Showing 177001 words to 180000 words out of 185716 words

Chapter 60 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4715

ta girgiza mata kai alamun karta yi kuka jiki a sanyaye ta mikewa aunty shahida wayr sukai sallama da mami ."


Shiru aunty shahida tayi tana tunanin yadda yau ma maryam zata zauna ita kadai batare da ango ba ,bata ki maganar mami ba domin tasan rashin mafuta yasa ta fadi hakan amman ita dole ta nemo mafuta dan baza bari maryam ta zauna ita kadai ba ko hisham daya tsinci kanshi da auren nana hauwa'u acikin kwana daya ya yarda ya amince har ma sun isa hall bare adamcy da aka dauki sama da watanni ana abu daya ,sosai kwakwaluwarta ta shiga tunanin abunyi zuciyarta ta bata shawarar ta nemi salim ya maye gurbin ango tunda daman jiya babu wanda ya gansa ."




da sauri zuciyarta ta amince da haka nan da nan ta shiga neman layin salim kira daya tayi masa ya dauka adaidai lokacin da suke shirin shiga mota dan zuwa hall "yaakayi my aunty ?kana ina salim ?gamu muna shirin zuwa hall ,yauwa salim dan allah kazo ka maye gurbin adamcy babu dadi maryam taje wajen diner ita kadai kafadansa ya daga alamun babu damuwa yace "okay shikenan an gama aunty ya yi discounneting din kiran yana duban sauran abokan tafiyarsa tare da yi masu bayani ,gsky aunty ta kawo shawara wallahi maryam na bani tausayi dan allah ya hadata da wani irin mutun mai shegen taurin kai, bari mu jira a fito daita sai mu mubi bayan motar ku, suna tsaye aka fito da maryam salim ya bude mata bayan mota ta shiga ta zauna shima ya shiga ya zauna aka rufe murfin mota yayinda mb da sauran abokan ango suka shiga motocinsu suka bar gida ."




Tamkar ango da amaryarsa salim yayi active suka jera har zuwa mazaunin ango da amarya aunty abida ta kallesu ta kwashe da dariya tana kallon mahaifiyarta ,"mumy kinga abinda nagani kuwa ?na gani abida jiya bai zo ba ga yau ma ,ai halin adam sai ahankali ,shiyasa nake ganin da wahala ki iya shawo kanshi ya auri sultana"kai mami karki hada sultana da wannan yarinya sultana ta kereta a komai duk yadda zamuyi ta shiga gidansa sÃĢi nayi idan allah ma ya taimakemu sai ya sota kinga komai zai zo mana da sauki ato allah yasa ,wannan lamari yayiwa abida dadi dan haka ta dinga jinta cikin tsananin farinciki ."


Hall ya cika makil da jama'a ta bangare dabam dabam maryam tayi shiru tana rike da jaka yayinda masu hoto da vedio suka dinga daukarsu hoto har sanda aka kira hisham da amaryarsa zuwa fili ahankali ya mike atare suke daga kafafunsu suka tsaya a fili tamkar wasu gumaka hajiya zulfa'u ta shigo da 'kawayenta da ankonsu iri daya ta dinga likawa nana hauwa'u 1k amma ko kalon hisham bata yi ba MC ne yayi magana wai ya yaga hajiya iya amarya takewa liki ."


murmushi tayi tace mishi "ai itace tafi cancata yar albarka yar gidan arziki gaba da baya irin albarka kaga dole ita ta dace da naiwa liki" aikuwa gurin ya 'dau shewa da tafi mutane wasu suce " wannan haka yake hajiyarmu Allah ya 'kara arziki hisham kuwa ya cika makil dan ganinsa tozarci ne abinda mumynsa tayi masa suka koma suka zauna aka kira maryam da angon bugi,maryam dake zaune wasu irin hawaye masu ciwo suka zubo mata ta yunkura ta tashi tsaye salim ya rike hannunta cikin nashi saurin kallonsa tayi sam bai damu ba ya kauda kanshi kawai ya soma tafiya daita ba dan ta soba ta dinga daga kafafuwanta ."


da zata taka step ya tsaya ta sauko ahankali yana daga mata rigarta d'an kar ya hardeta abun ya burge mutane mc kuwa ya dauka angon gaske ne nan ya fara zuba "kai wannan ango yana ji da matarsa yana son matarsa see love ai nan hankalin mutane ya sake karkata kansu aunty abida tace "dama shi ya aureta muka huta dan sunfi dacewa dashi sultana kuma da adamcy "ke dai kina qaunar sultana da wannan mai shegen taurin kan tsiya "duk zai daina ne bari dai ya shigo hannun mace ."


sosai salim ya kwashi rawa tare da maryam lokacin da aunty abida ta tashi taje liki byn tai liki ta kai bakinta daidai kunne maryam "karshe mai naci kenan da kin nuna baki raayi kamar yadda ATA yayi da yau baki wayi gari da aron ango ba wannan kawai ya isheki misalin irin halin bala'i da zaki shiga a gidansa "har aka gama taron aka watse aunty abida tana mata habaici wanda bata san dalilinta nayi mata hakan ba salim ne ya maida ita gida kai tsaye ta fito ko kallon inda yake batayi ba tashige gida ta rabu dashi dan taji haushin hannunta daya rike shima bai damuba yai tafiyarshi gida mrym tana shiga dakinsu kuka ta saka ranar yadda maryam taga rana haka taga dare ga kuka datasha kamar ranta zai fita."




Karfe daya daidai ata ya farka daga baccinsa ya mike da kyar ya shiga bathroom yayi wanka ya dauro alwala ya fito ya sanya vest da boxer sannan ya daura jallabiya mai garen hannu akai ya qarasa inda daddumarsa yake ya tada sallah bayan ya idar da salolinsa ya zauna yana tunanin awannin daya kwasa yana bacci , can ya mike ya fito zuwa falonsa ya bude fridge bai ga whisky dinsa ba ya kalli inda ya ajiye kwalayen sigari ko karan sigari daya bai samu ba ya maida murfin fridge din ya rufe da karfi yana jan tsaki ."




ya koma ya zauna ya zubawa zanen princess dinsa idanu yana kallonta yana zaune mami ta turo kofar dakin ta shigo idanunta ya sauka akanshi idanunshi sunyi wani irin girma ta zauna a kusa dashi bai yi magana ba har sanda ta soma mgn "adamcynah ka tashi ?"eh na tashi! ya fad'a kawai yana duban zanensa yanayin yadda ya amsa kamar yana jin haushinta."


ta numfasa kana tace "me yasa baka tashi lalata rayuwarka ba sai alokacin bikinka ?me ya kaika shan giya adamcy ?yanzu ka kyauta min kenan ?ka kunyatani acikin mutane kowa sai tmbyrka yake ka kuwa san adadin karyar da nayiwa mutane ? "ni fa bikin nan bashi da wani mahimanci agareni dan Allah sweetheart ki daina min magana akanshi sake daga min hankali yake "jin haka yasa ta canza magana "me zaa kawo maka? "shiru yayi yaki cewa komai dan idan ya bude bakinsa ba abinda zai ce a kawo masa sai giya da sigari su kawai yake buqata "bari naje na kawo maka abinci ta fad'a tana mikewa ta shafa kanshi sannan tayi gaba ."


Tana fita Ya kira yaronsa yace ya siyo masa giya amman wacce tafi duk wanda yake sha karfi da sigari yana ajiye wayar mami ta dawo dakin ta ajiye masa plet din abinci agabansa kaci yanzu da zafinsa ta wuce bai ci abincin ba har sanda yaronsa ya kirasa ya dauka yana cewa "ka shigo mana " mami tana falo okay ina zuwa ya mike tsaye ya sauko lokacin daya sauko mami ta tashi ta shige dakinta ya fita "ya ka dade ?yallabai go slow yafi yawa a shagon siyar da giya fiyye da shagunan siyar da abinci bare adaidai wannan lokacin "okay kaje kawai ya karbi ledar hannunsa kwalba biyar ne aciki sai kwalayen sigari ya dawo dakinsa ya ciro daya ya balle bai tsaya sirkawa ba ya kafa abakinsa bai sauke ba sai daya shanye tass sannan ya daura da sigari haka yayita sha har karfe biyu da rabi ya koma bedroom dinsa wanda alokacin ya shanye kwalba hudu yana kan ta biyar ."




*****
Washegari sunday ya kama daurin aure hisham bai tashi ba mumy ta dinga kiransa a waya gajiya yayi da kiranta ya dauka ya mike zaune yaji dalilin takura masa da take yi, yana dauka ta rufeshi da bala'i "wallahi hisham ka kiyayi fushina idan ba so kake nayi maka baki ba wallahi ka natsu ka shiga hankalinka ka bari ayi komai a gama lafiya "yanzu mumy me nayi ?daurin aure ne a daura mana ai ba lalle sai naje ba "okay ni zaka fadawa haka ?" to dan girman allah karka zo "da taimakon salim hisham ya shirya tsaf cikin wata dakakkiyar shadda gezner fara sol koda suka fito mutane sun cika acikin haraban estate din ."


Ahankali mb da sauran abokansu suka shigo falon ATA kowannensu sanye da farin yadi mai shegen tsada ,basu ganshi ba dan haka mb ya tura kofar bedroom dinsa anan ya gansa kwance a kasa shame shame tamkar matace ,da wani irin sauri ya qarasa inda yake kwance ya durkusa a gabansa yana cewa" Kai adam ka tashi mana lokacin zuwa daurin aure yayi fa "ya fad'a yana kallon kofar shigowa dakin "kai yasir kuzo ku ganshi ya qara shan giya ya bugu fiyye da jiya ya sake kallon fuskar ATA yana shafa fuskarsa ," kai wai meye haka ne ?subuhallah ya bugu kuma? inji cewar salim da yasir da suka shigo atare cikin tsananin tashin hankali."


" kamo shi mb yayi yana cewa "ku taimaka min mu daga shi gbdy suka kamo shi zuwa kan bed dinsa suka kwantar dashi suka dinga jijiga shi" ka tashi dan girman allah lokacin daurin aurenka yayi ,amman shiru kake jin ATA dan ko motsi baya yi numfashi ma da kyar yake fitarwa yasir ya kai hannu ya bude idanunshi yana kiran sunansa," kai ku duba fa kugani kwayar idanunshi sun dauke inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kai abokina ka bude idanunka muna tare da kai dan allah karka min haka bana son na rasaka ."mb ya fad'a cikin tsananin tashin hankali mara iyaka .


"kana jina abokina ka bude idanunka yana magana yana jijiga shi amman har lokacin ATA bai motsa ba bai ma san a halin da yake ciki ba duk yadda sukayi su tashesa amman abun yaki cikin tashin hankali mb yake kallonsa gabansa na faduwa acikin kwana biyu kacal da soma shirye shiryen biki ya zare ya fita haiyacinsa bai ta'ba tsamanin zai shiga wannan halin ba da shi karon kashi ya shawarci mami a hakura da auren kawai kowa ya huta ."


sosai mb yaji babu dadi ganin halin da amininsa yake ciki da sauri mb ya nufi kofar fita daga dakin kunnensa manne da waya yana cewa "hello sadiq kana ina ? "dan girman Allah ka ..ka taimaka min ATA nan ya zayyane masa komai cikin tashin hankali eh kazo da allurar please ya katse kiran ya koma cikin dakin har lokacin kwayar idanunshi bai dawo daidai ba ko dan sambatun nan na bugaggu bai yi ba ."


suna tsaye sadiq ya shigo ya fara dubasa "yana da rai numfashinsa ne yayi nisa sakamakon buguwar da yayi amman zan masa allura nan da wasu yan awanni zai dawo daidai ya ciro sirinji daga cikin bakar jakar daya shigo dashi ya hada duk allurar zaiyi masa bayan yayi masa ne suka fito daga cikin dakin dukkaninsu jikinsu a sanyaye inda zuciyar mb Ke bugawa da karfi kamar wasu kurame haka suka sauko babu ango, ganin mami yasa duk suka dan saki fuska dan karta gane akwai abinda yake faruwa sai dai kallo daya tayi masu ta fahimci akwai matsala tun kafin su kai ga fita ta nufi hanyar dakinsa ."


Tana shiga dakin yana kwance a buge Kmr jiya ta tsura masa ido bata ko liftawa ga wani tashin hankali data tsinci kanta ciki wanda bata ta'ba jin irinsa ba ,bta ta'ba nadama da danasani ba sai a safiyar yau din nan ,gabadaya jikinta ya dauki rawa kasa dauke idanunta tayi akanshi wadan da tuni sun rikice suna qoqarin zubar da hawaye cikin wani irin salo na yan shaye shaye taji yana kiran sunan "my princess kece rayuwata kece duniyata kinki bayyana min kanki saboda baki sona laifin me nayi miki ?yadda yayi maganar da sunan da yake ta faman kira ba qaramin rudar da mami yayi ba ,da sauri ta fito daga cikin dakin tana goge hawayen nadama da danasani sam sam bata ga laifinsa ko jin haushinsa ba domin itace sila jefa rayuwarsa cikin wannan halin ."


mutane masu mahimanci suna zaune acikin massalaci dake cikin estate din abdullahi auren Adam Tariq abdullahi aka fara daurawa tare da maryam abdulra'uf akan sadaki kankani bisa umarnin mami sannan aka daura na hisham Muhammad sani tare da nana hauwa'u tariq abdullahi duk yadda hisham yake son yayi jarumta amman a karshe sai da kwalla ta zubo masa jin an daura aurensa da wata ba da nuzlarsa ba .wani irin bakinciki ne mara misaltuwa ya lullube zuciyar hisham hannunsa salim ya rike cikin cool voice yace "ka sausautawa kanka sannan ka sanya aranka daman can nuzla ba matarka bace ."




Ana gama daurin aure maroka suka fara shela acikin mutane hamdala mami tayi alokacin daakce mata an daura auren sai dai zuciyarta bata cikin jin dadi sannan bakinta bai daina ambaton sunan Allah ba maryam kam fadawa tayi jikin aunty khadija tana fashewa da kuka mai karfi "aunty khadija ta soma rarrashinta kukan murna da kukan bakinciki maryam take bakincikinta yaya adam baya sonta na farinciki kuma burinta ya cika ta auri abun qaunarta ."hajiya zulfa'u ta kira salim cewar suzo da hisham bangaren hjy zulai suka shigo a tare da abokan ango hisham ko kallon inda nana hauwa'u take bai yi ba nan masu daukar hoto dake biye dasu suka shiga aikinsu anyi hotuna sosai ."






Da misalin karfe biyu na rana mami ta shiga dakin ATA tare da mrym yana kwnace adduoi ta dinga yi tana shafa masa a fuskarsa yayinda maryam ta qaraso ta kafeshi da ido tana kallonsa tana jin wutar sonshi na qaruwa acikin zuciyarta qoqarin mikewa yake nan mami ta kama masa ya tashi ta jingina masa pillow a bayansa kallonsu kawai ya tsaya yi kafin ya rufe idanunshi yana sauke ajiyar zuciya "adamcy nah yau ka zama cikakken mutun ina cikin farinciki an daura aurenka da maryam sannna ina cikin bakinciki irin halin daka jefa kanka ciki ta qarasa mgnr tana kuka ".




"meye kuma abun kuka bayan burinki ya cika ?ya fad'a yana goge mata hawaye "kukan murna da bakinciki ne , yau ina cikin farinciki da bakinciki ka taimaki rayuwar mahaifiyarka karka canza daga adamcy data sani ,rayuwa qaddara ce sannan kai muslim ne ka yarda da qaddara kayi farinciki da auren nan ka barwa allah komai "numfashi ya sauke baya jin zai yi wani farinciki da wannna auren maryam kam idanunta na kanshi har sai da taji sautin muryar mami ta doki dodon kunneta "maryam jeki hado masa tea ki kawo masa ta fice daga dakin."




Bayan fitarta da kyar mami tasa shi ya tashi ya shiga yayi brush da wanka sabbin kayansa ya saka lokacin da mami ke fesa masa turare maryam ta turo kofar dakin ta shigo mami ta karfi cup din hannunta da kanta ta dinga bashi a baki tana masa nasiha ita kam mrym duk hankalinta na kanshi sai faman kallonsa take shi kanshi mamakin irin kallon da take masa yayi wanda kallo ne mai dauke da tsantsar soyayya acikin lokaci kankani...."




Mmn sudais


💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗






*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.




Page 30




Ahankali ya d'auke kwayar idanunshi zuwa wani bangaren dabam yana jan tsaki dan bazai iya cigaba da kallonta ba "me yasa sweetheart take masa haka ?tasan baya son ganin yarinyar atare dashi amman ita burinta bai wuce taga sun kasance a waje d'aya ba."


"dan Allah adamcy ka cire damuwar nan aranka ka kwantar min da hankali ahalin yanzu babu abinda nake buqata kamar natsuwarka da kwanciyar hankalinka ,duk duniya babu wanda zai so maka kwanciyar hankali da farinciki kamar ni mahaifiyar ka saboda nice nafi kowa sanin ciwonka ."




"daga ni har kai da duk wani mai qaunarka babu wanda zai so ka qarasa rayuwarka haka batare da ka ajiye iyali ba , sannan zamanka kai kad'ai illa ne ga rayuwarka, idan wasu sun yarda da kai akan baka aikata komai na sa'bo ,wasu bazasu yarda ba, wasu zasu d'aukeka a matsayin mai neman mata ne duba da irin tarin dukiyar da allah yayi maka ,dan haka kayi hakuri ka rungume wannan rayuwar domin itace qaddararka dan adam bai isa ya canzawa kanshi qaddararsa ba."




sosai ya fad'a cikin kogin tunani hankalinsa ya bar duniyar da yake wanda hakan ya bawa maryam damar cigaba da kallonsa son ranta tana jin tmkr ta fad'a jikinsa ta rungumeshi ta rarrashi kayanta ,jin saukar hannun mami jikinsa ya sanyashi dawowa cikin natsuwarsa ya d'ago kanshi ya zuba mata idanunshi dake cike da matsanancin damuwa ."




"Ina neman alfarmar a wajenka a karo na biyu " wata irin razana yayi yayinda zuciyarsa ta soma bugawa da karfi kamar zai fasa qirjinsa domin bai san wace irin alfarma zata sake nema a wajensa ba ,bai ce mata komai ba ya cigaba da kallonta da tsumammun idanunshi yana mai allah allah yaji abinda zata fad'a."


"na gode maka da alfarmar da kayi min na farko na amincewa auren maryam da kayi alfarmar ta biyu ka taimakeni adamcy kayi min alkwarin bazaka sake kai kwalbar giya bakinka ba bare sigari " tayi maganar Kmr zata zubar da hawaye dan tuni kwayar idanunta sun canza kala ."


Wani naunayen ajiyar zuciya da numfashi ya sauke atare dan bai d'auka abinda zai fito daga bakinta ba kenan, ya d'auka zatayi masa magana ne akan tarewar yarinyar "kayi dan Allah dani amadadin giyar da zaka yita sha kana buguwa gara ka rike addua adamcy ,jikinsa yayi sanyi da jin maganarta ya risinar da kanshi kasa batare daya bude bakinsa ba a ransa yace "wannan rayuwarta ce ,ciwona ne ".




ta cigaba da kallonsa shi kuwa bai ce mata uffan ba dan baya son yayi mata aqawarin da bazai cika ba ,bugu da qari baya son a shiga rayuwarsa a barshi da damuwarsa kawai sannan abar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login