Showing 27001 words to 30000 words out of 185716 words
Chapter 10 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
a tura 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube.
Page7
........" Cikin mugun firgici da tashin hankali aunty khadeja da aunty shahida suka yi shiru gabad'aya suna kallonta cike da sansar fargaba da tashin hankali "me zasu fad'awa mami data d'auki soyayyar duniya ta d'aurawa aurensu ? " ita kam Maryam kasa kallon cikin kwayar Idanunsu tayi ta takure jikinta guri daya tayi kasa da kanta idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye gbdy ta kasa kwakwaran motsi a zaunen da take , wani iri take ji a gabadaya ilahirin jikinta ,sai lokacin taji wani irin kunyarsu tayi mata diran makiya .
ji tayi kamar ta tashi ta bar gurin sai Kuma taga hakan ba daidai bane ,basu cancanci haka daga gareta ba ,zasu d'auka raini ne dan haka ta cigaba da zama zuciyarta na tsalle da bugawa wasu hawaye masu zafi suka samu nasarar zubowa akan kuncinta tasa hannu ta goge wasu na sake zubawa ."
Sanyayyaye numfashi aunty shahida ta sauke tana gyara zamanta tare da janyo maryam zuwa jikinta tasa tafin hannunta tana share mata hawaye "kukan ya isa haka tunda baki son shi shikenan zamu san yadda zamu fahimtar da mani amman da zakiyi hakuri kiso AD hakika maryam da kin san kin dace miji na gani na fad'a ba dan AD ya kasance dan'uwana ba ,duk mace zata yi alfahari ya kasance miji agareta kuma uban ya'yanta ki tsaya kiyi tunani maryam karki yanke hukunci cikin tsoro da tashin hankali ".
Cikin tsananin kuka da tashin hankali maryam tace "a'a aunty shahida babu wani tunani da zanyi akan ya Adam dan yafi qarfina ta kowani bangare ban Isa na tsaya Inda yake ba bare na kasance mata agaresa ta Ina zan soma rayuwar aure dashi aunty shahida ? "Ta Ina zan fuskanci mutumin da bai qaunar ya bud'e idanunshi ya gani ? "duk duniya idan akwai macen da ya Adam ya tsana to nice "Ina zan kai tsoron da nake masa har nayi rayuwar aure dashi ? uwa uba baya Sona ta yaya kuke tunanin nima zan soshi har naso zaman aure dashi ?" wallahi aunty shahida ni tsoro ma yake bani ban ma san ta ya zan fara rayuwar aure dashi ba , da zarar nagansa bana samun natsuwar zuciya har sai na nisanta kaina dashi to ta yaya kuke tunanin zan iya zaman aure dashi Koda Ina son shi bare bana masa soyayya irin ta aure sai ta yan'uwantaka ?"
" ni yanzu tashin hankalina mami wallahi bazan so taji wa......."kuka yaci karfinta ta kasa qarasa maganarta "dan wannan karki damu Ina da tabbacin da zarar kunyi aure shikenan maryam ,bazai nuna miki komai ba sannan zaki daina jin tsoronsa inshallahu zakiyi farinciki a gidansa. "maryam ta zumburo baki "Allah aunty shahida bazan iya ba shine miskilanci shine girman kai , uwa Uba zuciya idan na auri ya Adam bazai barni na rabi Inda yake ba kullum zan tabbata cikin gallazawarsa wa zai ceceni a hannunsa ? ta Kalli aunty khadeja hawaye na gangarowa akan quncinta "yan'uwana ku taimakeni karku bari a had'a auren nan , ban rainaku ba sannan ban ki shawararku ba amman abar wannan maganar yanzu baku ji yadda nake jin zuciyata ba ,ji nake kamar zata fashe tsabar tashin hankalin jin maganarku , Kalli yadda jikina ke rawa aunty khadeja Allah bazan iya ba ta k'arasa maganar tana sake rushewa da wani sabon kuka."
Aunty khadeja wacce tayi shiru tana sauraronsu tace " duk na fahimceki Maryam amman yana da kyau mutun yayi dogon nazari akan duk abinda ya kunno kai cikin rayuwarsa zamu baki lokaci kiyi tunani sannan kiyi istahara ..?maganganu masu sanyi da kwantar da hankali aunty khadeja tayi amfani dasu gurin son janyo hankalin maryam duk da a rikice take amman tana fahimtar komai dake fita daga bakinta ,naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana mai kallon aunty khadeja sannan taja gindi zuwa Inda take ta riko hannunta d'aya cikin nata ta damke gam jikinta na sake d'aukar kyarma muryarta a raunane tace "aunty khadeja bazan iya aurensa ba bari ma na fada muku gaskiya akwai wadan da suke sona sosai ku bari ya nemo matarsa a waje zai fi zame mana alkairi ......"
duk yadda sukayi daita ta fahimcesu taki sai faman kuka take tana basu hakuri ganin yadda ta rikice sai kuka take tana rokonsu tana juya Kai yasa suka hakura da batun tare da sallamarta da kyar ta mike tsaye tana layi saboda juwar dake dibarta ta bar parlour, a tare aunty shahida da aunty khadeja suka Kalli juna suna sauke ajiyar zuciya " ban ta'ba tunanin maryam zataki amincewa da wannan had'in ba ,na d'auka zata fi kowa farinciki da murna zata kasance matar AD duba ga yadda naga 'yammata na maseefar son shi da son aurensa inji cewar aunty shahida "ai abun ba daga nan take ba aunty abincin wani gubar wani kuma ma ni banga laifinta ba shi kasan AD matsala ne bare a kai ga halin miskilancinsa aunty khadeja ta fad'a tana jan tsaki " bayan wannan miskilanci nashi bashi da wani aibun da zaa ki aurensa gaskiya kawai dan bata son shi ne abar zance zuwa wani lokaci sai mu fahimtar da mami .
"Haka ne amman ya kamata ki kirasa ki fad'a masa ba'a son shi ko ya dan rage jijji da kai da mislinci da nuna fad'i da Isan da yake "yanzu kuwa zan sheida masa aunty shahida ta fad'a tana ciro wayarta daga cikin handbag dinta kira d'aya ya katse ya biyo byn Kiranta "kazo yanzu muna parlour'n mami na uku , tana gama fad'ar haka ta katse Kiran tana jan tsaki dan tasan bancin halaiyan da yake nunawa maryam da babu yadda za'a yi takisa ".
maryam kuwa tana fita d'akinsu ta shiga ta zube kan gado tana kuka sosai har da shesheka tana jin rashin dadin kin amincewa yan'uwanta da tayi , ko babu komai yaci darajansu agurinta ta amincewa aurensa "mai yasa na ma su aunty shahida haka ?mai yasa bazan so zabin su ba kuma jininsu da suka fi qauna akan komai ?" hakika ban kyauta ba na yiwa yayar mahaifina butulci da yan'uwana sam basu canci haka daga gareni ba "why why maryam why do you do this to them ?tana cikin wannan halin nana hauwa'u ta fito da sauri daga bayi dan sheshekar kukanta ne ya hankaltar daita ganin yadda take kuka kamar wacce aka aikowa da sakon mutuwa yasa ta k'araso da sauri ta hau sama gadon tana mata magana cikin tsananin tashin hankali "menene marsi ? dan wani loakcin da haka take kiranta mrym ta sake fashewa da wani sabon kuka zuciyarta na zafi da qunci banci tsakaninta da nana hauwa'u basa boyewa juna komai tabbas da bazata fad'a mata ba zata boye wannan maganar ta barwa kanta ita kad'ai tunda tasan su aunty shahida ma bazasu fito da maganar ba .
sheshekar kukanta ya qara dagawa nana hauwa'u hankali jiki a mace ta kamota ta rungumeta tsam ajikinta itama ta fara hawayen tausayin yar'uwata duk da bata san dalilin kukanta ba a hankali ta soma jin sautin muryarta cikin kuka "na shiga uku nana hauwa'u na kasa yiwa yan'uwana abinda ya kamata na kasa bin umarninsu nasan zasu ji babu dadi a ransu tayi mgnr hawaye na gangaro mata ...."
"menene abinda kika kasa sannan su wani yan'uwa kenan ? ta fad'a tana sake rungumota jikinata' kiyi hakuri ki natsu marsi ki fahimtar dani abinda ke faruwa "naunayen ajiyar zuciya ta sauke sannan tayi mata bayani komai cikin muryar kuka tana mai zare jikinta daga nata ta cusa cikin tsakankanin qa'fafunta tana sheshekar kuka tare da kamkame jikinta .
Shiru nana hauwa'u tayi a matukar tsorace tana kallonta tana maimaita maganarta kafin daga bisani ta motsa bakinta ta soma magana a zafafe "hakika babu aibu a maganarki sister tunda shima bai sonki kema bai dace ki so shi ba amman wani hanzari ba gudu ba maryam nayi noticing ba ya Adam Kawai ne bakya so kowa ne bakyau qaunar yace yana sonki dan duk wanda ya nuna yana sonki gocewa kike".ta d'ago a hankali ta Kalli nana hauwa'u da take magana "kin tsareni da idanu ai gaskiya na fada aure fa rahma ne yana d'aya daga cikin dokokin Allah da manzonsa cewar aso aure Kuma a girmama shi me yasa ke bakya so ? Kalli yadda abbas da anás suke haukan sonki kmr zasu mutu byn su ma akwai wasu amman kullum wulakanci da tozarci ke shiga tsakaninku ,ki duba lamarina maryam kad'ai ya isheki ishara mutun nawa suka ce suna sona a rayuwa ? ."
Shiru maryam tayi tana kallonta hawaye na tsiyayowa daga kwarnin Idanunta "me na rasa ajikina ko a tare dani amman har yanzu shiru babu wanda yace yana sona ko acikin family's bare maganar aure ? bamu da wani lokaci maryam a shekarunmu na talatin a duniya ,idan akace babu lokaci ba komai ake nufi da hakan ba illa mutuwa ake magana domin zata iya zuwawa mutun a kowani lokaci ,ni dai shawarata anan kiyi addua abinda yafi zama alkhairi a tsakaninku da ya Adam Allah ya zaba miki ba kuka ba dan duk yadda zaki ki aurensa idan Allah ya qaddaro mijinki ne dole sai anyi ta qarasa mgnr tare da riko hannuwanta duka cikin nata tana kallonta a sanyaye kana ta cigaba da magana "kina da sa'a marsi arayuwarki da har akayi tunanin a had'aki aure da yaya adam byn akwai tarin yammata acikin danginmu wad'an da nake da tabbacin da sune aka nemi a hadasu dashi da tuni an wuce gurin."
" hakika mami ba qaramin qauna take miki ba ,
ba dan ya Adam yana dan'uwana ba yana da kirki daidai nashi marsi ,nagarta ga kyawawan halaiya da kyakkyawar zuciya illarsa dai rashin son magana da mislinci da km tsanar da yake nuna miki byn wannan bashi da wata aibu da za'a kishi , idan kika auresa zaki zamo matar da babu kamarta acikin matan duniya ,kema kuma haka ne kina da halaiyan da baza'a ta'ba barin kije ki auri wani ki barshi ba ."
"hankali nana hauwa'u ta dinga kwantar mata da hankali har kukanta ya tsaya ta qura mata Ido tana sauke ajiyar zuciya "ki saki ranki please idan ba kina son nima na shiga cikin damuwa ba "murmushi maryam ta sakar mata tare da goge hawayenta "yauwa ko ke fa matar yayana inshallahu ta fad'a tana mikewa ta bar d'akin mrym ta kwanta lamo akan katifa tana sauke numfashi sama sama tana tunanin mafuta zata amince ko kuwa zata tsaya akan ra'ayinta ne ?"
A parlour hajiya zulaiheart ya samesu zaune sunyi shiru kowannensu da abinda yake sakawa a cikin ransa , yayi sallama a ciki kmr baya so ,suma aciki suka amsa masa kamar yadda yayi dan gbdy haushinsa aunty khadeja take ji dan gaisuwar da yayi masu aciki ma bata amsa ba shima bai damu daya sake gaishesu ba dan ba kasafai yake son gaisuwa ba hasalima yawon gaisuwa na cikin abinda ke motsa zuciyarsa "ya k'araso cikin sanyin jikin nan nasa ya zauna akan kujera mai zaman mutun d'aya ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya ya fuskancesu batare daya yi magana ba ."
gyaran murya aunty shahida tayi kana ta soma mgn "burinka ya cika AD domin kuwa maryam taki amincewa da aurenka juyin duniya munyi daita tace bata sonka bata ga abinda zatayi da aurenka ba shikenan sai hankalinka ya kwanta ka zuba ruwa a kasa kasha tunda kai ma alal lalurati zaka aureta ba dan kana sonta ba , amman kasan da sani bazaka cigaba da zama haka ba dole ka fito da mata Kuma cikin wannan lokacin kayi aure dan kwancinyar hankalin mahaifiyarmu .." ban san dalilin da yasa kake kin yarinyar nan ba batare da wani huja ba wallahi sam banji haushinta ba kaso mai sonka haka zalika Kaki mai kinka inji cewar aunty khadeja wacce ta k'arasa maganar cikin tsananin fushi tana jan tsaki a fili wani mugun kallo ya watsa mata mai had'e da harara yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa , ta kawar da kanta gefe tana zuba tagumi ."
Shiru kowannensu yayi bayan sun gama zayyane abinda ke ransu shi kuwa yafi minti ashirin yana zaune zuciyarsa na wani irin bugawa batare da yace uffan ba kafin daga baya ya motsa lip's dinsa a hankali "sweetheart tasan da wannan maganar ?ya tambaya yana kafesu da Kyawawan idanunshi masu matukar kyau da bugar da zuciya sai dai a yanzu kallosu kawai zai sa ka fahimci tashin hankali da balain dake cikinsu "bata sani ba amman dole zata sani Kuma a yanzu "A hankali ya dinga girgiza kafarsa d'aya yana cizan lip's dinsa na kasa yana maimata Kalmar da aka fada masa mrym tace " bata sona ? wannan karon a fili ya fad'a yana kallon aunty shahida zuciyarsa na zafi da quna da tuttukin bakinciki mara misaltuwa ,kai tsaye tace "tabbas abinda ta fad'a mana kenan kai daga gani ma tana da wanda take so....."stop aunty shahida karki fad'a min haka mana taya zatace bata Sona?" wacece ita dan ubanta da har zata ce bata son Adam Tariq Abdullah ?"mace mai daraja da zuciya mai kin wanda yake kinta" ta bashi amsa da haka tana zabga masa katuwar harara."
murmushin gefen baki yayi wanda yafi kuka ciwo yana girgiza Kai "impossible babu wannan macen a fad'in duniya da zata ce bata son ni Adam wallahi ta raina muku hankali ne sannan tayi balain rainaku ni ko giyar wake ta sha bazata ta'ba fada min haka ba , numfashi ya sauke a maganarsa ta karshe sannan ya mike tsaye ya zuba hannuwansa duka cikin ajihun wandonsa ya soma taku kamar baya son taka kasa yana k'okarin barin parlour'n a matukar fusace har ya Kai bakin kofar fita ya tsaya cak batare da juyo ba "abar maganar nan a tsakankanimu banason sweetheart tasan komai zan san abunyi .."
"Da dai ya fiyye maka ka ajiye wannan shegen girman kan naka ka fuskanceta da kanka wata Killa zata yarda "inji cewar aunty shahida " ai ni idan na fuskanceta umarnin kawai zan bata Kuma dolenta tabi umarnina koda kuwa mutuwa zatayi yana gama fad'ar haka ya k'arasa ficewa daga parlour'n bai tsaya jin abinda zata ce ba .
girgiza Kai sukayi a tare "kinji ba aunty , kinji abinda yake cewa ko ?"wato shi bazai rusunar da kai ba, Komai ta karfi zai yi byn ita mace yar rarrrashi ce ." Allah dai ya shirya AD yasa ya gane kuma ya wanke masa wannan zuciyar tasa aunty shahida ta fad'a . bedroom din hajiya zulaiheart suka shiga suna qoqarin danne damuwarsu dan karta fahimci komai a hankali suka dinga nuna mata babu wata matsala sunyi mgn da maryam kuma ta amince "masha Allah "Kai alhamdulillah amman naji dadi Allah yayiwa rayuwarsu albarka wannan aure Ina son shi Ina qaunarsa Ina farinciki dashi yanzu sai a sanar da baba babba shi kuma ya nemi sauran yanuwansa aje neman aurenta gurin saidu ko ? "wannan haka ne amman ki dan tsaya tukun kinsan halin 'yan kayanki muna son ya dan saki jiki da mrym din su samu fahimtar juna sai ayi maganar aure hjy zulaiheart ta gyada Kai tana murmushin jin dadi "wannan ma shawara ce mai kyau Allah ya daidata tsakaninsu dan mrym bani da matsalata daita , nan sukayita biyewa hjy zulaiheart dan basa son tasan abinda ke faruwa ta shiga damuwa , domin kuwa muddin tasani akwai gagarumin tashin hankali a gidan ."
"Yana shiga d'akinsa zariya ya soma yi daga farkon d'akin zuwa karshe ya kasa zama kamar wanda yayiwa sarki karya can ya tsaya cak yana jan tsaki har lokacin mamakinta yake dan yasan aunty shahida baza ta'ba fad'a masa qarya ba daya qaryatata cikin zafin nama ya soma balballe botiran gaban farar rigar dake sanye ajikinsa ya cire sannan ya zame ash three quarter din da yake sanye dashi ya shiga toilet yana sake jan tsaki ya kunnawa Kansa ruwa yana jan numfashi da rarrashin zuciyarsa tare da son karyata zuciyarsa akan jin haushin maganar yarinyar shiru yayi ruwan na sauka ajikinsa " dole yana bukatar saita kanshi dan ya samu damar tarwatsa zuciyarta cikin ruwan sanyi ban da ma hauka da jakanci irin nata Ina ita Ina shi Adam ai sai dai darajan iyaye ?
shi da yake da mace kamar princess yarinyar da ta samu kyakkyawan mazauni a zuciyarsa me zai yi da mai jiki kamar na turkey, abinda batasani ba da abashi mace irinta gara ya kare rayuwarsa babu aure yana cikin toilet ya dinga jin sautin qarar wayarsa bai fito ba sai daya samu natsuwa sannan ya fito d'aure da white towel iya gwiwarsa ya tsaya gaban mirrow yana karewa kanshi kallon tsab sannan ya sauya kaya riga armygreen da wando baki kafafunsa sanye da takalmi fari sol ya zauna shiru akan kujera duk yadda yaso ya cire damuwar rashin son shi da'akace mrym batayi abun ya cutura wani irin zabura yayi ya mike ya kwashi wayoyinsa ya fito zuwa haraban gidan Inda security da escort dinsa ke faman safa da marwa suna ganinsa suka hau kikiniyar bud'e masa bayan mota suna furta" barka da fitowa ranka ya dade ya shiga ya zauna fuskarsa a hade batare daya amsa ba direbansa yayi saurin shiga mazaunin direba "aka bude makeken get din gidan ,motor daya da direba da wasu escort sukayi gaba sannan motar da Mr ATA ke cikin sai daya a bayansu suka bar gidan suna hawa kan titi kira ya shigo wayar direba sai daya nemi izini agurin A
Mr ATA sannan ya d'auka mgn daya ya katse kiran Tare da tmbyr mr ATA"ranka ya dade Ina muka nufa ne ? "gdn mb ya fada ataikace yana kallon gefe titi zuciyarsa na zafi ,tafiya mintuna kadan sukayi suka k'araso ikeja gra a kofar gidan suka ja suka