Showing 24001 words to 27000 words out of 110841 words

Chapter 9 - BAKIN CIKI BOOK COMPLETE BY ESHAT.txt

12 Sep 2025

68

yarinyar na ki
gagadon barcina, to ko ke din suke kwakwaxo a
kanki,ma zaki gwada min? Ta kece da daroya
tana fadin, aidama ni ban fadi ba. Aunty ke ce
xaki raina min yaya, alhalin koda mai kwado, ya
dara gaya. Tace, naji saikije wajen kwadon ki
gaya masa da kan ki, a kyalegaya agefe. Ta
rungumo ta, ayya my Aunty ba ma'yar haka dake
surukuta ta kaina! My lovely wife! Tatabe baki
tace, haka naji masu kyau ke da Al-ameendin
naki hakane? Tace ban so surutu, sai in fasa ta
kara kankakme ta, yauwa my swthrt, ke kadai ce
harabada. Tace, ko baki fadi ba. Haka ta lallaba
ta sukasasanta, don ta san halin Aunty Rabo, da
wasa xatace ba xatayi abu ba, amma sai sai ki
sha mamaki,taki ai watarwar da gaske. Ba yaya
Abdulkareemakadai, su Abba kan su sun sha
mamaki da wannan sako da yazo kunnuwansu,
sai dai Abba baiyi jayayyaba, du da yana shakku
cikin ransa, yana jin kamar Al-ameen ba zai bar
ta yin karatun bane. To amma idanya dubi
iyayensa, sai yayi saurin kauda wannantunanin.
Yanxun bikin abdulrahman shi suka gaba,sun
kyale fafutukar makarantar mama. Shi dai dadi
bai san yadda akayi ba kawai an masa ne
makarantarce bata samu ba, sai wata shekara.
Tun sati biyun sasuka wuce aka fara gabatar da
shirye-shiryen biki tahanyar kai kayan lefe
kaduna. Tun daga lokacin sumama babu xama,
kusan kullum fita sukeyi xuwakasuwa, domin
yawancin abubuwan bukata, daga nan minnar xa
su taho da su. Satin daya shigo shine yakama
kwana shida biki, don haka a gobe su mama
damutan gidan za su wuce Fandagori. A daran
ranarraba dare sukayi suna hira da Al-ameen,
saboda xasukwana biyu basu motsin juna ba.
Washegari dasassafe yaske bugowa. Sai da
kalamansa suka sa Mama kuka, don kalamai ne
masu ratsa xuciya, suhana ta sukuni, shi ya sa
bakinta gum! Tana tunanitare da kewar Doktan
ta, ji take kmar tace su sauketa koma gida. Ta
dai ya daurewa sannu a hankali tatattaro
nutsuwarta wuri daya, ta dauki dangana. Sunisa
kuma, ganin Ummanta ya debe mata kewar
masoyinta. Bayan sun ci abinci, sunyi sallolin
su,sannan suka ci gaba da tattaunawa akan
shirye-shiryen biki. Karfe biyar dai-dai lokacin
ne rana tayisanyi. Mama ta sheko wanka tayi
shafe- shafe, bayaga hoda bata karawa fuskar ta
komai ba, ta daukowata atamafa 'yar ingila
ruwan bula ta sanya, ta daura dan kwalin ta, ta
ziro bakaken takalma, ta yafo bakingale ta
rataya jaka. Duk wannan shirin na tafiya
wajenBaraka ne, wai nan ma ba kwalliyya tayi
ba, kawaiyanayin jikinta ne baya boye kyan da
kaya ke mata.Ta sallami Umma ta kama hannun
Ameera suka fitotare A kofar gida suka ci karo
da Ameer, yanaganin gari shi ma yace zaije.
Tace yaje ya fadi a gida,don kar a neme shi.
Daga nan ya kwaso takalman sa.Ya sheka a guje
cikin 'yan dakikai ya fito suka wuce.Suna gaba
tana biye da su, suna xuba mata labari,iya ko
jinsu bata yi, don tayi nisa a tunanin Doktan ta,
kalamansa ke shiga suna fita a kunnuwanta,
"kwanakigoma banji muryarki ba sakeena? Ai
yayi yawa, kitaimake ni kar ki sa asiri na ya
tonu a makarantarnan. Xauntuwa xanyi cikin aji
in kasa gane komai".Idanuwan ta suka tara
kwalla, tayi sauri ta shanye su,tana fada aranta,
ba xan xauna ba, ana gama biki xan koma......
Sannu 'yam mata! Muryar ta fito. Samaribiyu ke
xaune bisa benci a kaofar wani katon shagodaf
da bakin titi. Daya fai sol! Ga dogon hanci
damatsakaitan idanuwa, duk da cewa a xaune
yake, kana kallon sa zaka gane dogon gaske ne.
Gashinkansa kuwa mai santsin gaske ne, har
yana nannadewa duk da cewa bai da yawa
akansa, watauyayi aski. Kwalli ram! Ya xauna a
idanuwan kamarmace. Ga kuma alamar gashin
baki baki wulik! Akwance, guda kuwa wankan
tarwada ne kuma zamansa kusa da na farkon, ya
dushe gaba daya kyan sa.Gaba dayansu, ta san
su, amma tuni suka bace a kwakwalwarta, domin
shekaru masu yawa rabon ta dasu. Sannan ko a
wancan lokacin babu wata alakantsakanin su.
Shi yasa a yanxu take masu kallonmamaki,
yayin da farin yake kara fadada murmushinsa,
sannu ko? Ya sake fadi. Wani guntun tsaki
tayi,ta wuce abinta, sukayi sa'a babu wata mota
mai xuwa, don haka ta rike hannun yaran suka
tsallakatitin. Ka gani ko? Na gaya maka karka yi
matamagana, ba zata saurare ka ba. Yayi
murmushi yace,ko bata suarare ni ba, dole ne ma
ta so ni, domin irinwadannan su ne ke nema
kuma ban taba daga ido nadubi yarinya nace ina
son ta ba, tayi min kallon banza ta xubar ba.
Yace yau ka samu, saboda haka dukabinda kake
takamar ka na dashi, yau ka hangowacce ta fi
ka, kar ka kuma ka mance, bikinta sauran'yan
watanni suka rage, mijin da xa ta auran ma
bashianan kasar, kaga kuwa yafi ka komai. Ya
ja dogontsaki, aikin banxa, to meye ruwa na
dashi? Kasan Allah yarinyar nan sai dai in ban
so ta bi ra'ayi na ba,cikin dan kankanin lokaci
zan birkita ta, ko? Wlh, kajina ranste, yace
hakan dai babu kyau, tunda na gayamaka bikinta
ya kusa, sai ka hkr. Yace, kai ba xanhkr ba,
yanxu ma na fara sonta. Yana dariya yace,sai ka
shirya yaki da manyan kasa, na lura har yanxu
ba ka hankaltu ba. Yace, bar maganar nan tun
kafinran ka ya baci, don Uban ka! Yace, nayi
shiru. Zai fimaka kyau. Ya tashi daga kantar
shagon sa ya komaciki ya xauna a kujera. Bai
kara tankawa na wajen ba,haka shi ma bai sake
cewa da shi komai ba. Yayin daita ma mama ke
tafe tana sakin tsaki kamar tsaka. Ranta bace
tayi sallama gidan su baraka. Barakar ketsakar
gida tana wanke- wanken yamma. Tayi
tsallesama ta runtuma a guje suka runguma
juna. Inna taleko daga daki da sauri tana
tambaya lfya? Sai tagansu rungume da juna, tayi
dan tsaki tace, Ammadai Allah ya shirya ku,
kunji yadda gabana ya fadi? Suka nufo gunta
suna dariya, wayyo Inna, kinsankwana biyu ba'a
hudu ba. Tace, ku rika nutsuwa,girma kuke
karawa. Mama tace, to Inna. Suka shigedaki,
suka gaisa da Inna, sannan suka dawo
indaBaraka ke wanke wanke ta baro su Ameera
wajenInna. Ta kawo wa Mama kujera ta xauna
tana wankewa. Mama na mata dauraya. Ina
mutuminki?Tayi dan murmushi tace, karki sani
kuka don Allah,yau da kyar zan iya barci baraka.
Ko? Kuna da abindariya ke da likitanki nan, tace,
baiki tausayinmukenan? Tace shagwabar kawai
ke damunku, shi yamarairaice, ke kin
marairaice,, to wa zai rarrashi wani? Da kan mu
muke rarrashin junanmu. To yaza'ayi, ke kuwa
soyayya. Tace, baku da laifi, in gayamiki nima
na kamu. Ta mika mata hannu, ban mukashe,
don Allah, a ina yake? Suka tafa suna dariya
kafin tace, danKagara, wani dan aiki ya kawo shi
na garin, na yiniguda, in gaya miki ashe rabo na
ne. Muhammadsunan sa, yana aiki a sakateriyar
nan ta kagara. Tajuya idanuwa tace, ba shakka
ta muhammad. Allah yatabbatar da lkhairi. Tace,
amin. Suka kara tafawa, ai zaki ganshi, dan
kyakkyawa shi ga addini. Tace, baikai Aminu na
ba dai. Ta tabe baki tace, naki kikasani, ni kuma
nawa na sani. Kowa da gwaninsa.Tace,
gaskiyarki, kuturu ma sarki ne a gidan sa.
Shikika raina ma wayau? Tace, ba haka bane
wlh, aimisali ne kawai. Tace, na gane kowa jin
kamsa yakeyi a inda yake takama? Mama ta
gyara zamatace, har kin tuna min, wai yahse
wannan me masunansa? Wannan da aka jefe
babansa wajenkwartanci? Tace oh! Kina nufin
Dan liti? Yauwa shimyaushe ya dawo gain? Tace,
ai ya jima zai kai satibiyu. Ta tabe baki, na gaua
bude wani shago ne? Kai mutane ba su da
tunani, menen na barin Dan liti yaxauna garin
nan har da ba shi hayar katon shago?Tace,
manyan gari ma basu kore shi, wai zai koreshi?
Wai kin san ma wani abu? Yanxun nana xan
wuce,wai sannu 'yan mata yace dani. Tace, haka
yake,anyi gadon banza ido a mata. Shi jinsa
yake mai kyau, marasa tunani na binsa yana
lalata su. Kingashekarunsa shida rabonsa da
garin nan, amma yanadawowa 'yan mata na
masa layi, yana tijara su. Takaici ya ishi mama
tace, kwadayi, ba an ga ya dawo daabin duniya
ba? Ai mata mun shiga ciki, kwadayi kekai mu
ya baro mu. Allah ya shiryemu, tace ameen dai.
To wai shi da yayi miki magana menene nufinsa?
Ido waje tace oho! Shi ya sani, ke da baki wajen,
idankin tanka, nima na tanka masa. Allah ya isa
ma nayimasa, daya katse min tunanin dokta na.
Suka tafa,Baraka ta mike ta dauki kwandon
kayan ta shige dashi kicin. Mama ta dauki
tsintsiya ta sa ruwa ta kora wurin, ta share tas!
Suka koma dakin Baraka. Hirar takoma can tare
da tsara shagalin biki. Gab da akekiran magriba.
Mama ta baro gidan Baraka tayo matarakiya,
suna rike da hannauen yaran har bakin titi.Anan
Baraka ta tsaya tace, to sai na zo goben ko?
Tace, ina jira, don Allah ki zo da wuri. ISA, lah!
Kinga mutumin naki da zai rufe shago, ya hango
ki ya fasa.Kar ki bi ta wajen sake hanya. Kinsan
Allah bai isaba, bazan dauki nisa saboda shi ba,
idan ya matsamin sai ya sha mamaki, don xan yi
masa wnkinbabban bargo, kafin nan bar garin
nan. Ina son kimatar likita, amma ki tsaya bata
lokacinki wajen danliti asara ce, ki wuce kawai,
shi ya fi. Allah kokawata? Don dai ba ke yake
wa magana ba, shi yasahaushin bai damunki.
Tayi 'yar dariya, haka ne, ammaina rokon ki,
karki kula shi, ba don ni ba sabodaDokta. An
gama, kinsan wani abu? Cewa yayi idanwani yaji
murya ta kawai, ya cuce shi, abinda na tuna
kenan. Saboda haka kwalelensa, ba zaiji ba. Suyi
'yardariya. Kuje, yanxun xa'a kira sallah, sai
goben. Allahya kaimu. Ta sallamu su ameer, ta
tsaya sukatsallaha, sannan ta juya ta koma. Kai
tsaye mama tazao zata wuce. Dan liti bai
daddara ba, ya sake yimata magana, 'yan mata
an dawo? Ko kallo bai isheta ba, wannan karon,
ya daga murya ya sake fadin,Haba 'yammata ai
rika sauraran masoyi mana, don ba'a san inda
rana zata fadi ba! Kai, Dan liti yayi sa'atayi
alkwarin ba zai ji muryarta ba, amma da
yajiamsar da ba zai sake marmamrin kula ta ba.
Dawannan haushin ta iso gida. Suka yi alwala da
yaran sukayi sallah. Dare ya raba barci, yaki
zama cikinidanuwan ta saboda zafi biyu suka
hade mata, gakewar muryar sanyin ranta, ga
kuma takaicin rashinba Danliti amsa, har yanxun
yana mata kaikayi axuciya. Idan ta tuna kalaman
sa na karshe, ta kanjikamar zata mutu. Wai ba
'a son inda rana zata fadi ba? Ta kan kuta, ta
shanye hwayen idanuwanta. Hakata wayi gari da
ramar rashin barci, shi ya sa take jinkasala.
Xuwan Baraka ya sa ta gyagije ta mike
sosai,suna ta aiki. Ba'a jima ba, ango ya iso.
Gida ya karagauraye wa da shewa da guda.
Bayan sallar la'asarmutanen Abuja suka iso.
Sannu a hankali gida ya cika da 'yan biki na
nesa da kusa. Tundaga lokacinake ta dora
tukunya ana saukewa.... Ranar juma'a akwai
dinner a kd. Don hakaango ya kwashi su mama
da baraka tare da su danDanlami ya wuce da su.
Mama kam sai da mucetsarki ta tabbata ga
Allah gwanin halitta, ka ranste daAllah itace
amaryar. Tana gefen Yayanta, ya na ji daita.
Samari kowa idonsa na kanta. Cikin abokansa
kuwa babu wanda bai taya ba, amma ya ce mus
ansanya mata ranar 'yar watanni suka rage
bikinta.Kash! Duk wanda yaji sai ya numfasa.
Lallai Al-ameen gaskiyya, sai ma yanxu take
kara jinjinwatunanisa. Bata gama shan mamaki
ba, bayansundawo daga diner, misalin goma na
dare, suna sashin baki a gidan ango, inda aka
xubawa amarya kayandakinta. Suna tare da
Baraka hirar dinner kawai sukeyi. Dan lami ya yi
sallam ya shigo yace wa mamayaya Ali na
kiranta. Tace lfya? Yace kalau, yana canbaya. Ya
fice abinsa. Ta dubi Baraka tace, kinji
watasabuwa kuma. Tace, wata tsohuwa dai, ai
kun jima da Yaya Ali. Abin ne ta motsa, kin san
gyambo ne, tace,Allah ya ba shi sauki. Ameen
dai. Ta figi gyale ta yafata same shi a bayan
gida yana xaune bisa dakalinsokawe da fara'arta
ta tayi sallama, ya amsa. Ganinfusakar ta sake
ya sa shi ma jin sanyi cikin ransa,tace wai kana
kirana? Yace eh ina kuma fatan xaki saurare ni,
ta kara matsowa tana fadin me hana yaAli? Meya
faru? Ya mike daga inda yake yace ga gurixauna,
tace a'a yay Ali kayi xamanka kawai, no kixauna
ai ni nace ko? Ta xauna tana murmushi sannanta
dube shi suka hada ido, ya akayi? Yace
babukomai Mama, kawai so nake muyi hira. Ta
sunkuyar da kai tare da numfasawa. Yace nasan
tuni kin mantada ni cikin ranki, amma ni na kasa
mama, waccesahwara xaki bani? Ta dago kai ta
sake dubansa,tace me xaisa na manta da kai Ya
Ali? Karfa kamanta jininmu daya, dubi
fuskokinmu kamar mu daya,don me xan manta
da mutum kamar ka? Ashe lallai xan iya
mantawa da su Ya abdulkadeer. Ya
saukenumafshi yace, haka ne, amma kin san ina
miki waniso na daban ko? Sao dai ke kinyi nisa
da soyayyarwani, har kun kusa aure. Ba wai ina
masa ynaka bayabane, so nake ki gane har
abada ni mai sonki ne, bakuma xan taba fidda
rai da ke ba, sai ranar da na ga an shafa fatihar
auranki. Xanyi farinciki, idan har zakiyarda mu yi
hira koda labarin Al-ameen zaki rika bani,wlh
xan saurareki. Ta runtse ido, tausayin Ya Ali
yaryfeta, sai dai runtse idanuwan da tayi bata
ganinhotunan kowa face na Al- ameen dinta. Tayi
sauri tabude, idanuwanta suka kada, a sanyaye
take cewa, kayi hkr Ya Alli, komai mukaddari ne
daga Allah. Kayiaddu'ar Ubangiji yayi maka
sauyi na alkhairi. Sannankuma ina so ka sani,
ban taba kin ka cikin raina ba,kuma ba xan taba
kinka ba, shi aure nufi ne na Allah.Shi ne yake
shirya abinsa yadda yaso. Ina fatan kafahimce
ni? Ya gyara tasyauwa yana kallonta, yace, na
fahimce ki mama, na gode da gudunmawarki.
Toamma bana so kana damuwa. Yayi dan
murmushi, nadaina kanwata. To kai sai yaushe
zaka yi auran? Sairanar da na daina ganin Mama
a matsayin budurwa.Ta kalle shi tana 'yar dariya,
ka tsufa Ya Ali, ka fagirmi ya Abdulrahma. Kana
so a fara maka kiran gwauro ko? Hakan bai
dameni ba. Ni ya dameni, aceyayana gwauro.
Yayi dariya, nace ki bari na tabbatarna rasa
wacce nake so, sai in rufe ido in kwaso kowace
ce inyi maneji. A'a yayana, tsakani da Allahzaka
aureta, ai sunnan ba'ayin ta da maneji. Iba
dace,ibada kuwa akwai hakkoki cikinta.
Gaskiyane, amma kin san shan kojo kwanciyar
rai. Kuma kowane soyana da mizaninsa a xuciya,
ni na san babu macenda xan so tamkar yadda na
ke sonki. Ya Ali kenan,ka bar maganr nan don
Allah, na yi karya ne? Banfada ba. Bari na shiga
ciki, kin gaji da surutu na ko?Ta kada kai, a'a
wlh kawai barci na ji ya soma kama ni. Kindai
gajin kena. Eh, toh da xak duba agogonkakila ka
ganr dare yayo. Ya duba agogon ya dubeta,sha
daya da rabi ne kawai. Tayi sauri ta mike, wuu!
Aikuwa na kawai bane, dare yayi yaya. Kai
kankaidanka ganni da wni a wannan lokacin,
dole ka koranigida. Uhm hakane, amma banda
Al-ameen, don ban isa na rabaki da shi ba, do
ne? A matsayinka nayayana, idan bayi dai-dai
ba, dole ka hukunta ni kotare da wa nake. Yayi
dan murmushi, to na gode. Saiwani lokacin
kenan? Uhm..... Sai da safe. Allah yakamu lfya,
Ameen. Ya wuce ba tare da sake waigowaba. Shi
kuwa kallonta yake tayi har kule ya sauke
numfashi, ya koma inda ta tashi ya xauna, shiru
jimsannan ya kada kai cike da damuwa.
Damuwar mamaba a kan tausayin Ya Ali kawai
ta tsaya ba. Ji takekamar tayi abinda ba dai-dai
ba ga Al-ameen. Shi yasa xuciyarta ta rasa
sukuni ta rika korafo wajenBaraka. Allah ya sani
ba tadi tayi da Ya Ali ba, illa ta saurare shi ne
kawai don ta kwantar masa da hankali.Yaushe
rabon da yayi mata magana irin wannan?Tabbas
ta gane yana cikin matsala, dalilinsa da ya
sakenan ta tsaya ta saurari kalaman bakinsa,
wadandatake ganin amayo su xasusa ya sami
sukuni aransa.To ita gashi ta shiga matsalar,
gani take tamkar taci amanar doktanta. Ta
runtse ido hotunan sa sukabayyana gareta, yana
ta cuba murmushi muryarsa nafadin.. Shema
Alqali "Manufar kenan guda daya, zallar
kishinki.Bana so wani ya san cewa baki da aure,
ya lallaboyace xai miki magana, ai ko muryarki
yaji, ya cucuniwlh." A bayyane take magana
batare da sani ba, kayihkr dokta, Allah bada
wata manufa nayi ba. Barakadake kallonta, ta sa
hannu ta bubbuga ta. Ta mike firgigi dafe da
kirji, Innalillahi wa inna ilahir raji'un!Baraka
tace, wlh xaki xautu! Sambatu kikeyi, idanbaki
sani ba, ki sani yanxu. Ta numfasa tace,
barakaDokta na baya so kowa ya ji muryata. Har
'ya uwanki?To kunyi karya, dole aji muryarki,
musammamn su YaAli, domin dan uwanki ne,
kuma tare ya ganku. Shima ba irinsu yake nufi
ba, karki maida kankimahaukaciya mana. Ta
koma ta kwanta shiru,idanuwanta suka kawo
kwalla. Kada ki shiga rudun daxai dagula
lissafinki, a aikin baxa har karshenrayuwarki, ba
xaki daina magana da Yaya Ali ba, Al-ameen ba
zai hana ba, don ya san dolenkine. Dama kin
kwanta kinyi barci da ya fiye miki alkhairi. Ta
maida kai bisa filo taja mayafi abinta. Mama ta
saukenumafshi, ta gyara kwanciya bata san
lokacin dabarci ya sace ta ba. Tun safe suke
shirin tarbar 'yandaurin aure, karfe daya dai-dai
kafar gidan ango babumasaka tsinke da motoci,
bayan anyi sallah. Abokan ango tare da angon
kansa suka jagoranci tawagarxuwa gidan iyayen
amarya inda aka daura auranFadila ta ma
mallakar Abdulrahman halas malak!Daga cam
liyafar cin abincin rana akayi ta maza
zalla.Komai ya ji. Masha Allah! Babu bata lokaci
motocindaukar amarya suka koma, yayinn da
Mama da Baraka suka koma motar Abba. Anata
kirana sallarmagriba, amare suka suka
Fandagori, kebabban wurida aka gyara musu
cana aka sauke baki. Washe garisuka sha
gagarumar walimar da aka jima ba 'yikamarta ba
a Fandagori. Xuwa la'asar baki suka komakd,
aka bar amarya da lainta. Mama da baraka ke
tare da ita, suna ta tslkanarta, karfe biyar da
rabi ango yashigo, saboda haka suka fito suka
basu wuri. Daganan Baraka tayi sallama da
kowa, ta kwasokayayyakinta. Mama ta daukar
mata wasu suka kamohanya, tana yi mata rakiya
sun atafe suna hirar susuka doso shagon Danliti.
Da saurinsa ya fito ya xauna, yana jiran
karasowar su, suna xuwa kuwa yatanka, 'ya
mata ran gari! Ko kuna jin gaisuwa? Su kaba
banxa ajiyarsa, suka wuce. Sun dan jima bakin
titi,suna sallama kafin Baraka ta tsallaka, ta
kamahanyar gida. Mama ta juyo ta dawo, 'yan
mata ji manadon Allah! Dan liti baiyi xuciya ba,
ta kyale shi, ta wuce. Kawai ganinsa tayi ya sha
gabanta, haba 'yanmata, tunshekanjiya na ke
gaishe ki, me yasa bazakiamsa min ba? Bakin
ciki ya turniketa, kamar ta kurmaihu bata san
lokacin da ta amsa masa ba cikinxafinta. Tace,
wai dole ne? Ko ka ganayi kama dashirginka?
Yace Ya salam! Maida wukar 'yan mata, ba fada
bane, A zato na so bai taba zama laifi ba.Taja
dogon tsaki ta wuce shi. Ya daga murya ya
sakefadin, a daina fada da masoyi, don ba 'a san
inda ranaxata fadi ba! Taf! Yayi biyu kenan.
Kamar xata daure,amma ta kasa, cak!!!! Ta ja ta
tsaya, ta juyo ta dubeshi har ya koma maxaunin
sa, kusa da bokinsa, na rannan. Ta tako a nutse
taxo gefensa, ta tsaya sukakarewa juna kallo.
Yayi dan murmushi yace, ko ke fa?Ai idan kace
so an gama magana 'yan mata. Ta gyaratsayuea
fuska daure, " wai ba kai bane danliti? Ni ne.Dan
wajen buzu mai shayi ko? Ya
hadiyemurmushinsa, kwarai nine. Ta kara
kankance idanuwa, ta cigaba, wanda yaje
kwartanci din nan akakama shi, ya ci dan banxan
duka, wuya ta kashe shi,ko bashi bane? Wani
irin kallo yake mata, bai iyacewa komai ba, ta
kara karkacewa tace, ai kodamuke yara ba mu
da wayau sosai, tarihin bai bacemana ba na
munana ayyukansa, muna ganinsu cikin
idanuwan mu. Hijira a gudu bayan 'yan shekrau
adawo, ba shi xai goge rubutun ba. In bnda
abinDanlita, ai bindin rakumi yayi nesa da kasa,
kumagaskiyar hausawa da suke cwa kwarya bai
kwarya.Dube ni da kyau, kai kanka ka sanni ba
abokiyarhadin ka bace. Don Allah a rika nutsuwa,
ana tunanin abinda ya dace. Taja tsaki ta wuce
su, suna kallonta.Baby wanda ya motsa. Sun fi
sakwan uku bayantafiyarta. Babu wanda ya
tanka baokin yace, kaga irintako? Sai da nagaya
maka wannan yarinyar ba xatasaurare ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login