Showing 120001 words to 123000 words out of 185716 words
Chapter 41 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
aunty tace "allah yasa shi wai habib dan matsalar daake ta samu akan masu zuwa suna tafiya né yake jin haushi "nima na fahimci haka amman in sha allahu komai yazo karshe dan nasan yahuza bazai mata haka ba nima gsky na yaba da hankalinsa maza tashi kije maryama karki dade maryama bata ji dadi ba ganin habib ya tashi ya barsu km tasan duk akan mgnr fita ne ,amman babu yadda ta iya yaya sadam da aunty suna da karfin iko arayuwarta ta mike ta fita ta bar aunty da yaya sadam suna magana bata san abinda ya cigaba da wakana atsakaninsu ba ."
acikin duhu ta sheida murmushinsa ganin hasken hakoransa ta dan saki ranta da kawar da damuwar fuskarta barkanki da fitowa gimbiya maryama "numfashi ta fesar "kai ya kamata a yiwa barka da zuwa da kuma sannu da qoqarin zuwan da kayita yi baka samun ganina da km qoqarin da kayi da iyayena last week na gode sosai " ya dan kyaleta "iyayenmu dai na gyara miki ." maganarsa ta dan mata dadi wannan yasa ta dan sakin fuskarta kad'an "ya kamata mu samu waje mu zauna ko can ne ya dan nuna mata wani dakali dake makoftansu ."
tare suka qarasa amman shi yaki zama ya tsura mata ido ya kamata ace kece kika fara zama sannan ni tayi shiru dan tuni ta gane manufarsa ta dan kallesa da idanunta cikin sauri ta kawar da kai ganin kwayar idanunshi na kanta to shikenan na zauna kema ki zauna ta zauna tana gyara zaman hijab dinta sukai shiru na dan tsawon lokaci daga bisani ya dago ya dubeta "Maryama zuciyata duk ta gama tattara komai agareki a yanzu bani da wani shakka ko kwankwanto akanki muradina ne na samu damar da zan kawo kaina ga iyayenki domin a samu tsayayyen magana a tsakaninmu ."
Soyayyarki ta jima ajikina maryama nayi dawainiya da soyayyarki tun kafin ki kai wannan lokacin na koyar da zuciyata dabarun da kuma yadda na dauki hakuri dan kawai na samu soyayyarki ban ta'ba gazawa ba , ina sonki maryama da zuciya daya ban qara jin ina sonki ba sai danaji halin da ke da mahaifiyarki da kaninki kuke ciki a gidanku bazan boye miki ba ina jin tausayinku most especially mahaifiyarki domin ta fuskanci abubuwa dayawa akan rayuwa kuma tayi hakuri na tausayawa rayuwar da kuke ciki ki daure ki samar dani acikin zuciyarki mu daga darajan uwa da kuma danuwa mu tallafi rayuwarta data kanin mu dukkan wani muradinki zan bi na tabbatar kina da burin kiyi aiki byn kin qare bautar qasa kamar yadda naji kawayenki suna fad'a,burinki kiyi karatu mai zurfi Kiyi aiki ni nan zan barki Kiyi komai kike só zan barki ya dan saurara yana kallonta hawaye taji akan kuncinta tasan su da mahaifiyarsu abun tausayi né suna cikin tsananin kunci da bazai yuwu a boyesa ba ."
ahankali ta dubesa "naji dadin yadda kace zaka tayani kula da mahaifiyata da kuma danuwana mlm yahuza ina matukar son Mahaifiyata ina son na gatatan rayuwarta domin ita kadace dani na yarda da soyayyarka kuma na amince duk lokacin da kake da lokaci kofar neman aurena a bude take domin burin mahaifiyata kenan na tsayar da mijin aure fatana ka rikeni amana tayi shiru saboda kunyarta ta motsa ya sauke ajiyar zuciya a zahiri take fahimtar farincikinsa dan bai boye ba ."
Yayi murmushi yana shafa fuskarshi "maryama amanarki agareni bake zaki bani amanarki daga allah daya halicceni ce domin shi na dinga roko ya bani ke amatsayin mata aurena allah ya amsa tunda har kin amince min dan haka shi ya bani wannan amanar dan haka nayi alkawarin bazaki taba ganin sabanin haka daga gareni ba ,ba kuma zakiyi danasani ba , aurena zai zame miki abun alfahari bazan ta'ba gudunki ba bazan ta'ba juya miki baya ba ."Soyayyar sati uku da sukai da mlm yahuza ta fuskanci tsantsar son da yake mata kulawa kuwa har da mahaifiyarta abun mamaki kowa a unguwarsu yasan da soyayyarsu wasu nasa albarka wasu nacewa ba girin girin ba allah yasa a d'aure kar ya gudu ya barta kamar sauran."
******
Cikin wannan lokacin maryama da kawarta subai'a suka je adamawa domin suyi cam for three weeks bayan sunyi sati uku a adamawa alokacin mlm yahuza yayiwa wani mutun magana akayi masu change of location ita da kawarta daga adamawa aka dawo dasu lagos inda zasu fara bautar qasa a Z &A comapany dake kan titin guness bayan ciku cikun da mlm yahuza yayi masu domin shine ya shiga ya fita ya kar'bo masu letter suka kai wa nysc aka kar'besu a kamfanin bayan sun dawo lagos suka fara savieces dinsu wannan taimako da mlm yahuza yayiwa maryama ya wanke zuciyar habib yaji ya shiga ransa har ma ya fara kiransa da otherhaif kuma yake girmamasa yana mai jin ba qaramin dace yaruwarsa tayi ba domin kuwa samun maza irinsa suna da matukar wahalar samu ."
"gashi shi dai ba wani zurfi yayi a boko ba dan karatunsa iya diploma ne amman yana da hanya kuma yasan mutane sosai dan shugaban RRS mai ci alokacin abokinsa ne tare sukayi karatun tun daga primary har zuwa secondary inda anan suka rabu amman har gobe suna mutunci da abota , fara bautar qasa yayiwa maryama dadi dan daman zaman gidan ya isheta dan tun da suka qare karatu babu inda take zuwa bayan islamiyya gashi ita daman fita bai dameta ba saboda ita ba maabociya son yawo bace amman wahalar da take sha da yawon sata aiki da mutanen gidansu keyi yasa tayi maraba da da wannan fitar tata kullum fatan allah ya taimaketa tana qare bautar qasa ta samu aiki ."
Ranar wata asabar tana zaune shiru a side dinsu tana tunane tunane akan sakina tana matukar qaunar sakina aranta ta kasa jurewa abubuwan da take mata batare da tasan laifinta ba ,zuciyarta ta bata shawarar taje ta tmbyeta ko wani laifi tayi mata wanda yasa ta canza mata ,nan take ta amince da shawarar zuciyarta , dan hk ta mike tsam ta fito ta nufi side dinsu ta yi sallama a tsakar gida babu wanda ya amsa mata dan haka ta wuce daki inda tafi tunanin sakina take mintuna sha uku da zamanta amman sakina bata ko kalleta ba ."
Ahankali maryama ta tunkarareta da abinda ya shiga a tsakaninsu "haba "yar uwata mai na yi miki ki ke fushi dani tsawon Lokaci ko magana ba kya min mai nayi miki da hukuncina ya cancanci haka.?""Cewa na yi kin min wani abu?sakina ta tambayeta tana mai kallo cikin idanuwanta maryama ta sauke nata idanun ganin irin kallon da Sakina ke mata. Ta ce"tô Sakina tsawon lokaci naga bakya min magana, in da nayi miki laifi ne sai ki sanar dani na nemi yafiyarki bana jin dadin yadda kike nuna ko in kula gareni tsaki kawai sakina taja ta fice tana magana cikin ranta wanda sam maryama bata ji dadin abinda tai mata ba "na shiga uku maryama ta fada a ranta me zai sa sakina ta yi min haka kawata kanwata kuma yaruwarta masoyiyarta?ya Allah ka sanyaya zuciyar sakina akaina idanunta cike da hawaye ta baro side dinsu ."
Ranar wata laraba aunty salma da yaranta biyu suna zaune a tsakar gida aunty salma ta dubi sakina "wai Ke kwana biyu nan mai yake damunki ne sai ki dinga kadaita kanki kina wani shiru idan wani abu aka miki bazaki fad'a ba sakina tace" ko na gaya miki ba iya magance min zakiyi ba duk da ku ka jawo halin da muke ciki nida yaruwata shukura ,maryama dake kokarin shigowa cikin side din nasu ta dan. tsaya ta kasa kunne aranta tace "allah sarki ashe yaruwata laifi akayi mata tayiwa gidan kudin goro kowa bata shiri dashi."
aunty salma tace " koma me akayi muku zurfin cikinku ne ya janyo muku Ke kanki kinsani duk damuwarku kema kinsan zanyi qoqarin magance muku ita matukar ina numfashi acikin duniyar nan sanar dani menene aka muku da har yake saka ki cikin kunci "kusan rabin yan makarantar islamiyyarmu sun san yadda shukura ke son mlm yahuza amman kiri kiri kuna kallo wannan banzar ta juya abun ya koma kanta gashi har ana batun saka rana aure ."
Da alamun aunty salma taji dadin furucin sakina akan maryama domin duk irin kunci da halin koin kula da suke ciki da sakina bata gani ba bare ta shiga cikin maganar tayi musu sulhu "aunty salma tace" to meye keda yaruwarki ? maryama ta fahimci kalmar cikin zolaya tayi maganar ,ai kuwa nan da nan sakina da shukura suka bata rai cikin nuna tsantsar tsana "wannan banzar ce yaruwarmu daace kun koresu a gidan Kmr yadda kika ce ai da bata yiwa shukura kwacen saurayi ba yanzu gashi nan muna ji mun gani wanda shukura take so dole zata hakura "a'a waya gaya maku ai babu wani maganar wani hakuri ,kuyi hakuri tunda kun fad'a min ku bani kwana uku zaku ga abinda zai faru."
hankalin maryama ya tashi kwarai da gaske har yasa daga nan bata sake sanin abinda suka cigaba da tautaunawa ba saboda wani daci da zuciyarta ta dauka ."jiki a matukar ta sanyaye ta dawo side dinsu "ita bata san shukura tana son mlm yahuza ba da sam bazata amince da soyayyarsa ba sai ma ta hadasu amman yanzu ya zatayi ?ko da yake ta fahimci wani sabon salon cin zarafi ne ake son bullo mata mata dashi dan arabasu dan haka zata bari adduarta tayi karfin da bazasu samu nasara akanta ba tun daga ranar bata sake runtsa idanuwanta ba wajen kiyamul laili domin kiyamullaili tana qarawa nauyin mizanin bawa, tana qarawa mutun hasken fuska da samun kwarjini da d'ga darajan mutun acikin mutane kariya ga dukkan sharri tare da biyawa bawa bukata."
Duk bayan kwana biyu mlm yahuza yana zuwa wajenta Kmr yadda ta tsara masu dan bata son yawon zance ,tun bayan kwana biyu sunyi da mlm yahuza zai zo sai dai har karfe takwas na dare daya saba zuwa bai zo ba amman ta rasa dalili hakan ta kasa hakuri ta shirya tsaf ta fito zuwa bangaren Ummah ta iske shukura tana zance sai dan kasancewar dare bata lura da wa take zance ba sai dai kawai kamshin turarensa yayi mata kama dana mlm yahuza amman ko kadan bata kawo shi bane ta shiga bangaren umma tana zaune suka gaisa
Daga nan suka shiga hirar duniya har sanda shadaya ta buga ta mike tayi mata sallam ta koma side dinsu cikin tsinkewar zuciya dan bgabanta banda luguden bugawa babu abinda yake ."
Shigowarta kenan daga wani kamfani kai zanenta domin tallatawa ,da baba gali ta soma ci karo "yar gwal idan kin huta ina son magana dake dam taji gabanta ya fadi tun da take arayuwarta bata jin ranar da baba gali yace yana son magana makamanciyar haka ba km wai yar gwal yana son magana daita tabbas akwai mahimmiyar magana , bata kawo komai aranta ba sai tunanin watakilla ko mgnr mlm yahuza ce tayi karfi tunda ya sha fad'a mata yana son manya su shiga ciki ta nufi bangarensu ta kammala komai nata a natse ganin shima ya fita masaalaci tayi sallah har ishai sannan ta dawo parlour ta zauna zuciyarta na tunanin akan maganar da baba gali zai yi daita duk da bata san abinda zai sanar daita ba amman sai maganar ta tsaya mata arai cike sa fargaba ."
Karfe tara daidai umma ta aiko a kirata ita da aunty nan fa gaban maryama ya cigaba da fad'uwar da yake , tare suka fito da aunty alokacin shukura ta shigo daga zance tuni aunty ta wuce dan har ta kusan isa bakin side din umma, haka nan ta kalli shukura dake zaune kusa da aunty salma dake cin abinci atsakar gida ta sake gaishe da aunty salma ta wucesu ta shiga bangaren umma ta gaisheta cike da girmamawa umma taji dadi sosai ta tmbyi lafiyar habib ."
shiru ne ya biyo baya har na kusan mintuna asirin sai ga aunty salma da aunty hassana sannan byn an gaisa umma ta numfasa tace "Maryama wata tmby nake son nayi miki game da yaron nan dan gidan lawan yaro ?"dam taji bugawar da qirjinta yake ya qaru , tayi shiru domin bata damar tmbyrta ta cigaba da magana "tsakanin keda shukura wa yace yana só né ?"
Maryama tayi shiru lokacin da maganar ta doki dodon kunneta wannan wace irin magana ce akwai abinda umma batasani ba a tsakaninta dashi ?amman dai koma menene batasan abinda yasa take mata wannan tmbyr ba, ta bude baki zata bata amsa abinda Ke tsakaninsu sai kunya ta hanata tayi kasa kawai idanuwanta "Maryama tmbyrki nake baki ce komai ta sake yin shiru a karo na biyu tana son jin ba kece wacce kuka fara son juna ba har yake zuwa zance wajenki ba ? ta sake yin shiru tana son bata amsa sai dai bazata iya sanar daita ba tunda gashi ita da kanta tasani kuma tana da masaniyar wajenta yake zuwa, ita me yasa umma zatayi mata wannan tmbyr akan abinda ta rigada tasani tunda sau tari ita ke cewa taje idan yazo bata son fita ."
"Abinda yasa na kiraki nake tmbyrki shine dazu da yamma byn fitarki kai zane yan gidansu sunzo domin auren diya a gidan nan kuma sun bayyana wacce suka zo nema ni da azatona kece yahuza yake zuwa wajenki ashe yaruwarki shukura yake so ."
ba idanuwanta ba hatta numfashinta da kwakwa luwarta sai da suka daina aiki wani tsayawa tayi na wani lokaci kafin ta sauke naunayen ajiyar zuciya ta juya idanuwanta kana tashiga tunani da kwakwa luwarta batace komai ba saboda tashin hankali daya risketa ta sunkuyar da kanta qasa kawai tana jin damuwa mai tsanani "
"Magana nake maryama kinyi shiru daman bake yake nema ba yauruwarki yake nema ?ta qara yin mata tmbyr bata san abinda zatace ba ganin zata batawa kanta lokaci da jama'ar dake wajen yasa ta dago kanta tace "tunda shi da kanshi ya sanar da wacce yake nema ai babu laifi umma , umma tayi shiru kawai tana dubata ina son gane abun ne domin ni a tunanina Ke din ce yake zuwa wajen ki kawai ta dago tace "ba wajena yake zuwa ba wajenta yake zuwa tana gama fadar haka ta mike da sauri dan zamanta a waje zai yasa ta zubar da hawaye ta bayan bangarensu inda aunty Ke aiki ta labe tana kuka mara sauti dan kar wanda ya ganta ta tsaya anan ta rarrashin kanta ne dan karta dagawa danuwanta hankali."
Sai datayi mai isarta sannan ta fito ta shiga falo kai tsaye ta wuce habib dake zaune yana kallon ball dakinta ta shiga ta kwanta lamo akan katifa ahankali kalaman mlm yahuza daya dinga furta mata suka dinga dawo mata cikin kwakwaluwarta da taimakonsa gareta