Showing 129001 words to 132000 words out of 185716 words

Chapter 44 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4703

har ma da ya'yansu suna hira ummah ta kalli sakina da shukura da islam zaune suna tayasu hira ta kalli maryama dake faman dikar aiki "a'a ya zaku bar maryama da aiki ita kadai Ke shukura sakina islam kusa hannu kuyi tare mana na gayyatoku ne dan kutayani aiki ba dan ku zauna kuyi hira ba ,maryama ta fahimci maganar ba dasu shukura kadai ummah tayi ba har dasu aunt hassana tayi cikin rashin son aiki suka qaraso inda take gyara kaji shukura na kunkuni wanda bazai kai ga kunne ummah ba , maryama tace "kinga shukura idan baza kiyi ba ki koma ki cigaba da zamanki idan ma gbdy bazakuyi ba ku barshi duk zanyi dan kawai an sakaki aiki zaki dinga wa ummah kunkuni
ta watso mata harara tare da kallon banza "ke ki kama kanki dan na lura tunda mlm yahuza ya dawo da neman aurensa kaina kike min kallon gani gani nake miki kallon gani gani ko kike min ?"
maryama ta fad'a a dan hassale tana hura hanci .


"Ban sani ba banza kawai mai bakin jini sai wani 'bare 'bare kike dan kinga mai kudi zai
zo , abinda kome zaayi na banza né tunda babu abinda zai haifar sai cigaba da zaman gida da yawon ta zubar wai ana zuwa bautar kasa "Ke ni kike gawa magana "? an gaya miki me zakiyi ?"ai maryama cikin fushi ta zabga mata mari wani qara ta saki tana dafe kuncinta wanda yasa aunty salma da duk wanda suke wajen suka juyo zuwa inda suke ita kanta irin qarar da shukura ta saki sai da gabanta ya fadi ta tabbatar yau ta dibowa kanta ruwan dafa kanta "kutumar uban can me tayi miki kika zabga mata mari haka ?"aunty salma ce akan maryama take neman ba'asi cike da maseefa."




Maryama tayi shiru tana datasanin Marin datai mata hakan shi ya fusata aunty salma bata tsaya wata wata ba ta zabgawa maryama nata mari har biyu a kowani kunci "idan dadi né kema kiji ina dalili daga tazo ta tayaki aikin wahala sai mari jakar gidan ubanki ce ? taja hannunta zuwa kofar dakinsu tana share mata ruwan figar kajin data goga mata ."




Ummah tace "maryama me ya hadaku har daya kaiki ga marinta ? tayi shiru tana shayen zafin marin dan bazata iya fad'a mata bakaken maganganun data fad'a mata ba kawai ta rufe fuskarta saboda tuttukin bakinciki da zuciyarta Ke mata nan da nan kuka ya kwace mata umma ta qaraso kusa daita "kinsan kema uwarta bazata barki ba me yasa kikasa hannunki ajikin shukura ?sakina kanta ta tausaya mata tana son tayi mgn dan kare maryama da sheidawa ummah cewar ba laifin maryama bane laifin shukura né amman ta kasa ."


"kinsan halinta ya kamata ki dinga kiyayye duk abinda zai hadaku daita da yaranta ni wallahi nayi danasani ma sakasu cikin aikina kinga sakina tashi ki bisu kuje kema Islam jeki na gode kema hassana wuce idan bakin sun qaraso kwazo ku gaisa " kukanta ya fiyye mata maganar ummah , bata cewa ummah komai ba tana tsaye akanta ita kuma tana cigaba da kukanta ta share mata hawaye "kiyi hakuri kinji Allah zai saka miki maryama bata ce mata komai ba ta cigaba da aiki datasata domin tana ganin hakan shine zai fiyye mata akan kukan da take ."






Karfe tara da minti arba'in da daya daidai bakin suka shigo cikin unguwarsu cikin wata qatotuwa Jeep mutun uku ne a cikin matarshi da kuma shi kanshi alhj alqasim maude sai mai tuka su inda baba gali da yaya sadam suka fito tuni tsayuwar jiransu da sauri baba gali ya qarasa ya bude kofar da alhj alqasim maude yake da murmushi cike da kulawa suka gaisa sosai."




Alhj alqasim maude ya rike hannun baba gali yana cewa "Kai amma an jima ba hadu ba, ya jama'a ya iyali.?"baba ya ce,"duk lafiyarsu qalau barkanka da zuwa ya hanya? da irin wannan gaisuwa matarsa Hajiya mustafshir ta fito daga motar suka gaisa da baba gali cikin kulawa, sannan alhji alqasim ya rungume yaya sadam ajikinsa cike da farinciki dan duk sanda ya gansa yana jin farinciki sakamakon kamaninsa da mahaifinsa "sannu dana fatan kana lafiya ya fad'a yana shafa bayan yaya sadam ya dan zame kadan ya gaishesa "barkanku da zuwa dady da fatan baku sha wahala ba ?"babu wata wahala sadam sukai masu jagora zuwa cikin gida ."




kai tsaye babban falon ummah wanda aka qawatashi babu laifi anan abban sadam yake saukar bakinshi kujeru set guda zagaye a dakin sai dan teble a tsakiya na glass , parlour ya sha gyara har da turaran wuta kala hudu maryama ta saka a kowace kusarwa na falon ,suka zauna ana qara gaisawa da tambayar mutanen gidan hajiya mustafshira tana dan duba wajen tana murmushi itama tana dan ta'ba hira umma ta fito daga dakinta maryama na zaune gefe daya kuma aunty salma ce da sakina har ma da shukura da islam duk komai an gama shiryashi daidai ta yadda duk wanda ya gani bazai raina ba "maryama ki kawo wa baki abinda muka yi ta yunkura zata tashi islam tayi sauri ta dauka batare da an bata izini ba ta wuce dakin da farantin dake da kayan ."


Hakan yasa ta koma ta zauna batace komai ba sai dai ummah tace taje wajen baban yara mai Shgo zai bata sako dan haka ta fasa zaman ta gyara zaman hijab dinta ta fice daga falon roban ruwan faro ne guda shida wanda suka dauki sanyi da kwalbar multina shima guda shida ya saka mata acikin leda baka ta nufo ummah bata shiga dakin da bakin suke ba tana zaune suna hira da aunty data iske zaune kusa daita da jamar gidan tace "yauwa diyar albarka ki kai masu amman kawo mugani islam je dauko wadan can kofunan na glass acikin dakina cikin sauri taje ta dauko ta hada da bakar ledar da maryama ta shigo dashi taje ta kai hakan kuwa yayiwa aunty hassana dadi dan tafi son ace islam ce Ke kai kawo a masaukin bakin."




ita kuwa maryama ta rasa me yasa take son shiga dakin har da zalamarta aunty hassana da yayanta biyu kaulat da islam suka shiga suka gaisa sun dan jima aciki sannan suka fito sannnan ummah da aunty suka shiga bayan wasu mintuna aunty ta fito ita kadai zata wuce har maryam ta mike zata bita su koma side dinsu tare , aunty ta dakatar daita " ki tsaya idan ummah ta fito bata ganki ba zata damu ko bama haka ba dole Kinsan zata nemeki ."


"to ! kawai ta furta ta koma ta zauna bata shiga dakin ba dan ita a ganinta babu abinda zai kai ta ciki zama gurin bai mata ba dan harare hararen da take samu daga yammanta ta mike ta shiga dakin ummah tayi kwanciyarta duk da tana son ganin bakin amman haka ta hakura tana jin su sakina suna santin bakin fad'ar haduwar hjy mustafshira da irin kayan alfarmar da take sanye dashi ita dai shiru tayi bata damu ba domin ko sun tafi basu ga juna ba ita ba damuwa zatayi ba dan ganinta haduwarsu bazai wani qareta da komai ba ."




Kusan karfe uku saura suna hira dasu ummah da baba gali har ma da yaya sadam suka fito domin niyyar tafiya suka tsaya a falo inda jamar gidan suke zaune aunty salma da ya'yanta haka ma aunty hassana domin suyi sallama dasu "amman gsky yaranku basu da hayaniya amman dai duk sun yi karatu ko "? Murmushi baba gali yayi "Kai kasani dole suyi karatu domin sanin amfaninshi ita wannan tuni ta gama secondary kuma ina son rai zata cigaba ya nuna sakina ."


alhj alqasim yace "Allah sarki gsky karatu kam yana da matukar mahimanci kayi qoqarin da ka bar yaranka sukayi karatu dan da sun biyoka da rashin son karatu da abun bai yi kyau ba dan wannsn zamanin sai da karatu sukai dariya gbdy sakamakon jin abinda alhj alqasim ya fad'a "ai gsky ne yayanshi yafi sa son karatu sosai allah dai bai yi zai yi karatu mai zurfi bane Allah ya jikansa "Ameen hjy mustafshira ta amsa tare da jamar wajen ."


Alhaji alqasim ya nuna shukura "wannan yarinyar ussein ce ko ?"uhm uhm bata ita bace wannan diyata ce ta uku ita ina ganin tana bangarensu baba gali ya bashi amsa da haka ,allah sarki allah ya jikinsa shima yasa suna aljanna Ameen ai kasan ita maryama bata fiyye son shiga cikin mutane ba mussaman idan bakin fuska ne allah ya zuba mata kunya gashi ita har ta qare karatunta na digree yanzu haka ta fara bautar qasa ta kuma yi saukar alquranin mai girma tana da hadda uzu arbain da wani abu akanta ."


"kai masha allah a she dai kuna da zakakura acikin dangi ?"sukayi dariya kawai suna yiwa ussein addau "gsky ussein yayi saa arayuwarsa duk wannan rashin jin maganar daya ta'ba amman allah ya albarkacesa da samun yarinya mai kokari haka "? wallahi abun na allah ne yaransa ma duk masu natsuwa sai ma ka gansu, yabon ummah sam bai yi kowannensu dadi ba amman babu yadda zasu yi tunda umma ce
kuma sun san adalilin ta suka zo gidan"ai ina qaunar ussein domin shi din mutun ne mai barkwanci da son mutane ai naso na dawo qasar nan na iske shi a raye maryama tana cikin dakin ummah duk tana jin maganar Alhaji alqasim da ummah tana jin matukar qaunar mahaifinta alokacin da bataji tahirinsu da mahaifiyarta ba amman daga baya dataji komai sai ta daina kewar babanta duk da ba wani saninsa tayi ba dan duk lokacin data tunashi sai damuwarta ta ninku acikin zuciyarta ganinta shine ya raba aunty da yanuwata ,bugu da qari yadda kowa yasan mahaifinta baya jin magana."


kuka taji ya kwace mata "Ke shukura je ki kira min maryama taí Jim dan tasan tana dakin ummah amman dan bakinciki karta gaisa da bakin yasa ta fice Jim kadan ta dawo tace "aunty tace bata nan ,bata nan kuma ?ummah ta furta a fili tana qoqarin neman layin aunty can bayan Kmr second goma maryama tajiyo muryar ummah na kiran sunanta "maryama maryama !! hakan yasa tai saurin mikewa ta share idanunta da gefen hijab dinta ta fito ko hada idanu ta kasa da bakin saboda tsura mata idanun da matarshi da shi kanshi Alhaji alqasim sukayi ."




"Haka diyar ussein ta girma lallai dan mutun sai allah ussein din guda nawa yake har da 'ya haka ?ita dai maryama gaisuwa ce kawai nata domin bata da abun cewa hjy mustafshira ta shafa kanta sannunki kinji ya aiki da fatan yana tafiyar miki yadda ya kamata kyakkyawa dake tubarkalla masha allah shine kika fitowa kizo mu gaisa ko ?


Ta dan yi murmushi ta dago kanta tana kallonta amamn still ta kasa cewa komai "me ya sameki kamar kuka naga kinyi bata san hawaye na makale da idanunta ba da sauri tasa gefen hijab dinta tana sharewa hjy mustafshira ta qaraso ta dagata daga tsugunno datayi ta dan rungumeta ajikinta "babu mamakin maganr da mukayi ta mahaifinta ce tasa ta kuka ita kanta ummah ta shiga damuwar ganin hawayenta ,ki daina kuka kinji allah zai kai rahama kabarinsa Kiyi hakuri ki cigaba da yi masa addaua shi kanshi yana can yana alfahari da samu diya kamarki mai riko da addini kai kawai ta daga mata tana qara goge kwallar data taru a idanunta aunty salma da aunty hassana da yaransu kuwa babu abinda suke aikin yi sai harare harare iri iri da bakinciki ."


"Ai mahaifiyar ce ta shigo dazu muka gaisa ko ? alhj alqasim ya tambaya yana duban baba gali "Eh itace baba gali yayi saurin fad'ar haka ai tunda ussein ya mutu taki koma wajen danginta bare tayi wani auren ta cigaba da zama anan ai kasan yadda akayi aure danginta saboda rashin son useein din suka sall.."
"Eh nasan komai abban sadam duk ya fad'a min alokacin amman dai nayi tunanin komai ya wuce zuwa yanzu Alhj alqasim ya katse maganar ya zura hannu cikin aljihunsa ya zaro kudi bandir daya na yan dubu dubu ya damka ma maryama taki amsa tare da cewa ya barshi sai ummah ce ta karba ."




Gabadaya sai daya bisu da kudi yana cewa" in sha allahu zan sake dawowa nan kusa tare da yarana gbdy asan juna kafin mu tattara mu bar qasar yayi gaba yaya sadam ya bishi da baba gali hajiya mustafshira bata saki hannun maryama har bakin mota ita dai bata ce komai ba binta kawai take da alamun tausayinta ne ya game jikinta sai faman hakuri take bata sukai sallama tayi mata godiya sosai suka shiga mota suka tafi ."




Ita da yaya sadam da baba gali suka koma gida kai tsaye dakinsu ta nufa da yamma ummah ta shigo ta mika wa aunty kyautar kudin data samu aunty tace "a'a bazan karba ba ummah saboda me balkisu ? Ki rike kawai domin kece mai yin hidima acikin gidan nan bare ma akanmu wannan ai ba wani abu bane amana ce rike a hannuna, ni dai kawai ki rike ."
"to ki cire wani abu aciki aunty tasa hannu ta zari dubu daya ummah ta girgiza kai tana cewa allah baki isa ba kin kuwa san ko nawa ne dubu dari ne fa shine zaki cire dubu daya ta raba kudin biyu ta mika mata rabi allah sunyi yawa ummah bazan karba ba nifa ba butulu bace nasan ya kamata ta cire naira dubu biyar tana cewa wallahi iya su sun isa allah yasa albarka rantsuwar datayi yasa ummah bata qara cewa komai ba ta mike ta koma wajenta ."






Da yammacin ranar maryama ta shirya zata wuce makaranta islamiyya "aunty ni na wuce makaranta sai kin dawo princess idan kinga malam yahuza ki gaishe min dashi maryama tayi shiru tana kallonta
"Eh haka na fad'a har yanzu zuciyata tana qaunarsa dan haka kice masa ina gaishesa "to ! kawai maryam ta fad'a tasa kai ta wuce zuciyarta cunkushe da damuwar abinda baba gali yayi shi kansa alhj alqasim din yasan maganar bata dace ba shiyasa ya katsesa ".


ta kusan kai bakin get din Ardus salam ta hango mlm yahuza yana tahowa ta hanya mai fitar da mutun afanla ta cigaba da tafiya a natse adaidai lokaci daya suka iso bakin get ta gaishesa ya amsa fuskarshi babu annuri sosai bata damu ba domin sakon aunty kawai take son isarwa "aunty tace tana gaisheka "na gode kawai yace yayi gaba ya barta tsaye abun yaso ya bata haushi amman tunawa datai baya cikin haiyacinsa yasa bata ji komai ba sai dai ta kasa cigaba da daga kafafuwanta tayi shiru kawai bata san a tsaye take ba ashe ta kasa tafiya ne sai da wata kawarta lauratu tazo wucewa .




"Ke kuwa tsayuwar me kike anan kamar mai jiran wani nan ta diririce "Ke na hango ai kin kusan qarasowa shi yasa na tsaya ta dai jita ne kawai amman alamunta basu nuna hakan ba suka shiga makaranta tare koda mlm yahuza ya shigo ajinsu domin kara masu karatu ko inda take baya kallo sabanin da in har yana cikin ajin murmushinsa kadai ya isheta bayan an tashi ta dan tsaya hira da kawayenta koda suka rabu ta nufi hanyar inda suke tsayawa dashi anan ta ganshi shi da shukura ko kunya babu tasan kuma duk sharrin shukura ne dan ta gansu sosai ne hakan bai dameta ba tunda idan kayi da kyau zaka ga da kyau idan ma akasin haka kayi zaka girbi abinda ka shuka ta wucesu cikin fushin zuciya har ta isa gida abun na cinta arai wai yanzu duk abinda mlm yahuza yake fad'a mata akan soyayyarsa ya tashi abanza ya koma kan shukura hakika basu yi mata adalci ba amman ta barwa allah komai ."


*******


Zaune mr ata yake acikin masaukinsa yana jiran abokinsa bashir sosai yayi kyau sai dai ace masha allah dan yanayin gyara tattare da kulawar da jikinsa yake samu ya hana shekarunsa bayyyana dan idan ba kaji shekarunsa ba bazaka ta'ba cewa ya kai 40 wani abu ba , zaka dauka shekarunsa basu wuce talatin a duniya ba fatar jikinsa kawai ka kalla kasan kudi suna aiki ba karya haka ma kayan jikinsa tun daga kan wondo rigarsa takalminsa har zuwa agogon dake makale a hannunsa dukansu tsadaddun gaske né ,shine ma ya zana da kansa kaf duniya su uku kawai ke da irinsa shi mb sai bashir abokinsa rolex ne mai shegn kyau ."


ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login