Showing 96001 words to 99000 words out of 185716 words
Chapter 33 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
sultan ,fahad , hamid a wani goma sha biyu kawai na baku ku dawo da komai idan ba haka ba..... "me zakayi ?sultan ya katseshi cikin zafin rai "me ka isa kayi ?babu abinda ka isa kayi "
"kunsan su dabbobi basu gane yaren biladam sai na dabbobi yan'uwansu dan Allah karku dawo da kudaden nan alokacin da nace "yana gama fadar haka ya mike tsaye ya tura kujerar daya tashi baya ya fice ."nan hayaniya ta kaure kowa na fad'ar albarkacin bakinsa kai tsaye mr ata office dinsa ya koma ."
Karfe biyu daidai na rana mami na zaune a parlour tare da yaranta maryam da nana hauwa'u suka jiyo sallamar baba qarami sai da gaban mami yayi wata irin mummunar faduwa ya qarasa shigowa yayi wa kanshi mazaunin nana hauwa'u ta gaishesa haka ma maryam ya amsa fuskarshi babu yabo babu fallasa mami ta kallesu alamun su basu waje ,bayan sun tashi sun wuce mami ta fuskancesa alokacin da shima ita yake kallo "zulai naji shiru akan maganarmu banji kin neme ni ba har gashi an saka ranar auren adamu da wacan yarinyar yana da kyau nasan inda maganarmu ta kwana abun nan zai yuwa ko kuwa ?".
mami ta numfasa gabanta na faduwa domin dai ita kam bazata iya sake kuno wa danta wata damuwar ba maryam ma da yaya ya karbeta ?gara kawai ta ari bakin adamcy tace masa a'a tunda tasan ko ta tunkaresa da batun bazai ta'ba amincewa ba cikin shakkakiyar murya tace "nayi masa magana ammm..."sai tayi shiru tana jin nauyin fitowar maganar "amman me ki fada min abinda yace "Uhm daman cewa yayi wai mace daya ta .."
shiru tayi ta qasa qarasa maganar ganin wani irin kallon da baba qarami ke mata ido cikin ido furzar da iska yayi ya lashi lebansa na kasa sannan ya hade hannunwansa still idanunshi na kan fuskarta cikin danne fushinsa dan baya son ta gane fushinsa a fili saboda abinda kan iya zuwa yazo bare su suyi zargin da hannunsu ,cikin dakewa yace "yanzu dai kin nuna min bazan iya zuwa neman alfama wajenki kiyi min ba ko ?sam sam ba haka bane kai ma kasan halin adamcy idan kuma zaka iya masa magana da kanka to kayi kamar ma haka zai fi "no ba sai nayi masa kema uwarsa da kika haifesa bai ji maganarki ba maganar ubanwa zai ji ? " iya abinda ya iya fada kenan ya tashi ya kama gabansa ya barta cikin zullumi."
Mr ata a matukar gabalaice ya qaraso gida zuciyarsa tamkar zata kama da wuta , sai dai cike da qasaita ya shigo parlour'n Mami babu kowa parlour'n sai qarar tv da motsin masu aiki a kitchen ya zauna akan doguwar kujera ya d'ora kafarsa d'aya akan d'aya yana ciza gefen lips dinsa ,ko cikakken second goma bai yi da shigowa ba sai ga hindu ta shigo dan akan danunta ya shigo tunda mahaifinta ya fad'a mata yadda sukai da Mami ta kasa tsaye ta kasa zaune , zama tayi a kujerar dake fuskartashi ta tsura masa idanunta tana kallonsa tamkar ranar ta fara ganinsa tana qoqarin bude baki tayi masa magana ya mike tsam ya kwashe wayoyinsa ya haye samansa yana jan tsaki dan shi ya tsani yawon kallo , kamar ta dakatar dashi amman ta kasa ta cigaba da zama zuciyarta na mata wani irin bugawa akanshi ."
tana nan zaune har mami ta fito sanye cikin doguwar rigar na atamfar super exclusive sabuwar bugu ,mami bata tsufa saboda tsanani tsafta da gyaran jiki fuskarta a sake tace "a'a hindu yaushe kika shigo ?ban wani jima ba mami nazo wajen yaya ne "to ai bai shigo gidan ba tukun .
ya shigo yanzu ya hau sama "to shikenan bari naje dakin nasa nazo har ta juya hindu ta kirata sunanta cike da rauni "mami !"
Cak mami ta tsaya tare da juyowa ta tsurawa hindu ido "mami da gaske kin yiwa yaya adam maganata yace miki a'a ?"shiru mami tayi shiru ta rasa me zatace mata kafin mami tayi wata magana hindu ta cigaba da mgn cikin rawar murya "dan girman allah mami karki yi min tsakani da ya adam kullum zuciyata tafasa take akan sonshi Ke kad'aice zaki iya taimakawa zuciyata idan ba haka ba zan mutu cikin rawar murya mami tace "mutuwa kuma ?"kanta ta gyada mata tare da cewa "da gaske zan kashe kaina shine fansa akan soyayyar ya adam "na shiga uku ni zulai "mami ta furta acikin zuciyarta "kiyi addua hindu ni kaina zan só adamcy ya auri mata fiyye da biyu amman raayinsa ne auren mace daya macen dayan ma da kyar ya amince amman Kiyi addua nan gaba idan rabo sai ya qara dake da sauri ta runtse idanunta kana ta koma ta jingina bayanta da kujerar da take zaune tana jin wai irin faduwar gaba mai tsanani ahankali take zubar da hawaye ganin da gaske tarasa farincikin rayuwarta "anya kuwa mami nada tausayi da imani ."Anya mami bata da son zuciya ?"Tayi wa kanta tambayar tana jin radadi acikin zuciyarta bazata iya jurar rashinsa ba ,bazata iya ganin da wata a matsayin matarsa ba, yadda bazata zama matarsa a farko ba to babu wacce zata zama "hindu bari naje naga yayanku nazo hindu ta bude idanunta da kyau tana kallon bayan mami dake taku ahankali."
Kai tsaye kitchen ta shiga ta bud'e firdge kwalin dynsimo mai sanyi ta ciro ta rufe ta qarasa inda cup's suke ta dauki daya ta daura akan qaramin tray ta fito ta wuce a parlour ta samesa zaune akan kujera yana sanye da singlet da gajeren wondo ta bude kwalin juist din ta tsiyaya a glass cup taja qaramin table din glass din dake tsakiyar dakin ta dora tray ta mika masa cup ya girgiza mata kai tace "na kawo maka ruwan sanyi ?ya sake girgiza mata kai "coffee fa ? still dai kai ya girgiza aranta tace yau dai akwai damuwa ta d'an zauna gefensa "ka daina barin damuwa na hana zuciyarka sukuni "naji sweetheart amman ba wani damuwa bane zazzabi nake ji kawai "sannu bari naje na kawo maka magani ka sha "no need sweetheart thank you "kai har yanzu bakasan ka girma bane meye abun gudu a magani ?ni dai kawai bana só né da zarar na kwanta nayi bacci zanji daidai ,tô karka kwanta yanzu magariba ta kusa ya gyada mata kai yana mai runtse idanuwanshi ta mike tana cewa "me zaka ci dan tuwon shimkafa kayi yau idanunshi ya dan bude kadan "karki damu sweetheart yau bazan ci komai ba amman zuwa anjima I need coffee tasan haka tsarinsa yake wani lokaci sai ya kwana ya yini bai ba ."
*****
Tsawon kwana Uku kenan rabon maryama ta shiga harka mahaifiyarta har ma da habibi hakan kuwa ba qaramin taga masu hankali yayi ba gabadaya gidan yayi wani iri saboda rashin walwalar maryama ,ta kuma san duk akan abinda take son tayi ne domin tasan halinta tasan abinda take so da abinda bata só tana da tsananin hakuri amman idan kaga ta kafe akan abu to dole abun zai zama gaskiya ne ko alkhairi ga rayuwar mutun ,ta sani gsky take fad'a mata amman bazata iya abinda take bukata ba bazata ta'ba komawa garesu ba duk runtsi duk wahala zata daure ta cigaba da rayuwarta a yadda take yi , maryama fa ta dauki zafi sosai akan aunty da habibi duk lokacin da ta fito parlour'n tagansu sai ta koma daki ko taje bangaren umma bata dawowa sai dare da zarar tashigo kuma zata shige daki tayi kwanciyarta ko ta dauko kayan zanenta ta fara aiki ."
Da misalin karfe tara na daren ranar litini maryama tana zaune akan kujera ta cilla pencil a bakinta tana taunawa a hankali idanunta na kallon celling dakin tana nazarin abinda zata zana taji an turo kofar d'aki ahankali ta kai dubanta ga kallon kofar dakin ,aunty ta gani tsaye ,ta dauke kanta daga kallonta, aunty ta maida murfin kofar ta rufe ta soma takowa zuwa inda maryama take tana ganin haka ta mike tsam ta haye saman gado tayi kwanciyata tare da kamkame jikinta tana jin tausayin kansu na sake ratsa ko ina ajikinta musamman take jin kewar yanuwan mahaifiyarta da bata taba daura kwayar idanunta akansu ba amman tana jin ajikinta zasu samu kulawarsu da soyayya a duk sanda suka had'u kamar kowani dangin uwa tana kallo aunty ta zauna daidai inda fuskarta take dan hk da sauri ta runtse idanunta tana son tayi bacci ."
bacci bai samu nasarar d'aukarta ba ta juya dayan bangaren sakamakon kukan da Ke shirin kufce mata dan ita kanta dauriya kawai take akan sabon canjin data kawo a tsakaninsu hakan bai hana aunty ganin abinda take ba ,daidai inda fuskarta ke kallo ta dawo ta zauna tana dubanta hade da kamo hannuta cikin nata "me nayi miki my princess kike qoqarin Kaurace min byn Kinsan bani da kowa bani komai sai ku ? Kafin maryama tayi yunkurin cewa wani abu aunty ta sake jiho mata wata tmbyr "yanzu na cancaci haka a wajenki ,"?"Na lura kina bukatar rayuwata princess "idan kika bari damuwarki ta kasheni shikenan sau ki huta ai .... "
a d'an zabure maryama ta mike zaune daga kwance da take suna fuskatar juna da aunty yayinda hawayen idanunta suka shiga xubowa sharrrrrrrrr....."
" meye kuma abun kuka daga magana "kiyi hakuri aunty nasan damuwata na damunki ina kukan ne saboda an cuceki an rabaki da yanuwanki da iyayenki alhalin suna sonki , bansan yadda zan misalta miki yadda nakeji ba, aunty ki taba zuciyata kiji yadda take bugawa tayi mgnr tare da kai hannuta ta kamo hannu aunty ta d'aura daidai saitin zuciyarta dake wani irin bugawa tamkar ana buga mata guduma, tabbas aunty taji kokawar da zuciyar keyi amman bata yadda zatayi gurin raba zuciyar da damuwa addua dai ce kuma tana kanyita babu dare babu rana kuma tasan ubangijinta baxai barta haka ba batare daya duba lamarinta ba.
cikin murya me cike rudanin rayuwa maryama ta cigaba da mgn "bansa me zanyi abubuwa su dawo mana daidai ba har ki cigaba da rayuwarki kamar da? " aunty ki daina daukar iyayenki da yanuwanki a matsayin makiyanki ,iyayenki suna sonki fiyye da tinaninki ,sun nuna miki so da kauna tattare da kulawa da gata alokacin da kike zaman lafiya dasu aunty kema kanki Kinsan irin soyayyarsu garenki "aunty !!! ki daina ganin laifinsu sannan ki dai jin zafinsu dan su dauki fushi dake ?"
Su iyaye ne zasu iya yin komai suci lafiya a yanayin yadda rayuwa tazo miki cike da rudanin yaci ace zuwa yanzu kin samu y'anci ki tsinci kanki cikin farinciki da jin dad'in rayuwa kwana uku kawai da baki ga walwalata ba kin daga hankalinki inga bana cikin gidan nan ?"ina ga nabi wani na barki ya zakiji ? wallahi iyayenki suna can cikin tsananin kewarki kwatankwacin yadda kike jin namu da zaki koma garesu zasu karbeki su kuma yafe miki " kiyi hakuri aunty ki daina ganin laifinsu ta karasa fadar haka tana xubda wasu zafafan hawaye hade da rike hannun aunty gam tana me tausayawa rayuwarta ."
"Idan abubuwan dake faruwa suka cigaba da faruwa bana tinanin zuciyar dake kirjina zata cigaba da baguwa ni dai ki koma cikin yanuwanki dan Allah ki roki gafarar iyayenki su yafe miki mu cigaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba . ahankali aunty tashiga bubbuga bayanta "kukan ya isa haka
Inshaallahu zan .. zan.. koma garesu da izinin Allah sosai aunty ta dinga rarrashinta da gaya mata maganganu masu dadi da sanyaya rai har ta soma bacci ajikita cike da samun kwanciyar hankali .
Washegari kowa yasan maryama na cikin kwanciyar hankali wanda hakan ya kwantar da hankalin babib da aunty tare suka ci abinci kamar yadda suka saba ,maryama tana zaune a falo byn tayi wanka ta shirya tana kitsa gashinta gida hud'u sakina ta shigo suka sha hirarsu duk aunty na jinsu sosai taji dadi aranta ganin maryama ta saki ranta ,har sakina ta fita ta dawo "maryama amman yau zaki islamiyya?"eh!zani idan na gama zan biyo miki sakina ta qarasa fita ita kuma ta mike ta shiga daki tai sallah ta qara shiryawa ta dauki alqurani ta fito ta tsaya a bakin part dinsu sakina tana jiranta byn ta gaishe da aunty salma sakina ta fito ta tsaya kusa da maryama tana mata magana kasa kasa aunty salma ta bisu da harara har suka fice ,ta nemi guri ta zauna zuciyarta na tafasa ."
ta rasa yadda zata kawo karshen shakuwar sakina da maryama duk duniya bata da abinda ta tsana tamkar maryama tayi shiru cikin tsanani tunani abubuwa da dama take sakawa in dai da rai da lafiya sai ta rabasu domin itace kadai hanyar da zata nunawa maryama tsangwama da tsanar datayi mata shegiyar yarinya kamar mayya ko aljanna zatace banda abun sakina ai maryama matsala ce arayuwarta, yanzu ko saurayi idan sakina tayi yayi ido biyu da maryama ai tuni zaice shi ga wacce yake so yarinyar ta cika kyau haka kamar ita tayi kanta ta fad'a acikin ranta ta mike tsaye cikin takaici to ko afa zata kaiwa kukanta , zuciyarta ta kawo mata dauki da wannan tunani aikuwa hakan shine mafuta afa shine zai kawo mata karshen komai da karshen wannan shakuwartasu mayafinta ta dauka ta yafa ta fice daga gidan tana surutai ita kadai kamar yadda na shiga na fita na rabaki da duk wanda yazo da sunan yana sonki da aure yanzu ma sai na rabaki da sakina takowani hali ki cigaba da rayuwarki Ke kadai Kmr mayya acikin gidan nan ."
Tayi sallama aka amsa mata daga ciki dan haka ta shiga ta tsaya afa da yake ciki bai amsa ba yayi gyaran murya hakan ya tabbatar mata akwai wani aciki ta dan jira na rabin awa sannan wacce take ciki ta fito suka gaisa ta fice a karo na biyu tayi sallama ta shiga cikin dakin ta durkusa ta gaishe shi yana zaune akan daddumar sallah wani katon tray mai cike da katon kasa da wuri na duba ya amsa mata cike da kulawa "meye ma sunanki yaushe rabon na sakaki a idona ?"Aunty salma tayi murmushi tace afa kenan abine sai ahankali idan ka ganmu tamu ce ta kawo mu yayi murmushi ya dan shafa gemunshi yana lashe lebensa "to ina jinki fara bayanin abinda Ke tafe dake kafin na duba naga gskyar lamari ".
Mmm sudais
💗💗💗💗💗💗
MAR'ADAMS
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura wa wannan 0913691 8331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 15
"Aisha , saber, da mahamud , ta gani tsaye akansu suna huci kamar zakuna cikin matsanamcin tashin hankali mara misaltuwa suna kallonta kamar zasu cinyeta ai babu shiri daga bilkisu har ussein suka mike daga jikin juna hankalinsu yayi mugu mugun tashi ."
bilkisu ta tsaya tana kalle kallen inda zata boye acikin d'akin tare da cure hannayenta waje d'aya jikinta na