Showing 102001 words to 105000 words out of 185716 words
Chapter 35 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt
janyo yanuwanki sun wulakanta mana d'anuwan an tozarshi, tunda muke anan unguwar aka haifemu muka girma mukayi aure baa ta'ba wulakantamu ba sai yau kuma duk akanki ,kinsa ana dukansa kamar an samu ganga na rantse da girman allah matukar ussein..."
saurin toshe mata baki nayi ina cewa fatima karki rantse ,cikin fushi ta cire min hannu "ki barni aunty nayi magana kalli yadda fuskarsa tayi duk jini saboda Allah yau ayita ta qare ta kama kanta ta daina zuwa inda yake ,yanzu da suka zo suna hargagin banza da wofi da wulakanci shi meye laifinsa? yarinyarsu ya dace suyi wa magana ta daina zuwa inda yake dan muddin ta sake zuwa inda yake kafin ku dauki mataki mu zamu dauka dan ba daga sama ya fado ba azzaluman banza kawai kuma allah ya isa tsakaninmu daku tana fad'a aisha na fad'a."dan girman allah fatima karki sake cewa komai zo muyi magana na janyo hannunta " babu inda zani aunty ayita ta qare gwama su san muma bama son wannan diyar tasu kuma komai zai faru ..."
na sake toshe mata baki "dan Allah ki bar mgnr nan sulhu ake nema ."
Cikin ko in kula hjy rahma tace da wa zakuyi sulhu ?"kema Kinsan ruwa ba sa,an kwado bane baku kai wannan matsayin ba yanzu ma wannan maganar da nake duk sai na fashesa akan wannan matsiyacin "nayi tsuru tsuru ina dubanta "tsayuwar me kukeyi ku taho min dashi da sauri gali ya qaraso inda take hjy ai mun gama magana da yaronki, dan allah hjy kiyi hakuri ,in sha allahu tunda muka shiga cikin zance komai yazo karshe zanyi magana dashi "babu irin hakurin da baa bawa hajiya rahma ba amman tace sam sai an tafi dashi haka muna ji muna gani aka watsa useein abayan boot din mota aka wuce da
ussein ."
Kuka sosai maryama take kamar alokacin komai ya faru Kwantar da kanta umma tayi akan cinyarta tana rarrashinta "tabbas Aunty masoyiya ce ta gaskiya ,ta so mahaifinmu a halin babu ,ta zauna dashi har karshen rayuwarsa wallahi ba kowani d'an mai kudi bane mutumin kirki kamarta ,ta tsaya ta dubi mahaifinmu da kalmar so ta gaskiya
sai dai akwai illa umma Aunty ta jefa rayuwarta cikin matsala wanda a yanzu take shan wahala ".
" tabbas shine gskiyar dana dade ina nuna mata "baa jayayya da iyaye data yi hakuri tabi umarnin iyayenta tabbas zasu sauko dan kansu kasancewar akwai rabo a tsakaninta da mahaifinku ,cikin muryar kuka tace "mune silar jefa rayuwar mahaifiyarmu cikin wahala ko ? ta fad'a tana sheshekar kuka "karki ce haka maryama haka tata qaddarar take ,ita qaddara gata ko arziki ko nasaba bai isa ya canza maka ba ."umma ta numfasa sannan ta cigaba da magana ".
Bangaren su bilkisu kuwa tunda suka dauki hanya yan'uwanta suke magana suna zagin ussein cikin kuka bilkisu Ke rikon su "ku sani ussein bai muku laifin komai ba dan allah karku hukuntashi akan abinda bai yi ba" mari mahaifiyarta ta kifa mata haka ma aisha dan ubanki ki kama mana baki har suka kai gida zaginta suke direba na ajiyesu ya wuce da mahamud da ussein ."
a matukar gigice bilkisu tabi byn motar da kallo cikin tsananin firgici, keyarta suka tasa sai cikin bangaren hjy rahma ."Suna shiga part din hjy rahma suka turata daki suka daureta da igiya tamau sukasa saber ya dinga dukanta adaure tun tana ihu har tazo ta kasa a yadda ta fad'a min cewa tayi har da barkono mahaifiyarta ta nika tasa mata a gabanta da cikin idanunta wanda yasa tayi suman wuncin gadi ."
Bangaren mu rana babu wanda ya samu sukuni acikinmu gali yafi kowa shiga damuwa safa da marwa yake yana cewa "ban ta'ba kawowa araina duk hakurin dana basu ba zasu hakura ba , na dauka maganata zai sa su hakura amman ina kamar sake fusata mahaifiyarta nayi wadan nan mutane sam basu da imani ."wallahi basu da imani gali inji cewar hjy ka kalli irin duka da sukayi yarinyar nan bilkisu ko rikonta suke bai dace suyi mata irin wannan dukan ba ."
"wallahi ku sheida bilkisu bazata sha wannan wahalar a banza ba komai zai faru sai useein ya aureta ba dai bakinciki su kenan ba saboda suna takama da kudi ,ni bana da kudi amman ina da Allah alfarma annabi da alqurni sai wannan auren ya tabbata ko ina raye ko byn na mutu mutane sam babu imani aransu bazai hakura da aurenta ba sai dai su mutu fatima zatayi magana ta dakatar daita "banason jin komai daga bakinku sai fatan wannan auren ya tabbata ."
abban sadam ya fito daga bayi daman zagayawa yayi yace "har yanzu bazaku hakura da wannan maganar ba ? hjy tace "taya zaa hakura?" da sukutun fa suka wuce min dashi ?naga diyarsu ce tunda sunce basaso tarayyarsu a hakura mana "bazaa hakura ba bilkisu bazata sha wahala akan ussein ya tafi a banza ba ina sonta tunda tana son jinina ta gama min komai ni yanzu ta'bo min abokika Abdul zanyi magana dashi babu irin kiran da baayiwa Abdul ba amman wayar bata shiga ranar hjy bata runtsa ba kwana tayi tana kaiwa allah kukanta ."
Washegari ana idar da sallahr asuba tasa aka cigaba da trying dinsa amman shiru baya shiga sai karfe uku na rana ta shiga ya dauka da sallama byn sun gaisa hjy tace "Abdul ko kasamu labarin abinda Ke faruwa da useein ?bansan me yake cewa hjy ba amman naji tace "meye rashin kyautarwasa haramun ne dan soyayya tashiga tsakaninsu ?saboda shi talaka ne yasa basu dace ba to shikenan nan in sha allahu gamu nan zuwa ."
Tana gama waya tace muje gidansu bilkisu mu samu mahaifinta nace" a'a ta bari ni da gali da fatima muje da kyar hjy ta yarda ta barmu muje babu ita sai dai fatima tace bata zuwa koina nace saboda me kai tsaye tace min ta tsani bilkisu da yan gidansu sai da saadatu da gali mukaje da taimakon Abdul muka shiga estate dinsu sai dai baa bari mun shiga cikin gidansu ba a bakin get din gidan aka tsaidamu yayanta abubakar muka samu gani muka gaisa dashi babu laifi fuskarsa da dan rahma dan yafi mahaifiyarsa byn mun gaisa gali ya fad'a masa ko mu su waye da dalilin zuwanmu "ayi hakuri ranka ya dade ,hakika danuwanmu bai kyauta maku ba domin ya shiga hurumin da banashi ba soyayya da diya irin taku shima yasan bai dace ba , dan allah kasa baki ranka ya dade abamu ussein tun jiya da suka wuce dashi baa dawo dashi ba ,dan allah a maido mana dashi ."
shiru yayi ya kasa cewa komai ganin hk yasa gbdy muka kwantar da murya "ka taimaka kasa a sako mana ussein cikin ko in kula yace kuje zai dawo gida zuwa anjima amman kuja masa kunne ya fita a rayuwar bilkisu "in sha allahu komai yazo karshe cike da farinciki muka juya zuwa gida zaman jiran dawowar ussein ."bini bini sai mu leka waje ko zamu hangosa amman shiru har kusan karfe shadaya na dare har mun fidda rai dashi sai gashi an shigo mana dashi bangaren hjy yana dingisa kafa da kyar ."
da sauri muka taresa dan gbdy muna tare har hassana wacce tafi kowa shan kuka hjy kam cikin yanayi na tashin hankali ta isa garesa tana kuka "yanzu haka suka maka ussein ,kawai dan kana soyayya da diyarsu allah ya saka maka ,allah ya bi maka hakinka alfarma annabi muhammadu sai bilkisu ta zama mallakinka "wai meye hk hjy ana kokarin ya rabu da yarinyar mutane ya huta da wahala amman kina sake dagula masa lisaafi .
Gali ya fad'a yana kallon ussein " kai ka rabu musu da yarinya idan ba haka ba wallahi komai ya sake faruwa babu ruwanmu ,babu hannu babu kafarmu sai dai ka karata kai kadai dan bazamu iya wahala ba wadan nan mutanen marasa mutunci ne "wannan gsky ne gali babu ruwanmu dan bazamu iya dasu ba inji cewar saadatu ,to ku yanzu laifinsa kuke gani bakwa ganin na yarinyar ?ai yarinyar tafi shi laifi domin ita Ke zuwa inda yake wallahi na tsani yarinyar nan ."
"koni wallahi na tsaneta maryama wannan shima mafarin tsanar yanuwan mahaifinki ga mahaifiyarki alokacin ina kallon ussein wani irin numfashi mai zafi ya fesar kana ya samu waje ya zauna da kyar ya daura kanshi akan hannun kujera ya kwantar tare da lumshe idanun shi yana jin duk abinda kowa yake fad'a daya byn daya bayan wasu mintuna ya kuma budewa yana kallon kowa cikin sanyayyar murya yace "in sha allahu na rabu daita har abada dan kwana ne kawai a gaba da na mutu "ka kwantar da hankalinka muddin ina raye baka da mata sai bilkisu ka daina cewa ka rabu daita dan na nasan kana sonta har yanzu ."
"haba hjy wai me yasa kike fadar haka Kmr baki tausaya masa ? "yanzu ku yarinyar nan bata baku tausayi ?ita ma ba laifinta bane soyayya ce da qaddara ke tangaliliya da rayuwarta dacen iyaye ne batayi ba shiyasa take shan wahala amman itama abar a tausaya mata ce "gsky mu dai bamu yarda ba kuma ta ina zasu bada aurenta byn kina kallon haukan da suke akanta ? kusa ido kuga ikon allah muna zaune zasu nemo mu da maganarta da izinin allah "babu wanda yace uffan kowa ya mike ya kama gabansa ."
****
Bayan wata biyu da faruwar komai mahaifiyarta ta shiga neman taimako akan bilkisu dan kawai ta rabu da ussein , yau akarbo taimako daga wannan malamin gobe akarbo daga wancan malami , akwai inda aka kaita sai data d'auki alqurni ta rantse akan zata rabu da ussein , hankalinta ya tashi matuka taki amsa ta firgita kwarai da lamarin mahaifiyarta ."
fito da duka idanunta tayi tana furta tashi uku bataso ba amman mahaifiyarta na kallo mutumin yasa ta dauki alqurni tayi rantsuwa ta rabu da ussein har abada alhalin ita a zuciyarta ba haka bane "
babu laifi bilkisu ta zauna lafiya kamar sauran lokutan baya ta cigaba da rayuwarta gudun kar qurani ya cita ,yanuwanta suka dan sake mata kadan haka mahaifiyarta tun tana gudun abinda zai je ya dawo har ta hakura ta sake janyota jikinta kullum da irin nasihar da take mata "bilkisu ki zama mutuniyar kirki ba wai baa sonki bane yasa kika ga anayi miki duk abinda aka miki ana sonki ne yasa ake gudar miki wahala ,auren wannan yaron wahala zai zame miki arayuwarki , bakya ganin sauran yanuwanki ?kowa na cikin jin dadi me yasa sai ke kadai ce zaki zabar wa kanki wahala? "
tace "kiyi hakuri mumy ina tsananin son ussein amman zanyi iya kokarin na cire sonshi araina "ko kunyi imole ne ?hjy rahma ta tmbyeta ."tayi shiru tana kallonta" baku ta'ba shan jinin juna ba ?ta girgiza mata kai alamun a'a to ko ya ta'ba kwanciya dake ne ina nufin sex ?shiru tayi kawai ta kasa bata amsa tmbyrta "idan ya ta'ba kwanciya dake ne ki fad'a min nan ma shiru tayi kawai "karki manta Kiyi rantsuwa da alqurni akan zaki rabu dashi ta gyada mata kai "idan baki son mubarak naji na hakura amman ki kawo min wani banda wannan yaron dan banason shi daga nan ta zarce da nasiha na kwantar da hankali tana nuna mata rabuwa da ussein shine alkhairi arayuwarta wanda alokacin mgnrta na shiga ta kunne na hagunta ne yana bin ta dama ."
wannan sakewar yasa ta samu damar turawa ussein sako da duk wayar data shigo hannunta byn ta tura text sai ta goge haka haka dai har ta shirya barin gidan da yammacin ranar laraba ta fice daga gidan babu wanda ya sani sai lalubo wa sukayi bata gidan" abun bakinciki tana zuwa gidan nan da hassana ta soma cin karo lokacin ta dawo gida aurenta ya mutu "Ke tsaya ta daka mata tsawa me ya kawoki gidan matsiyata ?tace dan Allah Kiyi hakuri nazo neman ussein ne "ussein din kanin ubanki ne da kikazo nemansa ? yanzu har kin manta irin azabar daaka gana masa akanki ?"
"na sani amman Kiyi hakuri ta marairaice mata ta raba ta gefenta zata shigo tace "kina hauka ne ta kara buga mata tsawa wallahi kika shiga gidan nan da kaina zan fito dake na miki dukan mutuwa kuma bazan bari kiga ussein din ba har sai na danganaki da matsiyatan iyayenki masu kiran wasu matsiyata alhalin sune matsiyata , dan masu arziki basa yin abinda sukayi duk yadda akayi arzikin ma daga sama aka samu zaazo a ishe mutune "pata pata tayi mata batare da sanin hjy ba sannan ta korarta ."
bangaren hjy rahma taji shiru shiru bilkisu bata fito ba ta nufi dakinta sai dai wayam tagani babu kowa ta duba bayi nan ma still the same nan da nan duk ta rude sai zufa take fitarwa nan fa ta soma kiran yaranta tana tsaye sai ga aisha da mijinta haka ma sajida cikin tashin hankali aka kira abubakar da mahamud har sulaiman har khadija jugun jugun sukai kafin daga bisani suka fito zuwa nemanta har 12 :00 na dare ba labarinta babansu yace kowa ya tafi kawai makwancinsa har zuwa gobe aga abinda allah zai yi ."
daga gidan nan bilkisu ta rasa inda zata domin dai tasan idan ta koma gida azaba zata sha duk yadda zata fad'a cewar bata hadu da ussein ba bazasu yarda ba dan haka ta wuce gidan kawarta farida daman su basa tare da mahaifiyarsu , mahaifinsu ne kuma bai cika zaman gida ba kasancewarsa jamin tsaro in takaice miki kwana da kwanaki ana neman bilkisu baa ganta ba yayinda ussein yake gida abunsa idan kinga ya fita to zashi area ne kuma bini bini ya dawo gida ".
muna zaune aka zo nemanta basu ganta ba suka wuce intakaice miki kullum sai sun shigo unguwr nan sai dai basa ganinta sai dai su ganshi shi kadai duk inda suka je nemanta bataje ba duk ahalinta sun rude mazan kuwa sun bazu nemanta abu kamar wasa har sati baa ganta ba abubakar ya kai report police station duk hankalinsu ya tashi haka zalika ussein shima bai zauna ba duk inda yasan zataje yaje bai ganta ba kullum wayarsa tana hannunsa km a kunne koda zata nemesa duk ya rude ya rasa inda zai sa kansa ."
kowa a gidansu bilkisu kuka yake daga bangaren
yan dakinsu har sauran bangarorin dan kansu a hade yake kuma suna qaunar juna ,duk sun rikice sun baza cigiyarta koina kafofin sadarwa amman babu wanda yace ya ganta dan haka suka sa akayi arresting din ussein a tunaninsu ya boyeta sati daya yana tsare ana gana masa azaba har a underground aka saka shi , ranar daya cika sati biyu akabari muka gansa ,koda aka zube magana sune basu da gsky amman kudi yasa aka bamu rashin gsky muka dauka muna bada hakuri akazo dashi unguwar nan sarka hannu da kafa Kmr wani barawo aka bincika gidanmu daki daki lungu lungu baa ganta ba haka dakunan abokansa da dakinsa duk inda aka san yana zuwa sai da akaje dashi amman baa ganta ba aka sake dawo dashi station dokoki aka kafa mana .
daya daga cikin police tace tasan koina bilkisu take zata nemeshi dan haka da zarar ta kirasa ya tabbatar sun hadu ya kawota a haka aka bar maganar muka dawo gida wanda tsanar bilkisu ya sake girma a zukanta yan'uwansa hatta gali alokacin ya fadi maganganu marasa dadi akanta wanda shine har yau baya qaunrku da mahaifiyarku amman ita hjy tana sonta dan tayi kuka rashin ganinta da baayi ba ."
Kullum hjy tana cikin zullumi da addauar allah ya bayyana bilkisu wallahi hjy tana matukar qaunar bilkisu sam bata ganin laifinta komai zaa fad'a akanta bata gani , cikin ikon allah sai gashi ta nemi useein da number farida ya tmbyrta inda take ta fad'a masa bai bata lokaci ba ya nufi inda take yana isa sai da yayi mata mari masu kyau har biyu cikin tashin hankali yaja hannunta daga can gidan nan ya zarceto daita muna zaune sai gashi ya shigo daita ."
hjy duk tafi kowa jin dadi ta rungumeta ajikinta tana kuka mikewa tayi tace muje police station
Muna fitowa ta nemi limamin masalacin unguwar nan tai masa bayanin komai shima kuma ya fahimci akwai matsala duba da yawon zuwan da yanuwanta suke muna isa aka kira yan'uwanta ai a haukace suka shigo sabeer yayi kan ussein "kace bakasan inda take ba ? sukayar da kansa yayi dan rasa me zaice ."
liman da police suka tsaidasu suna kwantar masu da hankali amman suka kasa aiwatar da hakan suka rufeshi da duka hjy ta shiga tsakaninsu tana karesa tana kiran sai dai ku hada dani allah ya isa bata yafe ba ,ita kuwa bilkisu kuka take sosai tana fad'a masu bashi da laifi hasalima tunda ta bar gida bata hadu dashi ba sai yau cikin