Showing 111001 words to 114000 words out of 185716 words

Chapter 38 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4726

yana damuna ,sau nawa kina yi saurayi agidan nan a karshe ko ya gudu ko a kwace miki shi acikin gidan nan ?to ai duk ba mijinta acikinsu ne ,no no aunty akwai cutarwa aciki "to nufinka yanzu haka zata zauna babu mai zuwa wajenta ?"allah aunty dasu dinga 'bata mata lokaci gara ta zauna haka idan na girma na qare karatuna zan mata komai zan siya miki gida da mota itama heartbeat zan siya mata zan kai ku aikin haji ,kai har sojoji zan daukar maku escort duk inda zaku su dinga rakaku aunty da maryama basu san sanda murmushin jin dadi ya bayyana akan fuskarsu ba "shikenan after dad bazanje koina ba domin kai din tmkr uba ne a gareni "yauwa heartbeat sai yanzu naji hankalina ya kwanta muyi zamanmu ."




aunty ta kallesu ta girgiza kai "wallahi wannan ba rayuwa bace kin wani zauna ya tasaki gaba yana miki zakin baki ,wallahi ki daina biye masa Ke macece dole kina bukatar Kiyi aure shifa nan gaba kad'an zai ce zai yi aurensa dan wannan da son girman tsiya nasan .."no no aunty karki hadamu da heartbeat babu wani aure da zanyi na barta idan dole sai tayi aure ni zan kawo mata miji wanda zai dinga kwantar mata da hankali duk ranar da yayi gangancin ' bata mata rai na zage naci ubansa ".




"Lah lah lallai habib abun naka babba ne "allah aunty sai ma ya cika qaidodina sannnan "wannan ai gara kuje kuyi auren kotu ku huta maryama tai murmushi tana jin dadin yadda dan'uwanta ke tsananin qaunarta "babu kotun da zamu amman dole a kular min da heartbeat ko kuwa a tashi mutun aiki "uhm kaga tashina ta mike tsaye " bari naje na bawa baba gali da hassana hakuri na dawo ."




"haba aunty ai komai ya rigada ya wuce wani hakuri kuma zaki basu salon su samu damar ci miki mutunci "? A'a sai naje zaman lafiya yafi zaman dan sarki ina zan iya dasu gara dai naje ."Yauwa aunty kije ki basu hakuri wannan ai ba komai bane wata rana sai labari kai ma ya kamata ka bita kabasu hakuri wani irin kallo ya watsa mata yana cewa "allah kiyaye ai ni .."sai kuma yayi shiru sakamakon tuna alkwarin da yayiwa mahaifiyarsu ."


"ai babu abinda zai sa naje da habib sai ya qara dagula lissafi sunan wani police a isokoko ni na wuce sai na dawo "to aunty sai kin dawo tasa kai ta fice daga dakin ta barsu suka cigaba da hirarsu mai cike da kulawa da soyayya shi kam mlm yahuza tsawon mintuna nan duk yana tsaye yana jira Fitowar maryama ya duba agogon dake daure da taintsiyar hannunsa yaga lokaci ya tafi daman kuma yaron daya aika ya sheida masa komai dan haka a natse ya juya sai dai ya kudurce aransa zai dawo gobe."




Ahankali aunty take tafiya tana tunane tunane abinda zatace idan ta isa gaban baba gali a natse tayi sallama cikin bangaren nasu basu amsa mata sallamar ta ba dan haka taji gabanta ya shiga faduwa kafin ta kai ga yin wata magana taji aunty salma ta hau surfa mata maseefa kamar kullum "me ya kawo bangarenmu "ba komai bane hakuri nazo baku akan abinda habib yayi ,ya gama ci mana mutunci a gabanki shine dan munafurci kika kwaso jiki bayarwa , shegiyar munafuka kin wani marairaice fuska bayan kin gama zuga d'anki yayi mata walima ta uwa da uba zaki wani kwaso jiki to yanzu hakurin me kika zo bamu ?".


Numfashi aunty ta sauke ta samu waje ta zauna kusa da baba gali da ko kallon inda take bai yi ba a tun sanda ta shigo "kuyi hakuri gabadayanku in sha allahu nayi maku alkawarin wannan shine karo na farko da karshe da hakan zai faru ...."dakata bana son jin komai daga bakinki dan duk abinda zai fito daga cikinsa karya ne ni dai abinda nake buqata "ki dauki yayanki ku bar mana gidanmu tunda ussein yake raye bai tsina mana komai ba sai tujara gashi nan ya barwa dansa tsaraba har kamar ni wannan yaron zai dinga gasawa magana kuma a gabanki kina kallo yaron da ya kamata kiyita dukansa har sai kin kusan auna shi lahira amman kika zauna dan tsabar son ya'ya kina kallonsa yana surfa mana zagi ta uwa da uba ai wallahi bazai yuwu ba ."




Sake durkushewa tayi Kmr zatayi kuka batare da tasan abinda zata sake fad'a ba sai dai ita kanta a halin yanzu tana mai bakincikin hada zuria dasu tsaki aunty salma taja tana cewa "munafukar banza munafukar wofi sai anyi magana ki wani durkushewa mutane "ni dai ba wani tashin hankali nazo dominsa ba nazo ne dan na baku hakuri dan nasan danku bai kyauta ba "ni wannan yaron ba d'a bane domin kuwa d'ana bazai min haka ba hakuri aunty tayita basu da kyar baba gali yace komai ya wuce amman tajawa habib kunne aunty salma dai ce taki hakura ta mike tana masu sallama "sai da safenku allah kuma ya huci zuciyarku babu wanda ya kulata acikinsu har ta fice zaginta aunty salma take cikin tsananin tsana ."


Daga bangaren baba gali na aunty hassana ta shiga itama dai tujara tayi mata ta uwa da uba kaf danginta babu wanda ta bari bare iyayenta zuciyarta tayi nauyi kamar an d'aura mata dotse da kyar ta yunkura ta mike ta fito tana tafiya zuciyarta na kokawa. a inda aunty ta fita ta bar yaranta anan ta dawo ta samesu zaune suna hira "har kin dawo aunty ?suka had'a baki murmushi tayi tare da d'aga mata kai alamar" eh! my princess na dawo ".


"Yaya kuka qare fatan sun hakura "Eh to sun hakura my princess!ta fad'a zuciyarta cike da raunin kuka dan shi take bukatar yi a halin da take ciki shi kam habib bai ce uffan ba illa ya cigaba da sauraronsu"my princess Kinga dare yayi bamu samu girka komai a gidan nan ba ni yanzu ban san me zamu dan girka muci ba "wallahi aunty amman bari naje wajen Ummah watakilla bazamu rasa abinda zamu ci ba maryama ta fad'a idanun habib yana kanta "ko zaka raka ni ne? ta fad'a tare da miqewa..."Muje ! kawai abinda ya fad'a kenan maryama tayi murmushi "makalema kawai "kima ce bita zai zai ki huta gbdy muje suka jera ."




Suna fita suka had'u da yaya sadam ya fito daga side d'in din baba gali zai shiga side din ummah cike da farinciki habib ya qarasa suka gaisa! "A she rabon mu had'u ne yaya yasa heartbeat tace nayi mata rakiya ."ai ko baka fito ba yanzu nake shirin zuwa tambayarka a wajen aunty !Ya mika masa hannu ya kwana biyu ina fata dai komai lafiya? "Lafiya lau habib kawae aiki ne ya boye ni 2days ya karatu ?yace "alhamdulillah.!"




maryama ta bude baki da kyar ta gaishesa ya amsa mata cike da sakin fuska "Lafiya su aunty maryam"ji tayi kunya ya kamata da kirata aunty da yayi ! Ya gida da karatu ?Alhmdllh! ta fad'a cikin jin kunya"kema dazu nake tambayarki wajen Ummah take bani labari mai dadi lallai kin fita zakka acikin matan gidan nan kin tsaya kinyi karatunki yadda ya kamata allah yasa muji sakamakon mai kyau you're the best maryama duk nmj daya sameki a matsayin mata baqaramin dacewa yayi ba Allah yasa sawa karatu albarka dad'i maryama taji sosai dan duk cikin yanuwanta sadam ne kawai sai habib Ke mata fatan alkhairi idan wani abun farinciki ya sameta tace "na gode sosai yaya ."




Habib yace "a she dai yaya ka gane shiyasa sai na zaba mata na durje mata miji dan ita din ba kalar kowani nmj bace "kaga yaya karka kulashi mu je ciki mu qara gaisawa "wucewa sadam yayi side d'in Ummah maryama da habib na biye da shi sunata hiran duniya..."


Zama sukayi a parlour'n sadam ya fara kiran "Ummah Kina ciki ne? Eh! Ganin nan zuwa dan albarka har ka dawo ne? sadam yace" eh ! gashi na kawo miki maryamarki "ban gane ka kawo min maryama ba maryama da muke yini tare dan gulma zakace ka kawo min ita Bari dai nazo ganin nan fitowa ."


Bata wani bata lokaci ba ta fito cikin doguwar riga qaton tray ta aje a gaban sadam na fruits bismillah sannu da zuwa yau har da habib to duk sannuku "Ina yini "Habib yace " lafiya lau habib Ummah ta kalli sadam ta kalli maryama sai taga sun maseefar dacewa ina ma su kasance maaurata suna hirarsu gwanin ban shaaawa habib ya fahimci maryama kunyar sadam take ji sosai dan taki fad'ar abinda ya kawo su gashi shi yunwa yake ji ."


Maryama tace after dad ya kamata mu wuce dare nayi "a'a har zaku tafi kenan maryama to ai bakuci komai ba "karki damu Ummah "ban gane karta damu ba kinga nifa banason kunyar nan take wai ma wa Kike jin kunya anan umma ko yaya sadam ,?maryama tayi shiru tana mai sunkuyar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta "kinga Ummah nan ya fad'a mata abinda ya kawosu "kai maryama amman shine zaki jashi ku wuce to kuci me idan kun wuce? allah ya kyauta wannan kunyar taki kaga habib bari nazo ta fad'a tana mikewa tsaye ta nufi kitchen ".


Bata wani bata lokaci ba ta dawo hannunta d'auke da wani madaidaicin kula cike da abinci sannan da wata leda cike da su cincin wanda tayiwa sadam ta miqa ma maryama tace gashi kai km habib ka rike kula " mungode Ummah !Suka fito maryama nayi masa mitar abinda yayi dariya kawai yayi yana cewa "ina ganin gara kawai ayi yar gida mu huta da samari masu mana patrol "kai dai kasani ni nasani ko gaskiya suna tafiya suna jan juna har suka qaraso falonsu habib ya zauna yana kiran "washhhh allah maryama ta cire hijab dinta ta ajiye akan kujera tace "habib bari na kira aunty kanshi kawai ya gyada mata ."


Ahankali ta shiga d'akin sai dai abinda yayi matukar daga mata hankali shine ganin mahaifiyarta kwance rigingine akan katifa hannunta rike da wani hoto tana kallon hoton hawaye na zuba daga idanunta tana tuna irin rayuwar dadin da tayi ada kafin shigowar ussein rayuwarta ,bata haskowa kanta irin rayuwar da take ba sai data hadu da ussein soyayyarta ta gurba tunaninta ."


yayinda maryama ke kallon mahaifiyarta da ita kadai ta rage mata a duniya yanzu a natse ta qara taku biyu domin son ganin hoton waye a hannunta take kallo tana kuka wasu mutane tagani guda biyu cikin shiga na alfarma suna cikin koshin lafiya da farinciki ko baa fada mata ba tasan hoton iyayenta take kallo cike da nadama lumshe idanunta tayi "iyaye ba abun wasa bane , aunty iyaye suna da kimar da darajan da bazaa iya mantasu ba ."


ahankali taji sautin muryarta tana fita cikin kuka "nayi kewarka baba , nayi kewarki mamana yanzu ku har yanzu bakuyi kewata ba ?yanzu ku baku yafe min ba ko nemeni ba? wallahi ina sonku nayi kewarku ,nayi kewar kowa da kowa ta fad'a tana mai daura hoto a saman qirjinta tana shafawa tana kuka.."


Ahankali maryama ta juya tana zubar da hawaye masu zafi ta koma falo ta zauna kusa da habib tana sheshekan kuka nan take ya birkice ya soma tambayarta "heartbeat me kuma ya fara ?kukan me kike yi ? Ina aunty ?yayi mata tmbyr ajere cikin tsananin tashin hankali tasa gefen rigarta ta goge hawayen "yau aunty ta tuna da iyayenta tana daki tana kallon hotonsu tana kuka ni nasan zuciyarta na cike da qaunarsu shiyasa kaga ina son ta koma garesu ."


"habib soyayyar iyaye da yanuwa baa wasa dasu wallahi a tsakaninsu soyayya ce mai karfi ka misalta hakan akanmu musan da qaddara amman an cuci aunty an yi sanadiyyar rabata da kowa nata ,ta bar iyayenta akan soyayya gashi ta rasa soyayya taki bin umarnin iyayenta gashi duniyar taki mata dadi maryama tana kuka habib na rarrashinta har kukan nata ya ragu adaidai lokacin da sukaji tahowar aunty tayi saurin share hawayenta tana cewa ".


karka nuna mata komai da sanyi jiki ta qaraso "kun samo abinda zaku dan ci ?eh mun samu har da cinci tô maza kuci ku kwanta tayi maganr cike da rauni aunty kizo muci tare "aa ku dai kuci ku koshi aa wallahi tare zamu ci habib ya mike ya kamo hannunta ya zaunar daita ya bude kula abinci yana cewa kai abincin nan zai yi dadi maryama ta dauko spoon ta dibi abinci zata kai bakin aunty habib yayi sauri ya kwace spoon "bani ni zan bata da kaina suka sa da dariya ya soma bata abinci abaki yana fada mata kalamai masu sanyi ."


"idan nayi kudi bazan yi nesa dake ba zan kasance tare dake ,dan allah aunty ki daina damuwa akan komai kinji ki dinga tunawa cewa kina damu mu din zamu zame miki farinciki a rayuwarki Wallahi sai mun sa kinyi alfahari damu ki cigaba da addau ga heartbeat nan kwanan nan zata fara bautar qasa yanzu ma ina mata processing yadda zaa dawo daita lagos né daga adamawa wannan farinciki ya rage tarin qunar da zuciyar aunty take ciki tace "allah yayi maku albarka yayiwa rayuwarku albarka in sha allahu bazaku dangwama haka ba allah zai saukaka maku rayuwa ,Allah nake roko ya daukaka min ku na yafe maku duk abinda kuka min da wanda nasani da wanda ban sani ba suna cin abinci suna debewa juna kewa ."


******


da misalin karfe 9:00 na washegarin ranar lahadi mr ata ya fito parlour'n mami ,duk jikinsa yayi sanyi har wata katuwar rama yayi daman ya lafiyar kura ?ba wani jikin kirki bane dashi kusantowar aurensa da maryam yasashi jin kmr ana fixgar ransa ,shiru ne ya ziyarci parlour'n yana tunane tunane yana jin kamar idan ya tafi france kar ya dawo domin a lissafinsa sauran kwanaki goma cif a daura masa aure da yarinyar daya tsana fiyye da komai arayuwarsa byn kmr mintina goma mami ta qaraso da kanta ta had'o masa abun kari , chips da soyayyen kwai da ruwan tea mai kauri , ta janyo qaramin table gabansa ta ajiye kana ta zauna kusa dashi ta tsura masa ido tana kallonsa batare datace komai ba ."


ya dauki cup din tea ya kai bakinsa ya kurbi kadan yana mai runtse idanunshi shiru har wasu mintuna suka shude yana zaune itama tana zaune tana kallonsa da kyar ya bude baki "sweetheart! "kaci abinci first before anything adamcy , sannan kar naji kayi magana kaci abinci kawai yaushe rabon ka sanyawa cikinka abinci bare a samu magani yayi aiki ajikinka ? ji yadda ka dawo acikin kwanaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login