Showing 117001 words to 120000 words out of 185716 words

Chapter 40 - MAR'ADAM'S book Complete BY AYSHA A BAGUDO.txt

23 Nov 2024

4721

fara fitowa daga bakinta "ina qaunar ka yaya ? bai yi mamakin jin fitowar hakan daga bakinta ba domin ya rigada ya gama karantata tsab "na sani sai akayi yaya ?ya fad'a yana kallonta yana jin kamar ya soma yar yarfa mata maruka ta dawo haiyacinta "dan Allah yaya karka ce min a'a ! a kowani hali zan kasance tare da kai " ta maimaita hkn a fili yafi sau goma tana mai kai hannu ta shafa kasumbar dake kwance a fuskarsa ji yayi kamar ta shafa masa garwashin wuta ,shi fa duk duniya babu macen da yake jin zata ta'ba shi yaji wani abu ajikinsa sai princess ita ma din yanzu ya soma gogeta a zuciyarsa da rayuwarsa ."cikin fita haiyacinta
ta riko fuskarsa sosai ta sanya kwayar idanunta dake tsiyaya ruwan hawaye acikin nasa " ban san hka soyayyarka tayi tasiri acikin zuciyata ba sai dana qasa amsar soyayyar kowa ."




"Ban san tasirin soyayyarka ta kai mizanin da zan iya rasa rayuwata ba sai da naji zaka min nisa , yaya kaine duniyata ruhina yana tare da kai ako da yaushe , nayi yunkurin bayyana maka soyayyata a tun lokacin da mubina Ke mutuwar sonka amman na gaza aikata hakan ina ganin cewar zan iya cire soyayyarka na cigaba da rayuwata amman still na qasa domin kuwa every each second nake jin sonka na qaruwa a cikin zuciyata , ina ta qoqarin sheida maka halin da zuciyata take ciki kwatsam kuma sai ga batun aurenka da marsi bance ka bar marsi ba amman dan allah ka had'amu ka auremu " rokonki bai kar'bu ba bare wata alfarmar ya kamata ku koyi yadda ake iya control din zuciya "ka taimakeni ban san ya zanyi ba " kar allah yasa ki sani ya fad'a yana jan tsaki ."




kuka take sosai tana kallonsa tmkr ranar ta fara ganinsa shi kuwa haushi ne ya turnikesa a wajen zuciyarsa banda tuttukin bakinciki babu abinda yake , a ganinsa ma ta balain rainashi
shi zata kalla tace tana so alhalin ga hisham dake mutuwar sonta? "kayi hakuri dan girman Allah nasan zakayi tunanin komai akaina wallahi haka ne , dan na rigada na haukace akanka bazan iya jurar abinda nake ji akanka ba sannan bazan iya amsar soyayyar yaya hisham ba ,dan kona auresa gangar jikina ya aura zuciyata da komai nawa yana gareka da kawai zan iya rayuwa ..."




Ta riko hannunsa hawaye na zuba daga idanunta ta soma tafiya dashi taku d'aya biyu yayi ya tsaya cak , itama ta tsaya suna fuskantar hisham naunaye ajiyar zuciya ta sauke tana goge hawayen dake tsiyaya ,ahankali ata ya zare hannunsa dake cikin nata ya yarfar sannna ya zura cikin aljihun wondonsa yana jan tsaki "ya hisham! ta kira sunansa a kid'eme "banyi niyyar fito da sirrin dake zuciyata ba amamn ya zama dole na fad'a maka tunda na fad'awa yaya adam babu komai acikin zuciyata sai..." karki kuskura kiyi wannan ganganci dan kome zaki yi tawa zuciyar bazata amince ba "to kuwa gara ka ksheni da hannunka na huta dan nima bazan iya auren yaya hisham ba , yana sona ni kuma kai nake so.."you're very stupid Kiyi maza ki danna madannin gogewa ki gogeni arayuwarki da zuciyarki dan ni mallakin mafarkina ce " yana gama fad'ar haka ya juya ya haye sama yana taka step yana magana " hisham ka manta da shirmen wannan yarinyar ka soma naka shirin domin wannan auren ko zata mutu sai anyisa useless girl kawai ga inda ake sonku aka damu daku amman ku dinga kai kanku inda bazaa ta'ba sonku ba nonsense "




Hisham ya runtse idanuwanshi "kenan hasashensa ya tabbata , zarginsa ya zama gasky kenan akan ata yake shan wulakanci da tsana da wahala a wajenta ? ,"ya kalleta cike da tausayawa yace "daman ata Kike so ?jikinta yayi mugu mugun sanyi ta rasa me zata cewa hisham illa ta runtse idanunta gam tana jin zafi da ciwo mara iyaka a zuciyarta ,ta durkushe qasa tana kuka tana nemawar kanta mafuta dan dole tasan abun yi kafin a had'ata aure da hisham shima ya durkushe gabanta ya dago ha'barta ya sanya kwayar idanunshi cikin nata , tai saurin buge masa hannu tana kallonsa cike da tsantsar tsana "ka kyaleni ni wallahi bana sonka tunda burinka kenan na soka , dan girman allah ka rabu dani ka manta dani, ka manta da maganar ka ta'ba sona arayuwarka , ka mantani ta qarasa fad'ar haka tana fidda huci mai zafi ."


"Dan allah kiyi hakuri nasan irin ciwo da zafin da Kike ji acikin zuciyarki ciwo ne kwatankwacin wanda nake ji acikin zuciyata nasan zafin ciwo da radadin kana son wani baya sonka ,wallahi na tausaya miki amman me yasa nuzla ?"me yasa sai ata zuciyarki zata kamu da so byn ni ina qaunarki ya kai hannunsa yana share mata hawaye"ata bashi da wannan lokacin wahalar da kanki da zuciyarki kawai zakiyi babu wannan tausayin a zuciyarsa a karshe ya rungumeta ajikinsa tsam yana shafa bayanta ahankali ahankali babu yadda ta iya dole ta kasance rungume ajikinsa domin tana bukatar wanda zai rarrasheta kuka take sosai tana rungume ajikinsa "ki daina kuka nuzla dan zuciyata bazata iya ganin hawayenki da damuwarki ina matukar sonki da zaki bani dama da sannu zaki daina son ata ki soni ya fad'a yana qara rungumeta gam ajikinsa ahankali ya mike tsaye tare daita ya nufi kofar fita tun kafin mutane su shigo su fahimci halin da suke ciki ."




Washegarin da misalin karfe tara na dare ata ya shiga d'akin mami sanye cikin fararen kayan bacci wondo da riga , hannunsa rike da black cup dinsa dake dauke da ruwan coffee ,yayinda dayan hannunsa Ke cikin aljihun wondonsa ya samu mami tsaye a gaban wordrobe dinta tana qoqarin rufewa tana ganinsa ta sakar masa murmushi tana cewa "Masha allah adamcy nan ya karfin jikin ?alhamd sweetheart ya qoqari dani ?kwana nawa ya saura ai Allah Allah nike Kayi tafiyar nan ka dawo mu sha biki ranar bani da dama zan aurar da d'a daya tilo ya girgiza kai kawai yana ajiye cup din hannunsa akan bedside dinta ya tsura mata tsumammun idanunshi yana kallonta tmkr wani maraya "yaakayi adamcy nan duk sanda kayi haka akwai abinda kake son fad'a "haka ne sweetheart kin fi kowa sanin halina alfarma nazo nema ."


"Alfarmar kuma ?mami ta maimaita abinda ya fad'a
"Eh ina neman wata alfamar a wajenki sweetheart "ina sauroronka Allah yasa zan iya ,ya marairaice murya sosai kafin ya soma mgn "dan darajan Allah sweetheart ki qara min lokacin auren nan wallahi wallahi wallahi !!! kinji na rantse miki zan auri yarinyar nan zabinki , wasu yan kwanakin kawai zaki qara min har naje na dawo dan zan dauki lokaci a france daga nan ma zan wuce hollond yi wasu abubuwa masu mahimanci a yanzu na samu sauyin lokaci amman kuma idan kina ganin zaa iya yin komai ko bana nan fine na amince a daura auren ayi komai amman da zaa bari na dawo sai nafi farinciki kasancewar ina son a hada auren dana hisham da nuzla yadda take kallonsa ya fahimci kamar bata yarda dashi ba "na rantse fa duk wanda aka rantse wa bai yarda ba shi din bana allah bane nayi miki wannan alqawarin sweetheart zan aureta ".




"naji amman har zuwa wani lokaci ni wallahi zaka sani jin kunya auren sauran kwanaki ace an daga "karki damu sweetheart idan akwai damuwa kawai ayi ko bana nan amman na fi son ina nan ,sai kace wata tsiyar zaka kulla ko kana ?ya dan ciza gefen lips dinsa "bansani ba ko zan iya kulla wani abu a auren da bana só ?kaji dashi tunani tayi karta je a daura yaki dawowa ya bar yar mutane da nauyi akanta gara kawai ta qara masa lokaci idan ya dawo sai ayi"Kwanaki nawa zan qara maka ?uhm ko Kmr wata biyu haka yayi "what ! kai adamcy ban yarda da kai ba ,wallahi ki yarda dani sweetheart bazan baki kunya ba, ba kuma zan saba alkwari ba I promise you ,ka cika alqawari adamcy ,karki damu sweetheart na ranse fa ,shikenan na yarda da kai ta fad'a kafin su fad'a hirar duniya a nan yake bata labarin nuzla murmshi mami tayi tana cewa "adamcy nah mai farinjini ."


Zaune mr ata yake agaban hajiya zulaiheart sanye cikin suit wondo da riga bakake jikinsa na fitar da wani kamshi na daga hankali fuskar nan nashi dake kwance da kasumba tayi fresh tayi kyau tana fitar da wani haske na dabam mai daukar hankali abun ka ga fari mutun sallama ya shigo mata dan sauran awa daya jirgnsa ya daga zuwa kasar france "Allah kiyayya ya tsare min kai , ka kular min da kanka sosai banda wasa da abinci aci abinci akan lokaci kamar yadda doctor ya fada "in sha allahu zan kiyaye sweetheart. Allah ya qara girma,ya qara miki lafiya da nisan kwana mai amfani kema ki kular min da kanki "Ameen summa ameen nayi maka wannan alkwarin Allah yayi muku albarka gabadaya ku "inji mami ,sannan taja musu addu'a suka shafa tana shafa masa na hannunta a fuskarshi ."a tare suka mike suka fito inda tawagarsa Ke jiransa a haraban gidan shi kadai ne zaune a bayan motarsa limozin sai driver a mazauninshi, hawaye ya tsiyayowa mami sanda motocinsa suke qoqarin barin gidan sai take jin kamar kar ya tafi amman kamar yau ne zai dawo gareta wannan karan mami ta kasa daurewa sai da tayi qwalla, gefe tayi da kanta tana dauke hawayenta ."


*****


Yau tsawon kwana uku kenan mlm yahuza yana zariyar zuwa gidansu maryama amman kamar kullum bai samu ganinta ba yau ma daga massalaci ya wuto kofar gidansu yana neman yaron da zai aika cikin gidansu ko cikakken minti goma bai yi da tsayuwa ba, sai ga yaya sadam ya fito daga cikin gidan , nan ya mika masa hannu suka gaisa "ina fatan dai lafiya kwana biyu nan kake zuwa gidan nan ?"Lafiya lau wajen maryama nake zuwa sai dai duk zuwan da nake yi bana samun ganinta ,shine dan naci kake ta zuwa ?to ya zanyi sadam tunda zuciyata ta kamu da matsanancin sonta duk da bani da tabbacin ko tana sona amman nasan tana son fitowa inda nake habib ke hanata fitowa yanzu dai taimaka min ka fito min daita dan nasan muddin habib na cikin gidan bazai barta ta fito ba ,murmushi sadam yayi yana cewa "kai habib hukuma ne wannan yaron bari ina zuwa !ya juya ya koma cikin gidan ya shiga side dinsu maryama ."


a parlour ya iskesu gabadaya suna hirar duniya ya zauna yana fuskantar maryama suka gaisa da aunty sannan maryama ta gaishesa haka ma habib ya amsa masu da "lafiya lau cikin sakin fuska ,ya gida da aiki sadam ?Alhamdulillah aunty mun godewa Allah yace yana duban maryama "ga malamin ku yahuza can a kofar gida yana jiranki yau tsawon kwana uku kenan ina ganinsa ashe wai saboda ke yake zuwa amman bakya fitowa."wata irin kunya ta kama maryama ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zara zaran yatsun hannunta".




"ai ga d'an albarka dake hanata fita nan , ko shi zai aureta bansani ba ?yaro qarami dashi sai aikin nuna isa da iko ita kuma shegen son dan'uwa tana biye masa aunty ta qarashe maganar tana zabgawa habib harara ,habib bai ce komai ba ya tashi ya shige ciki dan matsawar yana zaune a falon bazai iya barin maryama ta fita zuwa koina ba km hakan zai sa yaya sadam yaji babu dadi "ai yahuza mutumin kirki ne kuma ga dukkanin alamun da gaske yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login