Showing 168001 words to 171000 words out of 185716 words
Chapter 57 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
har karfe goma sha biyu na dare ."Hjy salema dake zaune a bakin gadonta haka nan jikin ta ya dinga mata wani iri ,ta fito ta shiga dakin nuzla bata ganta ba dan haka ta juya ta fito daga dakin tana tmbayr aunty rabi wacce ta kasance diya kanwarta ce "umma bansa inda take ba amman bari na dubata a dakinta "ai daga dakin nata nike bangata ba shiyasa ma na tambayeki ." to bari naje na tmbyi aunty maijidda ko tasan inda taje da sauri ta wuce hjy salema."
A bakin kofar fita daga parlour'n suka hadu da aunty maijidda "Yauwa aunty maijidda ina nuzla ko ta fad'a miki inda zata "eh d'azu tace min zata wajen hisham amman bari na kirata nan ta soma qoqarin kiran layin nuzla sai dai numberta na shiga bata dauka dan haka ta kira layin hisham tana tmyrsa nuzla amsar daya bata yasa ta shigo d'akin hjy salema da mugun sauri ta isketa tsaye cikin faduwar gaba ."
Aunty maijidda batayi magana ba ta cigaba da kallon hjy salema "maijidda ko nuzla ta fad'a miki inda zata ?ta bude bakinta kenan zata bata amsa idanunta suka ci karo da envelop asaman dress mirrow din hjy salema an rubuta wannan sakon na umma da abba ne kallon da takewa envelop din yasa hankalin hjy salema ya kai kanshi "
gabadayansu gabansu ne ya shiga dokawa dan basusan me Ke kunshe a cikinsa ba tun baa kai ga budewa ba hjy salema ta soma furta kalmar "innalilahi inna ilahi rajiun azuci da fili dan ta gama shiga rudani "hannun aunty maijidda na rawa ta dauka ta bude envelop ta soma karantawa a fili hannunta da jikinta na wani irin wara ."
_Assalamu alaikum iyayena nasan aloakcin da zaku nemi ni ku rasa zaku ji babu dadi acikin ranku amman ina mai baku hakuri da neman afuwarku akan halin damuwar da zaku shiga a dalilina na tafe ne adalilin bana son aurena da yaya hisham na fito maku da manufata amman kun kasa fahimtata dan haka na yanke shawarar barinku ba dan raina yaso ba ina sonki ummanah ina sonki fiyyr da komai haka kai ma abbanah ina sonka zanyi kewarku sosai_
rabi ta nike takadar ta mayar cikin envelop din tana kallo hjy salema data zube kasa jinta ne ya dauke dip sakamakon abinda wasikar Ke dauke dashi duk wani kuzari da karfin jiki babu atattare da ita baya ga tashin hankali "ji take kmr ba ita bace anya nuzlarta ce kuwa ta ajiye mata wannna sakon ?
Aunty rabbi duk ta rude sai zufa take fitarwa nan da nan aka kira baba babba da yayyen nuzla maza har ma da hisham da ATA aunty rabi tace baba "kaji wani sabon tashin hankali nuzla ta gudu
ta mika wa yaya Ibrahim wasikar ya duba ,hannu hjy salema ya kama dan ta kasa motsin kirki binshi takeyi kmr rakumi da akala har uwar dakanta ya kamota yana qoqarin zauna daita taki zama tana fashewa da wani gigitaccen kuka tana furta sunan "nuzla! "ku nemo yarinyata dan allah ku nemo yarinyata abinda kawai take iya furtawa kenan "
"Ki kwantar da hankalinki hajiya zaa nemota yanzu ki zauna ki samu natsuwa ta girgiza masa kai tana mikewa ta fito tana kuka tana kiran sunan nuzla dole ya biyota damuwace karara ajikinsu, dukkan su da abinda suke sakawa cikin sanyi muryarshi wanda koda yaushe a haka take cikin sanyi ATA ya dinga kwantar wa da hjy salema hankali da tabbacin zaa ganta sai lokacin tadan dawo da ga mummunan mafaarkin da take dan gani take tamkar a dream ne ,, ta dan dawo haiyacinta sai dai kalmr INNALILLAHI INNAILAIHI RAJIUN take maimaitawa "
Numbobin yanuwa da abokan arziki aka shiga kira sai dai koina sai ace bata je ba duk suka rude kar ma hisham yaji labari duk ya rude ya rasa inda zai sa kansa idanunsa suka kada sukayi jajir gbdy ya nemi natsuwarsa ya rasa ji yake kamar zuciyarsa zata buga."gabadaya yan mazan babu wanda aka bari duk sun bazama nemanta hisham kam baya fahimtar komai duk maganar da salim yake masa baya shiga kunnuwanshi shiyasa yaji Kmr ya fita daga cikin motar ya taka da kafarshi watakilla nashi gudun zai fi na motar duk jikinsa tsuma yake kwakwaluwarsa ta hargitse kamar hauka zai kamashi a haka suka qaraso babban titin unguwarsu suna gama tsayawa ya fito da sauri yana dube dube amman babu ita babu alamunta ."
Numberta ya dinga kiran taki shiga har karfe biyun dare basu ganta ba suka dawo gida cikin damuwa baba babba yace kowa ya tafi kawai makwancinsa sai gobe aga abinda zaayi ."ranar kwanan zaune sukayi duk hankularsu a tashe hjy salema kuka kawai take zainab da aunty maijidda ce masu dan dauriya matar salim kuka take hjy salema duk ta rikice masu sai sunan nuzlata take kira ,hisham kwana yayi yana kiran layinta gbdy ya zare sai salim ne ya dinga kwantar masa da hankali ."
Washegari duk esatate din ya hargitse da labarin guduwa nuzla fad'ar irin tashin hankali da suka shiga bata baki ne yan biki sun cika gida babu abinda ake sai jajantawa juna ATA ya bada cigiyarta a duk kafafen sadarwa, lokacin da iyayen hisham suka qaraso daga masaukinsu dan su ba zaune suke a qasar ba hankalinsu ya tashi matukar most especially mahaifinsa sakamakon jin mummunar labarin abinda ya faru dan kallo daya yayiwa hisham ya fahimce sam hankalinsa bai jikinsa ga wata katuwar rama da yayi acikin kwana daya ."
amman ita mahaifiyarsa byn tashin hankali data shiga har 'bacin rai ta tsinci kanta ciki ranta ya baci matuka bare da ta samu labarin akan bata son d'anta ne ai sai taji soyayyar da takewa nuzla din ta juye zuwa tsana mai karfi "
Nana hauwa'u na zaune acikin dakinsu tare da maryam da diyana har ma da humaira , gabdayansu suna cikin jimamin abinda nuzla ta aikata "humaira tace "bansan me zai sa na gudu na bar iyayenta akan zaa aura min wanda banaso ,kowani iskanci mata sune kan gaba ku duba kuga shi nmj komai zaayi masa bazai ta'ba guduwa ya bar iyayensa ba amman sai kaga mace wai ta gudu wallahi nuzla really disappointed me ."
"maganarki gsky ai ko maryam ta isheta darasi gashi dai bata son yaya adam amman haka ta daure ta karbi kaddararta cikinsu babu wanda bata fadi albarakcin bakinta ba suna cikin wannan halin aka turo kofar dakin aka shigo hade da sallama gabdayansu suka waigo bayan suka kalli kofar dakin domin ganin wanda ya shigo ,hajiya zulfa'u suka gani sanye cikin doguwar riga na alfarma hannuwanta da wuyanta da yatsun hannunta duk gwal nd tayi kyau matuka sai dai kana kallon fuskarta zaka fahimce bata cikin natsuwa ."
Ta qarasa shigowa sosai yayinda gabadayansu suka maida hankalinsu gareta suka gaisheta cike da girmamawa ta danyi murmushi wanda kana ganin kasan na karfin hali sannan ta amsa , ahankali ta samu waje ta zauna agaban nana hauwa tana cewa "ku bani waje zanyi magana da nana hauwa'u gaban nana hauwa'u yayi wani irin faduwa ta hade hannuwanta waje daya tana wasa da yatsun hannunta har zuwa sanda suka fice daga dakin ".
"nana hauwa'u!" ta kira sunanta tare da jawo hannunta ta zaunar daita kusa daita bisa kujerar da take zaune akai "meye matsayina a wajenki ? tmbyr ta dan bawa nana hauwa'u mamaki amman dai ta bude baki ta bata amsa da "mahaifiya !" na gode mahaifiya zata iya yanke kowani irin hukunci akan diyar ta sai dai ni bazan yi haka ba sai dai na neman alfarma a wajenki ,nana hauwa'u tayi shiru kawai tana sauronta."
hjy zulfa'u ta cigaba da magana "ina neman alfarmar ki auri dana kuma yayanki hisham "
cikin wani irin yanayi mai cike da tashin hankali da tsoro abinda take shirin aikatawa ta dago da kanta ta tsura mata ido cike da tashin hankali "nasan zaki iya min fiyye da haka ,ki taimkeni kar na kunyata a gobe nazo da tarin jama'a ban san me zance masu ba idan baa daura auren nan a gabe ba ,cikin tsananin tashin hankali da firgici da tsinkewar zuciya da tsoro tare da kyarma nana hauwa'u ta fuskanci kanwar mahaifinta" dan Allah karki bani kunya nana hauwa'u ki amince min zaki samu dukkanin kulawa a gidan hisham cikin zuba mata ido tace "mumy yaya hisham..! karki ji komai kawai amincewarki nake nema "
Mmn sudais
๐๐๐๐๐๐
MAR'ADAMS
๐๐๐๐
๐๐๐๐๐๐
*AYSHA A BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
AREWABOOKS USERNAME
AYSHAABAGUDO
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page 28
..... Hajiya zulfa'u ta sake riko hannun nana hauwa'u gam cikin nata tana cewa "karki ji komai aranki hisham zai kula dake bazai ta'ba wulaqantaki ba wani yanayi nana hauwa'u ta dinga ji a gbdy ilahirin jikinta, kyarma da jikinta yake ya sake qaruwa ,babu abinda yazo mata alokacin kamar rayuwar maryam da yayanta adam yadda yake nuna rashin qauna garara agaban ko waye ,duk da mami dake tsakaninsu hakan bai sa ya hakura ya rungumeta a matsayin matar da aura ba."
ta daure ta cije amman tunaninta na zuwa kan maryam da yayanta ta fara hawaye saboda tasan me zai iya faruwa daita matsawar ta amincewa wannan auren ita kad'ai tasan yadda take jin zuciyarta a halin da take a lokacin wani irin tsananin tsoro ne ya shigeta ."
Kukanta ya d'aga hankalin hjy zulfa'u, jikinta ya soma kad'awa kamar mazari tana jin tsoron karta ki amincewa da muradinta amman duk da haka ta sanyawa jikinta jarumta tace "dan allah nana hauwa'u karki ce mun a'a rashin amincewarki zai sa naji kunya.wannan buqatar bawa ni kad'ai zakiyi ba har da martabar danginmu zaki yiwa kuka nana hauwa'u ta cigaba da yi har da shesheka tana mai tausayawa kanta ."
" tana son taki amincewa amman kuma bazata iya karya wa mumy zuciya ba tunda tasan ba ita kadai bace budurwa da bata yi aure a family ba ta tsallake kowa ta miki kokon baranta zuwa gareta ahankali ta d'ago idanunta dake cike da ruwan hawaye ta zuba mata "sosai ta tausayawa yanayin da hjy zulfa'u ta shiga dan a shirye take tayi komai akan amincewarta."
"Nasan kina tunanin halin da zaki tsinci kanki nรฉ a gidan hisham amman kisa aranki duk abinda zai faru na wani lokaci ne da sannu zaki zama tauraruwar agidansa idan kuma kikaji bazaki iya zama dashi ba ki fad'a min idan yayi miki wani abu na rashin kyautatawa just give me a call aurenku bazai qara ko second daya ba zan raba "ta fad'a tana jin d'acin kalmar aranta dan bazata so aurensu ya rabu zataso su kasance da juna har karshen numfashinsu."
Still dai shiru nana hauwa'u tayi tana zubar da hawaye "ki tausaya min diyata kar naji kunya ." ire iren sambatun da take mata kenan wanda ya haddasawa nana hauwa'u jin tausayinta mai tsanani bugu da qari ita din mutun ce mai mahimanci arayuwarta sannan taji dadin kalamanta tana ganin abun zai zo mata da sauki ta hanyar mumy muryarta a matukar sanyaye tace "mumy mami fa? "ina ..ina ganin ya kamata muji ta bakinta ?ta qarasa mgnr muryarta na rawa cike da in ina tare da sake sunkuyar da kanta ."
Hajiya zulfa'u ta d'aura hannunta daya akan nana hauwa'u tana shafawa tana jin wani irin sonta na shigarta fiyye da soyayyar dataji tana yiwa nuzla, har cikin bargon zuciyarta take jin nana hauwa'u wanda abun ya hade mata ne soyayyar mahaifinta da kuma na d'anta tilo da take dashi wanda a yanzu bata da kamarhi a duniya "nana hauwa'u maminki tasan da komai hasalima gurinta na fara zuwa har ga allah aunty zulai ta amince, tace daman burinta kenan taga kinyi aure kafin allah ya dauki ranta taga yan jikokinta na wajenki kullum adduarta fatan miji na gari take miki ,gashi kin samu domin hisham danuwanki yafi kowa cancata dake nmj nรฉ da idan mace ta samesa zataji dadin rayuwa dashi ,domin kuwa miji na gari nรฉ allah ya hadaki dashi ta amince dari bisa dari kawai a nemi amincewarki
Ta dago kanta tana kallonta
murmushi tayi ga kuma hawaye na gangaro mata tace "shikenan mumy tunda mami ta amince nima na amince kuma nayi miki alkwarin zan zauna lafiya dashi zan kawo miki farinciki arayuwarsa zakiyi farinciki da kasancewarmu ."
Nan take hajiya zulfa'u ta rungumeta tsam ajikinta cikin tsananin farinciki tana hamdala a fili "Alhamdulillah diyar albarka na gode nana hauwa'u ,kin tabbatar min da ina da matsayi a wajenki kuma zakiyi farinciki a gidan hisham in sha allahu bazakiyi kuka ba 'allah yayi miki albarka ta riko hannunta Tare da d'agata tsaye ta soma tafiya daita, binta kawai take har lokacin da suka fito zuwa falon gidan wanda a daidai wannan lokacin da karfe shadaya na safiyar ranar ta buga babban falon baba babba ya cika da gabdaya ahalin yaya Alhaji Abdallah."
dayawa daga cikinsu zukantasu na cikin da tsananin tashin hankali bangaren baba qarami wanda har lokacin bai san inda diyarsa hindu take ba ,haka baba babba wanda ya rasa diyarsa a daren jiya bangaren mahaifin hisham shima zuciyarsa cike take da damuwar halin daya baro dansa ciki haka hajiya salema tunda ta zauna hawaye kawai take gogewa wasu na sake zubowa haka zalika uban gayya ATA da zaa yiwa auren dole tun daya zauna idanunshi ke kallon sama tunani kawai kwakwaluwarsa keyi ."
babban parlour'n ya dauki shiru na kusan mintuna goma sha biyar kowannensu da abinda zuciyarsa take saqawa ,baba babba yayi gyaran muraya sannan ya fara magana a tsanake "zan fara da jajantawa kanmu halin da muka tsinci kanmu a ciki wannan lokacin amman nasan allah yana tare damu ,fatanmu allah ya bamu ikon cin jarabawar data fad'a mana nida dan'uwana" .
"ni ai ikon allah da kuma rashin qarar kwana ne kawai yasa har yanzu ban mutu ba akan rashin hindu inji cewar baba qarami jin abinda baba qarami ya fad'a cike da damuwa yasa ATA sauke kanshi ya kallesa kawai yana ta,be baki at the same time zuciyarsa na tsananta bugawa yana jin ina ma shine hisham da nuzla ta gudu ta barshi , ina ma shima wannan guntuwa shegiyar yarinyar ta gudu ya huta tunda itama ba son shi take ba "zaune amman zuciyarsa bata gaji da adduar samun sausauci daga wajen allah ba ".
" in sha allahu allah zai bayyana su gabdaya suka hada baki suka ce "Ameen allah ya kawo mana mafuta sun dade suna tautaunawa akarshe baba babba yace "yanzu ya zamuyi ? "dawa zaa maye gurbin nuzla a wajen hisham domin dai bazaa fasa d'aurin aurensa ba ?ya qarasa maganar adaidai lokacin da hajiya zulfa'u ta shigo falon hannunta rike dana nana hauwa'u tana cewa "karku damu ga wacce zata maye gurbin nuzla a wajen hisham nan domin kuwa na nemi alfarma a wajen diyata nana hauwa kuma ta amince da zata auri hisham tsakanin da allah ."
Da wani irin saurin hjy salema da kanta ke duke ta d'ago tana kallon fuskar nana hauwa'u zuciyarta cike tashin hankali mara misaltuwa yayinda idanuwanta suka sake cikowa da ruwan hawaye, kallo daya nana hauwa'u tayi mata ta fahimci halin damuwar da take ciki ga dukkanin alamun bata ji dadin hukuncin ba ,ahankali tayi kasa da kanta dan bazata juri kallon cikin kwayar idanunta hjy salema ba dan wani irin tausayinta ne ya lullubeta ,itama bata sรณ haka ba
sannan ba yin kanta bane babu yadda zatayi , da ahlinta su kunyata gara ta rungumi qaddarar auren yaya hisham ,kuma ma ai asirinsu zata rufa gabadaya har ita nuzla domin idan basu na gida da suka san ta gudu ba babu wanda zai sani ".
Kafin hjy zulfa'u ta sake magan tuni ATA wanda hankalinsa ya tashi matuka da jin maganarta yace "da gaske nana hauwa'u kin amince ko kuwa kina son yiwa mutane wasa da tunani nรฉ "?jikin nana hauwa'u a matukar sanyaye ta jinjina masa kai jikinta na kyarma jin yadda jikinta Ke rawa yasa hjy zulfa'u ta rikota sosai ta had'eta da jikinta saboda tsabar farinciki data haifar mata "amman dai nana hauwa'u kin kyauta Allah kuma yayi miki albarka allah yasa ki gama da duniya lafiya lafiya inji cewar baba babba ."
"Gsky kin kyauta sam ban yi tsamanin zaki mana haka ba hakika kin fitar da alhalinki jin kunyar duniya ,allah yayi miki albarka yasa ki gama duniya lafiya yadda kika rufa mana asiri kema allah ya rufa miki asiri duniya da lahira hajiya jamila mahaifiya ga aunty abida ta fad'a cike da jinjina mata."
gabadaya mutanen dake parlour'n addua suke mata tare da gode mata amman ban hjy salema da mami wacce tayi alkunya ,yayinda ita hjy salema bakinciki nรฉ Kmr ya kasheta ,duk da irin qaunarta ga nana hauwa'u sai taji a yau babu ita ta juye zuwa qiyayya mai zafi "me yasa zata amince da wannan auren bayan diyarta ce tafi cancata da auren hisham ?"ko bama haka ba a tunaninta ko auren wasu zaayi dabam ya kamata a d'aga shi sakamakon rashin diyarta da tayi amman hankalin kwance suke bayyana farincikinsu ."
wani sanyin dadi ne ya lullube nana hauwa'u jin dadin yadda ahlinta sukai alfahari daita ."muryarta a matukar sanyaye tace "me yasa zakuyita gode min dan Allah ku daina gode min nayi saboda kare martabar gidanmu nรฉ ,bazan so ahlina suji kunya ba a idon duniya ba halin yanzu abinda nafi buqata daga gareku shine addua