Showing 150001 words to 153000 words out of 185716 words

Chapter 51 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4708

cikin makeken office dinsa kai tsaye hanyar massalacin dake cikin ma'aikatan ya nufa yayi sallar azahar sannan ya bawa direbansa da masu tsaronsa umarnin tafiya police station babu bata lokaci kowannensu ya zama ready yana qarasa isowa aka bude masa mota ya shiga suka dauki hanyar police station yana shiga kai tsaye da cp Amir suka hadu suka tsaya suna magana akan nuzla suna gama magana cp yayi gaba zai masa iso wajen dpo ."tun kafin ya kai ga shiga dpo ya mike ya fito da kanshi cikin girmamawa yau ga matun kamar adam tariq abdullahi acikin station dinsu dan kasuwan daya fi kowani dan kasuwa kudi ya shiga office din suka zauna cp ya basu waje suka gaisa sannan suka soma tattaunawa akan nuzla ".


"ranka ya dade mai zai hana awuce kotu kawai ?ciza lip's ATA yayi yana girgiza kai muryarsa a matukar raunane yace "a'a nan ma ya isa banason aje ga kotu fatana ma ya zamanto babu hannunta ciki ,amman yanzu abi mataki na karshe ayi amfani da sheidar hannunta "muma shine last option dinmu domin shi zai warware komai ya runtse idanunshi hankalinsa na sake tashi babu wanda yake tausayi Kmr mahaifinta da mahaifiyarta yayyenta da kuma masoyinta hisham ya tuna halin daya gansa yau din gbdy baya cikin natsuwarsa haka ma yan'uwanta ya sauke naunayen ajiyar zuciya yana cewa "ko zan iya ganinta ?why not ranka shi dade "inspector runke !ya kwallawa yarsandar dake kan kanta kira cikin girmamawa ta shigo sai data sara masa sannan ta kame waje daya "jeki fito da yarinyar nan wacce akawo jiya "Okay sir ta fad'a tana juyawa cikin sauri ."




Tana fita ATA ya kalli dpo "amman babu wanda ya ta'ba lafiyar jikinta kawai gsky nike bukata ?"yallabai babu wanda ya ta'bata yarinyar ma bata da rigima tunda aka kawota take kuka, very gud kar wanda ya ta'ba lfyta in sha allahu yadda kace haka zaayi batayi ma rashin kunyar da zaa ta'ba lafiyarta ba kawai dai taki amsa laifinta ne ya qarasa mgnr adaidai lokacin daaka shigo daita kallonta kawai yayi yana mamakin yadda kamaninta ya canza acikin kwana daya da yinin datayi ga dai shi babu alamun duka ajikinta amman cizon tsoro yayi mata yankan qauna ga dotti ya soma zama ajikinta tana ganinsa ta fashe masa da kuka tana cewa "dan girman allah yaya adam ka ceceni kasa a fitar dani daga nan wallahi idan na cigaba da zama anan mutuwa zanyi wallahi ban aikata komai ba ."


ATA dake kallonta ya sake hade fuska babu wata alamun tausayi bata damu da yanayinsa ba dan tasan halin miskilancinsa da zafin zuciyarsa dpo Karan kanshi ya tausaya mata ya nuna mata wajen zama ta zauna ATA ya tsareta da idanunshi yana kallonta yayinda ita km ta cigaba da sheshekar kuka "har yanzu kenan baki shirya fad'ar gsky ba ?ban aikata komai ba me yasa zan amsa laifin da ban aikata ba wallahi kasa a tsananta bincike ni nasan ko waye acikin estate dinmu yake amman ni ban aikata ba ,wani kallo yayi mata sannan ya mike tsaye zaa yi bincike na karshe akanki kiyi adduar babu hannunki dan muddin ya zamoto kece zaki qarasa rayuwarki a inda yafi nan muni yana gama fadar haka ya bada umarnin a fitar daita tana kuka tana kiran sunansa aka fice daita ya kalli dpo yana sake jadda masa kar ta'ba lafiyar jikinta har sai an gama bincike yayi masa kyauta sannan ya wuce ."


*****
bayan tafiyarsu alhj alqasim ummah suna hira da maryama tace da zarar kin qare bautar kasa kema zanyiwa alqasim magana ya nema miki aiki mai kyau ta yadda zaki samu damar taimakawa aunty ,dan Allah ummah kiyi masa maganar idan ya dawo kinga yace qasar ma zasu bari kinga idan yasan da maganar wata killa zai barwa wani sallahu".
" in sha allahu maryama zanyi masa mgn kuma nasan zai min wannan alfarma bare kuma naga alamun kin kwanta masa arai murmushin jin dadi maryama tayi tace "ai duk saboda ke ne ummah darajanku naci banci haka ai bazan taka matsayin ko daura kwayar idanuna akanshi ba ".


hirar sukayi sosai cike da so da kulawa wata ya qare ummah ta saka ran zuwansu alhji alqasim amman shiru har wani wata ya kai goma dan haka ta fidda rai da ganinsa koda ummah tayi hirar da maryama ta rausayar mata da kwayar idanunta domin ita a ganinta haka masu kudi suke da fad'ar abu su fasa mussaman idan bai shefesu ba "ummah karki wani damu da rashin zuwansu tunda daman su suka saka kansu ba wani ne ya sakasu ba ."


Satin da suke ciki ya qare babu dalilinsu sai da aka sake shiga wani sati sai ga wayarsa yana sanar da yaya sadam yana nan zuwa ranar lahadi ranar suna jumaa dawowarta kenan daga wajen aiki ta samu labarin zuwansu daga bakin ummah ai kuwa dadi kmr ya kasheta da murna ta shiga side dinsu tana sanar da aunty cewar ranar lahadi zasu zo dan daman ta fad'a mata taimakon da ummah zatai mata sosai taga farinciki a fuskar aunty daman ita kadai take tausayawa a rayuwarta tana son ta taimakawa mahaifiyarta amman bata da hali ,dan zanen da take ba wani manya kudi yake kawo mata ba sakasancewar sai kayita bin office office na masu kudi dan ba kowa ya gama saninta ba bare su nemeta dan kansu, gashi tana son fitar da mahaifiyarta cikin wahalar da take ciki amman bata da iko sai dai ta mika lamuranta zuwa ga Allah dan ya kawo masu saukin halin da suke ciki.




ranar lahadi aka sake maimata irin hidimar daakayi masu a wancan ranar sai dai kuma wannan zuwan nasu akwai qarin abubuwa masu yawa daakayi karfe goma da yan mintuna motarsu ta tsaya a sabon titi market street wannan zuwa babu driver da babban dansa yusif da kuma kanwarsa Kausar sai dady da yake zaune a bayan mota ranar kamar wacan ranar yaya sadam ne ya tarbosu zuwa cikin gida sai dai shi Yusif bai shigo ba ya tsaya a haraban gidan yana amsa waya ."sakina aunty salma da aunty hassana da yayanta da baba gali duk suka fito tarbonsu ita kuwa maryama sai ta koma dakin ummah duk da tana bukatar farinciki wa rayuwarta amman sai ta boye kanta ."Kausar tafi yusif surutu dan ita take ta haba haba da su sakina da Islam da kaulat har ma da shukura da bata ta'ba ganinsu ba umma ta fito suka gaisa ta tmbyesu hanya ."






Wannan dalilin yasa ta fito daga dakin umma dan karta kwatanta na kwana baya sai dai ta kasa shiga cikinsu ta rabe can nesa dasu byn ta gaishe da dady ta fito ta zauna a tsakar gidansu hannuwan yusif acikin aljihu ya shigo bakinsa dauke da sallama wacce ta makale a fatar bakinsa ganin maryama ya tsayar masa da sallama ya tsura mata ido jikinta ya bata ana kallonta dan haka ta dago a natse domin ganin mai kallonta nan take ta firgita ta qara gyara zamanta da daidaitawar mayafinta." ya tsura mata ido sosai yana kallonta ahankali yace "sannu !"


sautin muryarsa ta doki dodon kunnenta amman ta kasa maida masa da sannun da yayi mata sai sunkuyar da kanta tayi dan bata son yawon kallo shine ma dalilin da yasa take yawo da nikaf duk inda zata dan sai mutane suyita kallonta wai tana da kyau da sauri ta mike ta nufi hanyar side dinsu ya dan lekota adaidai lokacin data waiga suka hada ido jin alamun tafiya yasa ya dawo da natsuwarsa sannan ya shiga cikin parlour'n umma da sallama tana ganin shigarsa ta dawo dan bata son tayi nisa ummah tazo tana nemanta ai kuwa tana zama tajiyo sauti muryar ummah tana kiran sunanta jiki a sanyaye ta shiga parlour'n ta durkusa."


Kausar na ganinta ta fadada murmushinta ta riko hannunta "mamana ta bani labarinki ta fad'a hannunta na cikin nata maryama tayi murmushi wanda Ke bayyana kyawunta tace "da fatan tana lafiya? tana lfy tana can tana kewarki tace kin fini kyau da kunya har ma da qoqarin karatu da fari na karyata amman yanzu na gasgata a ganin da nayi miki a karon farko ,alhj alqasim da ummah sukayi murmushi yayinda yusif sai kallon maryama yake bai ce komai ba Islam kam sai wani yatsina fuska take jin yadda kausar ke yabon maryama ,alhj alqasim yace "ku bamu waje kuje kuyi hira "maryama muje wajen mamanki mu gaisheta lumshe idanunta tayi tare da cewa "to !


Hannun kausar na cikin na maryama suka fice Islam na biye dasu a baya maryama ta lura da irin kallon da yusif yake mata dan haka tasha jinin jikinta ,suka shiga side dinsu kausar tabi falon da kallo sannan ta dawo da kallonta kan maryama "tabbas nayi farinciki da ganinki a matsayin wacce mamana ta yaba da halinta har ma naji qaunar yin kawance dake ."maryama tayi murmushi kawai dan ita bata iya doguwar hira ba sai dai acikin ranta taji dadi ,ko bakya sona da Kawa ?ya zaayi naki sonki da qawa ai daman ke qawata ce kuma yaruwata ,ta rike hannuwan maryama da'ace acikin gari kike da yanzu ana nan ana hada gumi akanki maryama bata fahimci maganarta ba sai dai ta fahimci tana yi ne akan kyawunta murmushi tayi tace "akan me zaa hada gumi akaina ."




Ta gyara zama "kyawunki yafi karfin zama acikin geto area bakowane acikin geto area hk zai iya cewa yana sonki ba saboda sanin kinfi karfinsa ko kina da samari ?"Sosai ta bawa maryama dariya ta kuma girgiza mata kai alamun bata da dan ganinta shi ya fiye mata sauki akan tace sun gudu sun barta ne ko kuma an kwace mata ,ai dole samari suji tsoron zuwa irin wannan kyau Masha allah wallahi ba wasa nike ba tun kafin na ganki momy ta fad'a min tayi min kyakkyawar qawa jinta kawai nayi domin ina jin babu wata macen da zan iya qawance daita anan amman ganinki na sha mamaki banda qawa zaki iya zarce komai agareni maryama tayi murmushi kawai tace "na gode ."




"Kinga yayana yusif?
Ta tambayeta tana kallonta "ko da yake ba sai anji a bakina ba maryama ta tsura mata idanu kawai tana kallon kausar cikin rashin fahimta dan ta fuskanci kausar nada yawon magana sosai ita kadai take kidinta take rawarta,dan ko tmbyr manufar abinda ta fad'a batayi ba ta rabu daita suka cigaba da hirar geto area ."acan kuma parlour'n umma alhj alqasim da baba gali da yusif da yaya sadam suna zaune bayan sunci abinda aka kawo masu saí alhj alqasim yace "ka gane wannan ?ya nuna masa yusif da hannu baba gali yace "yusif ne mana ya zaayi na kasa ganesa, a'a to yaron yanzu ne kwana kadan idan baka gansu ba sai kaga sun qara girma yusif yayi murmushi ya basar bai sake cewa komai ba ."




Bayan tashin ummah dady ya dube baba gali yace "Gali wato zuwan da mukayi wancan karon wani ikon allah mai dakina mustafshira tun ganin maryama sai taji qaunar yarinyar har taji tayiwa danta shaawarta a matsayin matar aurensa dalilin da yasa banzo kenan ba tun wancan watan danayi alqawarin ba yusif baya nan yaje canada wannan dalilin yasa na tsaya har sai ya dawo sannan zamu zo tare ,yaron yaso yaki wai tayaya zai zo geto area neman matar aure amman sai na shawarcesa daya daure yazo ya gansu gbdy wacce tayi masa sai ayi maganarta ."


Baba gali yayi murmushi zuciyarsa cike da farinciki yace "gsky abu yayi kyau mutun uku suna nan babu wacce akayi mgnr aurenta Islam da sakina sai maryama wacce take bautar kasa sauran biyu din km tun daga secondary basu cigaba ba amman dai ni ina son sakina ta cigaba alhj alqasim yayi shiru yana kallon Yusif yace kai duk gasu nan wacce ka tarar anan itace Islam din da nafisa ko ?baba gali yace a'a sakina wacce ta shigo karshe itace maryama "to kaji yusif itace sakina sai Islam wacce ta shigo karshe itace wacce mahaifiyarka tayi maka shaawar duk yayana ne babu wacce bazan yi murna idan ka aminta daita ba ,kai ma bazaa takuraka ba idan kaji babu wacce tayi maka sai a hakura ."


Yusif yayi shiru yana tsotsa keya yace " zabin momy shine zabin da yayi min dan haka maryama itace ta shiga raina a kallon farko danayi mata alhj alqasim ya washe baki yana murmushi baba gali ba dan ranshi yaso ba yace to shikenan duk da daman akwai maganar wani dake sonta amman dai babu komai sai abashi hakuri alhj alqasim ya tsayar da idanunshi akan baba gali "da kuma kace babu wanda yake nemanta da aure? ya tmbyesa cikin mamaki shi kuwa yusif ido ya ware sosai dan shi wallahi yayi mata ko sama da kasa zasu hade sai dai ya hakura ya bar masa ."


Baba gali yayi sauri yace "ai kasan samarin yanzu ba wani serious yayi ba amman sharesa kawai dan sama sama yake ma zuwa yusif ya sauke ajiyar zuciya alhji alqasim yace "shikenan ayi mata magana tayi miji shi wannan babu zuwa sama sama yazo kenan ayi mata magana sai muje mu gaisa da mahaifiyarta koda yaya sadam ya fad'awa umma murna har da sujja tayi ita kuwa Islam cikin kunci ta shige bangaren su byn ta gama ji sakina kam ko ajikinta dan ita tana son maryama bata dai san meke sata jin tsanarta ba ,maryama da kausar suka fito suna hira ganinsu yasa shi ya tsayar da hankalinsa akanta tabbas ta hadu yayi mamakin samun mace kamarta gata yarinya qarama just 20 amman ta hada abubuwa masu yawa dan ya darata da kusan shekaru shatakwas a duniya"


Alhj alqasim ya bukaci ganawa da maryama ta shigo a natse ta zauna tare da takwashe kafafunta kanta sunkuye yayinda yusif yake ta kallonta bai ta'ba sanin akwai baki mai kyawun da tafi fari ba sai akanta ko da yake bazaa kirata da baka ba sai dai chocolate colour" maryama ina son nayi miki wata tmby guda daya kuma ina son ki sanar dani tsakani da Allah ki sanar dani gsky ki daukeni tmkr mahaifi ne yake tmyrki ita dai shiru tayi tana tunanin irin tmyr da zai mata domin bata kawo komai aranta ba ko hasashen abinda zai tmbyeta "maryama ya'ya zamanku yake acikin gidan nan "?


Ta tabbatar akwai abinda alhj alqasim ya gani yasa har yayi mata wannan tmyr tabbas bata da tacewa ba zata iya fad'ar irin bambamci da abubuwan da ake mata daga bangaren baba gali da aunty hassna har ma da sauran yanuwansu wadan da suka kasance yanuwa ga mahaifinta tunda daman duk mutumin da bashi ya haifeka ba ,dole sai an gane kuma bai zama lallai ya soka ba ,ya qara mata tmbyr ganin bata da niyyar cewa komai hakan kuwa ya qara sa zuciyar yusif mace wa akanta gbdy ganinta yasa ya manta da husna yarinyar da suka dauki tsawon shekaru daita kawai taimakonsa bai kawota gidansu ba daya san shikenan ya tafka asarar samun maryama ."




Ya sake tmbyrta a karo na uku cikin sanyayyar muryarta tace "ban san ta inda zan fara ba amman dai bani da matsala muna zaune da kowa lafiya tayi mgnr tana sunkuyar da kanta shi kuwa yusif ya kasa dauke idanushi akanta alhj alqasim yayi shiru na dan wani lokaci sannan ya shaki iska yace "har mamanki ?ta sake gyada masa kai duk muna lfy bamu da wata matsala da kowa acikin gidan nan ita kam bata ga dalilin da zai sa ta fitar da sirri gidansu ,su din yanuwanta ne duk da basu dauketa a haka ba ." yayi shiru yana nazarinta shi dai ya fuskanci akwai matsala daga hasana har gali amman gashi ta boye masa yayinda zuciyar maryama ta dinga raya mata ta sanar masa gsky zaman da suke wanda naci ma da taimakon umma suke samu amman ina bazata iya ba ."


Wannan hali nata yasa yaji lallai ta qara shiga ranshi duk nmj daya sameta yayi saa a duniya domin macen dake iya rike sirrinta itace mace da haka ya gama yace ayi masa iso wajen mahaifiyarta a natse Umma tayi masu iso zuwa wajen aunty ta tarbi bakinta yadda ya kamata dan katuwar tabarma ta shimfada masu, alhji alqasim ya jima yana kallon aunty cikin tsananin tausayawa sannan ya dubi Yusif muryarsa sanyaye yace "ga mahaifiyar maryama suka qara gaisawa shima yana satar kallonta da alamun ya gano kyawunta maryama ta dauko duk da bata cikin sukuni amman fatar jikinta ta ya'yan masu kudi tana nan lafiya lau kyakkyawar fata mai sheki babu abinda ta rasa wajen auna kyakkyawa , hanci baki mai kyau idanu kausar kam kusa daita ta koma ta cigaba da zuba mata surutu nan da nan hira ta barke sosai atsakaninsu "




Alhj alqasim ya gano dansa na bukatar kebewa da maryama dan kallon da yake mata babu sauki yace "maryama fitar da wannan matsoracin yaga cikin geto area daga nan akwai abinda zai fahimtar dake ta dan yi murmushi tare da dago idanuta suka hada ido da yusif wanda yayi zuru da idanunshi akanta aranta tace "bashin me naciwa bawan allah nan yaketa bina da kallo? bai yi tsammanin zata iya fad'ar haka ba dan hk yace mata "bashin gaisuwa mana baki gaisheni ba sai lokacin ta fahimci a fili tayi mgnr ai kuwa da sauri ta mike ta fice daga parlour'n jamar dake zaune a wajen sukai dariya yayinda yusif ya mike ya fito tana tsaye a tsakar gidan rungume da hannunwanta ya qaraso inda take tsaye "ina kwana ta fad'a tana sunkuyar da kanta sakamakon idanunshi dake yawo a sansar jikinta "yanzu ne ina kwana ? to ai bashi ka biyo kuma gashi na baka."




Shiru sukai na dan lokaci ta sake sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ko zan iya tmbyarki ?kai kawai ta gyada masa tare da yin shiru tana mai jin tsanani kunya most especially idan ta fahimci sanar daita kalmar só zaayi ko mgnr aure dan ma wayewar karatuta ta rage mata wasu abubuwa ,amman duk da hk a shirye take da irin tmyr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login