Showing 42001 words to 45000 words out of 185716 words
Chapter 15 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
bille kota Ina an watsa miki shi ba'a ce anyi miki saurayi ba sai ni da fuskata take lafiya lau babu zane ko daya ,Kalli bakinki duk a warwatse kamar lefen sakarya shine zakice kinyi min saurayi , karki qara min irin haka wallahi banaso ai kinfini bukatar saurayi ."
Gabad'aya suka kwashe da dariya rukayya kuwa tsayawa tayi tana kallon maryam da mamaki nana hauwa'u kam har da zubewa kasa tare da rike ciki dan dry ."Ina ganin dai baki san aljanu sun shigi marsi ba ko ? ai babu damar ayi mata maganar maza sai hankalinta ya tashi ." nifa ba haka bane Ina da zabi acikin zuciyata Ina da ra'ayin irin mijin da nake son aure ba kowani shasha ba amman dai na barwa zuciya irin mijin da nake so Ke mai bille sai ki rike saurayin dan kinfini bukata ."
rukayya ta Kalli nuzla nuzla ta kalleta sannan a matukar fusace rukayya tace "karki qara cewa fuskata anyi min bille "to karya ne ba'a yi miki ba ? "idan bakya so nace miki hk nima ki barni da batun wani saurayi can tun da bance miki nayi ina son ba wadan da nake dasu ma sun Isheni bana neman qari sun dade a d'akin suna hira akarshe duk suka watse suka kama gabansu."
******
Karfe shabiyu daidai jirgin Mr ATA ya sauka a lagos a haraban gidansu tun kafin jirgin ya k'arasa sauka security's dinsa ke zagaye da gurin har sanda ya sauka , a hankali ya mike yana gyara zaman rigarsa Sannan ya fara takowa daga matattakalar bene yana taku da kyar cikin tafiyarsa nan nashi na Koda yaushe wato tafiya cike da alfarma da izza yana d'aga kafafunsa yana shakar iska da kyar tare da hura hanci escort dinsa already sun fito suna nan tsaye suna jiransa duk Inda ka duba acikin haraban gida masu aiki ne ke Kai kawo suna aiwatar da aikinsu."
yana qarasa saukowa escort dinsa da security's sukayi masa caaaa har zuwa Inda yake tsaye Inda ya fara taku suna biye dashi har zuwa bakin kofar shiga cikin parlour'n mahaifiyarsa na d'aya , yana isowa gurin yaja ya tsaya d'aya daga cikinsu mai suna muzammil ya bud'e masa kofar ya shiga yabi bayansa shi kad'ai rike da bakar jaka ATA bai tsaya akoina ba sai a babban falon mahaifiyarsa ya shiga ya zauna ya kame akan d'aya daga cikin kujerun falon ya d'aura hannunsa d'aya akan gwiwarsa yana d'an jijigawa yaronsa muzammil ya rankwafo ya ajiye masa jakarsa ya bashi izinin tafiya ya juya da sauri ..."
A hankali mami tayi sallama cikin had'ad'd'en falon a zaune ta samesa akan kujera ya lumshe lumtsatsun idanuwanshi ,da kyar ya bude baki ya amsa sallamarta batare daya bud'e idanunshi ko matsowa ba har sanda ta zauna akan kujerar dake kallonsa tana jin sanyi da farinciki mara misaltuwa da ganin kamilallen danta mai nagarta da haiba illarsa dai rashin ajiye iyali da miskilanci da zafin rai duk wannan farinciki daga ciki take jinsa dan bata bayyana shi ba .
a hankali ya bud'e lumtsatsun idanunshi ya mike ya k'araso gabanta ya rusuna har kasa "mun sameku lafiya sweetheart? Wani sanyin dadi Ya ratsata ta kai hannunta kanshi "alhamdulillah ka sauka lafiya ya aiki Ya fama da jama'a ? ta fad'a fuskarta babu yabo babu fallasa "alhamdulillah sweetheart yayi magana yana matukar tausayin Kansa dan yasan tunda ya zo ya dinga cin karo da matsaloli kenan dole sai yayi hakuri dan magana daya ce za'a yita ana mai maitawa ,."
A natse ya mike ya koma mazauninsa ya zauna
yana neman layin M.B da sauran friend's dinsa kafin kace me hjy zulaiheart tasa an cika masa gabansa da kayan itatuwa dabam dabam sai dai babu wanda ya d'auka yaci illa amsa waya da yake ta bangare damba dabam , nana hauwa'u ta shigo ta gaishesa cike da ladabi "yayanmu Ina yini ka dawo lafiya .?"
"Lafiya auta ykk ya fad'a atakaice" lfiya ta bashi amsa da haka sannan ta mike ta koma ciki dan yadda fuskarsa take a murtuke nan komai zai iya faruwa , haka rashida da muna yaran baba qarami sun shigo gaishesa a mutunce , babu yabo babu fallasa ya amsa haka akayita shigowa yi masa sannu da zuwa sai dai ya amsa atakaice ba tare daya bi ta kansu ba maryam ce kawai bata shigo kawo gaisuwa ba har sanda MB ya k'araso sai daya yi sallama a bakin kofar falon aka bashi izini shigowa sannan ya shiga .
ATA bai motsa daga Inda yake ba har MB ya shigo ya zauna cike da tausayin abokinsa dan kallo d'aya zaka masa kasan baya tare da walwala da farinciki har wata siririyar rama yayi "ATA..!" ya kira sunansa anatse ATA bai amsa ba illa zuba masa kwayar idanunshi da yayi yana sauraronsa "yana ga duk ka rame ? shiru yayi bai ce uhm ba bare uhm uhm sai dai ga dukkanin alamun hankalinsa na kanshi "dan Allah ka kwantar da hankalinka komai na duniya mai wucewa ne idan kabi komai a sannu da sannu komai zai zama normal ."
wani huci numfashi ya saki yana sake tsaida idanunshi da gbdy suke cikin damuwa akan mb
sai da yayiwa MB kallon wasu mintuna sannan ya furzar da abinda ya tsaya masa a makoshi mai mugun daci cikin son danne duk wata damuwarsa yace "na rasa yadda zan cire wannan damuwar MB "kallonsa MB yayi yayinda ATA ya Maida idanunshi ya lumshe "Ina zanganta ?ya furta a saman labbansa cikin tsananin damuwa "wa kenan ..?Idanunsa dake lumshe ya d'an bud'esu da kamar bazai yi magana ba sai Kuma ya furta ", princess.."
murmushi MB yayi "ka iya fad'ar sunan nan tamkar kai ka fara tsarashi a duniya "zaka ganta inshallahu Ina maka adduar ta zamo mutun ce ba aljana ba , sai abu na gaba ka fara da abinda mami take so "bana jin zan iya MB zan dai ta bin sweetheart a hankali har sanda zan samo yarinyar ko kuma na samo wata dabam amman wannan guntuwar yarinyar bazata zamo mata a gareni ba sun dade suna tautaunawa kafin daga baya sukayi sallama duk Kuma maganar da suke akunne mami sukayita ,
dan haka ta shaka sosai tun a lokacin ta fara shirya abinda zata masa ."
Tunda masu aikin gidan suka san ATA ya sauka kowan nensu ya shiga hankalinsa hatta shigowarsu part din hjy zulaiheart ya taikaita sannan komai cikin sauri suke yi kasancewar sun san shi dan Oya oya ne duk da ba abincinsu yake ci ba sai na mahaifiyarsa kuma bata zauna ba har washegari tana kan yi masa hidimar abincin da zai ci tare da abokansa Amar, shawul, shamsu MB sun baje a falonsa sai kwasar abinci suke Amar yace "friend duk fa matar da ka aura muddin bata iya girki irin na mami ba zaku samu matsala daita ",Sosai kuwa dan ni dai Ina ganin zan kawo fedy gurin mami a sake bata class na mussaman dan wanan girki yayi inji cewar MB " suka sa dariya banda ATA dake rike da waya yana duba mahimmam bayanai masu shigowa .
Sai daya rage mahimmam abubuwansa sannan
ahankali ya motsa lip's dinsa "gaskiya ne Ina son macen da ta iya girki kuma qala dabam dabam shiyasa kuka ga Ina dojewa auren yarinyar nan dan nasan babu abinda ta iya sai salo da rike waya da shiga social media ,ni Kuma ta Inda za'a samu matsala dani kenan dan bazan yarda da rashin kamun Kai ba.
gbdy suka gyda Kai batare da sunce komai ba sai can shawul yace "ai idan princess dinka ka aura ko bata iya girki ba zaka zauna daita haka har karshen rayuwarka ATA ya sauke numfashi kawai batare da yace uffan ba "kayi shiru ko ba haka bane ? Inji cewar MB "ka'ajiye wannan magana bama zata zo a haka ba am very sure ta iya komai ." Shawul yayi sigili yace " mai kmr mrym me zaiyi da wannan princess din taka ya watsa masa wani mugun kallo "ra'ayina kenan princess bana son mace irin wannan yarinyar da ake kokarin lika min yayi mgnr yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa.
"Wai Kai wayace maka ana auren mace mara kiba a yanzu Kai gaka ba jiki ba , Kai Kashi ita kashi kuzo Kuna haihuwar kasusuwa Kai da zaka samu mai nama irin Marym chubi daita komai zamzam inji cewar Amar gbdynsu babu Wanda bai dara ba MB kam har da fadowa yayi kasa daga kan kujera dan dariya "ko jini zamu dinga haifa ba kasusuwa ba. nafi sonta akan wannan mai siffar aljanu guntuwa gata nan dai fari ne kawai ya taimaki rayuwarta.
nana hauwa'u da mryam dake tsaye a bakin kofar falon hannu nana hauwa'u rike da tiren silver mai d'auke da gasashen kifi anyi raping dinsa ita kuma mryam na rike da tire na harish suka Kalli juna dan sunji abinda suke tautaunawa daga ciki , naunayen ajiyar zuciya nana ta sauke tace "mu shiga sister ta fad'a tana rike tiren hannun maryam dake k'okarin subucewa qirjinta na dokawa tace "a'a sister ke dai ki shiga ke kad'ai bari na tsaya anan har ki fito banason na shiga Ina jin tsoron kar ya disgani agaban abokansa ta k'arasa maganar tare da d'aura tire dake hannunata akan tiren hannun nana hauwa .
suna tsaka da hira suka jiyo sallama a bakin kofar falon MB ya bada izinin shigowa tare da komawa mazauninsa ta shiga a natse ta gaishesu cike da ladabi sai dai kallo d'aya zaka mata kasan ranta a 'bace yake ta tsani taji yayanta yace bai son mrym ko aibantata bare yau a gaban abokansa ."
Amar ya washe baki yana dubanta kana ya soma mata wasa kasance warsu abokan wasa "a'a gasu cubi hauwa fa ,farar mace alkyalbar mata Ina ganin nida madam zamu lalla'bo muzo ki sammana man da kike shafawa kullum ke da maryam kmr bakwa fita rana, gaku na nan dau kmr yanzu kuka sauko daga sama."
tayi masa banza tana jan tsaki a ranta "Ina kika baro mrym dan nasan ke daita 5&6 ne? ta sake sharesa tana kokarin ajiye tiren hannunta wayarta dake rike a hannunta tayi kasa zata fadi madadin ta bar wayar sai tayi k'okarin rikota Aiko tiren gbdy suka sullube a hannunta sukayi kasa tiren kifi ya kife nan take mai ya fara malala gabanta ya buga da karfi nan take jikinta ya kama rawa ta d'ago da sauri ta Kalli Inda ATA yake zaune gabanta na cigaba da fad'uwa ."
wani dogon tsaki ATA yaja kana ya soma magana cikin fushi da zafin rai " kunga irin haukan nasu ba koina zaaje da waya kamar wasu yan kauye "haba ATA me yasa zaka dangantata da Kalmar hauka tsautsayi ne ko babu waya a hannunta hakan zata kasance "shawul karka goyi bayan wad'an yaran sam babu abinda suka iya sai hauka komai na mata basu iya ba basu iya girki ba basu iya gyaran daki ba sam basu iya komai na mata ba yan iskan banza kawai sai aikin rike waya da surutun banza da wofi da maza kije ki dauko abinda zaki gyara min guri kafin na soma kwallo dake, sai naci ubanku daya byn daya kafin na koma idan Kuma baki dawo kin gyara ba kika turo min masu aiki sai na canza miki kamanni stupid kawai ."
fuuuuu ta fita tana zunburo baki a bakin kofar nana hauwa'u ta samu mrym tsaye duk ilahirin jikinta rawa yake gbdy duk ta Kara firgicewa
Ta kalleta tana hawaye bata tsaya yi mata bayani ba ta wuce dan tasan taji komai daya faru."
Kai tsaye kitchen Inda hjy zulaiheart take ta shiga ita Kuma maryam ta gudu tayi dakinsu , nana hauwa'u na gama shiga kitchen ta soma zuba balai "wai mami dole ne sai ya Adam ya auri mrym ne ."
"Dan girman allah me zai hana abar maganar kowa yaje ya auri wanda yayi masa ? mami ta dubeta a natse "me yasa kika fadi hk hauwa wani abu ne ya faru ?"to gashi can sai faman fad'awa su ya amar yake wai bai sonta guntuwa ce fari ne kawai ya ceceta mene mene ko ance masa itama tana son shi ne ? gsky kiyi masa mgn ya daina nima yanzu kafin na fito sai daya tozartani a gaban abokansa shiyasa wallahi ban so zuwa ba ,wallahi duk matar data auresa ta shiga uku da matsalolinsa wallahi ni dai a fasa had'in nan da marsi tana gama fad'ar haka ta juya fuuuu ta fita mami tayi murmushin takaici kawai tana girgiza Kai ,nana bata so komawa bangarensa ba amman babu yadda ta iya haka ta d'auki abun gyara ta koma kafin yaci ubanta ".
******
Washegari da misalin Karfe biyu daidai Kiran aunty shahida ya shigo wayar mrym tana d'auka tace ki samemu a parlour'n mami na biyu bata tsaya ji abinda zatace ba ta katse Kiran ,shiru tayi tana sauke wayar daga kunnenta jiki a sanyaye ta mike ta d'auki mayafin abayar dake sanye ajikinta tayi rolling din kanta ta fito ta nufi parlour'n gabanta na dukan uku uku.
zaune ta iskesu gbdy ya'yan hjy zulaiheart
banda nana hauwa'u ATA zaune yana rike da waya yana daddanawa sau dari zaka gansa to da waya ne ko system yana operate "samu guri ki zauna aunty zabiba ta fad'a tana nuna mata kan kujera kasa zama tayi a Inda ta nuna mata .
a hankali ta samu guri ta zauna nesa kadan dasu a qasa dan gudun balain ATA ta kasan idanunta take qare masa kallo sanye yake da dogon wando da riga mai gajeren hannu blue da ratsin fari kayan sun yi masa kyau sosai ga gashin Kan nan nasa sai sheki yake wanda da alama yana shafa man gashi ne yasa yake fitar da sheki ko yaushe ."
"Adam ga mryam nan "inji cewar aunty shahida "naga tantiriya mara kunya mara mutunci , uhm
Ina jinki ki maimaita abinda kika fad'awa aunty a gabana ". sai da gabanta yayi wani irin mugun fad'uwa taji wani abu ya tsarga mata tun daga qirjinta har zuwa kasan mararta take taji marata ta soma murd'awa taji wani abu mai d'umi ya zubo mata wanda bata raba d'ayan biyu na tsananin tsoronsa ne."
ta d'ago kanta a hankali taga har lokacin kanshi na sunkuye yana danna wayar hannunsa "ke har kin Isa kice wai bazaki aureni ba ?tayi saurin sunkuyar da kanta kasa tana sake jin digar wani abu mai zafi na diga a pent dinta wanda babu tantana jini ne yazo mata a dalilin tashin hankalin daya risketa ne
ya cigaba da magana fuskarsa a d'aure tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa "daraja kika ci bancin haka har duniya ta nade baki Isa ba , km baki Kai matsayin da zaki zamo mata agareni ba ."
ta d'an dago kad'an ta saci kallonsa adaidai lokacin daya dago idanunshi suka tsarke cikin nata wani irin yanayi ta tsinci kanta ciki wanda babu tantama na tsoro ne wani irin mugun kallo yake mata mai firgitarwa "Ina jinki fad'a min abinda kika fad'a masu ?"kaga AD ba dan ka tutsiye yarinyar mutane muka taro anan ba mufi bukatar amincewarta akan komai "no aunty shahida bari ta fad'a taga yadda zanci ubanta ".
"nace abar wannan mgn ta wuce ke mrym