Showing 30001 words to 33000 words out of 185716 words

Chapter 11 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4727

faka suka yi saurin firfitowa suka zagaye motar da Mr ATA yake ciki ,daya daga cikinsu ya bude masa murfin mota , masu gadin gidan muhd bello na ganinsa suka fara rawar jikin da kokarin kawo gaisuwa.


" Kai tsaye ya shiga gidan batare da neman iso ba waje ya samu a rumfar dake ajiye da kujera na alfarma dake haraban gidan ya zauna ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya wannan ya rigada ya zame masa jiki no matter how ya zauna sai ya d'aura kafa daya a kan d'aya , hannunsa daya ya d'aura a kan table yayinda wayarsa ke manne da kunneshi yana neman layin MB cikin kankanin lokaci ya bayyana a gabansa ."sai da gabansa yayi mugun bugawa hankalinsa ya tashi da ganin yanayin Mr ATA , ya zauna kusa dashi yana kallonsa "Lafiya friend na ganka haka kmr kana cikin damuwa ?"




shiru yayi masa zuciyarsa na zafi da tafarfasa kmr zata kama da wuta "please talk to me friend what's wrong with you ?"yin duniya mr ATA yaki magana shiru Shima yayi yana kallonsa zuwa sanda mai aikinsa ta k'araso rike da tire dake d'auke da ruwa da lemuka masu sanyi tun kafin ta k'araso ya amsa a hannunta dan yasan yadda mr ATA ya tsani ganin fuskokin masu aiki ya ajiye akan table ita Kuma ta juya da sauri .ta kasan idanunshi yake kallon yadda take daga ka'fafunta haka nan ya tsinci kanshi da kallon every step of her zuciyarsa na quna ."
MB ya tsiyaya masa ruwan ya mika masa "Kar'ba ka sha ka dan ji sanyi ATA ya numfashi ya sauke numfashi kana ya nuna masa kan table "ba ruwa nazo sha ba MB wai har ni wanan stupid monkey din zata ce bata so ......?"yayi maganar yana nuna qirjinsa da d'an yatsansa .


a matukar firgice MB yace "who's she ?"wannan monkey revenble person din mana har ni zata ce bata so? " is a lie she just say it "ka natsu plz nifa ban ma fahimceka ba amman duk da haka nasan babu macen da zata ce bata sonka "wannnan yar iskar yarinyar diyar kanin sweetheart dake fama da danyen jiki kmar daga alhalin china aka samota yayi maganar a tsawace yana dukan table din gabansa nan take tire da glass cup suka tarwatse MB bai tsaya bi ta kansu ba ya riko hannuwansa duka cikin nashi dan gbdy zuwa yanzu ya fahimci ko wa yake nufi "calm down ATA ba fushi yakamata kayi ba soyayya haka take kayi hakuri ka natsu musan abunyi tunda kaji kana sonta yanzu shawo kanta bazai yi mana wa......"


MB yayi saurin katse maganarsa sakamakon wani mugun kallon da ATA ya watsa masa yana zare hannuwansa dake cikin nashi "nace maka Ina sonta ne ? MB yayi saurin girgiza masa kai alamun a'a "to me yasa kace Ina Sonta ?wai naga kamar ka damu ne" "to bana Sonta kuma har abada bazan sota ba Koda kuwa tazamo mata agareni wallahi bazan sota ba kai bancin darajan sweetheart bazan ta'ba iya aurenta ba, bugu da kari ni mallakin princess ne ba kowace mace ba ,Ina son yarinyar nan MB Ina zaka nemo minta ?na saka 50 billion ga duk wanda ya nemo min ita ka taimakeni abokina ka tayani nemota wallahi muddin na auri yarinyar nan zan cutar da zuciyata sannan zan cutar da yarinyar mutane dan bana son mace irinta bazan yi mata adalci ba bazan iya italic ba ."


"Is okay ATA Ina iyakar kokarina wallahi amman zan qara ya kife kanshi akan table kmr wani karamin yaro zuciyarsa na zugi da rad'adin bakinciki "kayi hakuri friend ka sanyaya zuciyarka maryam bazata kika ba sai dai ta furta hakan ne adalilin yadda kake mata amman ni zan sameta muyi magana kune da kune da fahimta nasa zata fahimceni km zata yarda da au.. ."karka yi MB ka barta kawai kar Allah yasa ta amince "no no !! baza'a yi haka ba ai ba saboda ita ba darajan sweetheart zata ci, kasan yadda ta damu kayi aure , hakuri kawai zakayi a shawo kanta " ai bana sonta MB , ta'ba kaji yadda qirjina yake bugawa ,km yana bugawa ne duk akan yarinyar mafarkina tunda na fara mafarkinta ban sake samun natsuwar zuciyata ba burina na ganta na mallaketa " yayi mgnr yana furzar da iska tare da kamo hannun MB ya kai daidai saitin zuciyarsa dake beating very fast .


" ban taba jin soyayya ba irin wanda kake wa yarinyar nan " "wallahi ni kaina nakan zauna Ina wannan tunani MB ban taba gajiya da tunaninta ba daidai da second daya soyayyarta bata raguwa sai ma karuwa ya karasa maganar tare da yin shiru qirjinsa na dokawa da matsanacin karfin gaske".
maganganu masu sanyi MB ya dinga rarashinsa dashi har zuciyarsa ta dan yi sanyi a karshe yace "ka rage tsanar yarinyar nan ATA saboda baka da hujja tsanarta kabi umarnin mahaifiyarka kawai ku rabu Lafiya ita irin wannan tsanar idan ta juyi zuwa soyayya abun ba'a magana please aboki kabar komai a hannuna zan san abun yi ".


shiru ATA yayi kawai yana jinsa amman sam baya jin zai sota a rayuwarsa ko neman soyayyarta tare suka je matsalaci basu dawo ba sai da suka gabatar da sallahar ishai sannan suka dawo MB yayi dashi ya shigo suci abincin dare amman sam ATA yaki sai ma cewa yayi ya gaishe masa da madam da yaransa sadiq da hanif ya shiga mota suka d'auki hanyar gida ."hancin motar da yake ciki na shiga haraban gidan idanun maryam ya sauka akansa hakince a byn mota kanshi na sunkuye da alamun Idanunsa na kallon screen din waya ne , motacinsa na kokarin daidaita tsayuwa ita Kuwa tana zaune a baradan dake zagaye da kofar shiga ainin babban falon gidan akan fararen kujerunsa tare da lawan d'an PA din gwana kano,da kyar da balai ta fito gurinsa har sai da hjy zulaiheart tasa baki tace "taje su rabu lfy wulakanta dan adam bashi da amfani ,Jin motor ya tsaya ya dago idanunshi a hankali karaf ya sauka akansu Aiko ya balain had'e rai har sanda aka bud'e masa murfin mota ya fito yana taku kamar baya son taka kasa ta kasan idanunshi yake kare musu kallon tsaf acikin hasken daya haskaka gurin sai dai idan ba kwakwaran sani kayi masa ba bazaka gane su yake kallo ba .."


Gabanta sai luguden bugawa da ganinsa yake sai dai hakan bai sa ta tsaida maganar da ta fara ba "Lawan ka daina zuwa gurina saboda banason abinda zai sa na dinga maka wulakanci, "idan har kina ganin daidai ne abinda kike min ki cigaba mrym , numfashi ta janyo da kyar ta sauke" ni dai lalla'baka nake amman ka gagara ganewa ,"to meye dalilin da bazaki amshi soyayyata ba ? yayi mata tambayar adaidai lokacin da AAT ya k'araso gurin. tayi shiru saboda buguwar zuciyarta daya qaru Shima lawan shiru yayi yana kokarin mikewa domin gaisawa da ATA Amman Ina bai tsaya bin ta kanshi ba tuni ya shige ciki .


ya koma ya zauna yana kallonta "Uhm ki bani amsar tambayata Ina jinki me yasa baki Sona me na rasa mrym? yayi mgnr yana kallon jikinsa a ranta tace "many things lawan hatta sunanka bai min ba bare akai ga surar jiki sai data hadiye abinda ya tsaya mata a makoshi kana ta cigaba "Ina son namiji fari sol dogo sannan intelligent abinda zai kara kashe ni ya zamanto yana da tsoron Allah shikenan ya gama da rayuwata zan iya mutuwa akanshi " kasancewar mu bakake yasa ba'a sonmu kenan ? a'a bance bakin mutun bai yi ba amman ni dai a gurina mutun fari sol nake so Irina wallahi ni ko nmj baki zai bani rabin duniya akan sadakina bazan amsa ba na fison kalata dan banason black .."sake baki yayi yana kallonta gbdy yaji ya munzata aguri dan shi baki ne sitik kuma ba wani mai tsawo bane can sai dai baza'a Saka shi cikin sawun gajeru ba tun bai kai ga magana ba ta mike tsaye "to malam lawan ni zan shiga ciki ta nufi hanyar part dinsu bayanta yabi da kallo yana aiyana abubuwa dayawa akanta sai dai baya jin zai iya hakura daita dan yana son farar mace koda kuwa mayya ce .




Mmn sudais
๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—
MAR'ADAMS
๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–
๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—๐Ÿ’—
Book one
Free page






*AYSHA A BAGUDO*


WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO


bismillahirrahmanirrahim


Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.


Page 8




"Ahankali take tafiya cikin sand'a tamkar wata 'barauniya yana hankalce daita duk da idanunshi a runtse suke amman bazaka ta'ba gane hakan ba sai wanda yayi masa cikakken sani , da d'an sauri ta nufi hanyar d'akinsu tana sauke numfashi Tare da ajiyar zuciya ,ta cire mayafinta ta wula saman katifa sannan ta samu waje ta zauna tare da rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafa zuciyarta a matukar tsorace take duk da tasan ba wani laifi tayi ba amman tasan tsoronta baya rasa nasaba da muguwar kiyayya da tsana mai tsananin da ya adam yayi mata tayi shiru tana sake zurfafa tunaninta sam bata hango ta inda zata iya amincewa aurensa ba gara kowa yaje ya nemo abokin rayuwarsa a waje
domin rayuwar aure dashi daidai yake da kamuwa da cuttutuka kala dabam dabam ."


"mr ATA ya cigaba da zama a parlour'n yana karkada kafarsa daya har sanda hajiya zulaiheart ta shigo parlour'n fuskarta a sake amman ganin yanayinsa yasa ta d'an shiga damuwa muryarta a raunane ta soma mgn "Adamcy nah har ka dawo ? ya had'e rai sosai tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa tare da gyada mata Kai kawai batare da yayi magana ba "Lafiya naga duk kayi wani iri ?fuskarshi a murtuke ya soma magana cikin tsananin fushi "wa yace waccen yarinyar tayiwa saurayinta masauki akan kujerun zamana ?mami ta numfasa irin nasu na manya kana tace " ban da abunka Adamcy wa zai sa tayi haka ?" ta dai yi haka nรฉ dan tayi ra'ayi tรด ma menene aciki dan ta zauna da bakonta akan kujerarka kwana nawa ne ma ya saura ?"ni dai babu ruwana da wani kwana nawa ne ya saura ni dai banaso dan ba ra'ayi bane kawai raini ne idan ba haka ba kujerun da nake zama akai shine ya zama na zancenta?yayi maganar yana shan kamshi ."




"Kai dai wallahi anyi rigimamme wannan zuciya wannan zuciya !! Allah ya sausauta maka, bakaken magana ya dinga fad'a akan maryam batare da yayi la'akari da matsayinta a gurin mahaifiyarsa ba mami batace komai ba har sanda ya dasa aya sannan ta kira sunansa a tsanake "Adam !bai amsa ba illa ya tsura mata kwayar idanunshi dake cike da bakinciki yana kallonta ta sake kiran sunansa "adam ! "a karo na biyu shiru yayi still yaki amsawa tunda yayi haka tasan bazai amsa ba yasa ta soma magana cikin kaukausan murya "zaka iya yin komai da kake so amman at least kayi respect din emotion din wani idan kai baka son maryam ka girmama masu sonta kuma naji dadi da hakan ya faru domin kasan diyata ba rasa masoya tayi ba yasa zan hadaku aure."




wani kallo yayi wa mami yana mai rausayar mata da kwayar idanunshi cikin nata muryarsa can kasa yace "alright sweetheart amman da me zai hana ku bar masa ita ya aureta dan zata fi bukatarsa da duk wani abinda kuke bukata daga gurina "tabbas nasa zata samu, zata samu duk wata kulawa a wajen duk wanda ta aura acikin masoyanta domin kuwa suna mata tru love most especially lawan kalli kaga irin abubuwan daya zo mata dashi ."ta fad'a dan qara masa haushi dan babu abinda ya tsana sama da wannan arayuwarsa ,ai kuwa tayi nasarar takalosa."


" He most be a fool da har yake bayyanawa common mace emotiona dinsa ta wannan hanyar , Kinsan allah sweetheart ko mafarkina na hadu daita a zahiri bazan iya mata irin wannan haukan ba ta zabga masa harara alokacin da yake kokarin yunkura wa zai mike ta dakatar dashi "adam !koma ka zauna ya koma ya zauna a kufule yana dubanta "kowani dan adam da yadda yake irin tashi soyayyar idan kai abubuwan bai maka ba watakilla su samarinta ya masu ,dan kyauta yana da matukar kyau ga masoya domin yana qara damkon soyayya dan haka kar na sake jin ka fadi haka ,kai kullum kana yin kuskure amman kai gani kake daidai kake aikatawa ,kowani dan adam yana kuskure amman wannan bana tunanin akwai wani kuskure acikisa sai ma kyautatawa soyayya sam sam bana jin dadin abinda kakeyi ...."


"to ku aura mata shi dan allah kunga ni na huta daman ni wallahi bana sonta dan wannan auren babu abinda zai jawo sai damuwa I really has to tell you the truth before everything could mess up ya fad'a a matukar zuciye ."murmushi hjy zulai tayi dan gbdy ta fahimci dan nata haushi yaji koma tace kishi yake yaga maryam da wani ,ta girgiza kai "ai kasan bana magana biyu tunda muka tsaida magana da mahaifinta idan kaga baayi auren nan ba to mutuwa nayi ,idan ba mutuwa nayi ba kuwa na rantse da girman allah adamcy sai ka aureta kai ko yau na mutu a daura maka aure daita zan bar wannan wasiya maryam takace ta har abada haka zalika kaima nata nรฉ mutuwa ce kawai zata rabaku sannan kai ma muna jiran naka gift din soyayyar tunda ka kamu idanushi ya ware sosai akanta yana kallonta a rude tare da furta kalmar "what ?




" your gift !
ta fad'a tana tsare shi da idanunta "Allah ya tsareni da wannan shirmen hau..."shut up Adamcy ai baka da wannan bakin dan ka rigada ka haukace tunda kake son abinda babu shi a duniya kuma lallai ka tabbatar da ka kawo naka gift din soyayya ranka shi dade a matukar zuciye ya juya ,da sauri sauri ya dinga taka step zuciyarsa kamar ta kama da wuta ta sake saida shi "adamcy nah !wannan karon a fusace ya juyo kamar zai yi kuka yace "what again ? "kaje kayi wanka ga dinner dinka ya kammala "bana bukata ya fad'a a kufule ."this is totally nonsense my love ta furta tana sakar masa murmushi dan tasan bancin itace da abinda zai fad'a kenan a fusace ya sake juyawa yana girgiza kai ."




Hjy zulai zaune tana sake duba kayan da lawan ya kawo ta kiran maryam ta fito da sauri tana amsawa cike da girmamawa "maza tattara kayanki ki kai daki shi kuma Lawan din kin fad'a masa an tsaida miki miji dan ya daina wahalar da kanshi ? ta sauke numfashi sannan ta girgiza mata kai alamun" a'a ! "okay kice masa yazo gobe ina son ganinsa ta gyada mata kai kawai ta tattara kayanta ta shige dakinsu cike da zullumi ta bar Hjy zulai cikin zullumin wannan auren da take kokarin hadawa sam sam
bata jin maryam domin ita din yarinya ce mai tsananin biyayya da hakuri akan komai adam take ji tasan shi tasan halinsa shine matsalarta tunda yace bai sรณ tรด har cikin ranshi bai sรณ nรฉ sai ta tashi tsaye da rarrashi da addua ,zata bari adduarta yayi karfi da sadaka , sosai tayi zurfi cikin tunani ."


Bayan kamar wasu mintuna ya fito sanye da wasu kayan wondo da riga farare sol kana ganin shigar kasan fita zai yi ,lokacin daya sauko parlour'n babu kowa zuciyarsa nayi masa wani irin zafi kamar zai fito waje ,sai dai ya kasa fita koina Kmr yadda yayi niyya ya bude bayan motarsa ya shiga ya zauna yana sake jin bacin rai mara iyaka yana marmarin shan sigari domin shansa na rage masa bacin rai sai dai tunanin illarta yasa baya son yawo daita domin yana bukatar ya bar shanta na har abada ." mr ATA bai shiga gidan ba sai karfe shabiyu na dare yana daf da wucesu ya haye step yaji sautin muryar mami "adamcy !cak ya tsaya yana ciccin magani "zakazo ne ranka dade koni na taso nazo ?"tayi mgnr cike da tsokana."


jin ta fadi haka ya soma qokarin qarasowa inda take su maryam naganin hk duk suka mike suka kama gabansu byn sun masa sannu da zuwa bai amsa masu ba ya cigaba da tsayuwa "zauna ta nuna masa wuri kusa daita "laifin me mahaifiyarka tayi maka da ka dauki fushi mai tsanani daita ?
"what ?!
"Yes fushi kake daita mana tunda gashi kaki cin girkin data sha wahala ta girka maka da kanta sannan ka tsallake ka bar gidan nan tun 9:00 sai yanzu batare da kai mata sallama da zaka fita ba wanda hakan ba dabiarka bace muddin kana kasar nan duk inda zaka sai ka sanar min sannan ka dawo km kana kallona zaka wuce baka da niyyar ce min komai ya dan kalleta ta kasan idanunshi yana cewa "Wannan yake nufi ina fushi dake ? yayi mgnr a shagwabe Kmr

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login