakuri ki barwa allah komai ita rayuwar dan adam cike take da qudirin ubangaji kala kala ,dukkan rayuwa rubutacce alamari ne daga Allah duk wani d'an adam ya kamata yasan wannan ,haka Allah ya qaddaro nuzlah ba matar hisham bace duk yadda yake sonta yake muradin aurenta bazai aureta ba wata zai aura ,haka zalika itama nuzla ba abokin rayuwarta bane muyi fatan allah yasa hakan ya zama alkhairi agaresu ,ita kuma nana hauwa'u kuyi mata fatan nasara a rayuwar aurenta ita kuma nuzla allah ya karkato mana da hankalinta ta dawo gida."




hawaye ne ya gangaro daga cikin idanun aunty zainab da aunty amina bakinsu ya kasa furta komai sai kuka ita ma hajiya salema ta qara sautin kukanta sosai ,babu abinda bakinta ke furtawa sai ku nemo min yarinyata sosai jikinta ya dauki zafi rarrashinta kawai suke amman taki yin shiru bakinta ya cigaba da furta ku nemo min yarinyata "hjy ki barwa allah komai sannan ki kwantar da hankalinki ayi komai dake in sha allahu ana gama bikin nan zaa cigaba da neman nuzla ."




sanyayyen ajiyar zuciya ta sauke ga kuma hawaye na gangarowa akan kuncinta jin bai biyewa mahaifinsa da yace kowa ya cireta arai ba muryar cike da sautin kuka tace "Allah yayi maka albarka babu abinda yake damuna kamar rashin nuzla yau da diyata tana tare dani aka samu wannnan sauyin bazan ji 'bacin rai haka ba ,dan Allah ka nemo min nuzla zuciyata na cike da kewarta ,nayi nadamar goya masu baya alokacin da zaa hada auren nan ,banci na amince da yanzu yarinyata na kusa dani cikin kwanciyar hankali wallahi nayi nadama ku nemo min nuzla dan bazan iya jurar rashinta ba."






yaya Ibraheem ya dafe goshinsa yana jin zafin zubar hawayen mahaifiyarsa tana matukar bashi tausayi ya zai yi ya nemo nuzla ta ina zai fara ?sautin qarar wayarsa ce tasa ya sauke hannunsa ya ciro ya duba a gaban aljihunsa ya duba a hankali ya mike tsaye yana cewa "ku samu wani abu ku bawa hajiya taci sannan ku hada mata da maganin zazzabi tasha jikinta yayi zafi daywa zan dan fita amman bazan dade ba dan Allah ku cire damuwa da kudirinku ayi komai daku sannna kuyi qoqarin kwantarwa hajiya da hankali ".ya qarasa fada tare da ficewa daga parlour'n ya bar hjy salema da ya'yanta."




Cikin mintunan da basu wuce talatin ba sai ga hjy zulfa'u ta dawo masaukinta da meera mai lalle da make up ,ta shigo falon bakinta dauke da sallama tana cewa "my dear ina son yake ?"bai dade da shiga daki ba, ban san me ke damun hisham ba kinga yadda ya d'aga hankalinsa ya dinga hadani da allah akan lallai sai an fasa auren nan dan rashin sanin ciwon kai irin nashi ."




"rabu dashi zan sauke masa duk wani abinda yake kanshi tana gama fad'ar haka kai tsaye dakin da yake ta nufa ta tura kofar ahankali ta shiga yana kwance idanusnhi a runtse cikin tsnanin tashin hankali ."yaji motsin shigowarta amman yaki bude idanunshi har sai data qarasa shigowa sosai ta tsaya akanshi tana kiran sunansa "hisham !da kyar ya bud'e idanushi ya zuba mata cikin tsananin damuwa "tashi muje kayi min rakiya"


"zuwa ina kenan mumy ?kai dai ka tashi muje ta miko masa tafin hannunta ya mike da kyar yana cewa "dan girman allah mumy kiyi hakuri ki bar maganar auren nan nuzla ce rayuwata bazan iya rayuwa babu ita ba wannan yarinyar da zaa hadani aure daita bazata ji dadin rayuwa dani ba saboda ba ita zuciyata take so ba ,"bana son maganar banza hisham yarinyar data rufa min asiri kake fada min haka akanta idan baka kiyayeni ba zan mugun saba maka akanta amman mumy kina ganin ya kamata ki tsani nuzla irin ha .."?




"Kada kace komai dan banason jin komai daga bakinka matsawar tozarci né ga nana hauwa'u a halin yanzu bana ji bana gani ita kawai nake só itace rayuwata yanzu tunda zata rayu da kai kuma zan iya yin komai akanta dan ita zan iya sadaukar da farincikina hisham tashi muje ta sake miko masa tafin hannunta zuciyarsa cike da tashin hankalin ya sanya hannunsa cikin nata ."




suka fito zuwa parlour'n zasu wuce dady yana waya tace " my dear sai mun dawo ya d'aga masu hannu suka fito suka shiga gidan baya suka zauna yayinda meera mai lallae ke zaune agida gaba gama zamansu keda wuya direba yaja motar suka fice ahankali motar ke tafiya hajiya zulfa'u na cewa "hisham ka kular min da nana hauwa'u kada ka wulakanta min 'ya dan bazan lamuncewa hakan ba ,daidai satin zuciyarsa ya dafe dan zafin maganarta yake ji "ples mumy ki bar maganr haka zuciya zata tarwatse numfashi ta sauke da karfi bata qara cewa komai ba ."




kai tsaye abdullahi estate suka nufa bayan sun firfito daga cikin motar suka shiga gidan hajiya zulai falon gidan cike da mutane ,ana ganinta falon ya hargitse da hayaniya nan aka fara gaishe gaishe ana ga uwar ango da amarya shi kam hisham kanshi na kasa duk yadda abokan wasansa ke jansa bai dago kashi ya kalli kowa ba kusan ya matsu mumynsa ta sallamesa ya kama gabansa ,sai da hjy zulfa'u ta gama taja hanunsa suka nufi dakin nana hauwa'u inda ta iskesu zaune cirko cirko cikin zullumi .


suna ganinsu suka tattara hankalinsu ga mumy da hisham , ahankali hisham ya daura idanunshi akan nana hauwa'u sai dai kallo daya yayi mata ya dauke kwayar idanunshi akanta ita kam ta bala'i kafeshi da idanunta tana son gano yayinsa amman kallo dayan data ga yayi mata ya d'aga mata hankali wanda yasa gabanta ya dinga dukan tara tara ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta muryata a matukar sanyaye tace "mumy barka da dawo ."yauwa diyar albarka sannuki da qoqari kinji allah yayi miki alabarka ,allah ya jikan mahaifinki "Ameen!" nana hauwa'u ta amsa tana cigaba da wasa da yatsun hannunta yayinda gabanta Ke cigaba da faduwa."






" meera ga guri ki zauna ki fara aikinki ga wacce zakiyiwa lalle ."ta nuna mata nana hauwa'u "lalle zaayi mata to shi meye na zuwa dashi ?ya d'ago a natse ya kalli hajiya zulfa'u fuskarsa da alamun tambaya , shiru tayi masa tai masa nuni da kujerar dake fuskantar nana hauwa'u kin zama yayi ya cigaba da tsayuwa ,meera ta fara hada lallen da zatayi wa nana hauwa'u "ka zauna mana ka wani tsayawa mutane aka "ni mumy abinda ban fahimta ba me zanyi idan na zauna ?".


"ina son ayi mata lallen agabanka "what !? ya fad'a a hargitse ta gyada masa kai cike da mamaki yake kallonta nana hauwa ta sauke numfashi ta d'ago ta d'an saci kallonsa "mumy ki fahimceni ko ina son auren nan bazan zauna acikin mata ba bare bana só shiru mumy tayi zuciyar na rawa kafin ahankali ta motsa labbanta tace "ni zaka fadawa haka hisham ?"Shikenan na gode amman ka zauna kamar yadda na buqata ."gsky mumy sai dai Kiyi hakuri dan wallahi bazan iya zama ba "yana gama fadar haka ya juya cikin tsnanin damuwa ya nufi kofar fita "hisham! hisham !! hajiya zulfa'u ta dinga kiran sunansa amman ina tunda ya nufi kofar fita bai juyo ba, ta gyada kai kawai tare da samun waje ta zauna zuciyarta na mata wani irin zafi ."




"Mumy !
Nana hauwa'u ta kira sunanta muryarta a sanyaye ta d'ago tare da zuba mata idanunta "dan allah karki damu ki kwantar da hankali karki yi fushi dashi dole kowaye ya tsinci kanshi cikin halin da yaya hisham ya tsinci kanshi ya shiga damuwa ,a yanzu rarrashi yafi buqata ba takurawa ba "ta qarasa maganar tana mai sunkuyar da kanta tare da danne kukanta "na gode sosai diyar albarka in sha allahu muddin ina raye sai kinyi farinciki agidan hisham "murmushi nana hauwa'u ta sakar mata ba dan tana cikin farinciki yin murmushi ba sai dan ta kwantar da hankalin mumy ."




Ahankali meera ta fara zana mata jan lalle yayinda mumy Ke jan nana hauwa'u ajiki ta hanyar yi mata hira su kansu diyana da humaira har ma da maryam mumy ta burgesu matuqa ,ana zanawa nana hauwa'u lallen mumy na yabawa "Woww gsky lallen nan yayi matukar kyau meera ai kudin lallenki yafi karfin yadda kika caza dole ma na qara miki kudi ."gabadayansu sukai dariya meera tace "na gode hajiya koda meera ta gama mata bata wuce ba dan zata tsaya tayi mata make up din zuwa wajen dinner kowacce ta kama gabanta domin shirya kanta aunty shahida tazo ta d'auki maryam ta wuce daita domin shiryata ."


karfe uku daidai aka fara tsara wa nana hauwa'u kwaliya sosai tayi kyau cikin doguwar rigar less red wanda mumy ce ta kawo mata daman kuma ta tanada ne dan nuzla komai red tayi amfani dashi kasancewarta fara sol tayi kyau sosai abun sai wanda ya gani shima a 'bangaren hisham red din yadi yasa ba qarami had'uwa yayi ba nana hauwa'u gani take ba ya ita amma tana ganin hisham ta raina kanta saboda wani irin kyau da yayi mata ya zarta kyau sosai ."




Tsura masa ido tayi tana kallonsa tsaye shi kuwa ko kallon inda take bai yi ba illa ma cigaba da amsa wayar da'aka kirasa yayi ,wata qawar mumy ce ta riko hannun nana hauwa'u ta kawota kusa da yaya hisham suka jero suka shiga mota zuwa hall koda suka shiga mutane suna ta d'aukansu pic jikin nana hauwa'u yayi sanyi sakamakon kalon baza da yaya hisham yake mata ji tayi kamar ta hana daukar hoton amamn bata damar aikata haka duk tajita a takure kamar ta koma gida ."




Bangaren maryam kuwa an tsara mata kwaliya ta ban mamaki tayi kyau iya kyau cikin wani hadadden lace farin anyi mata dinki weeding gwan duk wanda ya daura kwayar idanunshi akanta sai dai yace Masha allah dan kyau kam tayi shi sai daukarta a hoto ake kafin angonta ya bayyana yayinda ango na can a buge mb, salim ,yasir suna tsaye akanshi sun zuba masa idanunsu cikin tsnanin tashin hankali dan sun razana da ganin halin da yake ciki hannunsa ya kai daidai saitin qirjinsa yana murza daidai inda zuciyarsa take bugawa da karfi yayinda gefensa hoton zanen princess dinsa ne yana kallonta yana zukar sigari."




Ahankali ya dauke gajiyayyun idanunshi da suka canza kala saboda bugawar da yayi akanta ya dan waresu akansu yaga still shi suke kallo kwalban whisky's guda uku agabansa inda yake dagasu daya bayan daya yana sha yana zukar sigari cikin tashin hankali ,idanunshi sun qara rikidewa sunyi ja sosai ,ganin bashi da niyyar daina shan giyar yasa a matukar zuciye mb ya ture cup din daga gabansa yace "why ATA ?" akanka aka fara irin wannna auren ?wallahi ka sani shan wannan abu bazai amfaneka da komai ba don't forget mami yau tana cikin farinciki kuma ta tara jamaa me kake tunani zataji idan taganka cikin wannan halin ?kana son heart attack ya kamata ne ?."




'Dago jajayen idanunshi yayi ya kalli mb bai ce masa komai ba ya kunna sigari ya kai bakinsa yana zuka yana kallon wani bangaren dabam "wannan wani irin kaskanci ne haka ATA kalli fa ,kalli irin rayuwar da ka jefa kanka daga shan sigari ka dawo giya ni har yaushe ka fara shan giya ?"ban sani ba kuma babu ruwanka da rayuwata haka ya kamata nayi ko na zama wannan ciwona ne ni kad'ai babu ruwan kowa dani ."


"why ATA? saboda wata soyayyar banza zaka kashe kanka akan wata yarinyar banza da ba gaskiya bace kana qoqarin 'bata rayuwarka, ka manta da wannan yarinyar ka kama wacce aka baka ka d'aura rayuwarka daita "salim !"ya kira sunansaa tsawace shiru salim yayi yana dubansa ya dauki kwalban giya ya kai bakinsa sai daya shanye tass sannan ya fuskancesu "akan mafarkina nake yi wannan abu ko ba akanta bane ni dai abinda nasani soyayyar da nake mata gaske ce kuma har abada domin Itace duniyata tana cikin nan a duk inda take nasan itama tana jin yadda nike ji acikin zuciyata."




"dan allah princess ki tausaya min bazan iya rayuwa babu Ke ba , idan babu Ke bazan iya cigaba da rayuwa ba ,ya mike da kyar yana layi ya dauki kwalbar giya ya fasa sannan yace "an hadani aure da wata guntuwar yarinya ita kuma nana hauwa'u an hadata da heart attack ,ajiyar zuciya ya sauke sannan yace idan hisham ya cutar da nana hauwa'u zan yanke komai dake tsakanina dashi wallahi wallahi I promise to make his life in to hell he will end his life in prison a firgice suke kallonsa zukatansu na duka tara tara idan kuma ban kaishi prison ba zan kashesa matsawar ya cutar min da yaruwata ."


ya nufi kofar bedroom dinsa sauran kadan ya fadi mb yayi saurin kai hannu zai tarosa ya buge masa hannu yana cewa "don't don't touch me just leave my room ya fad'a yana shigewa dakinsa yana shiga ya kwanta flat akan bed tamkar wani matacce ."
Dakin suka shigo gbdy suka rufa akanshi kamr zasuyi hauka mb ya hauro har saman gadon ya dagosa ya kwantar dashi ajikinsa ya kai hannu ya kamo fuskarsa yana dan marin kuncinsa tare da kiran sunansa "ATA ka tashi please karka zama haka yayi maganr yana kuka me yasa zaka mana haka ?"




salim da Yasir ma sunansa suke kira "wannan fa ya rigada ya bugu babu inda zai iya zuwa kamata yayi a fadawa mami "wa zai iya wannan karfin halin ?wa zai iya tun karar mami da wannan maganar ?bazan so mami ta gansa cikin wannna halin ba inji cewar yasir "to meye mafuta yanzu me zaa bashi ya dawo daidai ?abu daya ne zaa iya bashi shine kokin shi kuma yana fara shanta matsala ne arayuwarsa gara kawai duk mu kwashe duk wani kayan maye dake dakin mu barsa yayi bacci idan ya farfado zai dawo daidai ."




Ahankali ya motsa lip's dinsa "I can't marry this stupid girl I can't marry her coz she's not my type shine maganar da yake fitowa daga bakinsa "yanzu me zamu cewa mami ?a gaya mata gsky kawai yasir je kazo da mami ."Okay ya fad'a yana mikewa tsaye ya nufi kofar fita tare da mami suka dawo ai tana ganinsa ta daura duka hannuwanta bisa kanta ta fashe da wani irin kuka tana kallonsa tana furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun tana qoqarin zubewa kasa ganin gaba d'aya ATA baya cikin haiyacinsa ,dan tuni bacci yayi awon gaba dashi jikinsu a sanyaye ganin mami na neman zaucewa suka tarota suna cewa "kiyi hakuri mami Kiyi masa addaua " yanzu abinda adamcy zai min kenan ana gabe daurin auresa?" yanzu ka kyauta min adamcy ?




"gsky bai kyauta ba mami amman Kiyi hakuri girgiza kai mami tayi sannan ta sauke naunayen ajiyar zuciya ta mike da kyar ta fice daga dakin ."da kyar take jan kafafunta ta sauko ta tashiga 'daki tana kuka Allah ya taimaketa babu kowa acikin dakin domin mutane duk sun wuce zuwa hall ta kulle dakinta kuka mami take sosai ta kira aunty shahida kiran na shiga amma bata 'dauka ba dan haka ta kira aunty khadija ita kuma wayarta a kashe mami tarasa abinda Ke mata dadi sai da zaa fito da maryam aunty shahida ta lalubo wayarta nan taga missed call din mami yafi goma cike da jin tashin hankali ta soma neman layinta mami ta dauka cikin yanayi na damuwa tace "shahida !".






"Naam mami ya naji muryarki haka wani abu na damunki ne ?babu komai shahida ku wuce da maryam hall yau ma dai kamar jiya ita kadai zata zauna "shiru aunty shahida tayi kafin daga baya tace "mami ina adam din yake ?hakan nan mami ta kasa fad'a mata halin da yake ciki tace "yana kwance babu yadda yake bashi da lafiya ina maryam din take "gata nan a kusa dani "bani ita aunty shahida ta mika mata waya ,ta karba tana jin faduwar gaba mai tsanani".




"hello mami !" maryam ykk ? lafiya lau mami ya naji muryarki kamar kinyi kuka ? babu komai maryam fatan kinci abinci ? ta gyada mata kai tana cewa "Eh naci numfashi mami ta sauke "kina jina mrym ? tace "eh mami ina jinki "nasan zaki fahimceni zaa wuce dake hall yanzu yau ma kamar jiya Ke kadai zaki kasance bana son kisa damuwa acikin ranki kinji ki dinga tuna kina dani "to mami !" ta fad'a hawaye na cika idanunta aunty shahida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login