Showing 99001 words to 102000 words out of 185716 words

Chapter 34 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4720

sake d'aukar rawa bata ta'ba shiga tashin hankali da nadama irin na ranar ba domin har ga Allah bata ta'ba tunanin zasu bibiyi takunta ba ."


Nan da nan idanunta ya kawo ruwan hawaye ba tace komai ba, ta durkusa qasa bisa gwiwo
winta dan tasan sai na lahira ya fita jin dadi mahamud ya rike kungunsa yana cigaba da kallonta ,mamakinta kawai yake dawainiya dashi idan aka fad'a masa cewar zata biyo nmj har d'akinsa bazai ta'ba yarda ba, watakilla ma da sai ya wankawa wanda ya fad'a masa hakan mari "dan girman Allah kuyi hakuri ku yafe min ku rufa min asiri kar mumy tasani ta karashe mgnr tana kuka cikin tashin hankali mahamud ya buga mata wata razananniyar tsawa data hargitsa mata lissafi "yi min shiru makira bana son jin komai daga bakinki ."


nan take tayi shiru kukanta ya qaru ta kalli inda ussein yake tsaye shima kana kallonsa kasan baya cikin natsuwarsa "mahamud tsayawa kayi kallonta bazaka fara cin ubanta tun anan ba ? Aisha ta fad'a tana mata wani irin kallo shi kuwa wanda aka kira da mahamud tunanin yake idan yace zai ta'bata to babu shakka zata mutu idan kuwa bata mutu ba zata jikata ."


"dan girman allah Aunty ai.."ai bata kai ga fad'ar abinda take son fad'a ba taji wani gigitaccen mari hagu da dama akan kuncinta "you are very stupid bilkisu , akanki aka fara soyayya?" kin haukace kin makance akan wannan banzar ,me yasa zaki mance ko ke wacece ? wato soyayya tasa kin manta matsayinki ? cikin muryar kuka tace " a'a Aunty aisha ban mance ba amman kuyi hakuri wallahi bazan sake ba "hayaniyar yan yan'uwanta ya sake d'aga mata hankali shi kuwa ussein sunkuyar da kanshi. kasa yayi yana tunanin ficewa ya bar d'akin dan yasan Allah ne kawai zai kwacesa a hannunsu ."


Kai tsaye bilkisu ta nufi bayan kofa ta boye jikinta na wani irin rawa sakamakon jiyo muryar hajiya rahma tana cewa "ina bilkisu take naga kun tsaya jugun jugun ko ta gudu ne ? kafin kace me an samu wanda yazo ya fad'a mana halin da'ake ciki a guje na bazamo na bar hajiya dan bazan iya jiranta ba kasancewar tana fama da lalurar ciwon kafa ."


" ina tafiya ina neman layin yan' uwansashi da kyar na samu ta abban sadam yana gama jin bayanina cewa yayi babu ruwansa dan yasan halinsa da tara yammata , babu yadda banyi dashi ba yace bai zuwa koina ya kashe wayarsa jin abinda ya fad'a yasa na kira yayyensa mata ."


Ina shiga unguwar naga jamaa sun yi cirko cirko!! ga manya manyan motoci na gidansu bilkisu jere a kofar gidan ,haka ina shiga cikin gidan mutane na gani makil kowa na fadar albarkaci bakinsa ,yayinda muryar mahaifiyarta ya karad'e koina acikin gidan "da gaske ne bilkisu tana cikin wannna ru'babben d'akin ? Aisha ta nuna mata bayan kofar d'akin "tana ciki kuwa ga makira nan a bayan kofa ta fad'a tana zubar da hawayen takaici ."


"inna lillahi ! hjy rahma ta furta a fili cikin tsananin tashin hankali "kunji abinda naji kuwa wallahi ji nayi zuciyata kamar ta buga ?hankalin bilkisu ya bar duniyar da muke alokacin dan sai wuri wuri da idanu take shi kansa ussein kana kallonsa kasan nadama ne acikin ransa nadama irin wacce bata da wani rana ."


" amman bilkisu bakince min kin rabu dashi ba ?jikinta na rawa ta shiga gyada mata kai alamun Eh! tana bawa mahaifiyarta hakuri da wani irin fushi ta juya inda ussein yake cike da nadama ta shiga zabzabga masa mari ta koina "bana ce maka ka rabu mun da yarinya ba ? ba banace karka sake shiga rayuwarta ba?"Ko kaga yarinyata tayi kalar wacce zaka ce kana so ? ta juya zuwa ga bilkisu " Ke yanzu har wannan qazamin ne abun so a wajenki ? ta fad'a tana sake juyowa ta d'aga hannu zata sake tsinkawa ussein mari nayi saurin rike mata hannu ina bata hakuri "kiyi hakuri hjy sam ussein bai kyauta ba daya bawa yarinyarki damar zuwa inda yake ,ya karbi laifinsa ayi masa afuwa in sha allahu hakan bazai sake faruwa ba Kinsan kowa da irin jarabawarsa dukkanin rayuwa rubutaccen lamari ne daga Allah ,kuma kowani dan Adam yasan da haka ,yanzu tunda abun ya zama haka ku bamu dama sai mu turo ayi maganar aure "."




Wani irin kallo gabadayansu suka bini dashi ,hjy rahma tace "Allah ya tsareni na had'a zuria da wannan ta nuna ussein da yatsanta tana hararsa "wallahi bilkisuna tafi karfen aurensa ki kalleta sama da qasa ki kallesa ta ina hadin yayi daidai ? duk nasan da haka hjy amman a wajenta shine daidai bugu da qari rayuwar yarinyar ku zaku duba domin ita diya mace ce zata iya fad'awa kowani hali ."


"Ba kowani hali zata fad'a ba ko mutuwa zatai sai dai ta mutu na yarda na rasata gbdy akan na bawa wannan matsiyacin aurenta ta numfasa tare da sa tafin hannunta ta share hawayen idanunta "hjy ki daina furta haka shi soyayya allah ne yake had'awa , kuma babu ruwan soyayya da tsiya ko arziki yarinyar nan tana qaunarsa shima kuma yana sonta dan girman allah ki barsu suyi aurensu kowa ya huta sannna babu wanda yasan matsiyaci ko mai arziki sai Allah sannan babu wanda yasan mai gobe zata haifar ku barsu su aure juna domin samun kwanciyar hankali ."


bata kulani ba har na dasa aya ta fuskanci bilkisu yayinda gabadaya yanuwanta kacokan suka maida hankalinsu Kan ussein duk sun qagu suga hukunci mahamud akan ussein kasancewarsa soja , hjy rahma ta matso sosai kusa da bilkisu tana cewa "ba dai ni zaki wulakanta akan namiji ba ? ."babu irin rarrashin da ban miki ba ,babu irin hakurin da ban baki ba ,me kike son dani ? "wallahi zanyi dake bilkisu , yau zaki ga tozarci ganin idanunki tunda kika nemi ki wulakantani akan wani banza can wanda ba kowan kowa bane shi ,ba kowa bane iyayensa a duk fadin garin nan hasalima rayuwarsa a banza take ."


"zaki wulakantani akan wani nmj banza da wofi wallahi zanyi dake muddin kika ce shi zaki aura sai na tsine miki na tsinewa auren ,wallahi auren bazai ta'ba yin albarka tana mgn tana zabga mata mari a fuskarta da bayan hannunta , yayinda azaba tasa bilkisu ta shiga karewa dan kar marin yayi mata illa amman matar nan sai zabga mata maruka take kuma a fuska na rantse miki da girman allah maryama tayi mata mari yafi guda tara ajere ana goma ne bilkisu ta rike mata hannu kuma nasan azaba ce tasa tayi haka ,aiko matar nan ta danneta da iyakacin karfinta ta dinga dukanta tana cewa ni zaki rikewa hannu in sha allahu kema sai ya'yanki sun miki abinda kika min ,sai sun hanaki kwanciyar hankali kamar yadda kika hanani kwanciyar hankali a karshe kafa mata hakori a damtsen hannunta."




"wani irin gigitaccen qara bilkisu ta saki mai ban tausayi tana kuka tana neman d'auki gashi babu wanda ya kwaceta daga hannun mahaifiyarta sai dukanta take tana hadawa da zagi ganin haka yasa ussein ya nufi hjy rahma cikin tsananin fushi kamar mayunwanci zaki idanunshi sun kad'a sunyi jajur yasa duka hannunsa zai d'agata daga Kan bilkisu ai ganin ya ta'ba mahaifiyarsu gbdy yan'uwanta suka yo Kanshi shi da bilkisu cike da jin haushi suka dinga dukan su kamar zasu kashesu suna furta mahaifiyarmu zaka duka ? azahiri gaskiya ba wai dukanta yayi ba kawai ceton bilkisu zai yi daga dukanta, ina kuka ina basu hakuri ina qoqarin kwatarsa daga hannunsu amman ina sarkin yawo yafi sarkin karfi dan sai suka daina dukan bilkisu suka cigaba da dukansa shi kad'ai har sanda hjy ta shigo zubewa tayi kasa tana kuka tana cewa "zaku kashemun d'a ne to wallahi idan kuka kasheshi hukuma ce zata rabamu daku dan wallahil azim bazan ta'ba yarda ba ".


"kar Allah yasa ki yarda daman kece uwar matsiyaci ? "nice uwarsa kuma gatansa kuma ni d'ana ba matsiyaci bane dan me zaku masa haka ?
"ai yarku zaku jawa kunne ta daina zuwa inda yake shi meye laifinsa ? "laifinsa kulata da yake yi idan baya kulata bazata zo inda yake ba ,idan yace baya sonta karta sake zuwa inda yake ni nasan bilkisu bazata zo inda yake ba ki fad'a masa da babban murya ya rabu da kanwarmu ya zauna lafiya idan ba haka ba zamu 'batar dashi agarin nan ,kina ji kina gani zaki rasa d'anki har abada "hjy na fad'a 'yanuwan bilkisu na maida mata martani kuma basu daina dukansa ba ."




"neman layin 'yanuwasa mata na sake yi saadatu na d'auka na saka mata kuka ina cewa "bazaku zo ba sai an kashe maku da'nuwa ?dan girman allah kuzo ku hanzarta karku bari su illatashi "bilkisu cikin kuka ta rarrafa ta rike kafafun mahamud domin duk yafi dukan ussein cikin kuka tace "yaya dan girman allah kayi hakuri ka barshi karku kashe min rayuwata sannna karku rabani da dashi wallahi bashi da laifi nice mai laifi" .


"ya salam! ya furta a matukar fusace "wai bilkisu me ke damunki ne "?ta girgiza masa kai idanunta na zubar da ruwan hawaye kuyi hakuri nayi maku alkwarin bazan sake zuwa inda yake ba "muryar hjy rahma ta sake karade d'akin Aisha riko hannun makaryaciya karta gudu shi kuma sheidani ku fito min dashi yau zan nuna masa koni wacece agarin nan zanga uban da ya isa ya kwaceka Aisha ta riko hannun bilkisu gam bisa umarnin mahaifiyarsu sai dai bilkisu ta dinga turjewa nan ma wani marin aisha ta kai mata tuni daman fuskarta ta canza jini ya kwanta a duka idanunta ."


Mahamud kuwa qarasawa yayi inda ussein yake yace ya kama kunnensa ussein ya kama kunensa cikin kaduwa dan gbdy bai fahimci abinda yake nufi ba mahamud yace "you're very stupid I mean kayi frog jump Aishat ashe ma illiterate ne wallahi ko da wasa naji ka qara shiga harkar bilkisu zan mugun baka mamaki "mugun ma illiterate katon jahili liability kawai a haka zamu bashi aurenta sai kace kwakwaluwarmu ta juye ai har abada ,ka wuce dashi kaci ubansa ta yadda ko mai kama daita ya gani da mugun mugu zai arce ."


bilkisu na kuka ussein na frog jump nima ina biye dasu ina basu hakuri haka hjy hakuri take basu hankalinta a tashe muna fitowa kofar gida sai ga saadatu da fatima a rude basu tsaya neman baasi ba dan na rigada na fad'a masu komai sausauci suke neman masa amman mutanen nan suka ki banda cin mutunci babu abinda suke zubawa unguwa kuwa ya cika makil da jama'a yan kallo kowa na fadin albakacin bakinsu wasu suna ganin daidai ne matakin da suka dauka dayawa kuma laifin bilkisu suke gani ."


wani abu mai daci yan'uwansa suka hadiye tare da matsowa inda mahamud yake yana laftawa ussein belt a gadon bayansa "yanzu ina zaku dashi ?In ji cewar fatima tayi maganar cikin tsananin fushi "zamu tafi dashi inda zamu sake koya masa hankali," ya fad'a cike da gadara da isa "amman yana da kyau mu san inda zaku da d'anuwanmu kafin ku wuce dashi? Eh ! yana da kyau sai dai bani da wannan lokacin 'batawa idan aka koya masa hankali zaa iya sanar daku kuzo ku d'auki abinda ya saura ajikinsa "


Hjy kuka saadatu kuka haka ma fatima muna cikin wannan halin sai ga gali yace shine yayansa suyi hakuri su bar komai a hannunsa zai sa ya rabu daita rabuwa ta har abada ,mahamud yace "da dai ya fiyye masa kwanciyar hankali dan wallahi na sake dawowa akan case din nan sai dai ku dauki gawarsa" gali yace "to mun gode komai yazo karshe bilkisu ta bude idanunta da suka mata nauyi wani marayan kuka ta fashe dashi tana shesheka tana kallon kowa wanda ni nasan kukan da take alokacin bai wuce na rabuwa da ussein ba ."


fatima ta watsa mata harara hade da kallon banza tana cewa "kukan uwar me zakiyi wa mutane duk bake kika jawo masa matsala ba yana zaman zamansa muguwa azzaluma kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login