Showing 123001 words to 126000 words out of 185716 words

Chapter 42 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4709

hakika bazata ta'ba mantawa dashi arayuwarta ba ta dinga girgiza kai shikenan shima ta rasashi ,hawaye suka dinga zuba daga idanunta bata san tana shesheka ba sai dataji muryar habib yana cewa "kamar shesheka nake ji heartbeat tayi saurin gyara kwanciyarta tayi shiru tare da lullube kanta tana tunani abinda ya kamata ta fad'a masa idan ya qaraso gareta domin dai abinda yake gudar mata kenan gashi ya faru daita ta runtse idanunta sosai alamun ta fara bacci ganin hk habib ya juya ya koma falo ."




Bangaren umma kuwa gyara zama aunty tayi ta kallesu "hakika bakuyi adalci ba saboda ni nasan wannan yaron wajen maryama yake zuwa me zai sa shukura zata qaunaci wanda yake son maryama har ku iyayenta kusan hanyar da kuka bi kuka raba maryama dashi ?mgnr tayiwa ummah dadi ko babu komai yau zata gwada kunjinta akan damuwarta
Aunty salma ta gyara zamanta itama tasoma magana Kmr tana jira "kada a kawo maganar rainin hankali acikin maganar nan kina tunanin shukura zatace tana son shi ne ?".


"to kisani diyata bazata ta'ba cewa tana son wani ba shine da kanshi yace yana sonta kuskure yayi yace yana son maryama dan kawai ya samu hanyar da zai ce yana son shukura bude kunnuwanki da kyau yahuza ya dade da soyayyar shukura acikin ranshi nauyinta kawai yake ji dan hk ya fara gwada soyayyar daga kan maryama ganin bata da wani matsayi da aji ya dawo hanyar madaidaiciya ba kuma diyata tace tana son shi ba idan kuma har abun ya dameki sai kisa diyarki ta sameshi kice ya daina son shukura ya dawo kanta."


"Uhm kawai aunty ta furta a fili sannan a fili tace allah kai ne allah kai ka kawo ma maryama yahuza amatsayin wanda yake sonta byn ta rasa sauran kuma na tabbatar yahuza yana son maryama da gsky Allah kai kasan abinda akayi aka shiga tsakaninsu ya Allah kayi mata sakayya nasan zaka kawo mata wani wanda ya fishi komai "Wai me maganarki take nufi ?kina nufin an kwacewa maryama saurayi ne ko me ?"wannan ai gskyr da kowa ya rigada yasani ce maryama yake so kuma dan ita yake zuwa gidan nan ,na rasa wannan maseefar babu damar aga maryama da cigaba duk yadda zaa yi sai anyi an rabata dashi ".


"Dakata dakata!! su waye dasu waye idan zakiyi mgnrki Kiyi mgnrki a inda bazai zame miki damuwa ba , ina maryama take ?me ye tafi sauran mata da idan ta samu cigaba ake rabata dashi ?ita din gwal ce ko me ? inji cewar aunty hassana "tunda yaro yace ga wacce yake so ai magana ya qare sai ayi shirin aure "a'a hasaana wannan ba magana bace allah baya son zalinci kuma baya son wani bawan yayi ,hakika idan akayi auren nan an zalici maryama "umma ki rabu dasu hassada ke damunsu akan maryama ,amman maryama din da kuke gani tafi gwal wallahi kuma kaf zuriarku babu macen data kaita allah na tuba idan nayi alfahari ka yafe min ba alfahari nayi ba gsky na fad'a ."da sannu hassadar zata cinyeku ni natashi allah ya bamu alkhairi allah yayi mata zabin abinda yafi zama alkhairi arayuwarta da izinin allah maryama sai ta kawo maku wanda bazaki iya kwacewa ba tana gama fadar haka ta mike ta bar falon ."nan fa hayaniya ta kaure aunty hassana na zaginta aunty salma na qarawa ummah kuma tana basu rashin gsky ."




Aunty ta shigo parlour'n tana kuka nan da nan hankalin habib ya tashi ta wuce shi ta nufi dakin maryama tana kwance har lokacin tana zubar da hawaye tana tuno daddan kalaman mlm yahuza gareta atare suka fad'a dakin ta qarasa ta zauna bakin gadon ta kamo hannun maryama ta damke cikin nata jikinta har ya dauki zafi ta fashe da wani sabon kuka wanda yasa kukan maryama ya fito fili ta yunkura ta mike zaune cikin mawuyacin hali tana cewa "why aunty ?me yasa kike asarar hawayenki akan dan wannan abun ? "duk fa abinda kaga allah bai baka ba to ba rabonka bane Kiyi hakuri ki daina kuka please cikin rawar muryar habib yace "aunty meke faruwa ,abinda kake gudu dai ne ya sake faruwa sun rabata da yaron nan yahuza yaron kirki "what !?"


"Wallahi habib sun rabata dashi wai shukura zai aura ba maryama ba amman babu komai akwai allah wani irin ihu yayi yana kurma uwar ashariya ya juya maryama tayi saurin durowa ta rike masa hannu ya juyo ya kalleta "ki sakar min hannu heartbeat ba shukura ba hatta shi kansa mlm yahuza sai naci ubansa yau koni koshi girgiza masa kayi tayi "bashi da laifi nasan akwai abinda akayi masa domin da kunne naji komai nan ta zayyana masu hirar aunty salma da yayanta akan mlm yahuza, dan haka kasani mlm yahuza baya cikin haiyacinsa ,mlm yahuza mutumin kirki ne idan nace banji zafin rabuwa dashi ba nayi karya jikinsa a matukar sanyaye ya zame a zauna qasa ya dafe goshinsa da hannunsa daya yana jin ciwon abinda ya faru" yanzu abinda shukura tayi mana kenan ya fad'a cikin jin haushin ,to ya zamuyi mu mun dogara da allah aunty ta sake riko hannun maryamu "Allah yayi maku albarka a rayuwarku ,allah ya baki miji na gari, idan da rabo Allah ya juyo da hnkln yahuza ya dawo gareki ya kula dake ."




"Maryam tana kuka aunty tana yi tana goge mata hawaye "Kiyi hakuri maryama "kema aunty Kiyi hakuri bana son ki daga hnkln ki akan matsalar nan ,in sha Allah nan kusa Allah zai bani wani "In sha Allah bazai dade ba Allah karka barmu da iyawarmu ka iya mana dukkanin abinda bazamu iya ba har kusan karfe dayan dare suna tare kuma duk mgnr mlm yahuza suke aunty bata so tayi nesa da maryama , tafi son bacci ya zo mata tana tare daita
don Allah ki daina damuwa kinji ' yata ki kwanta Kiyi bacci Allah yayi miki albarka yayi wa rayuwarki data ' ya'yan da zaki haifa albarka, In sha Allah bazaki dangwama a hk ba Allah zai saukaka mk na yafe miki duka laifukan da kikayi min wnd na sani da wnd bn sani ba daga hk tayi shiru tana goge hawayen idanun maryama , amma tamkar sake kara mata su ake .


Ba sosai damuwa yake tasiri acikin zuciyar maryama ba bare irin wannan damuwar da idan da sabo ta saba amman tabbas wannan damuwar ta doketa sosai dan duk kwanaki bata iya bacci adduar nenan zabin allah kawai takewa kanta zuciyarta chunkushe da bakinciki mara misaltuwa har akayi kiran sallah asuba bata runtsa ba hakan yasa ta mike da kyar ."




Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗




*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 21










Duk da ba wani son mlm yahuza take ba amman tunanin rabuwa dashi Kullum yana bibiyar zuciyarta dan duk yadda take qoqarin ta yakicesa daga tunaninta abun ya cutura ba dan komai ba sai dan tsananin kirkinsa da tausayinsa gareta komai na duniya ya fitar mata a rai hatta zaman gidansu ya fita ranta saboda Harare hararen da take sha daga kowace fuskar ta mutan gidan wanda hakan yasa ta kasa samun sukunu ta rasa da me zataji da kwace mata saurayi da suka yi ko kuwa da nemanta da fitina da suke yi ?."



Tana kwance shiru akan katifa kamar mai barci alhalin ba baccin take ba. aunty ta leko d'akin tana kiran sunanta "princes baki ta shi bane ? tasan dole ta kasan tashi saboda abinda ya faru dole zai hana zuciyarta sukuni ."ahankali maryama ta yunkura ta mike daga kwanciyar da tayi ta ari murmushi da sukuni ta dasa a ranta tana cewa "aunty na tashi , tayi haka ne dan kada aunty ta gano har yanzu abinda ya faru yana ranta har yasa ta qara mata zancen addu'ar ma data kwana yi cikin dare ya d'an sanyayyar mata da zuciya, kuma har ranta taji ta samun sauki dan har yanzu data mike tana maimaita adduar Allahuma ajirni fi musibatihi wa aklifini khairan minha yafi sau babu adadi dan bata san iyaka adadin data yi ba , aunty ta riko hannunta cikin nata suka fito zuwa parlour ta zaunar da maryama ta lumshe idanunta cikin sanyayyar muryarta tace "aunty ina after dad ?"






"Tun safe ya fita zuwa filin kwallo amman nasan yana kan hanya dawowa yanzu numfashi ta sauke da karfi sakamakon tunawa datai yau asabar ce daman kuma ranar asabar da lahadi sune ranakun daya ware domin zuwa filin kwallo , ta mike tsaye a natse ta nufi hanyar kitchen domin had'a kan kayan wanke wanke ta jiyo sautin muryar aunty tana cewa "ina zaki ?" .


"zan shiga kitchen na had'a kayan wanke wanke na wanke ne ." tayi maganar cike da raunin zuciya Kmr zatayi kuka , shiru aunty tayi tana kallonta cike da tausayawa kallo d'aya zaka mata ka fahimci bata cikin natsuwarta da kwanciyar hankali tayi wata muguwar rama " ga abinci akan table ki d'auko kizo ki karya kafin ki fara aiki ."


ta sauke numfashi sannan ta rausayar da kwayar idanunta bata jin cin komai amman kuma bazata iya cewa aunty bazata ci ba dan tasan bazata ji dadi ba dan damuwarta damuwar aunty ce , idan ta runtsa aunty ta runtsa ,idan ta kwana Jin motsinta to haka itama bazata runtsa ba ,ta dinga kai kawo kenan a tsakanin d'akinta da nata ."




Jikinta a matukar sanyaye ta qarasa inda kular abincin yake ta bud'e ,shiru tayi tana kallon abincin , sai data d'auki second goma tana kallon abincin sannan ta kalli aunty fuskarta d'auke da tambaya "ummah ce ta aiko mana dashi , sanyayyen ajiyar zuciya maryama ta sauke sannan ta d'auko Kula tazo ta zauna kusa da aunty ta fara ci a natse , ba wani abincin kirki taci ba ta rufe kular tana qoqarin mikewa tsaye aunty tace "har kin yi me kenan princess ? " ki koma ki qara cin abinci duk fa kwanakin nan ina lura dake ba wani abinci kirki kike ci ba ,ki taimakeni ki manta da abinda ya faru ga gobe can tana d'aga muna hannu kullum cikin miki addua nake , nayi imani allah bazai barki haka ba zai kawo miki wani mafi alkhairi."




"Wallahi aunty na koshi ne sannan idan ban hakura ba ya zanyi aunty ? nasan haka Allah yaga dama dani kuma na kar'bi qaddarata ni kawai mlm yahuza nake tausayawa domin duk ranar da zai dawo haiyacinsa sai yayi kukan bakinciki abinda ya faru , tana gama fadar' haka ta shige kitchen ta ajiye kular abincin da taci ta rage ta fara da had'a kan kayan wanke wanke ta wanke sannan ta share d'akunansu ta fito da sharar har tsakar gidansu domin kasancewar weekend ce kuma daman ta saba hakan a duk ranar weekend ."


Lokacin data fito duk mutanen gidan suna zaune suna hira ganinta suka hau fad'a
fad'ensu da suka saba akanta musamman aunty salma da aunty hassana da yaranta kaulat da Islam dan ita sakina shiru tayi tana sauraronsu haka ma shukura sai dai duk lokacin da suka had'a ido da shukura sai ta zabga mata harara ,sai dai allah da ikonshi sam bata ji komai game da abinda tai mata ba illah iyaka tausayin mlm yahuza dana mahaifiyarta dake ranta ,adadin soyayyar aunty gareshi mai yawa ce, domin shine saurayi na farko da aunty taji ta gamsu dashi ,shine mutumin da rabuwarsu ta ta'ba zuciyarta ,shine wanda har ta tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login